Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ya d'auketa kamar baby sai dai kawai Farida taji an d'agata sama, da sauri ta kai dubanta a fuskar Harun d'in, da sauri kuma ta kauda kanta daga kallon fuskar tashi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da k'arfi saboda kusancin da suka samu.
Sosai ta k'ank'amesa a jikinta har yanzu hawaye take sai sauke wata irin ajiyar zuciya take.
Abbakar dake tsaye kamar wani sakarai yayi kwafa yana cizon yatsa yabi bayansu.
Har yanzu gari bai idasa wayewa ba, a haka suka ci gaba da tafiya.
Suna cikin tafiya Allah yasa suka gano wani ruwa mai yawa a gabansu, dan haka da sauri suka d'inguma zuwa can domin yin alwalla suyi sallar asubahi.
Har bakin ruwan Harun ya aje Farida wajan ajeta ne ya d'an rankwafo kad'an yana son direta a wajan, d'an kunnan kunnanta ya kama abun rigarsa, yana son barin wajanta amma d'an kunnan nan ya rik'esa, dole tasa shi sake rankwafota sosai, har suna iya jin lumfashin juna, wani irin azababben kallo yake jefanta dashi, ita kanta kallonsa take cike da rauni take k'ok'arin janye nata idon a kansa, sai dai ya kasa bata damar hakan.
Harya cire d'an kunnan nata bata sani ba, Saida taga ya mik'e sosai ya bar wajan da take.
Wata irin ajiyar zuciya Farida ta sauke tana binsa da kallo, tana sake jin wani abu game da wannan bawan Allahn.
Abbakar dake d'uke yana d'aura alwalla yana kallon duk abunda suke yi, yaja tsaki yakai cikin kwando, yo a bazan domin gaba d'ayansu harkar gabansu suke, hatta Doctor Fahat dake nanik'e da Anam sai soyewarsu suke, izuwa yanzu sun d'an saba, kuma Anam d'in dama tuni tasan yana sonta, dan haka tafiyar nan da sukayi sai wata shak'uwa ta sake shiga tsakaninsu, dan har Anam d'in tana jin zata iya basa zuciyarta zata iya zama dashi.
Asiya ko duk a rud'e take duk da taga babu kowa a inda suka tsaya domin yin sallar.
Captain Harun ne ya fara kammala sallar kamin a hankali ya mik'e yana nufar wani tsauni da yake wajan wani k'aton dutse ne suka tsaya ruwa na gudana a wajan.
Abbakar ma da sauri yayi sallar tashi tsabar abunda ya hango yake son aiwatar a yanzu d'in.
Su ko sauran a tsanake suke sallar tasu.
Captain Joha na daga gefe yana kallon yadda suke bautar Ubangijinsu abun har ya fara d'an birgesa sosai.
Suna cikin haka kamar ance Farida ta waiga inda Harun yake tsaye ya bada baya kawai taga wata Zombies ta tsaya a bayansa ta b'illo ta cikin wani kogo dake akan dutsin, kwata-kwata Harun baiji motsinta ba, saboda ya lula duniyar tunani.
A zabure Farida ta kwalla kiran sunansa.
A d'an mamakance ya waigo, ai waigowar da zaiyi yaci Karo da Zombie mace sanye take da wasu jajayen kaya, gaba d'aya kayan an farkasu daga wani wajan, jini ne kota ina ke zuba a jikinta, hannunwanta a bandare suke sai jan k'afa take had'e da wani gurnani marar dad'in sauraro.
A zabure Farida ke neman yadda za'ai ta fara hawa dutsen su duka ma zabura sukai suna niyar hawa saman shi.
Captain Abbakar da shi tun d'azo ya hau zaman nashi yana daga tsaye gefensu.
Sunyi mamakin yana tare da Bindiga amma bashi da niyar Harbin Zombie d'in nan dake gaban Harun d'in tsaye.
Ja da baya Harun yake babu tsoro a ransa, ga rami dake a bayansa yana ja da baya yana kusantar ramin.
K'afarsa d'aya harta fara gocewa a wajan da ramin yake.
Bindigarsa yake lalube duk ya rud'e shima, koda ga ciro ta kwata-kwata babu bullet a cikinta, haka a jikinsa duk masu yawan suna wajan Captain Joha.
Ganin haka Farida ta sake zabura tana kiran sunansa.
