Mejo Najeeb Book 1 Compelet Autar Alheri

Author :  Autar Alheri Category :  Read Hausa Novels

Chapter   23 / 38

66K to 69K   out of 111.9K words

labarin abinda
yafaru tsakaninta da mutanen gidansu abbanta yakoreta dakumu inda taje har kawo yanzu
datake gidansu mijinta....tunda Isseta tafara bawa innar halima labarinta take kuka cikin mugun
tausayin yarinyar shakka babu Taga rayuwa dominma Allah yatemaketa da wannan baiwar
Allah (maah kenan) tashiga lamarinta da ba'asan iya inda abin zekaiwaba Allah yaƙara tsare
gaba..

Kallon Ammi tayi tace "wannan baiwar Allah fa daga ina kukazo da ita?? "Ammin Isseta ce
inna itace wadda nake zuwa gunta asibitin mahaukata wadda kike bawa abinci idan zanje nakai
mata.."ahh too Masha allah itace aibanganetaba halima tunda naji kince batada hankali amma
kuma naga wannan kamar lafiyarta qalau.. "Hakane wlh inna bawanda zega Ammi yace batada
lafiya kawaide dan bata maganane yanzuma Maah ce tace akawota wurinki Anan zata ɗan
zauna kwana biyu muga yadda jikin nata yayi...Hakane kam to babu damuwa ai Allah dai
yabata lafiya..Ameen y Allah suka amsa atare kana Isseta tace "inna akwai zam zam agidannan
kuwa?? "Eh akwai barana ɗauko Miki tafaɗa tana Miƙewa domin taɗauko mata...Suna'nan
zaune suna jiranta segata ko tadawo da gorar zam zam ahannunta tamiƙawa Isseta ɗin...bayan
ta karɓa tayi kamar yadda maah Tagaya mata na saka wannan ƙololon acikinsu..


Acikin gari

Sosai brothers ɗin Isseta suka hargitsa garin gombe wurin neman ƙanwar tasu..domin kuwa
nazeer yasanarda wani abokinshi yaron minister kuɗi dake garin Abuja wato fadeel sosai
fadeel yashiga tashin hankali inda yabaza jami'an tsaro akan neman Isseta kab garin gombe
dama wasu garuruwan dake cikin Nigeria....lokacinda su police ɗin suka Nemi picture ɗin
yarinyar don anemota dakyar akasamu wani wanda suke tare itada zubaida da halima tun suna
ƴan 10 year Kuma yanzu Isseta tazama cikakkiyar budurwa amma ba yadda za'ayi doline dashi
za'ayi anfani wurin nemanta tunda babuwani, dashi suka shiga neman Isseta babuji babu
gani..tofa Hakan yasa sosai police suka haddabi garin gombe babu shiga babu fita indai
bayazama doliba kuma kowacce mota zata wuce se anbinciketa tukunnah zata samu damar
wucewa ko governor jihar gombe dayaji labarin abinda police keyi a jihar yabincika se aka gaya
mishi ƴar shugaban ƙasar Niger ce ta ɓata Alhaji Abdussalam idiris...aiyanajin Hakan yace
aƙara lunka bincike da'akeyi duk inda wannan yarinyar tashiga abincikota yabada kwana
ukku. Tofa abu yabirkice agarin gombe abaki ɗaya duk wanda kecikin garin yasanda labarin

ɓatan ƴar shugaban kasar Niger Hakan yasa abin ya fara yawo a social media.

