Mejo Najeeb Book 1 Compelet Autar Alheri

Author :  Autar Alheri Category :  Read Hausa Novels

Chapter   20 / 38

57K to 60K   out of 111.9K words

yatarasu.

"Ajiyar zuciya alhaji Abubakar yasauke kamin yace "to yanzu dai tun da duk mefaruwa tafaru
abinda zamuyi Ayanzu shine neman mafita domin kawo sauƙin abin, mafitar kuwa itace kazaɓi
ɗaya acikinsu domin bazeyu kazauna dasu su biyu ba doline ɗaya zaka saka kazauna da ɗaya
tunda ubansu ɗaya kamar yadda megarinsu yagaya muna....."gaskiya kam Hakan za'ayi zaka
saki wannan daba iyayenta ne suka kawotaba kuma dama can ahakan aka tsara zaka saki
ƙaramar kazauna da yayar, cewar dady...wani irin waro ido mejo Nejeeb yayi cikin tashin
hankalinda ya bayyana ƙarara akan fuskarshi...kamin yayi magana alhaji Abubakar yace "ah'ah
alhaji baza'ayi Hakanba ita wannan sun daɗe tare bakasan tun wani lokaci suke tareba kuma
shi najeeb ɗin bakasan ra'ayinshiba abinda za'ayi za'abashi zaɓi ne yaɗauki ɗaya acikinsu idan

kuwa wani abin na auratayya yataɓa shiga tsakaninsu da wannan ɗin tofa babu zancen
yazauna da waccan doline ita ɗin zeɗauka se ahaƙura da hawwa'u tunda dukkansu abu ɗaya
ne. "Hakane kam dady yafaɗa kafin yamaida dubanshi akan Najeeb yace "kagaya muna
gaskiya kataɓa kwanciyar aure da wannan yarinyar??? Gaban general aliyu ne yafaɗi jin
wannan tambayar menauyin gaske da akeyiwa aminin nashi domin yanada tabbacin baze
amsataba, sedai begama zancen zucinshiba yaji cool voice ɗinshi yana faɗar "yes I have sex
her time by time,,mun rigada mun zama Abu ɗaya nida ita, Hakan kawai yatsinci kanshi da
fadar Hakan....!








Autar alheri ✍️



MM _ NN

Book 3

Page 59 & 60

"Ido general aliyu yazaro jin wannan kalaman na aminin nashi wanda yanada tabbacin
bagaskiya bane, to miyasa yafiɗi Hakan? Kuma agaban duka iyayensu, kenan Hakan nanufin
yakamuda soyayyar yarinyar ne? Yayiwa kasanshi tambayar da amsarta abayyane take...shi
kuwa dady mutuwar zaune yayi babu abinda yake tunani Aranshi illa yoshe najeeb Yakoma
marar kunya Hakan ? Ashe ze iya faɗar Hakan agabanshi? Su Hajiya mama mahakan abin
yake agaresu domin gabaki ɗaya kalaman mejo sunsakasu shuck...fannin General faruk kam
ba'amagana domin kafe mejo kawai yayi da ido yana kallo ko kiftawa babu, lallai tabbas labarin
najeeb yakeji haryanzu begama saninshiba.

Gabaki ɗaya kowa awurin yayi tsit bakajin motsin komai illa na'urorin lantarki dake aiki a
perlor....Alhaji Abubakar ne kawai yasamu zarafin buɗe baki Shima cikin mamakin dabegama
sakinshiba yace "shikenan zance yaƙare kutashi kuje zamu nemeku...ai yana rufe bakinshi mejo
yamike tareda riƙo hannun maryama ze mikarda ita...da mamaki dady ke kallonshi kafin yace
"inakuma zakaje da ita?? "Gida zan maidata, yafaɗa lokacinda yagama miƙarda ita tsaye.
"Humm dady yasauke ajiyar zuciya kafin yace "ba'inda zakaje da ita anan gidan zata zauna
harse iyayenta sunbaka ita dakansu tukunnah....ido mejo yaɗan zaro kamin yabuɗe baki zeyi
magana kenan Alhaji Abubakar yace "kaga najeeb zancen alhaji Khamis gaskiya ne doline se

iyayenta sunsan tana hannunka sa'annan zamu baka ita tunda kaga yanzu ai yayarta nagidan
doline semunje can garinsu angaya musu abinda kefaruwa dakuma wadda kai kazaɓa kaga
daganan seka saki waccan tukunnah kazo da wannan ɗin amma bazeyu kucigaba dazama
atareba bayan dukkansu Aurensu nakanka...Hakane kam. Cewar dady.
Ɗan cije lips ɗinshi naƙasa yayi kana yajuya kawai yahaura pert ɗinshi, general aliyu yatashi jiki
asanyaye yabi bayanshi hakama general faruk...itakam mufeedah data dasƙare tinɗazu
haryanzu bata motsaba.

