TANTABARA COMPLETE BOOK BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Muhammad Surbajo Category :  Arewa Pen

Chapter   13 / 13

36K to 36.7K   out of 36.7K words

sukasance cikin tsaro har zuwa rantsarwa.

Badan yasoba ya amince da zaman nasu agidan nata,inda anan su yaya kabeer sukazo suka gaisheshi da jiki,inda mummy tai musu tarbar mutunci da karramawa ba tare da nuna ƙyama ko hantara ba.

***********


An gudanar da zaɓe lafiya inda jamiyyar su mummy tai nasarar lashe zaɓen,koina murna ake da yadda zaɓen ya gudana,


Bayan komai ya lafane,mahboob yace mummy tabarsu su koma gida,amma tace su ƙara zama,abindabasu saniba shine rabuwa dasune bataso tayi shine yasa take hanasu tafiya.

Yau mahboob ya ɗauki fanan a mota sika tafi yawon shan ice cream suka barwa mummu yaran agida.


Bayan sun fito daga gun shan ice cream ɗinne suka ci karo da wani gurgu,tsugunne gun motarsu,

"malam lafiya kuwa?"cewar mahboob danshi yafi zaton ma mahaikacine.


Ɗagowa yayi yana kuka ba kowa bane Fahad ne,ba ƙafafu duk amyanke,agigice fanan tai bayan mahboob dan gaba ɗaya halittarshi ta sauya,kyan da yake taƙama dashi dik babu,dan ko haƙoran gaba bashi dasu,ga wasu ƙuraje dake ruwa ajikinshi ba ƙyan gani.

."tun isowarku nagane ki fanan,kinga yadda hakkinki yamaisheni fanan,yanzu haka cutar ƙanjamauce ajikina su khairat suka shafamin,ita khairat tuni ta mutu sakamakon faɗan da sukayi da amira akan kuɗi ta caka mata wuƙa ita ameera tana prison yanzu haka,ni motace ta bigeni na koma haka,fanan dan Allah ki yafemin nasan na cutar dake ki gafartamin." ya faɗi yana kuka kamar ze shiɗe.


Ita de fanan da gudu ta faɗa mota ita tsoronshi ma takeji.

Mahboob ne yabashi amsa da cewa"Allah ya gama hukuntaka fanan bata da abun faɗama baƙin azzalumi"yana kaiwa nan ya shige mota yaja suka barshi agurin yana kuka.


********


Saida fanan ta kwana biyu bata dawo daidai daga firgicin ganin fahad ba,shima saida mahboob ya nuna fushinsa kamin ta mance komai.

Yau mummy ta kira me ƙunshi tazo har gida tayiwa fanan,aka mata ƙunshi na gani na faɗa,mummy da kanta take ɓare kunshindaya bushen,nadiya ta shigo gidan.


Ba ƙaramin mamakin yanayin data gansu tayiba baki buɗe take binsu da kallo.

Ba yabo ba fallasa mumy ta amsa gaisuwar da nadiya ke mata,taci gaba da ɓarewa fanan lallan.

"Mummy gunki nazo "cewar nadiya a kunyace.

"Go ahead inajinki,ko kinga bare anan?"cewar mummy ba tare data kalleta ba.

Shuru nadiya tayi ta kasa magana se soshe soshe take.

Ganin hakane yasa fanan miƙewa,tabar gurin dan ta basu damar yin magana.


"mummy nazo ne inbaku haƙuri kan abinda nayi kuma kisa mahboob shima ya yafemin yamaidani dakina,su daddyna sunce ba ruwansu shiyasa ni nazo"

"nadiya dade na tilastashi auranki,amma yanzu ba ruwana tsakaninku,inyaga dama ya katɓeki ruwanku inyace beso ma duk ruwanku dannhaka kicireni acikin sabgar ku"cewar mummy cikin tsare gida.

Suna haka mahboob ya shigo gidan ya dawo daga gun doctor bala.


Kallo ɗaya yayiwa nadiyar ya ɗauke ido, se yanzu ya tuno da ita,maganganun data faɗamasa a asibitine suka shiga dawo masa kunnensa.

Mummy yayiwa sannu da gida,sannan ya wuce cikin ɗakinshi.


Yana zuwa takarda yasamu ya rubuta mata takardar saki,sannan ya dawo falon,ko mummy bebi takanta ba ya miƙawa nadiyar yace afusace"ga takardarkinan na sakeki saki ɗaya nasan tunda kinsamu labarin ban mutunba ne kikazo amsat takardarki to gatanan"yana kaiwa nan yajuya yakoma ciki,


Itako nadiya kuka tasa tana roƙon mummy,kan tasa baki,mummy ko batace komaiba, haka nadiya ta gaji ta tashi tabar gidan tana kuka,se yanzu take danasanin abinda tai masa.

********


Bayan tafiyarta suma suka kimtsa suka bar gidan na mummy zuwa nasu wanda yagaji da haɗuwa dan sabo mummy ta sa aka tsara musu.


Rayuwa tayi daɗi,suna zaune cikin so da ƙaunar juna,yayinda fanan ta koma makaranta bisa jagorancin mijinta uban ƴaƴanta,dan haihuwar tsaya mata tayi tun daga kan ƴan uku bata ƙara ba.


Ƴan uwan fanan gaba ɗaya ta ɗagasu sunzama wasu suma ,kuka ya ƙare a familynsu se godiya da alfahari da fanan akoda yaushe.

Ƙawar mahboob ko baturiya tuni fanan ta datse kawancen,da ike abinda takeso yakeyi beko musa ba,dan yanzu yazame mata rakumi da aƙala,abinda takeso yakeyi,haka ƴan uwanshi sosai suke sonta.
.
Mummy ko jitake kamar ta maidata ciki sabida son da take mata.


ALHAMDULILLAHI

Nan wannan labari yazo ƙarshe Allah kayafe mana kura kuranmu kabamu ikon yin daidai. amin.

Nagode da haƙurinku gareni,nagode sosai insha Allahu yanzu nadawo fully ready zaku dinga samuna akai akai,komai yayi normal yanzu Alhmdllh.







muje zuwa.

*07044600044*




13 / 13