TANTABARA COMPLETE BOOK BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Muhammad Surbajo Category :  Arewa Pen

Chapter   4 / 13

9K to 12K   out of 36.7K words

asibitin zatonta a abuja ne,kallonta takai gunsa,akaro na farko data fara yarda ta kalleshi,shima ita yake kallo.

Kyawunshi ne yasata saurin runtse ido tana karanto duk adduar datazo bakinta,dan yanzu ta tsani duk wani namiji me kyau.

Cigaba yayi da driven har suka ƙaraso gida,koda yayi parking ya fita ita ƙin fitar tayi,dawowa yayi ta ɓangaranta yace a tausashe"muje ko"

Ɗauke kai gefe tayi tace"gidanmu nakeson zuwa ni"ba tare data kalleshiba.

Murmushi yayi yace"to fanan zan kaiki amma ay kinsan niko ke bame ikon yin hakan nan take kasancewar ba ƙasar mu bace nan suna da tsari da dokoki da suka sha banban da namu dan haka ki fito muje ciki atsara yadda hakan zata faru kwana kusa."ya faɗi yana murmushi

Ɗan jim tayi tana nazari kamin daga bisani ta waigo tana kallonshi hawaye na biyo idonta ta haɗe hannayanta guri guda tace cikin kuka"naji zan shiga cikin gidanka amma na haɗaka da girman Allah kar ka keta mutuncina,a ƙasar da bani da kowa se Allah"ta faɗi wani kukan na sake kwace mata.

Shuru yayi yana kallonta,sosai kanshi ke cike da tarun tambayoyi amma yagaza samo amsarsu,dan haka kauda tunanin yayi yace yana murmushi"ba fasiqi bane ni fanan,duk da ban kasance nagari ba amma bana zina,dan haka kibini da zuciya ɗaya,in kuma ma baki amince da zama dani gu ɗaya va to abu mafi sauƙi ke kishiga nan ki zauna ni kuma zan wuce hotel inzauna kamin zuwa ranar dazan maidaki nigeria,dan nan muna paris ne"ya faɗi ba tare da damuwar komai ba.

Sosai fanan ta gamsu da batun yatafi hotel ɗin dan haka fitowa tayi tana faɗin"nafi gamsuwa da zamana ni kaɗai ɗin anan"

"baki da damuwa fanan muje in nuna miki komai se in tafi,in kuma baki gamsu ba to kije da karanbani kya gane komai"

A hankali ta fara takawa hakan na nufin ta gamsu daya nuna matan,binta yayi abaya saidai kowa ta ɗaga ƙafarta da nufin tafiya ji yake kamar ze shiɗe sabida yadda mazaunanta ke rawa.

Gaba yayi ta bishi abaya dan gudun kar ya aykata abinda be dace ba.

Minti talatin ya kwashe wajen nuna mata komai da yadda zatai amfani dashi,sannan ya wuce ɗakinshi ya kwashi abinda ze buƙata,sannan ya dawo falo inda take tsaye tana jira ya fita ta rufe ƙofar.

Ɗaya daga cikin Wayoyin shi ya bata yace"akwai numbata aciki in kina buƙatar wani abu ki kirani"

Amsa tayi tabi bayanshi da kallo dan juyawa yayi ya fice abunsa.

Yana fita ta kulle ƙofar,sannan ta wuce kitchen dan samawa kanta abinda zataci.

Taliya ta dafa ta ɗauko har tukunyar ta dawo falo ta zauna taci abunta ta ƙoshi sannan ta maida tukunyar.

Ɗaki ta wuce tai wanka,sannan tayi sallah ta haye gado,tana tunanin irin yankan ƙaunar da fahad yay mata,wasu hawayene suka wanke fuskarta,masu zafi.

Kauda tunanin tayi tafara tuno innarta da ƴan uwanta,da son sanin yadda ma akayi ta haɗu da wannan me jajayen kunnuwan har ya kawota paris?

Wayar daya bata ta zaro aƙasan filo,hoton wata kyakkyawar matace afuskar wayar,wacce ko bata saniba mahaifiyarshice dan ga kamanni nan.