Hajiya mama ce tasauke ajiyar zuciya kana tamiƙe tare da riƙo hannun Isseta tace muje ƴata,
suka kama hanyar pert ɗinta...Hajiya Umma ma nata ɗakin tanufa dukkansu zuciyoyinsu
adagule da wannan mirɗaɗɗen al'amarin.

Sukuwa su anty hawwa amarya sunacan pert ɗin da'aka ware musu sunashan kallo sam
basusan wainarda ake toyawaba agidan...

Mejo kuwa yanashiga perlor shi yazube akan kujera tare dafe kanshi dake tsananin sara mishi
Yanajin wani irin kuna Aranshi, wai ace Kamarshi da girmanshi dawayonshi dakomai Dady
zerika tallarshi sekace wani mace? Wai miyayiwa majaifin nashi dake mishi arin wannan
abubuwanne? Kodai bashine yahaifeshiba? Yana cikin wannan tunanin yaji andafashi tabaya
koda yaɗago yaga general aliyu akanshi, mayarda idonshi yayi yalumshe....zama general aliyu
yayi adede lokacinda general faruk ma yashigo perlor.

Cikin tausayi yake kallon aminin nashi domin yasan tabbas wannan abin da Dady yayi mishi ba
daɗi kokaɗan, taya zakiyawa yaronka aure amma besaniba seda aka kawo matar gida
tukunnah? Ko maryam inda ƙaddara bata haɗasu da Maah ba kenan bazesanda auren ba se
ayau? Za'ace yasaki ɗaya yazauna da ɗaya sekace zamanin gaba'gaba suke ayanzu..ajiyar
zuciya yasauke bayan yagama zancen zucin nashi yakwantarda murya kana yace "Najeeb I'm
very sorry for that please nasan badaɗi sam amma karka saka wannan abin aranka inaso
kaɗauka kalar taka ƙaddarar kenan, sa'annan kasani cewa iyayenmu sunwuce komai agaremu
doline muyi musu biyayya akan duk wani hukunci dazasu zartar akanmu sekaga munsamu
nasara arayuwarmu dan Allah karka ɗauki wannan al'amarin dazafi please.. "wannan gaskiya
ne general aliyu yafaɗa mejo kayi haƙuri Kamaida komi ba komiba kaji friend, general faruk
yafaɗa Shima cikin tausayin abokin nasu domin kobesan komaiba arayuwar mejo wannan abin
kawai dayagani ayau yasan cewar akwai matsala.

Ajiyar zuciya mejo najeeb yasauke kamin yabuɗe blue eyes ɗinshi yana kallonsu, abin mamaki
kuma seyayi wani ɗan murmushin takaici kana yace "it's okay dama ba abinda nasaka araina
Aliyu domin gata dady yayimun na ɗaura min aure da kyakkyawar mace kuma metausayina tun
batasan wayeniba koda dady be auramin itaba dakaina zan nemeta na aura domin idan baka
mantaba Aliyu aranarda mukaje Delta state Maryam tasadaukarda tata rayuwar taceci tawa,
awannan lokaci ko namiji bakowanne ze iyayin abinda tayiba tindaga wannan lokaci nasakata
acikin matanda nakeda burin aura..shiru yayi yana taune lips ɗinshi naƙasa ga dukkan alamu

