Author : Zahra Muhammad Surbajo Category : Arewa Pen
tunda tafiyace ta rukuni,"
"inaga mantawa yayi ay masa afuwa mummy"
"Ba komai bala Allah dawo dashi lafiya amma kadinga masa faɗa dan Allah gaba ɗaya yaron ya sauya ba yadda yake da ba"
"Insha Allahu mummy zanyi iya yina"
Sun jima suna hira,kamin yamata sallama ta tafi,yana hanya yana ƙara godewa Allah da baaji mutuwar sarki a bakinsa ba.
******
Saida suka kwana biyu a england sannan ya buɗe wayarshi ya kira mummy inda tai ta masa faɗa yana bata haƙuri,ƙarshede suka shirya tsakanin ɗa da uwa sai Allah.
Koda ya kira nadiya ƙin ɗaukar wayar tayi,saida ya bata 10 missed call bata ɗaga ba,ayko yana kashewa ya matsa numbarta a black list,yayi blocking ɗin a social media handles ɗinsa duka,dan yaji haushin hakan,data masa shi yafiso koma menene ya haɗasu to banda gaba amma ita taƙi gane hakan.
Fanan wacce tunda ya fara wayar tabar gurin dan bashi damar ganawa da iyalinshi,dawowa tayi taga yanayinsa cikin ɓacin rai,bata bi baasin me ya ɓata masa ba,taje ta kwanta ajikinshi tace,"baby kasan wani,abu,?"
Girgiza mata kai yayi bece komaiba,amma ya bata natsuwarshi dan zatonshi labarine me tsayi zata bashi,gyara zaɓa tayi taci gaba da cewa"baby ina sonka wallahi"
Wani sanyi yaji azuciyarshi ya rungumeta a jikinshi yace"nima haka habibty"ya faɗi yana shinshina wiyanta.
Ayko cikin salon mu na mata ta ɗauke hankalinshi daga barin tunanin damuwar daya shiga,suka faɗa wata duniyar ta so da ƙaunar juna,bata barshiba saida ta tabbatar da ya dawo mahboob ɗinta.
*****
Tun daga wannan rana kullum seya gaisa da mummy amma be ƙara kiran nadiya ba,
Itama anata ɓangaren ko bi ta kanshi bata yi dan ya ɓata mata rai kuma tasha alwashin saita jashi aƙasa,tunda beda mutunci,nida ke gefe nace anya kuwa nadiya.
muje zuwa.
*07044600044*
[9/29, 06:50] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra surbajo*
*46*
Tsawon watanni shida kenan da tafiyar tasu, cikin fanan na wata tara yanzu,gaba ɗaya ta kumbura,ko tafiya da kyar take yi,saida taimakon mahboob,tausayinta yake ji,kamar ya amsar mata cikin ya maidashi jikinshi.
Kullum yana gaisawa da mahaifiyarsa da ɗan uwansa faisal,amma nadiya koda wasa be ƙara neman numbarta ba,saidai duk ƙarshen wata yana tura mata maƙudan kuɗaɗe,ta hannun amininsa doctor bala.
Yauma kamar kullum tana zaune kan carpet
shikuma yana matsa mata ƙafafunta da take kukan suna mata ciwo.
"habibty bafa daidai bane ki ƙi amincewa ay miki scanning,dan de kawai banason ɓacin ranki ne yasa na barki amma wlh banajin daɗin hakan ko kaɗan."cewar mahboob cikin yanayi na rashin jin daɗi.
Langaɓe kai tayi tace kamar me shirin yin kuka"kayi haƙuri mijina,dan Allah wlh banaso aje ne afara lissafo matsaloli,shiyasa nake tsoron aymini"
"Fanan wacce matsala kuma,komai fa ki dinga ɗarsa alkhairine aranki se Allah ya dubemu,"
"Cikin nawane yayi girma da yawa baby,sannan ni ban taɓa ganin me cikin dayakai girman wannan ba,shine yasa nake ganim nawa da akwai matsalane yasa hakan"ta faɗi hawaye na biyo idonta.