Rasa me zatayi awayar tayi kawai saita kunna data,kunnawarta keda wiya,saƙwanni sukai ta shigowa wayar daga whatsapp insta da sauransu.

Ba tare da tunanin komai ba ta faɗa kan whatsapp ɗinshi.inda saƙwanni wata me suna nadiya keta shigowa da yawansu.

A hankali ta shiga kan saƙwannin,inda taga saƙwannine na roƙon yasota keta shigowa wayar wanda sosai taba fanan tausayi,dan taga sonshi take kamar hauka.

A hankali ta fara maida mata da amsa da kalaman amincewa da soyayyarta,ay saƙon na shiga taga ta sake dawo mata da ansa cike da farinciki na murna.

Tausayi taba fanan dan so masifa ne,

Nadiya ko acan nigeria ihu tasa ta nufi ɗakin mummynta tana nuna mata saƙon amincewa da ita da mahboob yayi.

Sosai mummy taji daɗi ganin farinciki afuskar ƴartata,tace"shikenan kuka ya ƙare,ko nadiya?"cewar mummy tana dariya.

"mummy yace nan da dawowarshi nigeria fa zaa mana aure wayyo ni daɗi"ta faɗi tana tsalle na farinviki.

Ranar nadiya bata bar mummy ta runtsaba,dan farincikin amsar soyayyarta.

Itako fanan tayi hakane dan samawa nadiyar sanyi aranta kona kwana ɗayane.hmmmm

Kashe datar tayi ta kifa wayar aƙirjinta tana tuno rayuwa,a hankali take takura kanta wajan tuno numbobin yayanta kabeer,wanda ya ɗauketa mintuna talatin kamin numbobin su sake jera kansu akanta.

Jikinta har rawa yake ta fara danna numbobin,tana gamawa ta danna kira,

Kabeer dake zaune a shagon ɗinkinshi ganin kira da baƙuwar number daga ƙasar waje sosai abun yabashi mamaki dan shide a iya saninsa daga niger ma beda me kiransa bare paris.

Ɗaga kiran yayi bakinsa ɗauke da sallama.

Fanan najin muryar ɗan uwanta kawai saita fashe da kuka,da ƙyar tace "yaya kabeer nice fanan"

Wayyo kabeer gurin ƙoƙarin miƙewa tsaye har faɗuwa yake,bakinshi na kakkarwa yace"fanan fanan fanan kina ina ne haka dan Allah"ya faɗi hawaye na biyo idonshi.

"ina paris yaya"ta faɗi cikin kuka,zata kuma magana katin ya ƙare sakamakon kiran nigeria da tayi.

Kabeer kiran numbar ya fara jikinshi na ɓari saidai taƙi shiga sabida mahboob yasa wayar atsarin inba shi ya kiraka ba ko ka kirashi vaze xoba.



muje zuwa.

*07044600044*
[8/14, 07:09] Ummu Fadila: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*13*



Tunda suka bar unguwar in banda kuka ba abinda fanan take,ko kaɗan ji take rayuwarta bata da sauran amfani dama ta mutu da yafi mata alkha'iri.

Mahboob zuciyarshi in banda tafasa ba abinda take sabida jifansu da akayi, ga kukan fanan wacce ya gaza rarrashinta dake barazanar tarwatsa masa xuciya.


"malam kaimu kano kawai"cewar mahboob wa direban cikin fushi.

Da sauri fanan ta tsaida kukanta ta ɗago ta dubeshi tace"ka barni anan dan nan ne garina koma menene iyaye da ƴan uwana nanan don Allah"ta faɗi hawaye na biyo idonta.

"Fanan komai ze iya faruwa dake wanda ni bazan so hakanba dan haka kibari komai ya lafa mazo daga baya"ya faɗi cikin sigar rarrashi.

Shuru tayi alamun ta gamsu,dan haka driver ya miƙa dasu titin kano.