akwai abinda yake tunani. Muryar General aliyu ce takatse mishi tunin inda yake faɗar kamarya
cikin matan dakakeda burin aura har mace nawa zaka aura mejo? Yajeho mishi wannan
tambayar.....ɗan kallonshi yayi dagefen ido kafin yace "ɗaya kafin na haɗu da Maryam bayan na
haɗu da ita kuma suka koma biyu.. "iKon Allah to wacece tabiyun?
"Nima bansantaba amma inaso nasanta domin itace yarinyar data fara temakona amafalkin
daya kasance gaskiya ne ba mafalkiba idan kaduba bayyanar Maah agareni hakan nanufin
cewar Itama tabbas zata bayyana kuma zan aureta in sha Allah..."iKon Allah wannan gaskiya
ne najeeb amma kuma inaso kasani abune wanda yake aɓoye Allah ya bayyanama amafalki
kamar yadda Maah tafaɗa amma kasaka aranka balallaine dan maahh ta bayyana agareka ba
ya kasance Itama wannan yarinyar tabayyana agareka kawai kayita addu'ar zaɓin Allah kuma
zamu tayaka in sha Allah.

"In sha Allah I'll do it, kafin kuma yace "please minene shawararku? banasan zaman Maryam
agidannan koda kwana ɗaya ne kuma banason jayayya da dady akan zancen, yakasara zancen
cikin damuwa. "To miyasa bakaso tazauna mejo? Inagafa kowanne irin zamane zatayi baze
ɗauki lokaciba, sekuma yasaka dariya yace dan iska kodai abinda kagayawa su Dady ne
kakeson maidawa gaskiya domin wlh Allah nasan ƙarya kikeyi ba abinda yataɓa shiga
tsakaninku, kai kardai nayi ƙaryar nima namantada nakusa mugun gani last time maybe
aranarne kayi ɓarnar, yakarasa zancen yana sheƙewa da dariya..wata muguwar harara mejo
yabanka mishi kafin yace munafikin banza ina ruwanka..."ahh meda wuƙar yanzu miyasa
bakaso tazauna anan ɗin?.. "Humm bazaku gane bane akwai matsala agidannan wadda
bansan daga ina take faruwaba.."wacce irin matsala kuma? Cewar general aliyu.."Humm kaide
bari abunma badaɗi wlh "nan mejo yabasu labarin matar dake leƙenshi Aban ɗaki dakuma
kwartancin datayi mishi yana bacci, yaƙarasa maganar zuciyarshi na kuna cikin ɓacin rai ninafi
tunanin bamutun bace ayanzu duba da yadda take ɓacewa lokaci ɗaya.. "Humm gaskiya kam
da matsala indai Hakane mejo domin ko aljana ce haduwarsu da Maryam akwai haɗari acikinshi
sabida naga abinda nagani da idona wanda kai baka ganshiba..nan general aliyu yabasu
labarin tashin ciwon mejo agidan da Isseta take dakuma abinda yafaru na zuwan gimbiya
mardiya....wani irin zaro ido general faruk yayi cikin mugun tashin hankali da mamaki yace
"agabanka friend ? Kuma katashi daranka? Lallai Kanada ƙarfin zuciya wlh danine awurin sedai
afitodani, yakarasa zancen yana share guminda yawanke mishi fuska.

Shi kuwa mejo ko ajikinshi wani miskilin murmushi Mayayi Aranshi yace "that's good aikuwa
yanzu ma nasamu damar barinta agidan kuma wlh koda bala'i a pert na zata riƙa
kwanciya....shidai general aliyu yanacan yana dariyar general faruk yayinda mejo kezancen
zucinshi har aka kira magarib sukashiga anan bathroom ɗin dake perlor mejo sukayo alwala
kana sukafito tare da nufar masallaci..

Isseta na bedroom ɗin Hajiya mama zaune bayan ta gama sallar magarib tana tunanin wannan
abubuwan dasuke faruwa da ita daga wannan se wancan Allah sarki amminta kotana ina
ayanzu? Kotasamu lafiya? Allah dai yasa halima naziyartata kamar yadda umaima tagaya
mata...tana cikin wannan tunanine tajiyo ana magana a Perlor, cikin mamaki take sauraren

