Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
jikin Motar suke, had'e da bubbuga jikin Motar suna son cimma na ciki, wasu tsabar naci harda baki suke sawa suna buga jikin Motar suna wani irin gurnani da gunji.
Anam zubewa tai kawai a k'asa tana sa hannunta ta dod'e kunnanta tana runtse idonta, k'irjinta na tsananin bugawa, gabanta sai fad'uwa yake, domin idan tana kallon yadda suke son fasa gilashin Motar su cimmasu zuciyarta na iya bugawa nan take bata shirya ba.
Ba ita kad'ai ba hatta su Asiya an cure waje d'aya ji take dama bata zo wannan tafiyar ba, ko duniya za'a bata kuwa, ai bata d'auka masifar cutar idan ta kama mutum haka yake komawa ba sai yanzu.
Wani birkin Harun yaja yana juya sitiyarin Motar had'e da bata wuta, yana juya kan motar da k'arfin so yake ya zubar da wadda suka mak'ale masu, domin idan bai hakan bama, suna gaf fasa gilassan Motar.
Kusan gaba d'ayansu wa'inda suka mak'ale suka zube a k'asa, wasu nan take ya take su suna ihu da gurnanin nan nasu marar dad'in sauraro.
Sauke lumfashi suka kama saukewa, harda su Abbakar a ciki.
Harun yana kallon kowa ta gefen ido, cike da takaicin wai suma tsoro suke ji kamar dai Matan, amma sai su wani nuna basa ji, cike da takaicinsun yake tokin mai sake furta komai ba.
Sunyi tafiya mai tazara sosai, kamin suka ji direban daya d'akko su daga Airport yana fad'in.
"Akwai taswira a cikin Motar nan a wata durowa dake gaban motar, Captain idan kun tashi neman hanyar zuwa asibitin zaku iya d'akkota domin ta nuna maku hanya.
Ni a nan zaku sauke ni, Allah ya k'addara saduwa".
Jiki a sanyaye Harun yaja birkin Motar ya tsaya, wajan babu kowa sai wata irin iska dake busuwa sai kuma motoci da suka tsaya babu komai a ciki wasu na ci da wuta wasu ko gawawwakin jama'a ne a ciki sun mutu, wasu ma sun k'one k'urmus a ciki, babu gilamar Zombies a wajan, amma wajan daka kallesa zaka shaida an gama da mutanan dake rayuwa a wajan gaba d'aya.
"Amma ni abunda ka ce ya ban mamaki, kai ya akai aka turoka d'aukar mu?, baccin ka ce fad'ar shugaban Goa ta gaza, ya aikai harka k'araso inda muke?, mi yasa zaka ce mu sauke ka nan wajan?"
Cewar Harun yana d'an juyowa yana fuskarta mutunan.
"Tun kamin ku iso nake a Airport d'in, shi yasa koda nabar wajan shugabamu, jami'an tsoro ne suka min jagora har izuwa Airport d'in, da kyar muka iso, duka mu uku ne muka taho tarbarku, a hanyarmu ta zuwa mun had'u da Zombies masu had'arin gaske, wadda har muka rasa mutum d'aya a cikinmu, sai da muka iso Airport d'in tsautsayi ya sake fad'awa akan d'ayan jami'an tsoron, sai ni kad'ai na rage, nima na tsorata, dan haka na sami wannan motar na shige cikinta, na zauna zaman jiranku, ko motsi kad'an banayi, domin tsoro na kar Zombies su fahimci akwai sauran mutum a cikin Airport d'in, domin idan suka jiyo k'amshin mutum to zakai ta ganinsu suna b'allowa tako ta ina, abun na su kamar asiri, duk nesan da suke da kai zasu iya jiyo k'amshinka su taho inda kake.
Allah ya taimake ni har na ga saukar jiragenku shine na fito, ku kuma kuka shigo motar naja muka fara tafiya.
Hak'ik'a da na san abunda zaku ce kenan kuna shirin zuwa asibitin nan, nada baku shawarar kubi jiragenku su koma daku K'asar da kuka fito".
Tashi tsaye Captain Joha yayi kawai suka ga yaci kwalar rigar direban nan yana fad'in.
