TANTABARA COMPLETE BOOK BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Muhammad Surbajo Category :  Arewa Pen

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 36.7K words

shiga kafin kowa kune,farko,cikinku ba wacce na aura dan in wulaƙanta,kowaccenku na auretane da zuciya ɗaya,ina da kawaici akan abubuwa da dama amma bazan yiba akan wacce tace bazata zauna lafiya dani da abokiyar zamanta ba."

"Mahboob lets me clear it to you,ni nadiya nafi ƙarfin wulaƙanci,wlh,baka isa ka haɗani kishi da wannan abun kace bazan magana ba,seda kace fanan ma ne na tuno fuskarta,ba itace tsohuwar ƴar blue film ɗin da aka haskoku tv tare bane,ƴar blue film da social media kaf ba inda baa santa ba....."bata ƙarasa abinda takeso ta faɗi ba mahboob ya ɗauketa da mari fuska biyu.

Da gudu fanan ta fice daga ɗakin tana kuka jikinta na kakkarwa.

"ni ka mara mahboob Akan waccan tsinanniyar?"ƙara kwasheta yayi da mari rai aɓace yace .

"Duk ranar da kika kuma kiran uwar ƴaƴana da wannan sunan wallahi sena datse igiyar auran dake tsakanina dake,zaki san kinyi kuskure."yana kaiwa nan ya fuce a fusace.

Fanan na zuwa ɗakinta haɗa takardunsu tayi ajaka bayan ta kulle ƙofar ɗakin,da ike visarsu anyine akan zataxo haihuwa,shiyasa ta haɗa komai,ko kayan sawa bata tsaya ɗauka ba,ta goya ɗaya abaya ta rungumi guda biyun,ta rataya jakar kayan abincinsu wacce tasa takardunsu ciki.

Mahboob koda yazo yaji ta kulle ƙofar masallacin da yayi a bayan gidan ya wuce da nufin in ya dawo yasameta.


Saida ta tabbatar da mahboob ya tafi masallacin dan ta dubi lokaci tasan be wasa da sallah,ta fito ta kulle ɗakin nata tai ficewarta daga gidan idonta na zubar da ƙwalla.

Taxi ta hau da sauri tace ya kaita airport,ba musu ya ja suka tafi.

Koda sukaje airport jirgin da zzshi nigeria se ƙarfe tara na dare ze tashi, ticket ta siya ta cike duk abinda yadacr,batare damuwar komai ba ta adana kanta inda tasan ko ya biyo bayanta baze ganta ba.

Koda mahboob yazo ya ƙara taɓa ƙofar yaji a kulle zatonshi kulle kanta tayi dan haka ya shiga yimata magiya kan tazo ta buɗe amma baa kulashiba.


Ko kaɗan beyi zaton bata cikin gidan ba,haka yay ta ƙwanƙwasar ƙofar har wajan ƙarfe goma na dare beda niyyar barin gurin.

Me renonsu ce ta fito daga ɗakinta tazo ta sameshi,tace cikin harshen turanci"madam fa bata nan,naga fitarsu ita da yara,ina mata magana ma bata jini ba"


Da sauri ya cakumota yace cikin fusata,"ta fita fa kikace?"

A gigice ta gyaɗa masa kai,da sauri ya koma ɗakinsa ya ɗauko spare key yasa ya buɗe ɗakin,drower da sukasa takardun zamansu ƙasar ya nufa da gudu yana zuwa ya ganta abuɗe ba komai ciki agigice yake bincike ko ina naciki yaga ko ta bar mishi nashi seyaga duka ta haɗa dasu.


Da gudu ya fics daga ɗakin ya faɗa mota yaja da mahaukacin gudu ya nufi airport,yana kiran numbarts amma akashe take.

koda yazo airport ɗin samu yayi jirgi me tafiya nigeria ya ɗaga awa ɗaya da rabi data wuce.

muje zuwa.

*07044600044*
[10/9, 09:52] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*52*



Mahboob zamewa yayi ya zauna daɓas agurin idanunsa na zubar da ƙwallah,a hankali yake furta"fanan akan me zakimin haka, bafa ni nayi laifinba,ko dama jira kike kisamu ƙofar yimin hakan,haba fanan,kin tafi da passport ɗina taya zan biyoku,baki kyautamin ba fanan"ya faɗi cikin kuka.