*******


Cikin mintuna ƙaɗan kafafen sada zumunta suka fara posting hotunan Mahboob rungume da fanan,ɗauke da bayanin"ɗa ga tsohon shugaban ƙasa kuma ɗa ga ministan jin ƙai da walwala,hajiya maryam sani fari mahboob sani fari rungume da wata matashiyar budurwa wacce tayi ƙaurin suna gun sanaar blue film,inda ƴan uwanta da ƴan unguwa duka suka koreta,yanzu kuma ta dawo tare da mahboob inda yasha alwashin duk wanda ya kuma korarta xe sa arusa unguwar tasu"

Cikin ƙanƙanin lokaci gidajan redio dana tv suka shiga watsa labaran,inda mummy na gida batasan meke faruwa ba,taga kiran mutane nata shigowa wayarta inda kowa ta ɗaga se ace ta kunna tv taga meke faruwa a ƙasar.

Jikin mummy har ɓari yake ta kunno tv dan ganin abinda akeso ta gani ɗin.

Lokacin ko data gani rasa inda zatasa kanta tayi,ganin yadda mahboob yajanyo mata tangarɗa atafiyar siyasarta da darajar gidansu.

kashe tv faisal yayi,dan suna tare, alokacin.jagwab mummy ta zame ta zauna a ƙasa ta dafe kanta,tsabar takaici batasan lokacin da hawaye suka shiga wanke mata fuskaba.

"mummy kiyiwa yaya afuwa kuma kimasa kyakkyawan zato sabida kinga......"lafiyayyan marin da mummy ta ɗauke fuskarshi dashine yasashi yin shurun dabe shirya ba.

Saɗaf saɗaf ya fice a falon riƙe da kumatunsa.



*******

Cikin dare suka iso kano,wayoyinshi akashe suke dan haka kai tsaye gida yace akaisu,suna sauka ƙofar gidan ya sallami me motar,shi kuma yaja fanan zuwa bakin get ɗin gidan.

Koda masi gadi suka gansu tare sunyi mamaki,inda suka gasgata abinda aka faɗi a media.

Koda yaga sunata kallonsu some how be kawo komai ba,yasa kai zuwa cikin gidan tana biye dashi abaya.

Sosai gidan nasu ya burge fanan duk da batasan koshi waye ba tasan de ɗane ga wani ƙusa aƙasar duba da yawan jamian tsaro dake gadim gidan nasu.

Kanshi txaye part ɗin mummy yamata jagorancin zuwa dan ta bata masauki kan ya maidata ga iyayenta.


Mummy wacce tunda magriba datagani takasa tashi agurin datake,tana zaune taji sallamarshi tare da muryar wata mace.

A razane ta ɗago dan son gasgata kunne da idanuwanta,ayko tana ganinsu ta miƙe jikinta na kakkarwa,tace bakinta na kumfa.

"mahboob ashe abinda nagani a tv gaskiyane hakan be ishekaba shine ka ɗauko min ita ka kawomin gida wanna ƴar blue film ɗin,to wallahi tun muna shaida juna ta fice daga gidan nan kamin nasa a ɓatar min da ita a doron ƙasar nan"Ta faɗi tana huci.

Cike da mamaki mahboob ya dubi mummy yace"mummy inaso ki natsu mubar maganar xuwa gobe da safe se ayita amma yanzu agajiye muke pls mum"ya faɗi yana langaɓe wiya.

"wallahi mahboob minti ɗaya ta kuma yi acikin gidannan sena tsine maka"

Jin abinda mummy tace ne yasz fanan wacce tun shigowarsu take kuka juyawa ta fice da mahaukacin gudu,yayinda shima mahboob ɗin yabi bayanta da gudu saidai yana zuwa get masu gadi suka tsareshi ita kuma ta fice da gudu.


Duk yadda yaso su barshi ya bita sun hanashi dan sarkin yawa yafi na ƙarfi.

Durƙushewa yayi akan guiwowinsa yana zubar da ƙwallah.

Wacce zuwacan fasaha tazo masa kawai yayi farat ya ƙwace bindigar ɗaya daga cikinsu yayi attacking ɗinsu yana faɗin"ko in fita ko inkashe duk wamda yayi yunƙurin hanani"ya faɗi kokacin da yaja kunamar bindigar .

Ayko sa xauri suka buɗe masa ƙofar yako fics da mahaukacin gudu yana ƙwala mata kira bayan ya ajiye musu bindigarsu.


muje zuwa.