Waigawa yayi bayansa ganin rami ne sai ruwa dake zuba ta kasan ramin, zaka iya sauka ta kasan dutsen ya saukar da kai inda ruwan yake zuba, ramin ba wani mai uban zurfi bane.
Fad'awa yake k'ok'arin yi Abbakar ya shammace su yana saita Zombie d'in nan zai sakar mata bullet, kawai sukaga ya sakar ma Captain Harun a tsintsiyar hannunsa.
Baya-baya Harun yayi yana nuna Abbakar cike da mamaki, wani ihu Farida ta saki ganin yayi baya ya fad'a cikin ramin.
sai ya fara nuna bashi ya zo harbi ba Zombie d'in dake a gabansa ita ya zo harbi sai aka samu kuskure ya same shi.
Sai lokacin ya harbi Zombie d'in nan ta fad'i a wajan.
Farida ko basuyi aune ba ta nufi ramin tana kiran sunan Harun da k'arfi tana son fad'awa itama ciki.
Tana niyar fad'awa kawai taji an ruk'o mata hannunta.
A zuciye ta juyo ai ko ganin Abbakar ne ta d'aga hannunta tana sharara masa mari har biyu.
Da sauri ya dafe k'uncinsa yana zare ido waje nuna kansa yake yana fad'in.
"Keee ni kika mara?".
"Ta mare ka d'in akwai abunda ka isa kayi mata ne?, macuci Maci Amana, wallahi Abbakar ka bani kunya, yanzu nasan babu abunda ba zaka iya aikawa ba".
Cewar Jaho daya k'araso wajan hankali a tashe.
Abbakar yana wani ciccin magani yake fad'in.
"Nifa karka sake ka k'ara zargi na ko ka tuhume ni, domin na ce ai bashi na zo harbi ba, kawai kuskure ne aka samu na harbe shi, amma ni bashi zan harba ba, daga taimako sai abu ya zo da haka?, komi zanyi sai ka wani ce ina sane nayi".
Ganin yadda Jaho ke son d'auke sa da mari na taikaici yasa Doctor Fahat shiga tsakaninsu yana jin haushin Abbakar d'in shima.
Suna wannan gardama da maida magana kawai suka ji k'arar Farida ta fad'a cikin tsaunin tayi k'asa.
A zabure suka matsa sosai suna kallon k'asa tsaunin ganin ruwa a k'asan.
Da sauri Captain Joha yayi azamar sauka daga dutsen domin zuwa inda nan yake da tabbacin zasu iya fitowa daga cikin ruwan.
Bin bayansa sukai Abbakar na addu'ar Allah yasa Captain Harun d'in ya mutu.
Suna sauka ta inda ruwan yake sukai tsaye suna kallon ta inda zasu fito, domin shi Captain Harun ya iya ruwa, to amma Faridar fa?, gaba d'ayansu zuciyoyinsu sun cika da fargaba amma banda ta Abbakar, Captain Joha ya cire rigarsa yana son fad'awa cikin ruwan domin nemo su.
A wajan Farida tana fad'awa cikin ruwan ta toshe hancinta tana son yin k'asan ruwan tunda ba wani iya ruwan tayi ba.
Captain Harun ko azabar da yake ji hannunsa ce tasa shi kasa fitowa daga cikin ruwan, har yana shirin sumewa a ciki, kawai yaji k'arar wani ya fad'o ruwan.
Da kyar ya fara neman wadda ya fad'o ciki, ai kamar ance ya waiga wani shashi dake a cikin ruwan, ya hango Farida na niyar nutsewa sosai a cikin ruwan, gashi tana niyar sumewa.
Ai sai yaji ya nemi ciwon nasa ya rasa da sauri ya nufi wajanta. Tarbota yayi a jikinsa sosai da k'arfin hali ya fara niyar fitar dasu daga cikin ruwan.
Captain Joha na niyar fad'awa cikin ruwan idonsa ya hasko masa Harun yayo saman ruwan ya fiddo da kansa yana shak'ar iska har wani jan lumfashi suke da k'arfi zuciyoyinsu na bugawa da mugun sauri.
Jawota ya rink'ayi har suka kawo bakin ruwan, ita ya fara fitarwa kamin ya fito gaba d'aya, yana fitowa ya sube a wajan yana dafe hannunsa da Abbakar ya harba.