Da ƙyar ya tashi agurin ya hau mota yana haɗa hanya ayko gidan dabe isa lafiya ba kenan yayi accident.

Nadiya na gida taji ana buga ƙofar gidan bayan an matsa bell,da batai niyyar zuwa ta buɗe ba,dan tun bayan fitarshi taxo ta tambayi me aykin fanan kan abinda ya faru ta faɗa mata,to zatonta shine,can de taje ta buɗe ganin jamian tsarone sosai tsoro ya kamata,bayan sun nuna mata id card ne suka sanar da ita mahboob yayi hatsari,yanzu haka yana asibiti.

Bata wani damu sosaiba dan tasan sabida fanan yayi hatsarin,komawa tayi ta yafo gyale tabisu abaya zuwa asibitim.

Tasha matuƙar mamakin ganin halin da yake ciki,in banda rai me alfarma zatonta ma ya mutune sosai yabata tausayi,yayinda gefe ɗaya kuma yake bata haushi.

******

Fanan ta isa nigeria lafiya,kai tsaye gidan auranta ta nufa,dan ita dama ba ta taho da sunan ta tafi gidan su bane,


Samu tayi gidan nasu agyare fess dan megadin gidan kullum seya gyara kamar yadda mahboob ya umarceshi kamin su tafi.


Ajiye ƴaƴanta tayi dake ta faman kukan gajiya da rashin sabo,wanka ta fara musu da ruwa me zafi sannan ta basu abinci itama tai wankan,ta nufi kitchen ta samawa kanta abinda zataci.

Se bayan taci ta ƙoshine ta dawo hayyacinta,kewar mijintace kebin kowanne sashi na jikinta ahaka ta lallaɓa kusa da ƴaƴanta dake bacci itama ta kwanta.

Bacci yay awon gaba da ita me cike da mafarkai marasa daɗi.

*******

Mahboob seda ya kwashe wata guda a coma,a duk tsawon lokacin nadiya ke amsa wayar hajiyarshi inda ta shaida mata bayajin daɗi ne sakamakon ciwon haƙori da yake likita ya hanashi mgn saidai chatting,hajiya bata kawo komaiba se nadiya tai ta chatting dasu a mazaunin mahboob ɗin.

Ya jima a haka sannan ya farfaɗo koda ya farfaɗo bawai lafiyace dashiba dan kuka da mararshi yake gefe guda na ciwo,se fanan kawai yake kira,wanda hakan sosai yayiwa nadiya zafi,duk da ba ita ke jinyarshi ba maaikatan asibitinne amma ay kullum tana kan hanyar zuwa,amma shine dan wulaƙanci zai kira wata fanan.


Likitane ya buƙaci ganin nadiya,bayam sun gaisane,yake shaida mata matsalar mahboob.

"madam mijinki ya kamu da matsala a ƙodarshi,wacce guda ɗaya ta lalace ɗayar luma bata da ƙarfin riƙeshi,dole se anmasa dashen ƙoda, to bamu da donor,shine yasa nashaida miki in akwai yadda zaayi ko ke agwadaki agani in zaki iya bashi'

A zabure ta miƙe tace "wai ni in bada ƙodata Allah ya kyauta wlh bazan iyaba,tabɗijan,hmmm dama ban sanar da uwarshi halin da yake ciki bane zatona ze warke to amma tunda abun yana neman vrayuwarshi akwai buƙatar in sanar da ita suzo su gana"tana kaiwa nan ta fice daga offics ɗin zuwa ɗakim da mahboob ɗin yake.

Tsayawa tayi akansa a hankali ya ɗago yana kallonta batare da damuwar komai ba tace"ance dashen ƙoda zaay maka ko tonide bazan iya baka ba dan rayuwa wiya gareta dan haka zanje in sanar da mahaifiyarka inyaso kotacan ɓangaransu zaa samu donor ɗin,dan haka Allah ƙaddara saduwa,inkuma rai yayi halinsa ayafemu"tana kaiwa nan tasa kai tai ficewarta daga ɗakin.