muryar juwaira domin kab ƴan gidansu bawanda bazata gane muryarshiba, batagama mamakin
miyakawo juwaira garinba taji tana faɗar "Ummi wai dagaske ne wannan zancen da'ake faɗa
agidannan? Dagaske ne yah najeeb aka aurawa mata har biyu kuma ciki hadda yayata?
Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un nashiga ukku ni juwaira taƙarasa zancen tana fashewa da kuka.
"Cikin lallashi Ummi tace "haba juwaira mikikeyi Hakan please kiyi hakuri mana dama tunfarko
dakika ɗauko soyayyar yah najeeb seda nahaneki badan komai ba sedan sanin waye yah
najeeb yayanane nafiki sanin halayyarshi ciki da waje shiba irin sanarin dake kula mata bane
sam yah najeeb mace bata gabanshi, amma baki yaddaba anan gidan ina gaya Miki mansura
nashige mishi bako cewa tayi tana sonshiba shige mishin kawai datakeyi amma sekinga yadda
yayi mata shegen dukan mutuwa kuma wlh cousin sister ɗinshi ce niba abinda zance Miki anan
illa kiyi haƙuri.. "haƙuri Ummi wlh bazan haƙura ba bashegiyar yarinyar dazan barwa yah najeeb
koda kuwa wannan yayarce tawa wlh bazan bar matashiba sabidashifa nabaro garinmu
nazonan atunanin mutanen gidanmu duka gun dangin mamarmu naje domin mamar kawai
nagayawa gaskiyar inda zanje Seyanzu kuma bayan sunzo sunganni nakoma a tutar babu??
Wlh sam bazeyuba.. "to shikenan tunda Hakan kika zaɓa nidai baruwana domin wlh bazaki
jamun dukan banzaba agun yah najeeb..sunacikin wannan surutun Isseta taji sunyi shiru..Ashe
Hajiya mama ce tashigo Perlor shiyasa sukabar zancen.......shigowa tayi ɗakin tasamu Isseta
zaune inda tabarta murmushi tayi mata kana tace "Maryam kingama sallar? Eh nagama, Isseta
tafaɗa kanta aƙasa...to shikenan zokiyi wanka sekici abinci kinji..to kawai Isseta tace tare da
Miƙewa tabi bayan Hajiya mama takaita har bathroom tahaɗa mata ruwan wanka dakanta tare
da zuba mata turarukan wanka masu gyaran jiki da daɗin ƙamshi kana tafice daga bathroom
ɗin...sosai Isseta taji daɗin yadda matar kemata Hakan yasa tayi wankanta hankali kwance
amma zuciyarta fall tunanin zantukan juwaira..bayan tafito tasamu wata abaya milk color ajiye
akan gado tare da pant da bra duka sababbi ga dukkan alamu na ummi ne Hajiya mama
taɗauko mata.

Wurin mirror tanufa tagyara jikinta kana tasaka abayar kawai tare da zura hijabin datayi sallah
domin pant da bra ɗin Ummi kam bazasu yimataba, ahakan tazauna bakin bed ɗin tana
tunanuka dayawa gefe ɗaya tunanin juwaira takeyi gefe ɗaya kuma tunanin mejo Najeeb takeyi
ko awanni hali yake domin tafahimci yanayinshi kamar ranshi amugun ɓace yake..ahakandai
Hajiya mama tasake dawowa takawo mata abinci tafita, itako Isseta data buɗe kayan abincin
sekawai ranta beyadda dataci abincinba kumadai dama batajin yunwa Hakan yasa taɗauki fruit
ɗin dake kai kawai tasha..


Gombe

Misalin ƙarfe 8:00pm
Hajiya Hannah ce zaune tana wayada megidanta Alhaji Abdussalam cikin kunar Rai take bashi
labarin duka da mama bintu tabata gameda zaman Isseta agidan babban abinda yafi tada mata
hankali anan shine aurenda akace mlm Musa yaɗaurawa maryama kuma wai basusan angonba
sabida yamaidata ƙasƙantaciya marar asali....tunda suka fara wayar alhaji Abdussalam ke
sauraren ta yana jinjina girman uban giji daya ƙadartawa ƴar cikinshi irin wannan rayuwar kuma