Gidansu Isseta

Yan kai amarya sun dawo lafiya Sedai sunzo suntararda baƙon al'amarin agarinsu dama
gidansu baki ɗaya domin suna sauka kozama basuyiba samarin gidan suka Basu labarin
abinda yafaru tundaga farkon zuwansu Hajiya Hannah harkawo yanzu...tunda mamansu yah
balah taji wannan zancen hankalinta yayi mummunan tashi tanemi nutsarwa tarasa domin kuwa
Taga zahiri tunda bataga iyya hassi ba agidan gaya kuma anbirkita garinsu sabida nemanta,
"innalillahi wa'inna ilaihiraji'un to wai duk ya'akayi Hakan tafaru ya'akayi duk zamanda sukayida
wannan yarinyar basusan cewar ba ƴar gidan bace seyanzu da rana taɓace? Wama zaatayiwa
wannan tambayar acikin mutanen gidan? Mama bintu ko mlm Musa shida batama ganiba? Tab
dijam lallai sun ɗaukowa kanshi jidalin dayafi karfinsu,,,tanacikin wannan zancen zucinne cikinta
yamirda tasuri buta takewaya....afannin yaran gidan kuwa sosai zubaida da jidda suka yi farin
cikin jin labarin Isseta ƴar wani babba ce ba ƴar gidan ba fatansu kawai ayanzu Allah ya
bayyanata..anty bilki kuwa batayi farin ciki ba kuma batayi baƙin cikiba domin ita damuwarta
ɗaya ce ƙwallafa ran datayi akan Isseta tasan ba samunta zatayiba domin kam koda anganta
ayanzu tayi matanisa....haka dai gidan yazauna wasu na farin ciki wasuko na cikin magun
tashin hankali yayinda yawon shiga ban ɗaki yaɗaurawa Mamansu yah balah aure.


South Africa

Jirginsu mejo Najeeb nasauka sekuwa ga motar hotel ɗin dasukayi bukking tazo ɗaukarsu
dama su biyar sukaje captain Jameel, captain Ameer, sekuma su jagororin tafiyar...bayan sunje
hotel ɗin kowannensu yaɗauki ɗaki ɗaya amma general parlor ɗaya ne bayan sunyi wanka sun
huta duk suka bayyana a perlor suna fira inda kowannensu yabuɗe wayarshi tare da seta wayar
da network ɗin ƙasar yadda Zasu iya magana a akowacce ƙasa batareda sunsaka layin ƙasar
ba....aiko suna buɗewa Kiran Alhaji Abdussalam idiris nashigo wayar general faruk...cikin
girmamawa yaɗaga yana gaida shugaban ƙasar nasu...Seda suka gama gaisawa kana Alhaji
Abdussalam yashiga gaya mishi abinda kefaruwa dashi na ɓatan ƴarshi...cikin mugun mamaki
general faruk yace "ranka yadaɗe dama Kanada ƴa mace bayan su sapwan?? "Eh faruk itace
ƙanwarsu dan Allah idan kundawo daga tafiyar dakukayi kanemi temakon sojojin Nigeria wurin
nemanta please, yafaɗa araunace cikin neman alfarma kamarba shugaba ba....ajiyar zuciya
general faruk yasauke kana yace "shikenan ranka yadaɗe in sha Allah zamuyi iya baƙin ƙokarin
mu Nida ƴan uwana zan sanar musu sutayani nemanta amma aturo muna picture ɗinta.. "toh
shikenan za'aturo in sha Allah ngd sosai faruk.. "bakomai ranka yadaɗe Allah dai ya bayyana
mana ita...ameen y Allah...daga Hakan sukayi sallama.

"Miyake faruwane General?? Cewar general aliyu. "Wlh yarinyar shugaban kasarmu ne ta ɓata
a Nigeria nan yabasu labarin abinda kefaruwa kamar yadda Shima alhaji Abdussalam ɗin
yafaɗa mishi yanzu.. tunda yafara maganar gaban mejo Najeeb kefaɗuwa besan daliliba amma
zancen yadakeshi sosai domin jiyayi kamar maryam ɗinshi ce taɓata�(alsarki mejo rashin sani

tafi dare duhu) general aliyu kuwa sosai yajajanta abin shida su captain Jameel daganan suka
shiga tsara yadda Zasu fuskanci abinda yakawosu..


Gombe

Gidansu Halima

Wannan ƙololon na narkewa Isseta taɗauki ruwan taɗorawa amminta abaki tare da temakon
halima suka samu tashinye kana suka shafe mata sauran akanta zuwa fuska kamar yadda
Maah ta umurceta, bayan sungama suka zuba mata ido kawai suna kallonta kusan minti 10
basuga sauyi atareda itaba har aka yi minti 40 har sun fidda rai suna tunanin maybe bayanzu
abin zeyi aiki ajikintaba kawai sukaga tafara hamma tana miƙa kamar wadda ake miƙewa duka
kasusuwan jikinta namiƙewa arazane duk suka yi kanta suna neman riƙota kawai se sukaga tayi
baya tafaɗi kwance se bacci.....dukkansu da ido kawai suka bita cikin tsoro da fargaba innar
halima kuwa se addu'a take tofa mata domin dukkansu sun tsorata, kusan minti 30 tana
akwance kamar matacciya sekawai sukaga tabuɗe idonta tare da yunƙurin mikewa zaune tana
salati da bakinta take faɗar hasbinallah wani'imalwakin wani imalmaula wani imalnaseer...ido
suka zaro atare suna ƙokarin temaka mata tamiƙe zaunen cikin mugun mamaki da tsantsar farin
cikin ganin yau ɗaya sunga maganarta ara yuwarsu...seda tazauna Dede tukunnah tashiga
binsu da kallo kamar yadda suma suke kallonta kafin tabuɗe bakinta dayayi mata nauyi dakyar
tace hubbey...!