Wasu hawayene masu zafi ke fita a idanun mahboob wanda na baƙin cikin rashin matarshi fanan ne,yana da tabvacin in itace bazata masa haka ba.

*********


Nadiya ta isp nigeria lafiya,inda saida ta kwana biyu da zuwa sannan taje gidan iyayen mahboob ɗin,


A falo ta samu mummy bayan sun gaisa mummy tace cike da mamaki"nadiya to ina mahboob ɗin kika baroshi?"

Glass ɗin idonta ta gyara sannan tace"yanacan rai a hannun Allah"daga haka ta kwashe dik abinda ya faru ta sanar da ita har auransa da matar daya aura ɗin da dalilin ciwon nashi.

muje zuwa.

*07044600044*
[10/12, 09:57] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*53*



Tana direwane ta ƙara da cewa"to ko azamanin nan ko kinga ay kyautar ƙoda ba abune me sauƙi ba,shiyasa nai tahowata"ta ƙarasa batun tana taunar cingam.

Jikin mummy ɓari yake,ta rasa meke mata daɗi,bakinta sarƙewa yake ta dubi nadiya tace"azatona koda bazaki bashi ƙodar ba,zaki tsaya kiyi jinyarshi inma mutuwa zeyi ya mutu agabanki, amma nadiya shine kika baromin ɗan kika dawo"mummy ta ƙarasa mgnr hawaye na biyo idonta.

"wai ko kunnenki be ji da kyau bane nace miki aurefa yayi harda ƴaƴa"cewar nadiya cikin fushi.

"Auran da yayine abun kallo first koko lafiyarshi nadiya?"

Zumɓura baki gaba tayi ta miƙe tace"what ever ma de nidena baroshi,na barku lafiya"tana kaiwa nan tai ficewarta daga falon,ba tare da damuwar komai ba.

Mummy batace komaiba ta lalubo number faisal ƙaninsa bugu ɗaya ya ɗauka,yana gaisheta bata amsaba tace cikin kuka."faisal kayi duk me yiwuwa atanaji private jet,daze kaimu england gobe,ɗan uwanka nacan ze mutu"ta ƙarasa mgnr cikin kuka.

Hankalin faisal ne yayi mummunar tashi, da sauri ya kashe wayar ya taho gida dan yaji meke faruwa.

Daƙyar ta iya tsaida kukanta tai masa bayanin abinda yake faruwa,shuru yayi yana nazari kamin ya miƙe ya fice daga gidan hankali tashe.

Bedawo gidan ba,saida ya tabbatar da jirginsu yazama ready, sannan yadawo ya sanar da mummyn.
.Ranar ba wanda ya runtsa acikinsu,har gari ya waye,suka ɗunguma airport.

Sha ɗaya na safe jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar ta enhland mummy kuka kawai take faisal na rarrashinta.

Sun isa lafiya,direct asibitin suka wuce dan suga halin da yake ciki.

Mahboob sanda yay arba dasu kuka yasa,gaba ɗaya sukai kansa suna kukan suka rungumeshi,

"mummy kiyafemin nasan kinji komai ki gafarceni"cewar mahboob daƙyar sakamakom ciwon dayaci ƙarfinshi.

"baka da lafiyar da zamuyi wannan maganar mahboob,bama itace gabana ba,burina kasamu lafiya ɗana"cewar mummy cikin kuka.

Sun jima ahaka kamin su barshi suje office ɗin likitan nasa suji me ake da buƙata.

Bayan sun gabatar da kansu ne ya musu bayanin ciwon na mahboob tare da basu tabbacin inde baa samu anmasa dashen ƙodar ba ze iya mutuwa.

"doctor agwadamu aga ko zamu ya bashi "cewar faisal yana kuka.

Kwantar musu da hankali yayi sannan ya kira nurse ya haɗasu da su,suka tafi ɗakin gwajin.

Anyi duk abinda yadace sede daga mummyn har faisal ɗin ba wanda ze iya bashi dan duka suna da matsala.

Ranar sunyi kuka kamar zasu mutu,sabida tausayim mahboob wanda inba taimakon Allah ba sunsan rasashi zasuyi.