Sakin ƙafafun nata yayi ya rungumeta ajikinshi yace yana shafa gadon bayanta"ba haka abun yakeba habibty,wannan cikin naki baki da tabbacin ko ɗa nawa ne aciki,in yafi ɗaya zeyi girma mana innkuma ɗayane zaki ganshi ƙato,dan haka ba matsalar komai kinji ko,anjima da dare muje adubamin ku dan Allah ki amince"ya ƙarasa mgnr cikin magiya.
Murmushi tayi tace "to baby zanje amma dan kai kawai"
"godiya nake amaryata"
Daga haka lamarin ya fara sauyawa,ɗagowa tayi ta dubeshi a marairaice,zatayi magana ya rigata da cewa"in baki baniba ina zani in samu,dan Allah ki sammin wlh bazan wice 30minutes ba pls"ya faɗo kamar marayan daya rasa uwa yanzu yanzu.
Haka ta barshi yayi yadda yakeso,dan tasan bata da hujjar hanashi kanta dan kawai cikinta ya tsufa, ta galabaita sosai kan yasami biyan buƙatar .
Daƙyar ya taimaka mata suka koma ɗakinta dan a falo aka kwashi dabgen.
Bayanta taji ya riƙe mata,ayko ta durƙushe agurin tana yarfe hannu,tun tanasa ran abun ze lafa amma ina gaba ma yakeci.
Hankalin mahboobne ya fara tashi,ganin halin da take ciki,da sauri ya ɗauko mata doguwar riga ya zura mata shima ya saka,ya sunkuya yasa dukkan ƙarfinsa ya kinkimeta,dan ta kasa koda miƙewa ne.
A mota yasata,yaja da mahaukacin gudu suka fice daga gidan zuwa asibiti,itako fanan ita kaɗai tasan azabar da takeji,murƙususu kawai take tana kiran sunan Allah.
Suna isa asibitin aka karɓeta,sakamakom anan yake ayki ɓangaren ƙwaƙwalwa.
Dubawar farko likitar ta sanar dashi haihuwa zatayi,dan haka bashi hula da face marks sukayi yasaka aka shige labour room da ita.
Injinan scanning ɗin suka sa mata inda ya nuna zata haifi ƴaƴa uku biyu maza ɗaya mace kuma komai lafiya lau.
Mahboob bata kan scanning ɗin yake biba hankalinshi nakan matarshi ganin yadda take shan azaba gaba ɗaya ya firgice.
Saida aka kwashe awanni biyar bata haihuba,tun mahboob na ɗaurewa ƙarshede fashewa yayi da kuka,yana riƙe da hannunta.
Itama salati kawai take da duk adduar datazo bakinta,yace aymata cs sunce zata iya da kanta.hakanne yasa ya haƙura.
Ayko cikin hukuncin Allah ana haka saiga kan ɗa ya faso,ƙanƙameshi tayi tana addua da kuka duka atare,shima kukan yake kashirɓan,dan har jiri jiri yake gani .
Tana wani nishi me ƙarfi ɗan ya fito,ko numfasawa batai ba ɗayan ya kunno kai shima,inda mahboob ya cika da mamakin ganin hakan,shima be jima ba,ta macen ta kunno kanta itama,
Tana haifarta taji duk wani ciwo ta dena jinsa,wani irin sanyi taji ranta inda ta ɗaga hannu sama tana godewa Allah.
Shiko mahboob tuni ya faɗi yayi sujudushshukur ga Allah bisa kyauta da ƙarin da yay masa.
muje zuwa.
*07044600044*
[10/1, 08:55] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra surbajo*
*47*
Tun a asibitin ya shaidawa su yaya kabeer da doctor bala batun haihuwar fanan,sosai suka tayashi murna.
Basu jima sosai ba aka sallamesu zuwa gida cike da farincikin haihuwar,in banda albarka ba abinda yake sawa fanan ɗin,tun tana amsawa har tadena sede murmushi.
Bayan sunje gida Da kansa ya taimaka mata tai wanka da ruwa me zafi,ya ɗan gasa mata jikinta.
Su duka biyun suka yiwa ƴaƴansu wanka atare,dik da ba iyawa sukayiba a tsorace duka suka wankesu.