Autar alheri ✍️


MM _ NN

Book 4

Page 69 & 70

"Kallon juna akayi tsakanin Isseta da halima kamin Isseta tayiwa wannan baiwar Allah

kyakkyawar runguma tana fashewa kuka cikin kukan take faɗar"Alhmdllh Allah alhmdllh ammina
wayyo daɗi halima ammina tasamu lafiya Allah nagodema Ammi tadawo hayyacinta alhmdllh
sekuma tasake sake saka kuka cikin mugun farin cikin datakeji aranta...ahankali Ammi taɗago
hannunta Itama tana ɗan buga bayan Isseta alamar rarrashi Itama idonta tab da ƙwallah sedai
kuma murmushi takeyi, sunjima ahakan kamin Isseta taɗago daga jikinta tana kallonta tana
sakin dariyar farin ciki....halima ma ahankali tarungume ta tareda faɗar "tabbas kuwa Isseta
Ammi tasamu lafiya doline kiyi kuka amma na farin ciki Allah mungode ma dakabawa wannan
baiwa taka lafiya, Taƙarasa zancen tana ɗagowa daga jikinta Itama tana murmushi.

Itadai Ammi da ido kawai takebinsu tana murmushin yaƙe amma takasa cewa komai, ganin
Hakan yasa innar halima cewa "sannu baiwar Allah. "Ido tazubawa innar halima ɗin kafin
tabuɗe bakinta dake mata mugun nauyi tace yawwa sannu,,,tana cewa Hakan sekuma tabi
gidan da kallo tare da maida idonta akan innar halima tace "baiwar Allah dan Allah nan inane?
A,ina nake? Ina hubbey? Ina jazlan? Ina yayana? Ina matarshi ? Mikuma nakeyi anan ɗin?
Kuɗin suwaye? Duk atare tarinƙa jerowa innar halima tambaya babu ko pustop �

"Nisawa innar halima tayi kana tace "nan garin gombe ne baiwai Allah kuma duk waƴannda
dakike tambaya mu bamusan kowa ba daga cikinsu kekawai muka sani...idon Ammi ne suka
ƙara cikowada ƙwallah tace "gombe inane kuma gombe? Tatambaya ga dukkan alamu
tunkamin wannan matsalar tasameta batasan inane gombe ba. "Garine baiwar Allah acikin
ƙasar Nigeria yake keba ƴar Nigeria bace halan? Ƙwallar data cika idontace tazubo mata kamin
tace niba ƴar Nigeria bace minene zekawoni Nigeria kuma? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un dan
Allah kukaigi gun ahalina Ina matuƙar kewarsu, Taƙarasa zancen cikin kuka.