duk acikin kalaman Hajiya Hannah zancen wannan Auren ne yafi tsaya mishi arai, nisawa yayi
kana yace "Hannah wannan matar dakikasa aka tsare adawo da ita cikin iyalanta kuma zankira
general faruk ingaya mishi ɓatan maryama domin yanemi temakon jami'an tsaron ƙasar Nigeria
wurinnemanta, kisani duk abinda yasamu maryama karmu zargi kowa sekamu mundaukota
munkawo ƙasar da batada kowa se Allah kuma munkasa waiwayarta dudda Cewar ba'asan
ranmu Hakan takasanceba muma kuwa bedace muɗora wani laifinba. dan shiru yayi Yanajin
yadda zuciyarshi keƙuna akan wannan lamarin kafin yacigabada faɗar "abu ɗaya ne bemin daɗi
ba shine aurarda maryama Hannah domin kuwa maryama nada mijinta tunzuwanta duniya
aurene kawai ban ɗaura musuba kuma inda tabbacin kinsan Hakan sabida Hakan zanshigo
Nigeria in sha Allah domin munemi kowaye aka ɗaurawa mata aure dashi yasakarmin ƴata,
yana gama faɗar Hakan yayanke wayar yaname dafe zuciyarshi dayakejin kamar zata fashe
sabida ƙunci.....da kallo Hajiya Hannah tabi wayar hannunta kamin ta'ajiye tana tunanin
zantukan megidan nata tabbas yanada gaskiya acikin kalamanshi amma Hajiya tabawa itace
selar komai Allah yasaka mata akan wannan matar..

Gidansu Isseta

Abba kuwa tun da yafita bayan tafiyarsu Hajiya Hannah bekoma gidanshiba se cikin salamainin
dare yayi biɗir biɗir dashi kamar wanda akatuno daga kabari sabida tashin hankali gabaki ɗaya
ya hargitsa kanshi domin ya shiga firgici marar misaltuwa haƙiƙa yayi nadama yayi danasa nin
korar maryama babu adadi...koda yashigo gidan mama bintu nazaune tsakiyar gidan Ita kaɗai
tana lazimi, dagashi har ita bawanda yacewa kowa komai yashige ɗakinshi.

Lagos

Bayan sundawo daga masallacine general aliyu da general faruk sukatafi shikuwa yashigo
domin basu baro masallacin ba seda aka yi sallar isha'i yana shigowa yawuce part ɗinshi domin
besamu kowa a general parlor ba, cire kayan shi yayi zeshiga wanka kawai gabanshi yafaɗi
Hakan kawai yashiga fargabar shiga wankan agidannan, shiru yayi yana tunanin abunyi har
kusan ƙarfe 10:00pm yana zaune har Hajiya umma tashigo takawo mishi abincinshi tafita,,yana
zaune yarasa tinanin ma dazeyi can Isseta tafaɗo mishi arai yafara tunanin yaza'ayi tazo part
ɗinshi domin ya san idan tana ciki bawanda ze leƙashi Aban ɗaki to Amma Tayaya? Domin
yanada tabbacin Hajiya mama bazata bari tazoba,,yana cikin wannan tunanin ne wata dubarar
tazo mishi cikin Sauri yaɗauki wayarshi tare da Kiran Ummi tana ɗagawa yace tagayawa
Maryam tazo takarɓi kayanta na sakawa daya ɗauko mata amma suzo tare daga Hakan ya
kashe wayar.

Miƙewa Ummi tayi tacewa juwaira ina zuwa daga Hakan tanufi bedroom ɗin Hajiya mama koda
tashiga Isseta na kwance akan gado hajiya mama nagefenta tana lazimi, sallama tayi tukunnah
ta isarwa da Hajiya mama saƙon yah najeeb. Hajiya mama batakawo komai arantaba tacewa
Isseta tatashi suje.....itako kamar Jira takeyi tamiƙe sanyeda hijab ɗinta tabiyo Ummi suna
fitowa perlor sukayi ido huɗu itada juwaira dake zaune...wani irin miƙewa juwaira tayi tare da
zaro duka idanunta tace Isseta....!

Autar alheri ✍️

MM _ NN

Book 4

Page 61 & 62

"Itama Isseta kallon nata takeyi ido cikin ido...cikin mugun mamaki juwaira tace "dama Isseta
kina raye baki mutuba?? Tayi mata tambayar kamar wata zararriya. "Au tambaya kikeyi
koneman sani?� Cewar Isseta cikin renin hankali, kafin tagyara tsayuwar ta tace "dama
tunanin dakukeyi kenan? Namutu? Humm to idan ma mafalki kukeyi kufalka juwaira domin
kuwa maryama tana Raye cikin ƙoshin lafiya tare da ingaccen farin ciki Danake samu daga
mijina kuma abin alfaharina, taƙarsa maganar tana sakin wani shi'umin murmushi wanda kallo
ɗaya zakayi mata kasan cewar da biyu tayi wannan mlaganar...ido juwaira taƙura mata ko
kiftawa babu yayinda ilahirin jikinta rawa yakeyi amma takasa cewar komai daganin yadda
bakinta ke rawa kasan magana takesonyi amma tashin hankali yahanata muɗe bakin ballema
tace wani abun