Abbakar dake tsaye ya wani dafe kansa yana sake jin tsanar Harun d'in, sai ya d'an maze yana sake matsawa inda yake yana wani cewa.
"Alhmdllhi tunda baka mutu ba sannu, kayi hakuri Sir wallahi tsautsayi ne Zombie d'in gabanka na zo harbi ba kai ba".
Kallonsa kawai Harun yake bai ce komai ba, sai kawai ya d'aga masa kai.
Farida dake kallonsa cike da tsananin taikaici itama ta girgiza kai, tunda ya lauya magana, babu yadda zasuyi tunda basu da cikakkiyar shaidar cewa bada gangan yayi ba.
Captain Joha ne ya mik'e yana fiddo wani d'an an
al'makashi da ya d'akkosa tun a cikin motar da suka fara hawa, ya d'akko sa ne gudun ko wata rana Bindigarsa ta fad'i ko bullet d'insu ya k'are, duk da sun taho dashi da yawa sosai a jikinsu.
Kamo hannun da aka harbeshi yayi yana son cire masa bullet d'in dake cikin hannun nasa.
Runtse idonsa da k'arfi yayi yana sakin y'ar k'ara jin yadda yasa bakin almakashin ya raba almakashin biyu yana sa d'ayan tsinin ya danna shi cikin tsokar hannun, wata uwar k'ara Captain Harun ya saki jikinsa na d'aukar rawa na wani irin azababben rad'ad'i da yaji Kwakwalwar kansa ta d'auka, da ma duka jikinsa, shima kansa Jaho d'in sai da runtse idonsa kamin ya cire bullet d'in, yana ciresa yasa wani farin gyalle ya d'aure wajan.
Ba abunda Harun keyi sai sauke ajiyar zuciya a jere a jere.
Farida na daga gefensa sai hawaye take tana faman masa sannu.
Kallo kawai ya bita dashi, yana jin wani azababben sonta lokaci d'aya yayima zuciyarsa dirar mikiya bai shirya ba, sau biyu kenan tana k'ok'arin ceto rayuwarsa, shi yasa yaji duk duniya ta gama shiga zuciyarsa, wani irin kallo mai cike da k'auna yake binta dashi.
Abbakar na kallon abunda ke faruwa zuciyarsa sai wani irin turiri take na bak'in ciki.
Har bai san lokacin daya saki tsaki ba, gaba d'aya suka bisa da kallo.
Sai lokacin da suka ji k'arar tsakin da Abbakar yaja ne suka d'auki idonsu daga cikin na juna, suna basarwa.
Doctor Asiya gulma na cinta ta wani tab'e baki, tana kusa da Doctor Halisa tana fad'in.
"Nifa wancan Captain Abbakar d'in na tsane sa fa, tun zuwan Farida na gane take-takensa fa sonta yake, kuma ni gaskiya sunfi dacewa da Harun d'in can wallahi, k'ila ma bak'in cikin hakan yasa shi Harbinsa yana sane".
Y'ar dariya kad'an Halisa ta saki tana juyowa inda Doctor Asiya take ta ce.
"Ashe wata rana zaki goyi bayan gaskiya?, nima nan sun gama birgeni Allah kuwa".
D'an wani kallo Asiya tayima Halisa kamin kuma ta saki murmushi tana sake kallon su Anam ta ce.
"Kinga wasu masoyan can ai manne da juna suma. Ina bin gaskiya mana, wani lokacin ne ni d'in ce sai a hankali, ai wannan tafiyar ce da mukayi ta sake koya min hankali har darasin rayuwa, wannan tafiyar ta koyar dani abubuwa da dama. Ni banga dalilin da zaisa nayi gaba da wani a cikinmu ba, saboda baka san wadda zai taimakeka ba ai, muna cikin wannan iftila'in tsayawa ma jin haushin wani ko ka k'ullama wani mugunta ba naka bane wallahi, saboda baka san yadda zaka kare ba kaima".
Dafa kafad'arta Halisa tayi tana cewa.
"Wallahi nima abunda ke cikin raina kenan Asiya, ni dama dai banga wadda nake jin haushinsa a tafiyar nan tamu ba, amma duk da alama shi Abbakar d'in can akwai mugun abu a ransa wallahi".
"Yaji dashi Halisa, ya dai kuka da kansa shine kawai".
Fad'in Asiya tana kallon Abbakar d'in tana tab'e baki.