Isseta da halima ma kukan sukeyi suna kallonta...yayinda innar halima ke share ƙwalla afakaice
kar yaran nata suga rauninta tace "wlh baiwar Allah bamusan komaiba gamedake domin
wannan yarinyar dakike gani itace sanadiyar haɗuwarmu dake kamar yadda suka bani labari
tace wata rana tafito zataje isilamiyya ne taganki kwance bakida lafiya agefen wani shago babu
kowa awurin, tayi ƙokarin temakawa takaiki gidanki domin atunaninta ke ƴar uguwarce sekuma
Taga batasankiba data tambeki ananne tagano akwai alamun hauka ataredake dubada kalar
shigar jikinki dakuma yanayinki to daganan setakaiki wani kangon gidan biredi ta'ajiye ki taje
tasiyo ruwa tawanke Miki baki tukunnah tabaki maganin ciwon ciki sekikaƙi sha abin yabata
mamaki sosai sedai ganin yadda kiketa dafe cikine yasa tayi tunanin ko yunwace kikeji Hakan
yasa tanufi gidansu taɗauko Miki abinci abinmamaki kuwa sekika karɓe abuncin dasauri kika
hauci wannan abin yatsawa wannan yarinyar arai sosai daga wannan lokaci tafara dawainiyar
kulawa dake tamkar mahaifiyata tamaida Miki gidan biredi tamkar gidanki kullun tana kan
hanyar gyaranki keda muhallin datayi Miki kayan abinci kayan anfani omo sabulu komai ajiye
Miki takeyi kamar yadda ake ajiyewa kowacce mace dudda cewar bakyayin anfani dakomai
Sedai idan itace tazo tayi Miki kuma tundaga lokacin kike zaune agidan biredin Bakije ko inaba
kina zaune aƙarƙashin kulawar ta har inda akazo lokacinda tamaidaki asibitin mahaukata dake
garinnan domin sama Miki lafiya abisa temakon wata baiwar Allah wadda Bama jinsinmu ɗaya
da itaba, bayan Maryama tayi aurene ƴar uwarta taci gabada kula dake acan asibin har izuwa
yau da ita wannan baiwar Allah tace suɗaukoki sukawoki wurina kuma tabasu maganin

dasukayi Miki anfani dashi cikin iyawar Allah da buwayarsa gashi kinsamu lafiya.....tunda innar
halima tafara magana Ammi takafeta da ido ko kiftawa batayi babu abinda kemata yawo akai se
kallimar hauka, tambayar datake yiwa kanta ɗaya ce wai itace mahaukaciya? Itace tayi hauka?
To garin yaya? Ina ahalinta suke? Miyakawota Nigeria? Gabaki ɗaya ƙwaƙwalwarta
tatoshe..wani irin kukane yazo mata me cinrai sosai takeyinshi tana girmama ubangijinta dayayi
mata wannan jarabawar domin haqiqa shine kawai ze iya jarabtar bayinsa aduk ta hanyarda
yaso babu mahani.....Isseta ma kukan takeyi hakama halima...sosai Ammi tayi kuka tajima
tanayi kamin tatsagaita tashiga rarrashin su Isseta Hakan tasakasu ajikinta tana shafa bayansu,
cikin muryar kuka tace "ngd ngd sosai yarnan sekuma kuka yaƙara cin ƙarfinta...cikin sauri
Isseta tarufe mata baki tare da faɗar"dan Allah kiyi shiru Ammi dan Allah karkice komai ni wlh
duk abinda nayi Miki nayine sabida Allah kuma wlh tamkar mahaifiyata Hakan nakejinki araina
bantaɓa yimiki wani kallo wanda bana uwa ba dan Allah idan har kin ɗauke ni ƴarki karki ƙara
yimana dogiya albarkarki kawai muke buƙata Ammi...ɗan murmushi Ammi tayi kana tace "Allah
yayi muku albarka Allah yabiyaku da gidan aljannah Allah yabaku wanda Zasu bauta muku fiye
da yadda kukayimani Allah yafaranta kuma kamar yadda kuka faranta mini banida bakinda
zanfadi farin cikina agareku sedai zan dawwama inamuku addu'ar fatan alkhairi
arayuwarku....wani irin daɗi ne yalulluɓe ƴaƴantan cikin farin ciki suka ƙara rungumeta suna
amsawa da amin ya Allah...innar halima ma amsawa tayi tana murmushi.