"mummy abada sanarwa a social media a can nigeria nasan zaa samu me bashi mummy in kikasa maƙudan kuɗaɗe mummy inada tabbacin zaa samu"cewar faisal cikin ƙarfin hali.

Mummy ta gamsu da bayanin faisal dan haka ta bashi umarnin ayi hakan.

Ayko kuɗi ya biya bloggers,cikin awanni kaɗan ko ina ka duba posting ake da hoton mahboob ɗin kwance cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai.wanda duk me imani in yaganshi seya tausaya masa..

**********

Fanan tsawon lokacin data baroshi bata da kwanciyar hankali,ganin ko flashing be taɓa mata ba bare ya kirata, se ta ɗauka yayi fushine,gashi taga ya jima bezo online ba,kuma inta kirashi bata samunsa,sosai hankalinta ke tashi.

Tanaji kamar ta koma amma bazata iya zama gu ɗaya da nadiya ba wacce tasan tana can ɗin.

Tafe take kan instagram tana ɗan ɗebe kewa kwatsam taci karo da abinda yay matuƙar razanata,hotunan mahboob ana neman me bashi kyautar ƙodar da zaa dasa masa yaci gaba da rayuwa.

A gigice ta miƙe tana haɗa hanya,ko gabanta bata gani sunam Allah kawai take kira ta nufi,ɗakin da yaranta ke ciki suna ta wasansu ,bata tsaya tunanin komai ba ta kwashesu,ta ɗauko jakar dasukazo da ita wacce tunda tazo nigeria madarar ƴaƴanta kawai ta cire aciki,ta rataya,ta ɗauki ATM wanda ya kasance na Mahboob ne.

Megadin gidan tajewa aruɗe kan yasamo mata taxi,ayko haka ya mata dan besan meke damunta ba,fatan adawo lfy ya mata ta fice.


Duk yadda taso barim ƙasar aranar hakan besamuba seda ta kwashe kwananki uku kam tasamu ayiwa ƴaƴanta visa,suma saida ta saki mahaukatan kuɗi sanan tasamu biyan buƙata jirgi ya ɗaga dasu zuwa ƙasar ta england.



muje zuwa.

*07044600044*
[10/12, 10:37] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*54*




Sun isa lafiya direct gida ta fara xuwa ta ajiye yaran dan sunyi waya dame renonsu ta shaida mata tana gidan har yanzu.

Tana dire yaran ta wuce asibitin,hankalinta atashe,koda ta isa su mummy basa ɗakin da yake, dan haka ta ƙarasa inda yake da gudunta.

Tana zuwa ta faɗa kanshi tana kuka,da sauri mahboob wanda kejin muryar kamar a mafarki ya buɗe idanunsa ayko suka sarƙe ana juns,wani murmushine me cike da zallar farinciki ke bayyane kan fuskarsa,yayinda itako kuka kawai take,tana ƙara shiga jikinshi.

"da rabon zamu gana dama habibty,"ya faɗi yana murmushin ƙarfin hali

hannu tasa ta rufe masa baki tana kuka tace'Ban sani bane mijina kayafemin dan Allah,kuma insha Allahu rayuwarmu tare da saura bazaka mutu yanzu ba"ta faɗi tana rungumoshi.


Share hawayenta tayi ta nufi office ɗin doctor,gabatar da kanta tayi as donor,ayko doctor yasa aje a gwadata,cikin hukuncin Allah ita ba matsalar komai zata iya bashi.

Farincikin da tayi dajin hakan be misaltuwa.

Su mummy suna harabar asibitin likitan ya kirasu ya shaida musu, ansamu donor,wayyo mummy har faɗuwa take gurin tasowa da gudu,faisal ne ya ruƙota, suka nufi office ɗin doctor ɗin.

Basu damu da sanin koma waye donor ɗinba,sude kawai fatansu ayi aykin dan haka hannu sukasa atakarda,suka baro office ɗin,kan suje ga mahboob wanda besan wainar da ake toyawa,ba tuni an kaishi ɗakin tiyata,shiyasa basu haɗu dashiba.