Sun dad'e a wajan saboda waje ne marar yawan hayaniya, dama kuma cikin daji ne kad'an suka d'an shigo, to babu wani Zombie a wajan, sai wannan macen da suka gani Zombie, duk da dai basu da tabbacin wasu Zombies d'in ba zasu sake fitowa daga wajan ba.
Dan haka da kyar Jaho ya kama Harun suka mike da kyar Harun ya ce ma Jaho ya barshi zai iya tafiya da kansa.
Farida na gefensa har yanzu.
Captain Joha ne ya bada umarnin a fiddo da taswirar nan su ci gaba da neman hanyar zuwa asibitin nan. Sai ma yanzu ya tuna gaba d'ayansu wayoyinsu babu layin K'asar a ciki, har yanzu layin Nigeria ne cikin wayar tasu, yo wasu ma sai yanzu suka tuna cewa ashe fa akwai waya a jikinsu.
Ta wasu da suka fiddo harta d'auke babu ma chaji a jikin wayoyin nasu, sauran da bata d'auke bama suna d'an latsata ta idasa d'aukewa gaba d'aya.
Dan haka suka maida wayoyin a jikinsu da ace akwai chaji akwai kuma layin K'asar da tabbas sai sunyi kiran K'asar su Nigeria ta k'ara kawo masu taimako na jirgi k'arami wadda zai taimaka masu zuwa asibitin nan ba wata gargada ko matsala........
EPISODE 16
Hasken rana ne daya shigo cikin gidan ya dalle masu fuska shine yasa suka fara motsa jikinsu.
Anjali ce farkon tashi tana bud'e idonta da sukayi mata wani irin nauyi.
A hankali ta mik'e tana jin gaba d'aya jikinta na mata wani irin azababben ciwo.
Shafa fuskarta take tana sauke wani irin lumfashi a hankali.
Kamar saukar aradu taji kota ina jikin gilashin widows na gidan da jikin k'ofar da suka samu suka datse ta da kyar ana bugasu lokaci guda.
A zabure ta mike kamin k'arar bugawar da akema windows d'in da jikin k'ofar fita daga gidan ta tayar dasu Faruk a mugun firgice.
Hanan ce ta matso kusa da Anjali idonta a waje jikinta ya fara rawa.
Ta jikin window d'in gidan suka hango Zombies ne sun zagaye gidan gaba d'aya hatta jikin k'ofar gidan sune.
Babu ta inda zasu iya fita.
Wani irin kuka marar k'arfi Hanan ta saki tana cewa.
"Shikenan yau tamu ta k'are wallahi, sun gama zagaye mu fa gaba d'aya babu ta inda zamu fita hatta jikin windows sune".
Wani irin miyau Faruk ya had'e zufa na karyo masa kota ina a jiki.
Al'ameen ne yayi hanzarin d'aukar wani k'arfe da jiya ya fasa ma wannan matar da suka tarar ta zama Zombie a cikin gidan, ya rik'e sa sosai a hannunsa yana fad'in.
"Ya kamata kowa daga cikinmu ya d'au makami domin kare kai, zan bud'e k'ofar ne, saboda mu samu mu fice daga wannan gidan, idan ba haka ba suna gaf fasa gilassan window d'in nan da idasa b'alle k'ofar gidan su shigo ciki".
A rud'e Anjali ta saki Hanan data nanik'e mata a jiki, ta ruga kitchen wuk'a ta d'akko wata zureriya har guda biyu ta mik'ama Hanan d'ayar.
Jikin Hanan sai rawa yake ta amshi wuk'ar hannunta na rawa da kyar ma ta iya rik'e wuk'ar sosai a hannun nata, hawaye na mata zuba, tunda take bata jin ta tab'a jima wani ciwo, wai yanzu ita ce rik'e da wuk'ar nan ne dan kawai ta kashe wani d'an Adam wadda ya riga da ya zama abun tsoro abun gudu cikin mutane.
D'ago kanta tayi ganin Faruk ma ya rik'e wani dogon k'arfin labule a hannunsa daya fisgoshi jikin window d'in gidan.
Gadan-gadan Al'ameen ya nufi k'ofar zuciyarsa na tsalle sosai.
Hatta su Anjali suna baya jikinsu na rawa had'e da wata bugawar zuciya mai tsananin gaske.