Kamin Ammi takalleta Itama tana murmushi tayi mata godiya Sosai kamin tace "Inason komawa
ƙasarmu bawai Allah domin nasan awanne hali ahalina suke ciki sabida idan nafahimta Dede
awannan labari dakika bani dakuma yanayin jikina dana kallah ya tabbatar min dacewar nayi
shekaru cikin wannan lalurar..
"Muryar umaima suka tsinkayo tana faɗar "Hakane kam tabbas kinyi shekaru baki tare da
ahalinki kuma suma suna buƙatarki kamar yadda kike buƙatarsu to Amma kisani lokacin
haɗuwa dasu beyiba kiɗan ƙara haƙuri kaɗan dakansu Zasu bayyana agareki in sha Allah,
takasa maganar tana shigowa cikin gidan....dukkansu da kallo suka bita, innar halima tace
"wacece ke? "Umaima ce innarmu aminiyar maah ɗita, Isseta tafaɗa tana murmushi. "Ayya
Allasarki yi haƙuri bawai Allah nayi mamaki ne jin kawai kinsaka baki acikin zancenda mukeyi
kuma naga bansankiba..."Karki damu bakomai bane yanzudai zan ɗauki maryama namaidata
gidan mijinta domin lokacinda nayiwa mijinta alkawarin medata yayi..."wacece maryama? Ammi
ta tambaya. "Yartaki ce maryama gatanan, innar halima tanuna mata Isseta...wani ƙayataccen
murmushi tasaki kamin tace Masha Allah, sekuma ta kalli umaima tace naso nazauna da ƴata
Kodan naji ɗiminta ataredani amma Zaki ɗauketa to idan kika ɗauketa se yoshe Zaki maidamin
ita??? Tatambaya tana murmushin...Itama umaima murmushi tayi kana tace bazan iya ɗauke
maryama daga garekiba har abada domin jini baya ƙarya maryama babu wanda isa yaraba jini
ɗaya se Allah sabida Hakan Karki damu duk lokacinda gimbiya laweesat tace nakawo Miki ƴarki
ashirye nake dana kawota gareki.....ido Ammi taɗan waro kaɗan sekuma tace "baiwar Allah
a'ina kikasan sunana maryama?? Tatambaya da mamaki. Dariya umaima tayi kana tace Karki
wani damu dasanin wannan maryama domin kuwa Allah nabamu iKon sanin abinda baku
saniba wanda ya yardar muna da musani sabida Hakan sanin sunanki bawani abin bane
agareni balle ma gakida Sunan ƴar lelen gimbiya laweesat... murmushi sukayi dukkansu kafin

waninsu yaƙara magana sukaga babu umaima babu dalilinta koda suka waiwaya kuma babu
Isseta...murmushi kawai Innar halima tayi kana tace barana haɗa Miki ruwa kiyi wanka
maryama mesunan ƴata sekizo muci abinci..daga Hakan tamiƙe batareda tajira cewar Ammi
ba..inda tabarsu itada halima tana ƙara bata labarin Isseta dakuma yadda take shan wahala
wurin kulada ita...wannan labari da halima kebawa Ammi kuwa baƙaramin ƙara sanya soyayyar
Isseta yakeyi azuciyar Ammi ba.

Lagos

Umaima bata ajiye Isseta ko inaba se bedroom ɗin Mejo Najeeb inda ta ɗauketa,tayi
tafiyarta....ɗakin tabi da kallo tana tuna mejin nata ayanayinda suka kasance jiya, agefe ɗaya
kuma tana tuna amminta dataji ashema sunansu ɗaya maybe hadda Hakan yasa takeson matar
sosai aranta, murmushi tasaki kamin tamiƙe tashiga bathroom tayi wanka tare da alwala tafito,
tayi sallar azzahar tukunnah taje gun mirror Tayi shafe shafenta, kana taɗauko kayanta da
umaima taɗauko mata ɗazu buɗewa tayi taɗauki wata abaya ash color me rashin baƙi atasaka
tayi rolling ɗin mayafinta, Masha Allah sosai tayita kyau matuƙa domin dama can Isseta
kyakkyawar macece ajin farko....kayan taɗauka tashiga jerasu acikin widrop ɗinshi seda
Tagama tsab tukunnah tashiga gyara ɗakin bayan Tagama tadawo perlor tanacikin gyaran
perlor ne Hajiya mama tashigo part ɗin domin Taga kotadawo...cikin girmamawa dajin kunya
tace mama inawuni. "Lpy qalau Maryam kintashi tashi Ashe? Cewar mama tayi mata kamar
batasan bata gidanba. "Eh Natashi mama, tafaɗa kanta aƙasa....."to shikenan idan kingama
kisauko muci abinci gaba ɗaya ko akawo Miki naki ananne?? "ah,ah mama zanzo yanzu in sha
Allah..to shikenan sekin fito, Hajiya mama tafaɗa tana barin pert ɗin.