Ummi jiyotayi dasauri tana kallon Isseta cikin mamaki Itama tace "Maryam musah gombe dama
kece? Ɗan murmushi Isseta tayi kana tace nice Maryam Khamis sahabi naga baki ganeni bane
shiyasa banyi Miki magana ba amma koni nayi mamakin ganinki dama nanne gidanku? "Nanne
kuwa Maryam Ashe dai haryanzu Sunan Isseta bemutuba ana faɗar shi, tafaɗa cikin farin cikin
ganin Isseta domin dama Ummi da juwaira a school ne suka haɗu harsuka fara ƙawance kuma
juwaira da Isseta amakaranta ɗaya sukayi secondary school agarin Rimi boding school kuma
Ummi ma acan tayi karatun shiyasa sukasan juna. ƙawance kuma da'akeyi tsakanin juwaira da
Ummi alokacin suna school da Isseta Ummi tasoyin ƙawance da halima dataga basada ra'ayi
da ƙawancen ne yasa tayi accept ɗin juwaira dake shigemata dan suyi ƙawance shiyasa suka
zama ƙawaye..

Cikin farin ciki Ummi tace Maryam ina halima Attahir gombe? "Tana'nan lafiya qalau Maryam.
Humm iKon Allah kenan dama kece matar yah najeeb? "Yeah nice kuwa, Isseta tafaɗa tanayin
wani farfar da manyan idanuwanta.

Wani irin tarine yasarƙe juwaira cikin mugun sabon tashin hankali take nuna Isseta dayatsa cikin
rawar murya tace "matar yah najeeb?? Kuma Isseta?? Inaaa wlh sam bazeyuba ƙaryane wlh

baki Isaba Isseta narantse da Allah idan kin isa shegiya nake mafalkina? Cikar burina farin
cikina duk kirusamun? Ai wlh kinsha ƙary...kafin tarufe bakinta Isseta tazo gabanta tare da
ɗaukar yatsarta taɗora akan lips ɗinta tace "shiiiiii relax juwaira relax mana duk wannan tada
jijiyar wuyan naminene? Duk akan mace ɗaya da mijinta? Mijinda bekosan kinayiba? Haba
ƴammata Karki bada mata mana, kizama me class kijira naki rabon yazo domin najeebullah
yamiki nisa shiɗin mallakin maryama ne kuma kisani tunda yazama mallakin maryama
yaharamta agareki sabida baki isa fatanyar datayi noma agonata ba kema tanoma taki gonar
sam bazeyuba bakeba duk wata akuya marar class najeebullah yayi mata nisa tamkar nisan
sama da ƙasa, taƙarasa zancen tana sakin wani shi'umin murmushi...hannu juwaira taɗaga zata
mari Isseta cikin sauri ummi tariƙe hannun tana faɗar"marin matar yayana kuma agabana
juwaira? Haba kema kinsan bazeyuba, tafaɗa cikin ɓacin rai tanayin jifada hannun juwaira.

Murmushi Isseta tayi kana tace "barta maryam barta tajawa kanta bala'i, tareda watsawa
juwairar wani mugun kallon gargaɗi...baki Ummi tabuɗe zatayi magana kenan wayarta taɗauki
ƙara koda taduba Taga yayan nata ne cikin sauri tace please anty Maryam muje Kinga yah
najeeb nakira wlh inbamuyi sauri ba duka zansha domin masan kekam bazeyiwa sarauniyarshi
komaiba, tafaɗa tareda kamo hannun Isseta suka bar perlor...wani irin kukane yasuɓuce wa
juwaira wanda yazo mata tindaga zuciya cikin sauri tatoshe bakinta tare da rugawa aguje
bedroom ɗin Ummi.

Su ummi kuwa suna fitowa suka samu Hajiya Umma da yah munir da sajad a general parlor
suna zaune

20 / 38