Bayan natsa ne aɗakin baccinsu tare da ƴaƴansu mahboob yace"fanan lokaci yayi dazan sanar da iyayena batunku,wannan farinciki da nake ciki baze yiwu in ɓoyeshi ba,wallahi son da nake miki a halin yanzu raina fansane ga rayuwarki baze yiwu inta ɓoyewa ba,tun kina ke ɗaya yanzu kun zama huɗu,wallahi bazan iyaba"
A sanyaye ta kalleshi tace"baby tsoro nikeji hajiya ta rabamu,wallahi zan iya mutuwa,in haka ta faru"ta faɗi hawaye na biyo idonta.
"dole mufi ƙarfin tsoron mu fanan,ki zama cikin shiri,kuna ɗan ƙara ƙwari zamu tafi gida,baze yiwu inci gaba da ɓoyeku ba."
Shuru tayi batace komaiba,dan ita gaba ɗaya tsoro ya gama kamata,dan tasan tsanar da ta nuna mata farkon haɗuwarsu ba abune na wasa ba.
********
Yaran sunci sunan mahaifinsa da mahaifin fanan yayinda ƙaramar akasa mata sunan mummy,suke musu inkiya da,hameed,haneef,se haneefa.
Kulawa ta musamman mahboob ke basu,dan har ƴar ayki baturiya ya ɗauko ma ta dake tayata kulawa da yaran.
Wani kyau fanan tayi na musamman kamar me rayuwa a ruwa.Kullum suna waya da yayyanta suna ƙara nuna mata yadda zata kula da kanta kuma tanayi.
Mahboob yashiga damuwa sosai sakamakon rashin tsarkin fanan,dan ya saba tunda suka zo england ba ranar banza seya kwanta da ita,to yanzu jinin haihuwa ya hana,shiyasa gaba ɗaya ya takura.hakan ne yasa ya koma tsohuwar taadarsa tashan giya dan ƙauracewa zina.A boye ba tare da fanan ta sani ba.
Yau tun safe da suka baro ɗakin mahboob basu koma ba shi kuma be fito ba jin shurun tayi yawane yasa fanan zuwa ɗakin nashi dan taga meya hanashi fitowa.
Yayi nisa gurin kwankwaɗar giyarsa,ko kaɗan beji shigowarta ba,dan besom zubawa ma a cup kwalbar yake ɗagawa yana sha,
Sabida jiya da mahaukaciyar shaawarta ya kwana,duk da tana iya bakin ƙoƙarinta wajan ganin ta kwantar masa da hankali da ƴan dabaru amma shi yafiso ya nutsa ciki gaba ɗaya.
Fanan na shiga ɗakin tai arba dashi riƙe da kwalbar giyar yana sha,agigice tace"mezan gani haka?"ta faɗi lokacin data zube kan ƙafafunta tana kuka.
A gigice ya buɗe idonsa da sukai ja ya saukesu akanta Rasa abinda zeyi yayi kawai seyayi ƙasa da kansa,be taɓa danasanin giyar dayakesha ba se yau,wata irin kunyace ta kamashi da kuma tsoron matakin da fanan zata ɗauka akansa .
"dama kai mashayin giyane ban saniba?"ta faɗi cikin kuka.
"kiyi haƙuri dan Allah fanan"ya faɗi araunane.
Tashi tayi ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake cewa komai ba.
muje zuwa.
*07044600044*
[10/1, 09:26] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra surbajo*
*48*
Mahboob sake ruɗewa yayi ganin ta fice ta barshi,tashi yayi da ƙyar ya kwashe giyar dake cikin fridge ɗinsa,yaje toilet ɗinsa ya farfasata,yama rasa yazeyi kawai ya dawo ɗakinsa ya zauna yayi shuru yana tunanin mafita.
Tun daga ranar fanan ta sauya masa,daga gaisuwa bata sake kulashi,hatta yaran ta hanashi ɗaukarsu,daya shigo zata haɗe rai ta nuna bataso ya taɓa mata,gashi taƙi bashi damar kare kansa gameda laifin nasa.
Saida suka kwashe kwanaki 21 a haka,gaba ɗaya mahboob ya fice hayyacinsa,ya rasa meke masa daɗi,itako fanan tai masa hakane dan tasamu yadena shan giyar,kuma a binciken datake in ya fita gun ayki ta tabbatar da yadena sha,dan kwalaben daya fasa a toilet ɗinxa ma ita ta kwashesu.