"Ohhh my God, mi yasa baka bamu duk labarin nan tun farko ba?, da bazamu tab'a barin jiragen da suka sauke mu su tafi bamu hau mun nufi Asibitin da kaketa fad'in hanyar zuwansa akwai hatsari ba, kashhh wallahi kwata-kwata bakai ba Mutanan nan, k'ila ma da had'in bakinku wajan had'a duk wannan masifar".
Da sauri Captain Harun ya mik'e daga inda yake yaje ya kwace direban a hannun Joha yana cewa.
"Miye kake haka Joha?, idan rai ya b'aci hankali ke nemo shi, muyi hakuri kawai amma komai ya riga da ya gama cab'e mana, tun farko bai kamata kawai a turo mu babu cikakken bayanin ainafin yadda zamu fuskanci abun ba, da ba zamu sha wahalar nan ba gaba d'aya. Koda yake na manta Y'ay'an Manyan K'asarmu ne fa a cikin K'asar nan, dole a turomu kawai kara zube, domin mu tarwatsa nemansu kawai, amma ba wai taimakon K'asar suke son muyi ba, ai ba haka ake turo mutane su taimaki jama'a ba".
Anam dake k'asa zaune har yanzu ta tab'e baki tana murgud'a ma Captain Harun shi, yo a banza ma baima san tana yi ba.
Itafa burinta yanzu kawai ta ci karo da y'ar uwarta had'e da Y'an uwanta su Faruk da ma duk wa'inda sukai tafiyar dasu.
Doctor Fahat ne ya ce shima.
"Ya kamata mu bar wajan nan gaskiya, ya kamata idan sauka zaiyi kawai mu sauke shi ya tafi, mu kuma mu kama hanyar zuwa asibitin nan ".
Na'am kawai sukai da maganar Doctor Fahat d'in, suka bud'e masa k'ofa ya fita, Captain Harun ya koma wajan mai toki yaja Motar suka bar wajan, shi kam direban yana d'aga masu hannu ya bar wajan da gudu.
Taswirar Captain Joha ya bud'e inda direban ya ce masu tana nan, ya zaro ta, dogowar takarda ce mai tsayi da fad'i, warware ta suka farayi suna duban zanen dake jikinta.
Su Captain Joha da Abbakar ne suke karanta taswirar domin sun saba duba irinta da ma, a hankali suke karanto abunda ke jikin taswirar............
EPISODE 13
Suna cikin gudu kamar an jefo wani mutum kawai suka gansa a gabansu shima yana faman tik'a uban gudu.
Jan birki yayi yana wani irin hak'k'i kamar ransa zai fita saboda gudun daya sha.
Hanan ce ke kallonsa cike da d'an tsoro ta ce.
"Bawan Allah daga ina?. Gaskiya ni yanzu bazamu sake yarda da kowa ba, yanzu haka an riga da an cije sa, kar mu yarda dashi wallahi".
Faruk zaiyi magana mutunan ya rigasa fad'in.
"Ko kad'an banji haushin abunda kika fad'a ba, kina da gaskiya, nima, Allah ne ya had'amu dan na gaya maku k'ila naga y'an uwanku y'an K'asar ku, sunzo taimakonku domin fitar daku a wannan k'angin da kuke ciki, dama mu kanmu dake cikin k'asar nan wadda basu koma zombies ba. Ni ne wadda ya d'auke su daga Airport har zuwa wani waje inda na sauka, domin su wani asibiti zasu nufa wadda zuwansa akwai had'ari a yanzu.
Zaku iya neman hanyar zuwa wannan asibitin domin had'uwa da y'an uwanku".
Gaba d'ayansu idan ka kalli fuskokinsu cike take da tsananin mamakin abunda mutunan nan yake fad'a, sai kuma y'ar murnar data rufesu akan fuskar tasu.
Kamin Faruk ya fad'i abunda yake son sani kawai idonsa ya hasko masa wani Zombie da yanzu ke kusa da mutanan nan ya basa baya baima san dashi a bayansa ba gashi gaf yake dashi.
K'ara mai k'arfi Faruk ya saki yana son nunama mutanan shi da son yabi a hankali ya goce masa.
Amma ina mutunan rud'ewa yayi yana juyowa gaba d'aya, mai-maikon ya zille masa sai kawai ya tsaya ina fasa ihu duk ya rud'e yama rasa miye ya kamata yayi don ceton kansa.