Acikin Awannin da basu wuce biyar ba har anyi dashen ƙodar da aka ciro ajikin fanan cikin nasara,aka kaisu ɗakin hutu.

Mummy kukan farinciki tayi tayi har muryarta ta dashe,ta rasa da wanne baki zatayi godiya,hawaye kawai ke biyo idonta na murna.

********

Acikin awa ashirin da huɗu mahboob ya farka,a hankali yake magana,da sauri suka rufu akanshi dan suji me yake cewa.

"kutaimaka ku nemomin fanan,tazo asibitin nan amma tace zataje ta dawo amma bam kuma ganinta ba"ya faɗi da ƙyar.

"wacece kuma fanan yaushe tazo nan ɗim?"cewar mummy.

"matar dana aura mana mummy,uwar ƴaƴana tazo jiya nan"

"Da da kake ciwon uban me ya hanata zuwa gaidaka,se jiyan,in ta damu dakai, to wlh xanji da ita da kaina"cewar mummy cikin fushi.

Mahboob bece komai ba mummy taci gaba da faɗanta har ta gaji tai shuru.


Anata ɓangaren fanan itama ta farka kuma garau take jinta kamar baa cire wani abu ajikimta ba.

Likitan ta tambaya jikin mijinnata ya shaida mata da sauƙi. sosai.

Me aykinta tazo har asibitin da yaran dan suna ta kuka basu ganta ba sunƙi cin abinci sosai ayko haka nurse suka gyara mata zama ta shayar dasu nono,ayko suka ɓingirr anan suna bacci,ranar yini sukai asibitin se dare suka koma gida shima seda aka bari sunyi bacci sannan aka ɗaukesu.

**********

Tsawon kwana bakwai da musu aykin kowa ya samu sauƙi dan mahboob har yawo yake fita a harabar asibitin damuwar rashin fanan ce ke hanashi sukuni.


Suko su mummy kusan kullum se sunje sun gaisheta da jiki a matsayin donor ɗin data taimaki ɗansu..

Sosai suka saba da mummy da fanan batare da mummy tasan itace matar ɗan nata ba.





muje zuwa.

*07044600044*
[10/12, 12:09] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*55*



"Mummy ya kamata ku kaini ingaida donor ɗin nan tawa mana,tunda nasamu sauƙi zan iya zuwa."cewar mahboob yana murmushi.

"badamuwa zakaje amma ka bari se anjima da dare se mu kaika kanmu tafi masaukinmu"cewar mummy.

"au baku sauka agidaba mummy se masauki?"mahboob yatambaya

"wallahi shugaban ƙasarmu ne yace na sauka gidan gomnati kawai base nasha wiyaba shine yasa,amma tunda kasamu sauƙi semu zauna agidan naka kanmu koma gida."

Haka de sukai ta taɓa hirar su kan mummy tafice daga ɗakin zuwa na fanan.

Da faraa fanan ta tarbeta lokacin ankawo yaranta tana basu nono,cike da mamaki mummy tace"ayya kice shayarwa ma kikeyi ashe?"

A kunyace fanan tace"eh wlh,baa barinsu tare danine yasa bakya ganinsu".

Cike da shaawa mummy ta ɗauki yaran ɗaya bayan ɗaya tana ajiyewa mamaki fall fuskarta tace"da mun haɗa jiɓi,dake da se ince wainnan ƴaƴan ƴan uwan ƴaƴanane sabida kamar tasu har ta ɓaci"

Murmushi fanan tayi tace"ayya ikon Allah kenan"

Sun jima suna hira akan yaran kamin mummy tace"ƴata kin taimaki ɗana amma har yau baki faɗi nawa zamu biyaki ba duk da bazamu iya biyanki ba amma de ɗan ihsanine baki sanar damu ba".

"mummy ni banzo garin nan dan sanarwarku ba,kawai nazone dan duba jikin mijina inbashi gudunmawar da nake ganin zan iya bashi shine dalilin zuwana mummy".