Yayinda ta duƙufa kuma gun gayawa Allah ya shirya mata shi yadena abinda yakeyi.
Yau da wuri ya baro office dan so yake yazo ya nemi yafiyar fanan,dan yanzu jiyake kamar ya kashe kansa dan baƙin ciki.
A falo yasameta tanawa yaran wasa akan abun wasan su,suna dariya tunda yanzu kwanansu arbain da biyar.
Tsayawa yayi yana kallonsu cikin so da kaunar juna yanaji kamar yaje ya rungumesu amma yana tsoron meze biyo baya.
ɗagowa tayi ta kalleshi sosai tausayinsa ya kamata,ganin yadda ya koma kamar bashiba.
A hankali ya ƙaraso gabanta,ya zauna kusa da ƙafafunta yace a sanyaye"Fanan laifina tsakanina da Allah nane,kuma na tuba nasan ze yafemin,amma ke kin hana komai yamin daɗi,fanan kamar dama jirana kike ki kamani da laifi,kinsa na fara tunanin kashe kaina fanan,yakamata ki yafemin don Allah wallahi ƙarfin shaawarkine yasa ni ci gaba da shan giya duk a ƙoƙarina na kaucewa zina,dan tun kan mu haɗu inasha,kuma bayan munzo nan ban ƙara shaba saida kika haihu,wallahi nadena fanan"yafaɗi muryarshi na rawa.
Hawaye kebiyo idonta,ta dubeshi tace"watakan zaka kashe mana kanka baby,yakakeso to in fuskanci duniya da wainnan ƴaƴan,me kakeso in faɗa musu in suka girma?wallahi duk ranar da kabari zuciyarka ta fara tunanin aykata hakanma ban yafe maka ba"ta faɗi cikin matsanancin kuka.
A tsorace ya rungumota jikinshi dan zatonshi zata tureshi,se yaga ta ƙanƴameshi tana kuka.
Shima rungumeta yayi,yana rarrashinta tare da mata alƙawarin baze kuma ba.
Wannan rana mahboob jinta yayi kamar ranar aka kawo mishi ita,dan farin cikin shiryawar da sukayi,gashi tayi arbain ayko ankwashi dinner a wannan dare.
Tunda suka shirya mahboob yadawo hayyacinshi ya dawo mahboob ɗinshi,yayi fari da ƙiba ta musamman dan fanan na bashi duk kulawar data dace.
********
"Ki shirya gobene tafiyar,tunda shi bezoba toke seki bishi,nasa an binciko address ɗimsa kawai suprise zaki bashi,tunda shi beda hankali"cewar mummy lokacin da nadiya tazo gidan sakamakon kiranta da tayi.
"mummy nifa gani nake kawai ki ƙyaleshi zezo dan kansa,amma in na bishi gani zeyi na damu dashine wallahi"cewar nadiya a baki amma acan ƙasan zuciyarta ba ƙaramin kewar mijin nata takeyiba.
"dole zakije gobe nadiya dan haka ki zama cikin shiri,na yanke hukunci"cewar mummy.
Ayko nadiya cike da farinciki tay wa mummy sallama ta wuce gidanta taje takimtsa kayanta,ta waya tai sallama da iyaye da ƴan uwanta.
Da safe direban mummy yaje ya ɗauketa yakaita airport,batasha wahalar komaiba dan private jet ne,kasancewarta na ƴar mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar.
Jirgin nadiya yaɗaga da ita zuwa ƙasar england sede addua da fatan Allah kaita lafiya.
muje zuwa.
*07044600044*
[10/3, 10:45] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra surbajo*
*49*
Da wuri mahboob ya fita gun ayki yau,bayan fitarshi,kamar kullum fanan zaune a falo ita da yaranta tana musu wasa,se dariya sukeyi abun gwanin burgewa.
Turo ƙofar falon akayi aka shigo,ba tare da sallama ba.
A gigice fanan ta ɗago kai dan ganin me shigowar,se a lokacin ta tuna bayan fitar helen me tayata reno bata kulle ƙofar ba.
Nadiya ce tsaye suna kallon kallo.hankalin fanan inyayi ya tashi da ganinta,hantar cikinta sosai ya kaɗa dan tasan nadiya a hotunan bikinsu da mahboob.