Al'ameen da Faruk ke k'ok'arin isa inda yake had'e da son taimakonsa, kamin ma suyi tak'o biyu Zombie d'in nan yayi kokan kura ya cafke masa wuyan rigarsa, had'e da kai bakinsa saitin wuyansa ya kafa masa hak'oran nan nasu masu tsinin gaske.
Wata irin kururuwa ya saki mutunan yana karajin zafin uban cizon da Zombie ya danna masa a wuyansa.
K'arshe ma kayar dashi yayi k'asa, suna gani ya fisgo fatar wuyan nasa da k'arfi yana wani gunji yana ci.
Farida da bazata iya ganin irin kisan da za'ai masa ba, da saurinta ta d'an matsa daga wajan zuciyarta na karyewa, hawayen da kullum ke mata zuba sai ta neme su ta rasa, tsabar kukan data ke sha hawayen harsun gaji da zuba a koda yaushe idonta ya bushe.
Suma gaba d'ayansu baya suka ja suna jin yana ihun neman taimako amma babu yadda za'ai su iya taimakonsa.
Wani irin kuka Al'ameen ya saki ma zallar bak'in ciki yana kukan yana fad'in.
"Yanzu dan Allah ya za'ai musan asibitin da zasu nufa?, wannan wane irin bala'i ne?, munga samu munga rashi, mu shikenan haka zamuyita bulayi har sai Zombies d'in nan sun k'arar damu gabai d'aya ne?".
Kowa a cikinsu mamakin kukan Al'ameen yake domin duk cikinsu yafi kowa k'arfin zuciya, amma yau shine yake kuka, lallai yaga tashin hankali.
Bashi kad'ai ba hatta Hanan kuka ta saki na bak'in cikin rasa mutanan nan da sukai a yanzu, wani irin mugun haushin Zombie d'in nan ne ya rufe mata zuciya.
Har bata san lokacin data waiga Allah ya bata sa'a taci karo da wani k'aton dutse ta kinkimesa da kyar, bata tsaya ba ta nufi inda yake k'asa sai cin naman mutunan nan yake.
Baiyi tsammani ba kawai yaji saukar dutse a kansa, nan take ko kan nasa ya fashe jini ya fara zuba, wani irin ihu ya saki yana zubewa babu rai a tare dashi, domin ihun farko daya saki bai sake koda motsi bane.
Sauke ajiyar zuciya suke gaba d'aya, Faruk na duban Hanan yana mata alama da tayi dai-dai wallahi, kamin Al'ameen ya ce.
"Ai wallahi da ke baki kashe sa ba, ni ne nan wadda zan kashe sa, domin dama nayi niyar Allah bamu barin wajan nan sai na halaka wannan Zombie d'in da yayi sanadiyar mutuwar wannan bawan Allahn".
Kamar ance su waiga kawai suka ji ihun Farida daga nesa dasu.
Wata irin hautsinawa zuciyoyinsu suka yi da mugun k'arfi har wasu daga ciki suna dafe saitin zuciyar tasu.
Hanan ce farkon kwala kiran sunan Farida.
Domin gani sukai Zombies sun tura ta wata kwana wacce bata b'illewa, sai binta suke a baya, ita kuma tana ihu.
Kuka take jikinta na rawa kamar mazari zufa ta wanke mata fuska, k'irjinta sai d'agawa yake, tana kuka tana kiran sunan duk wadda ta sani.
Gaba d'ayansu ne suka rugo inda take suna kallo abun ke shirin faruwa.
Hanan kuka ta saki tana son nufar inda Farida take, Anjali ta rik'eta, sosai take fisge-fisgen ya barta ta k'arasa itama idan ya so su kasheta dama ta gaji da wannan guje-gujen da suke, kusan kwanakinsu nawa suna abu d'aya, babu ma alamar ranar da zasu fita daga cikin wannan bala'in daya same su.
Wani shago ne Farida ta gani bata tsaya sanya ba ko kawai ta fad'a cikinsa tana jawo k'ofarsa da k'arfi ta gark'ame k'ofar zuciyarta na bugawa.
Tana rufe k'ofar ta saki tana dafe k'irjinta zamewa tayi a bakin k'ofar kawai ta fashe da wani kuka.
Ta dad'e tana kuka mai cin rai kamin ta mik'e tana bin wajan da kallo.