Da azama ya bud'e k'ofar gidan, ai ko kamar jira suke suka fara fad'owa cikin parlon.
Al'ameen d'aya b'uya bayan k'ofa bayan ya bud'e gidan ya d'an fito yana kwad'ama na farkon shigowa.
Kamar danno su ake cikin gidan haka suke shigowa suna wani irin gurnani suna tafiyar nan tasu a bandare.
Su Anjali ne da Faruk suka fara artabu dasu, Anjali data samesu zata daka wani irin tsalle ta caka masu wuk'ar a tsakiyar kansu, shi yasa nan take suke zubewa babu rai.
Hanan ko sai zare ido take tana tsaye daga gefe tama kasa komai sai jikinta dake rawa zuciyarta na bugawa kamar zata fasa k'irjinta ta fito.
Su Faruk sun manta da Hanan domin duk d'aukarsu itama Zombies d'in take kashewa ashe basu sani ba tsaye take kamar wacce tayi suman tsaye.
Sun kusan kashe rabinsu kamin Allah yasa Faruk ya fara fita daga cikin gidan Anjali a bayansa sai Al'ameen dake niyar ficewa da gudu, kawai kamar ance ya waiga ya hango Hanan tsaye can tsakiyar parlon ta tsaya sai zare ido take ko motsi bata yi.
Kwala kiran sunanta yayi da k'arfi ta firgita ta dawo yaccinta, zabura tayi tana sakin k'ara ganin wani Zombie da Faruk ya kwad'e ya mike kamar ba'a bige masa kai ba, sai ma wani irin gunji yake yana k'ok'arin cafke mata hannu, ai bata san lokacin data d'aga wuk'ar nan iya k'arfin ta caka masa ita a tsakiyar k'irjinsa ba, wani uban gurnani ya saki yana zube k'asa.
Da gudu ta k'araso inda Al'ameen ke mik'a mata hannunsa, domin wasu Zombies d'in cikin wa'inda sukai artabu dasu suna niyar sake mik'ewa, da k'arfi ya rik'e hannunta yaja ta suka fice daga cikin gidan, da k'arfi Al'ameen ya tsaya yana gark'ame k'ofar ya rufe.
Da gudu gaba d'ayansu suka bar wajan.
Gudu suke ko waiwayen bayansu basa yi har Allah ya kawo su bakin titi. Sakin hannun Al'ameen Hanan tayi tana zubewa k'asa dafe da cikinta daya k'ulle sauke lumfashi take da kyar idonta a rufe take fad'in.
"Wallahi na gaji, ni dai inajin bazamu iya tsira daga farmakin wa'innan dodannin ba, na fara karaya gaskiya".
Su duka tsayawa sukai Anjali na cewa.
"Zamu tsira da yar dar Allah, kin tuna akwai y'an K'asarmu da suka zo cetanmu?".
Hanan tana sauke wani lumfashin tana cewa da kyar.
"To amma ai bamu san ta inda zamu fara neman su ba, suma yanzu haka suna can suna b'ulayin neman namu, Goa fa k'asa ce babba ba wai y'ar karamar k'asa ba ce. Ni babban abunda ke damuna ma rashin Farida da mukayi wallahi idan na tuno ni ce silar jawota cikin tafiyar nan haushin kaina nake ji, ji nake inama ni ce na rabu da ku ba wai ita ba".
Ta k'are maganar wasu hawaye na zubo mata.
Jikinsu ne ya sake karaya suma jiki a sanyaye Faruk ya matso inda take zaune a k'asa ya ce.
"Insha Allah zamu nemi asibitin da naji wannan mutunan da muka had'u dashi yake sanar damu can zasu nufa, naji ya tab'a cewa a k'arshen Goa asibitin yake, yanzu kamata yayi mu fara neman hanyar zuwa asibitin".
D'an ware idonta Hanan tayi cike da wata y'ar kwarin gwaiwa ta ce.
"Da gaske Faruk kaji lokacin daya ce haka?".
Murmushi ya saki kad'an kamin ya ce.
"Tabbas naji lokacin da ya fad'i hakan, yanzu sai ki tashi mu ci gaba da tafiya har Allah yasa muci karo da wannan asibitin, tunda ma kinga ai munyi nesa da ainafin cikin birnin Goa d'in".
Tashi tayi tana jin wata kwarin gwaiwar zuwa asibitin nan