"ke wacece?"cewar nadiya cikin isa da ƙasaita.
Mazewa fanan tayi tace"sallamace"
Yatsina fuska nadiya tayi tace"nan ba gidan mahboob bane?"
Banza da ita fanan tayi ba tare data bata amsa ba.
Hakanne yasa nadiya cewa"salam"
"Wasalam"fanan ta bata amsa,
"inason amsata nan gidan vana mahboob bane?"nadiya tasake faɗi.
"gidansane akwai matsalane?"cewar fanan dan ta kauda tsoronta aranta gudun taga gadon baccinta.
"toke me kike agidansa,harda wasu tarkacen yara ke wacece?"cewar nadiya cikin fushi.
"ni matarsa ce uwar ƴaƴansa,yara kuma duk tarkacensu agidan ubansu suke,kinga shi baze ga sun yi tarkaceba ay"
Wawan marin da nadiya ta ɗauke fanan dashins yasata yin shuru bata shirya ba"karki kuma faɗamin wannan zancan banzan,mijina nice kaɗai mallakinsa bayan ni bashi da wata mata dan haka ki kiyaye kafin nasa ki raina kanki."
"kinyi kuskuren marina,amma na baki bashi,duk ranar da kika kuma gigin kai hannunki jikina zakisha mamaki"cewar fanan a kausashe,tana kaiwa nan ta tura ƴaƴanta suka bar falom zuwa ɗakin mahboob ɗin suka barta tsaye ita kaɗai cikun wasiwasi.
Fanan na shiga ɗakin,wayarshi ta kira,ayko cikin faraa ya ɗaya wayar,yace"daɗina ya akayine?"
"Lafiya lau baby,dama baƙuwa kayi daga nigeria"ta faɗi a tausashe.
Shuru yayi yana ɗan nazari kamin yace"nadiya ko?"
Asanyaye tace"eh ehtace"
Runtse ido yayi ya fesar da iska sannan ya buɗe yace"Ganinan zuwa gidan,kinji ko"yana faɗin haka ya kashe wayar ya miƙe,ya nufi gidan ransa na masa susa,
Nadiya ko se safa da marwa take afalon gidan ranta na mata zafi,kanta gaba ɗaya ya kulle ta rasa mezayi ma,
Minti talatin ya sadashi da gidan nashi,da sauri ya fito amota,ya shiga falon.
Da sauri nadiya ta waiga dan taga waye,mahboob ne tsaye yana binta da kallo.
Bece mata komaiba ya sa kai ta wuceta zuwa gun fanan,dan yaga awanne hali take.
A fusace nadiya ta mara masa baya yana shiga ɗakin itama ta shiga tana huci tace"ni zaka gani ka wuce mahboob,wallahi nafi ƙarfin wannan wulaƙancin,kuma yanzu base anjimaba inaso insan wannan kucakar,zaman me take agidannan nan wacece ita da wainnan yaran?"ta faɗi afusace.
Mahboob rai aɓace yace"zaman aure take agidan nan kuma matatace yara kuma nawane"ya bata amsa batare da tunanin komaiba.
Bakinta har karkarwa yake tace"nufinka kayi aure ba tare da sanin hajiya ba ko wani naka,?ni ka yaudara?"ta faɗi hawaye na biyo idonta
"da sanin wani koba da sanin waniba wannan ba abune daya shafekiba,matade tawace kuma ƴaƴamma haka,banason tashin hankali yasa nazo da iyalina nan,in har kinsan shiyakawoki to zo na maidaki airport ki koma"ya faɗi yana nuna mata hanya.
"wlh ƙaryane mahboob baka isaba ka tozartani,ba inda zani,haba nayi mamakin rashinnkulani bayan kazo nan ashe ka ajiye madadine anan,to wlh baze yiwuba dole hajiya ta zaɓa maka wacce tafiso dan wallahi bazan zauna da kishiyaba"
"kanki akeji nide na gama magana duk ma wanda zaki faɗawa ki faɗa masa matata ce uwar ƴaƴana"yana kaiwa nan yajata sika fice daga ɗakin tana kuka,be ajiyeta ko ina base spair ɗakin gidan,kan gado ya wurgata sannan ya bita ya danne tana ƙoƙarim tashi.
muje zuwa.