Cikin rashin fahimta mummy tace"ayya kice kema kina da mara lafiya amma baki taɓa faɗa mana ba bare muje gaisheshi"

Gyara zama fanan tayi sannan tace,ba tare da tsoron komaiba,"mummy ki gafarceni,bisa shigowa rayuwarki data ƴaƴanki batare dana nemi izininkiba,mummy mahboob ɗanki shine mijin nawa kuma uba ga wainnan ƴaƴa dake hannumki,"ta ƙarasa maganar a raunane.

Mummy kasa cewa komai tayi dan batun ya girmameta,miƙewa tayi tsam ta fics daga ɗakin ɗauke da yaran guda biyu tabar ɗayar agun fanan ta wuce ɗakin mahboob dake zaune sina hira da faisal da doctor baɗa dan shima yazo dubashi.

Tana shigowa da yaran mahboob ya miƙe da sauri yace bakinshi na rawa"mummy kinga fanan ɗinne,ay nace miki tazo rannan"ya faɗi yana ƙoƙarim amsar yaran.

.Guri mummy tasamu ta zauna tace,hawaye na biyo idonta"mahboob fanan matarka ashe itace donor ɗin data ceto rayuwarka"ta faɗi tana hawaye.

"what! mummy nufinki ƙodar fanan ce ajikina?"cewar mahboob jikinshi na ɓari

"hakane mahboob,nima se yanzu ta sanar dani matsayinta agunka dana nemi ta faɗi nawa takeso inbata."

"Mummy ki kaini gunta dan Allah"cewar mahboob yana sunbatar ƴaƴan nashi.

"muje yaya inkaika"cewar faisal yana jan rigar mahboob ɗin.



Ba musu suka bishi abaya da doctor bala zuwa ɗakin da fanan ɗin ke ciki.

Cike da mamaki yake kallonta itako se murmushi take masa me kashe zuciya,da sauri ta taso ta ƙaraso gabansa ta rungumeshi tace"Allah na gode maka daka rayamin mijina"ta faɗi hawaye na biyo idonta.


Su faisal ne suka amshi yaran shima ya rungumeta da ƙarfi kamar wani ze ƙwace masa ita..


Sun jima ahaka kan su saki juna su zauna,mahboob riƙe da hannunta yace"ke alkhairice agarenj fanan najima dajim hakan ajikina,kinmin komai baby ina miki son da inbanda Allah ba wanda yasan ƙima da darajarsa azuciyata,fanan kece komai nawa."

Mintsininshi tayi tace"kacika surutu babe"dariya duka suka saka ana tsokanarshi.

*******


A ranar aka sallamesu a asibitin mummy kunyar fanan takeji, ta rasa da wanne ido zata kalleta,yau gashi ƴar talaka tai mata abinda kuɗinta ya gaza yimata,ƴar masu kuɗin datakeso ƙarshe guduwa tayi ta bar mata ɗan nata.

Har sukazo gida mummy batacewa komai sede ido,haka ta shige ɗaki,fanan da mahboob suma ɗakinsu suka shige faisal da doctor bala ko gari suka koma .

"baby tsorofa nakeji kaga mummy batace komaiba har yanzu kallonmu kawai takeyi"cewar fanan aɗan tsorace.

Murmushi mahboob yayi ya rungumota yace"ay munyiwa mummy 2 :0 kunyace tasa mummy kasa magana bawai haushinmu takejiba,kiduba kiga taranma fa na gurinta,kina ganin in fushi tayi zatayi hakan"ya faɗi yana shinshina wiyanta.

Dariya tayi mara sauti tace"nide duk hukuncin da zatamin ma zan ɗauka ta taimakeni tabarni in ƙarasa rayuwata anan"ta faɗi gamida ɗora kanta kan ƙirjinshi.

Rungumeta yayi yana faɗa mata kalamai masu daɗi.

*********


Wata guda suka share bayan samun sauƙinsu sannan sukayo gida nigeria gaba ɗaya,a ɗam zamansu tare mummy ta fahimci fanan yarinyacr me tarbiyya da sanin darajar mutane ko kaɗan bata da hayaniya hakanne yasa take ɗan sakin jiki da ita.

Koda suka dawo nigeria,agidan mummy suka sauka,ba yadda mahboob beyi da ita ta barsu su tafi nasu gidanba taki,acewarta wani satin zaayi zaɓe dan haka dole

12 / 13