Ido waje take bin shagon da kallo tana ganin ashe babban shagon sayayya ne, mai k'ofofi daban daban.
Ai da wani irin sauri ta mik'e tana nufar wata k'ofa ta baya ta bud'e ta fice daga Shagon.
Sai dai tana fita ta riski kanta a wani waje na daban.
Wani irin sabon tashin hankali ne ya rufe Farida. Yanzu ba dai ita d'aya zata rink'a tafiya ba?, yanzu idan wani abu ya same ta fa?, kai bama ita ba ya za'ai ta sake had'uwa da y'an uwanta?.
Wasu hawayen tashin hankali ne suka sake b'alle mata.
Jin motsi yasa Farida wata muguwar zubura ta baza da gudu, gudunma da kyar take iya yinsa tsabar wahala duk ta gama kwashe k'arfin nasu da kuzarin da suke da shi.
A wajan su Hanan ko ta birkice masu sai kuka take tana ihu tana turjewa.
Da kyar Faruk yayi namijin k'ok'arin jawo hankalin Zombies d'in da suka yayyab'e bakin k'ofar da Farida ta shige.
Jansu ya rink'a yi suna binsa suka bar bakin k'ofar.
Kamar mahaukaciya haka Hanan ke buga k'ofar zuciyarta na tsinin tsinkewa na tashin hankali.
Suna bud'e k'ofar suka ga babu Farida babu alamarta.
Har k'ofofin suka bud'a amma babu Farida.
Zubewa kawai Hanan tayi tana d'ora hannunta a saman kanta tana rushewa da wani kuka na tsabar tashin hankali da wata muguwar nadamar da tasan bata da anfani.
Sunyi cirko-cirko hatta Anjali kuka take wadda hawaye ne kawai ke mata zuba.
Gunji-gunji suka fara ji, hakan yasa suka yi niyar barin wajan domin wata unguwa ce ta marassa k'arfi suka cinsu kansu a ciki, an hargitsa unguwar tayi muni da yawa, gaba d'aya mutanan unguwar basa jin akwai wadda ya rige yayi saura bai gama kamuwa da cutar ba, wasu sun mutu wasu sun koma zombies.
Da sauri Anjali ta ja hannun Hanan tana k'ok'arin tayar da ita, amma Hanan ta fisge.
K'irjin Anjali ne ya buga da sauri ta dubi gabansu ganin Zombies sai sako kai suke inda suke sunji k'amshin mutane a wajan, sai k'ara yawa ma suke suna gunji da shinshine-shinshine
Da wani mugun sauri Faruk ya sab'i Hanan domin gaya bata da niyar tashi, ita fa sun lura bata k'i a barta su halaka ta bama.
Dan haka da kansa ya d'auketa kamar baby suka bar wajan da sauri.
_________________________
Suna cikin karanto taswirar kawai suka ga Mota ta tsaya taja birki.
Captain Harun yayi-yayi aamma tak'i tashi.
Hankali a tashe Asiya ke fad'in.
"Mun bani, miye yasa Motar nan tsayawa a wannan mahaukaciyar unguwa?, Fisbilillahi duba unguwar nan da muka shigo".
Ta k'are maganar tana kallon yanayin wajan da Motar ta tsaya masu.
Tabbas unguwa ce amma yadda kasan Mak'abarta, kusan gidajan mutanan dake wajan ci da wuta suke, can gefe sai kaga mashing ne naci da wuta, daga gefensa mutum a kwance ya mutu an masa mummunan kisa, can gefe daka kalla mota ce anyi hatsari da ita mota da mota, wasu sun mutu a ciki, wasu ko gawarsu ce gefe, wasu sun risa k'afarsu wasu ko hannu wasu ma kwayar ido ce aka kwalkwale kai wani ma fuskarsa ce aka cire gabai d'aya, babu kyan gani, ko ina dai a hargitse, sai wani irin ihu-ihu had'e da wani koke-koke da suke iya jiyowa nesa da su, babu Zombies yanzu a wajan, amma ko wane lokaci sun san suna iya jiyo k'amshinsu su biyo k'amshin su iso inda suke.
Gaba d'ayansu sun razana sosai da yanayin wajan da suka tsinsu kansu ga Mota ta mutu, yama za'ai su ce zasu fara tafiya a k'afa?.