*07044600044*
[10/7, 09:57] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra surbajo*
*50*
"ka ɗagani mayaudari ba abinda zaka faɗamin inngamsu dan cutade ta gidan duniya kagama yimin ita,ka ɗagani nace!"cewar nadiya cikin ƙaraji.
Ɗagatan yayi kamar yadda ta buƙata,sannan ya zauna itama miƙewa tayi ta zauna tana ci gaba da kukanta.
"tun kan na aureki nake tare da fanan nake sonta,amma haka na daure na barta na aureki,sai daga baya naje na aureta itama,kuma kamar yadda kike gani har haihuwa mun samu,dan haka kiji da kyau,ba keba wallahi ko hajiya bazata rabani da ita ba,dama naso rarrashinkine bawai dan ki rufamin asiriba,sedan kawai anmiki kishiya baki sani ba,"Cewar mahboob ba tare da damuwar komaiba.
"Wannan damuwarkace amma ni wallahi sai anyi duk balain da zaayi bazam zauna da waccan abar as kidhiyataba,dan wannan cin mutumcine"ta faɗi tana hawaye.
"agurinki kenan amma ni agurina tazo ayadda nakeson mace tazo, bata da wani aybi dan haka kisan me zaki dinga faɗi akanta,kuma balai da kike kiran zaayi to ba anan gidan ba sede ko ki koma inda kika fito se ayi balain acan amma anan baze yiwu kizo ki ɗaga mata hankali ta kasa shayarmin da ƴaƴa da kyau ba,"
"Au mahboob har gorin haihuwa kakemin?"ta faɗi afusace.
"duk yadda kika ɗauka nide na faɗa miki"yana kaiwa nan ya tashi ya fice daga ɗakin ba tare daya sake bin ta kanta ba.
Kifewa tayi agurin tana kuka me tsuma zuciya ta rasa akan me ya kamata tai tunani.
Shiko yana fita ɗakin fanan ya koma inda ya samu bata ciki sede me renon yaran tare dasu,juyawa yayi zuwa kitchen inda yasamu tana haɗa abinci.
Ta baya yaje ya rungumeta ya ɗora kanshi akan wiyanta yana ɗan jujjuyata,yace cikin raɗa"baƙya gajiya ko madam,har kin shigo kitchen"
Shafo fuskarshi tayi tana murmushi tace"ga baƙuwa munyi ay dole azo ay mata girki ta ɗauko hanya"ta faɗi tana murmushi.
Juyo da ita yayi ya na murmushi tabbas fanan ɗinshi ta mori hali,shiyasa yake sonta,"kina da kirki sosai,maza to ki kammala bari inje inyi wanka dan bazan koma offics ba senaga yanayin zaman naku."ya faɗi yana murmushi.
Itama murmushin tayi tace"dama kaje kawai baby,zan kula matsala bazaa sameta daga ɓangarena ba"
"nasani fanan barni de inzauna daku hankalina zefi kwanciya"yana kaiwa nan ya mata kiss a goshi ya wuce
Ci gaba tayi da girkin nata,har ta kammala ta shirya komai akan dinning sannan ta wuce ɗakin nashi dan tayi wanka acan ta kimtsa tunda aɗakin tana da kayan sawa.
koda ta shiga samu tayi yana shirin shiga wankan kallo ta bishi dashi tace"Meya hanaka yin wankan tun ɗazu?"
Murmushi yayi ya kamota yace "ke nake jira kizo kimin ya faɗi rungumta.
Batace komaiba dan tasan bazaa wanye lafiya ba agurin wankam.
Ayko ilai suna tsaka da wankan suka katse akazo aka raya sunna sannan aka koma toilet ɗin cike daso da ƙaunar juna.
Bayan sum fito sum kimtsane suka rankaya zuwa ɗakin da nadiya ke ciki hannayensu riƙe da juna.
muje zuwa.
*07044600044*
[10/9, 09:02] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra surbajo*
*51*
Nadiya binsu tayi da ido kawai,dan abinda ya girmeka sede ka kalleshi,bakinta ya gaza cewa komai.
Kan kujera sukaje suka zauna,sannan mahboob yace"Nadiya,dake da fanan,makullan sirrinane,sabida ku matanane,duk wata matsala dazan