Tunda Ummi takai anty hawwa pert ɗin Hajiya mama Basu haɗu da juwaira ba se yanzu
dakowa yafito cin abinci domin koda sukaje part ɗin juwaira na bedroom ɗin Ummi itako anty
hawwa a perlor suka zauna itada ummi dudda bafira sukeyiba amma suna zamansu atare suna
kallo...yanzu ma Ummi ce takira juwaira akan tazo suyi lunch domin ƙa'idar gidance idai kowa
yana'nan to a general parlor akecin abinci, sedai idan bakajin yunwa seka bari seka buƙata
amma muddin alokacin zakaci to atare za'acishi.......juwaira na fitowa idonta yasauka akan anty
hawwa dake zaune tana kallo, zuwa tayi zata wuce kawai anty hawwa tace "ke juwaira
bakiganni bane? Zaki wuce bako magana? Tukunnah ma miyazaunar dake bakibi su zubaida
ba? Tatambeta cikin isa adoli ita babbace....wani wulakaccen kallo juwaira tajefa mata kamin
tace "au zamanki nakeyi dazakice miyasa bantafiba? Ke kanki dakike taƙamar waike amarya
Anan kika sameni kuma kibari har idan kinsamu wurin zama agidan tukunnah kiyi yunƙurin
korar wani, tana gama faɗar Hakan taficewarta...baki anty hawwa tasaki tana kallon ƙanwar tata
cikin mamakin furucinta kamin tasamu damar yin magana Hajiya mama tashigo perlor cikin
mamakin ganinta zaune sakeda baki tace"hawwa'u miyasa bakifita gun lunch ba?? Kefa ba
baƙuwa bace kinzama ƴar gida tashi mana kije cikin ƴan uwanki kici abinci kinjiko..."okay kawai
anty hawwa tace kana tamiƙe tafita...da kallo kawai Hajiya mama tabita kafin tagirgiza kanta
Itama Takoma perlor.

Zaune suke dukkansu akan dining table, Hajiya Umma, Hajiya mama yah munir, yah sajad,
mansura, auta siyana, ummi, juwaira, anty hawwa. Dukkansu suna zaune Hajiya mama nayin
saving ɗinsu yah munir se tsokanar auta siyana yakeyi yana faɗar "ƴar lelen yah najeeb yatafi
yarshi ko sallama basuyiba yanayi yana mata gwalo cikin tsokana yace yanzudai mungano
yah najeeb yadenaji dake siyana se haƙuri....kuka siyana tasaka tana rigima tare da faɗawa jin
mahaifiyarta tana faɗar "umma kinji yah munir ko? wai yah najeeb bayasona. Taƙarasa zancen
tana sake sakin kuka.. faɗa Hajiya Umma tafara yiwa Munir tana faɗar yadena tsokanar mata
yarinya...Hakan yasa yace to "shikenan yi haƙuri nadena barama nakira mikishi kiganshi..yana
gama faɗar Hakan yashiga WhatsApp tareda Kiran mejo video call domin yaganshi a
online...seda takusan tsinkewa kana yaɗaga yana kwance akan makeken bed ɗin hotel room
ɗin dasuka sauka, yanasanyeda ƙaramar riga red color Kuma buɗaɗɗiya agaba duk sumar
ƙirjinshi awaje takwanta tayi lufff kamar abarda yakeyiwa shampoo buɗe blue eyes ɗinshi
yayi dasuke a lumshe sabida jin muryar autar tasu, tana faɗar "yah najeeb na..bece mata
komaiba se kallonta dayakeyi da wannan rikitattun idanuwan nashi, ga dukkan alamu ƴan
miskilancin nataredashi ayau...jin yayi shiru kuwa yasa auta siyana sakin kukan shagwaɓa tana
faɗar"yah najeeb dagaske kadena Sonako? Shi yasa kaƙiyin magana Taƙarasa zancen tana
sakin kuka ga dukkan alamu dai mejo yasangarta siyana sosai. "Ahankali yabude baki cikin cool
voice ɗinshi mekashewa ƴanmata jiki yace "ohh my god angel stop crying please kinji. Wayace
Miki nadena sanki? Yafaɗa akasalance domin gabaki ɗaya tunanin sahibarshi maryama ne cikin
ranshi koda Munir yakirashi. Tunda mejo Najeeb yafara magana wurin yayi taittt bakajin komai
awurin se sautin daddaɗar muryarshi....cikin shagwaɓa siyana tace yah munir ne.. "Humm yace
ahankali kafin yacigabada faɗar "bagaskiya bane kirabidashi kinji idan nadawo zamuje yawo
ko?

23 / 38