*07044600044*
[8/14, 07:09] Ummu Fadila: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*14*


Jin kiran da yake mata besa ta tsaya daga gudun da take tana kukaba.

Ganin bata da niyyar tsayawa ne yasa ya ƙara nashi gudun ya cimmata,da zafin nama yasa hannu ya fincikota ta waigo tana kuka tace"zuwa yanzu ya kamata ace kadena sa kanka cikin matsalata,dan gudun ɓatawa kanka suna dan Allah"ta ƙarashe maganar tana me durƙushewa akan guiwowinta tana kuka me tsuma zuciya.

Durƙusawa yayi ya kamo hannunta yace"ƙaddarar kowa da yadda Allah ya zanata,ni tawa dake acikin zanenta,koma menene fanan nq miki alƙawarin tsayawa tare dake duk wiya duk runtsi kawai muyi addua"ya faɗi cikin sigar ƙarfafa mata guiwa.

Wayarshi ya ciro ya danna numbar doctor bala abokinshi,baa jimaba ya ɗaga,tun kan yayi magana ya rigashi da cewa.

"Doctor me nake gani yana trending haka,wai ba wannan mahaukaciyar da ka taimaka bace wannan yarinyar?"cewar doctor bala aɗan hargitse.

Kallon sashinta mahboob yayi sannan ya sauke ajiyar zuciya,yace"ehtace doctor,ina buƙatar inda zan ajiyeta cikin daren nan,dan mummy ta koreta,ataƙaice de yanayin ya ɓaci dan gobe nakeson siyamana ticket mu koma"

"Katuramin location ɗin da kuke zanzo yanzu in ɗaukeku"cewar doctor bala da sauri.

Kashe wayar mahboob yayi ya turawa doctor bala location ɗin.


Fanan har zuwa lokacin bata dena kuka ba,kallonta mahboob yayi yace cikin sigar wasa"zauna kita kuka hawayenki ya ƙare ki rasa wanda zakiyi in zaa kaiki gidan miji uwa uba kuma in yazo amsar sadakinsa,maga me ara miki nasa hawayen kiyi kukan"ya faɗi yana leƙa idanunta.

Murmushine ya kubce mata me haɗe da kuka,lokacin data tuna ay ita ta gama cinye first night ɗin nata atiti.

Suna tsaye doctor ya ƙaraso gurin,da sauri suka shiga motar yaja suka bar gurin.

Kai tsaye gidanshi ya nufa dasu,dan dare yayi sosai.

Matar doctor Me suna Aisha macece me kirki dan haka hannu biyu ta tarbesu,gefe ɗaya kuma tausayin fanan ne fal zuciyarta.

Jan fanan tayi ɗakinta,ta haɗamata ruwan wanka, da ƙyar ta rarrasheta ta shiga wankan.

Tana fitowa ta bata doguwar riga ta saka,taje ta kawo mata abinci taci sannan ta ɗauro alwala ta fara rama sallah.

Shima mahboob BQ ɗin gidan doctor ya saukeshi,wanka yayi ya ɗauro alwala,sannan doctor ya bashi kaya ya sauya.

Sallah yayi tukunna sannan yaci abinci,bayan ya kammala ne doctor bala yace a tsanake.

"mahboob wai da kake ta wahala da yarinyar nan kasan komai akanta koko wahalarce bata isheka ba?"

"Doctor ko insani ko kar insani kawai nide na lashi takobin saina zama sanadin tsayawar hawayenta,becouse she is too young,to face this problem,tana buƙatar taimako,ta ɓangarori da dama doctor ka daure ka shigo cikin tafiyar nan muyi jihadi"ya faɗi a raunane.

"kalmar ƴar blue film da ake alaƙantata da itafah?"doctor bala ya sake jefo masa tambayar.

.Shuru mahboob yayi yana juya kalmar a bakinsa,kamun yace"bani da wata masaniya akan wannan kalmar doctor,hasalima naje kaita gidansunefa duk abinda kaga ya faru ya faru,bansan komai ba doctor"ya faɗi a sanyaye.

"to akwai buƙatar kasani,dan kar ka jefa kanka ramin da bazaka iya fitowa ba"cewar doctor bala.