Wani miyau Doctor Fahat ya had'e yayi k'arfin halin fad'in.
"Kodai man motar ne ya k'are?".
Captain Harun daya fahimci hakan shi tun d'azo ya d'an d'aga kansa yana tashi daga gaban motar yana dubansu yana gyara Bindigarsa ya ce.
"Ya kamata muyi hanzarin sauka daga cikin Motar nan, tun kamin su riske mu a ciki, bazata tashi ba man motar ne ya k'are, kuma bamu da inda zamu sami mai bare musa, gara mu sauka ko Allah zaisa mu sake cin karo da wata Motar mai lafiya"
Ya k'are maganar yana kallon su, kamin ya sake cewa.
"Kowanne ku ya d'auki makami domin kare kansa".
Ai tun kan yakai k'arshen zancensa Asiya ta rarumi wani k'arfe har yana rinjayarta ta rik'e sosai.
Ta baya suka rink'a sauka suna fita daga cikin Motar.
Suna fita suna waige-waige gudun kar wani abun cutarwa ya shammace su.
Sai dai suna gama fitowa daga cikin Motar abun kamar jira ake suka ga wani Zombie yana tafiya a slow an cire masa hannu d'aya sai d'ayan da yake mik'asa gaba yana gunji.
Wasu ne suka sake gani amma ba saitinsu suke ba tafiya suke suna shinshina hanci.
A hankali Harun ya kallesu yana d'ora bakinsa yana alamar subi a hankali su bar wajan, kar hankalinsu yama dawo inda suke.
A hankali suke taka k'afarsu suna sun barin wajan.
Kamar saukar aradu Asiya ta taka wani k'arfe ya bani wani sautin daya jawo hankalin Zombies gare su, ai ko kamar almara suka ga kota ina fitowa suke suna biyo inda suka ji k'arar.
Asiya kusan suman tsaye tayi zuciyarta na wata irin bugawa sosai, tana dafe da k'irjinta idonta a runtse.
Wani tsaki Doctor Fahat yayi ransa ya d'an b'ace da Asiyar, domin komai zatai bata yi na hankali, dan Allah yanzu miye hakan data yi?, bata iya kallon gabanta sosai sai iyayin tsiya da kaud'i kawai ta iya. Abunda yasa basu son kashe Zombie d'in suma fa mutane ne cuta ce ta maida su haka, k'ila da an samu maganin da zai iya warkar dasu a asibitin da suke son zuwa zasu warke, wata k'ila.
Dole tasa Captain Harun saita Bindigarsa ganin suna gaf inda suke.
Kai tsaye ya fara sakar masu wuta yana harbinsu, ba dan yana so ba.
Su ko sai wani irin ihu suke wadda baya fita da kyau, wasu na zubewa a k'asa, ana Harbin wasu, wasu na sake biyosu.
Ja da baya suke yi su Captain Joha na harbi sun iya saiti sosai, shi yasa suna harbawa suke samun Zombie d'in.
Su Anam sai ja da baya suke cike da tsoro, abunda suka d'auka domin kare kai yana a hannunsu sai had'iyar miyau suke na tsananin tsoro da firgitar kar wani abun ya same su.
Wani ihu ne suka jiyo wadda ya razana su, ya kusa sa zuciyar wasu daga cikinsu harbawa basu shirya ba, duk d'aukarsu ko d'aya daga cikinsu ne Zombies suka kama.
Sai dai suna waige-waige son sanin inda ihun ke fitowa.
Su Asiya tsabar yadda zuciyarsu ke bugawa har saida suka runtse idonsu da k'arfe.
Da d'an gudu gaba d'ayansu suka nufi inda suke jiyo ihun na fitowa.
Sauran Zombies d'in basu idasa kashewa suna binsu a baya, danma tafiyar tasu sai ka ce masu son iya tafiyar.
Wani irin dafe k'irji Anam tayi da k'arfe ta kwala kiran.
"Faridaaaaa".
Farida dake k'asa wani Zombie ya rik'e mata k'afa tun d'azo sai artabu suke ita dashi tana son kwace k'afarta shi kuma ya rik'e sai kokowa suke, ihun data fasa kuma ganin yana son kai mata cizo had'e da sun yakushe mata k'afa shine bata san lokacin data saki ihun