Sun jima sina tattaunawa gameda matsalar kamin doctor ya masa saida safe ya shiga cikin gida shi kuma ya kulle ƙofa ya kwanta.

*********

"Wallahi fanan ce,hakan na nufin ta dawo nigeria kenan taje tsohuwar unguwarmu hakan ta faru da ita"cewar kabeer lokacin daya tara sauran ƴan uwansu yana musu bayanin abinda ke yawo a social media da manyan kafafen yaɗa labarai.

"kaga yaya to zama be ganmuba,tunda de ƴar uwarmu ta dawo,mu fita nemanta kanmu tsaye inaga hakan zefi"cewar ɗaya daga cikin yayyan nata.

"Ba magana bace ta mu fita nemanta,maganacefa ta cewa fanan nacan tare ɗan minister kuma ƴar takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa,ta ina zamu fara nemota in mun fita?"cewar aunty habiba ɗaya daga cikin yayyanta.


Shuru sukayi su duka,kamin kabeer ya nisa yace"muyi haƙuri mu jira nan da sati guda in har fanan bata zoba ko ta nememu a waya ba to zamu fita media mu nemeta tunda abun nakan trending yanzu haka da munyi magana zata yaɗu."

Gamsuwa sukayi da shawararshi,dan haka kowa ya tashi ya kama gabansa cikin shirin zaman tsammani.

********
Yau kwanan fanan da mahboob biyar a gidan doctor bala,inda mahboob keson subar gidan jibi.dan matakan tsaro mummy tasa a faɗin ƙasar dan anemo mata shi,inda har gidan doctor bala suka zo basu ganshiba dan mummy ta kwatanta musu


Yau da wuri suka tashi,dan ita fanan ma kusan kwana tayi tunanin ƴan uwanta da mahaifiyarta,shiyasa gari na wayewa ta roƙi aisha ta bata wayar ta aro,inda tace"inaso in kira gidane pls."ta faɗi lokacin da take mata magiyar ta bata.

Ba musu Aisha ta bata wayar dan ita sosai take tausayinta.

Number yaua kabeer ta danna ta kira,inda bata jima tana ringing ba ya ɗaga.

Tana jin muryarshi ta rushe da kuka,tana faɗin"yaya kataimakeni"

Wayyo kabeer yana jin sautinta hawaye suka fara biyo idanunsa lokacin yana cikin abokansa sunje ɗaurin auren amininsa kano can kurna babban layi da suka je kanon tun daren jiya sabida ɗaurin auran na safe ne, har harɗewa yake wajan faɗin "fanan banason jin komai kawai ki faɗamin inda kike yanzu"

"Yaya ina kano nasarawa GRA"ta faɗi cikin kuka.

Address ya buƙata ta tambayi aisha ta faɗa mata ta faɗa masa.

Da gudu ya faɗa motarshi da ya siya ba jimawa peugeout 206.

Tada ita yayi yabar harabar gurin,ji yake kamar yayi fiffike ya ganshi a gra ɗin.

Aisha ficewa tayi zuwa kitchen dan ta duba abincin data ɗora musu na safe.

Wayar na hannun fanan tana kallon fuskar wayar tana jiran yayan nata.dan tagaji da ɓoye kanta.

Baa jimaba ya kirata,da sauri ta ɗaga yace"ina ƙofar gudan fanan".


Ay ko kashe wayar batayiba ta fice da gudunta ba tare data ko bi takan aisha dake kitchen ba.

Lokacin mahboob sun fita shida doctor zuwa asibiti dan ya gaji da zama guri ɗaya.shiyasa yasa facemarsk suka fice..

Tana fita tai arva da yayanta tsaye yana ta waige waigen son ganin ta inda zata ɓullo.

Da gudu tayi kansa,shima haka,suka haɗe a tsakiya ya rungumeta gamida ɗagata yana juyawa.


Tsananin farincikin da suke ciki baze faɗuba na ganin juna.

"yaya mu gudu mubar gurinnan kan su dawo dan Allah"cewar fanan cikin kuka.

Ayko jikinshi har rawa yake ya juya da gudu yasata amota yashiga ta tada suka bar gurin.

Ko da wasa be koma gun bikin aminin nasa ba,ya kamo hanyar kaduna,yana driven hannunsa riƙe da hannun fanan yana ganin kamar zaa ƙwaceta.






muje zuwa.

*07044600044*

[8/15, 05:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*15*



Kabeer gudu yake bada wasa ba hankali fanan be kwanta ba seda taga sunbar jihar kano gaba ɗaya,sun wuce tashar ango sunzo kunkumi.

Ajiyar zuciya ta sauke me nauyi ta dubi yayan nata wanda shima ita ya kalla,yace"fanan kode cutar dake sukeyi ne yasa kike gudunsu"?

A sanyaye tace"ko ɗaya yaya taimakona yake sede bazan iya ci gaba da zama tare dashi ba dan mahaifiyarshi bata sona,har abun ya shafeshi shiyasa na barshi dan ya fuskanci mahaifiyarshi ya bata haƙuri su shirya."ta faɗi hawaye na biyo idonta.

Ganin hawayenta ne yasa kabeer bece komai ba yaci gaba da driving,dan so yake sukai gida lafiya seya jata jiki yaji abinda ke faruwa.

Har suka shiga kd fanan bata dena ƙwalla ba,ga mamakinta tsohuwar anguwarsu ba nan ya kaita ba sabuwace yanzu ,tun kan tayi mgn ya rigata da cewa"bayan barinki gidane muka dawo nan"

Shuru tayi batace komaiba,har yazo bakin gidan,inda suna tsayawa taga anbuɗe musu get sun shige ciki,

Gidan bashi da girma amma anmasa get da gurin ajiye mota wanda abun ya bata mamaki.

Fitowa tayi shima ya fito suka shiga cikin falon gidan.ayko sauran ƴan uwanta kamar jira sikayo kanta da gudu dan tun suna hanya kabeer yay musu wayar sun taho.


Kowa rungumeta yake ana mata murnar dawowa,itako se raba ido take tanaso taga innarta amma bata ganta ba yasa tace asanyaye"inna tana fushi dani har yanzu ko?naga taƙi haɗuwa dani dan Allah ku bata haƙuri"ta faɗi hawaye na biyo idonta.

"inna ba fushi take dakeba dan ta jima da rasuwa,sede ki bita da addua"cewar kabeer.

Kuka fanan tasame tsuma zuciya dan batasan inna ta mutuba,ta jima tana kuka basuyi ƙoƙarin hanataba,dan kar ya zame mata ciwo inbatayinba.

Saida ta ta rusuna ne daga kukan,aunty habiba tace mata"inna kamin mutuwarta taso ganinki,mukai ta nemanki bamu gankiba,haka ta mutu da begen ganinki amma ta yafe miki kuma tace itama ki yafe mata"

"innata na yafe miki dama kuma ni banji haushin kiba komai yafaru nice sila,nice naso ganinki kan ki rasu innata"cewar fanan gamida sake fashewa da kuka.

wanka sukasata tayi taci abinci sannan suka barta ta huta Bayan tayi sallah.

********

Mahboob suna office ɗin doctor bala yaji fanan na yawan zuwa masa arai,sannan in yaji hakan se gabanshi yay ta faɗuwa,hakanne yasa yacewa doctor bala.

"tashi ka kaini gida in dubo lafiyar ƴar mutane Doctor"ya faɗi yana duban agogon hannunshi.

Murmushi doctor bala yayi sannan yace"sabida matata bata iya kulawa da lafiyarta ba?"

Ɗan yamutsa fuska mahboob yayi yace"nide kaini zuwa da kai ay yafi saƙo"

"To matata bari kaji ni kaina kulawa da tawa lafiyar take bare fanan"ya faɗi cikin sigar tsokana.

"may be akulawar dakai tai masters,dan haka taso mutafi"

Ayko dariya sukasa su duka,sannan bala ya taso ya kullo office suka bar asibitin.

Suna shiga harabar gidan suka samu Aisha tsaye da maigadi hankali tashe,suna parking ta nufosu da gudunta tana faɗin "kun ganta a hanya?"ta

4 / 13