Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
dai wani Zombies yayi nasarar cafke tsintsiyar hannunsa, ga k'ofa ana niyar rufata da tsiya, domin gaba d'aya Zombies d'in ne ke neman dawowa ga jikin k'ofar.
Kokowa suka farayi Abbakar jikinsa sai rawa yake, tsautsayi yaje d'aukar wayarsa data sullub'e a k'asan Motar asibitin da suka iso da ita yanzu, ya kuma d'akkota ne aka barsa a baya.
Wata irin karta Zombie d'in nan yasa farcensa mai masifar tsini ya yakushisa a tsintsiyar hannun nasa, kamin da k'arfi Captain Harun ya jawosa suka fad'a cikin Asibitin suka zube a k'asa a tare, k'ofar kuma aka mayar da ita aka rufe, Zombies da suka k'araso bakin k'ofar suka rink'a bugata da k'arfi suna yakushin k'ofar suna gurnanin nan nasu.
Tashi tsaye sukai lokaci guda, Abbakar ke kallon Captain Harun karo na biyu kenan da yake k'ok'arin taimakonsa har yanzu wani abu baisa ya ji zai bar Captain Harun d'in ba.
Faruk ne ya fara lura da inda aka karci Abbakar, da sauri ya matsa inda suke yana nuna shi da inda aka karcesa yana cewa.
"Garin yaya aka karceka"
Wata irin zabura Abbakar yayi yana kallon inda aka karcesan, ido waje yake kallon wajan, wani irin tsoro ne ya rufesa zufa kota ina ta fara tsatstsafo masa.
Wani irin tsoro ne ya rufesa na kar y'an asibitin suce sai ya fita daga cikin Asibitin kar ya zame masu annoba.
Dafasa Harun yayi yana cewa.
"Ka kwantar da hankalinka insha Allah tunda mun shigo asibitin nan zasu iya baka taimako, kuma muna tare da Doctors d'inmu kwararru domin dama abunda yasa muka shigo Hospital d'in nan kenan".
Abbakar bai san lokacin daya saki kuka ba, kawai sukaga ya rungumeta Harun yana kuka wiwi sai bashi hakuri yake yana ya yafe masa, bai tab'a tunanin haka ce zata fito daga bakinsa ba, k'ila da shine Bindiga zaisa ya harbesa don kar ya zame masu matsala a cikin Asibitin, tunda babu Zombies ko d'aya a ciki.
Kowa shuru yayi yana kallon yadda yake kuka Harun ko baiji komai ba wajan fad'in shi dama bai wani rik'esa ba, hasali ma sai ya nuna shi baiga abunda yayi masa ba, idan ma akwai to shi ya yafe wallahi.
Wata irin muguwar kunya ce ta kama Abbakar, ai sai ya fara godema Allah da yasa duk muguntar da yake shiryama Harun babu wacce tayi tasiri babu wacce yayi nasara akansa, godiya ya rink'a jerowa ga Ubangiji da shine yayi hikimarsa da idan yaje cutar dashi yake karesa.
Suna tsaye wani Doctor ya fito yayi masu jagora zuwa cikin Hospital d'in.
Sun cika da mamakin ganin iyayan mutanan dake cikin Asibitin, an tara su waje d'aya, wasu marassa lafiya ne sunyi jingum-jigum dasu wasu na kuka wasu kuwa daka kalli fuskarsu tashin hankali ne ba d'an kad'an ba.
Jiki a sanyaye suke kallonsu.
Basu tsaya nan ba aka shige dasu Anam cikin wani d'akin had'a magani da dai bincike na musamman.
Suna shiga d'akin ba b'ata lokaci dama suna da Doctors ba laifi da yawa a cikin Asibitin.
Jinin Abbakar aka d'iba domin dama suna buk'atar wadda ya kamu da cutar zasu fara bincike akansa.
Wata allura aka yima Abbakar wacce tasa shi wani irin dogon bacci nan take.
Sosai Su Doctor Fahat suke bincike da sauran Likitocin da suka tarar a cikin Asibitin.
Bincike sukai ba d'an kad'an ba, kamin su samu wata mafita, to amma fa mafitar idan akace za'ayi ma mutum allurar da zai warke daga wannan Cutar sai ya d'auki tsawon kwana biyar koma fin haka kamin a samu ya dawo dai-dai.
Sun tsaya sunyi nazari babu yadda za'ai mutanan Goa su warke daga wannan Cutar gaba d'ayansu, yawansu ya isa haka, babu yadda za'ai ma su iya kamo su suce zasuyi masu allura, ai abun akwai matsala, sai dai idan mutum an cijesa bai kai ga komawa Zombie d'in ba, shine kawai zasu iya masu wannan allura da suka gano har ya warke.
Nan take aka fara yima Abbakar ita domin yin gwajin farko dashi.........
EPISODE END
To sai dai suce Alhmdllhi tunda aka ma Abbakar allurar nan wacce suke da yak'inin ita ce zata magance annobar nan, sai gashi safiyar washe garin da suka zo asibitin wajan k'arfe sha biyu dai-dai Abbakar d'in ya farka yana wani irin amai bak'ik'k'rin dashi, yayi aman mai shegen yawa kamar zai amayar da abunda ke cikinsa, ashe gaba d'aya gubar nan dakesa Zombies cin mutane ita ce ya amayar da ita, yana yin aman nan take ya mik'e garas dashi.
Gaba d'ayansu Doctors ne suka d'auki tafi had'e da tsananin murnar gano maganin wannan cuta.
A cikin Asibitin suka had'a wani gaggarumin taro had'e da yabama juna bisa namijin k'ok'arin gano maganin cutar da ta mai maida mutum kamar wani Dabban daji mai cin naman mutane.
Su Captain Harun Hukumar su suka kira aka turo masu jirage domin d'ebesu zuwa gida Nigeria.
An sake turo bataliyar Sojoji had'e da helicopters masu yawan gaske, dai-dai saman asibitin suka tsaya a sararin samaniya, su kuma su Captain Harun saman asibitin suka je inda Helicopter zai iya sauka igiya aka rink'a zura masu suna kamawa sai ayo sama da mutum cikin Helicopter, kusan sai da aka fara d'ebesu kamin kuma a fara jidar mutanan dake cikin Asibitin ana fitar dasu daga k'asar Goa gaba d'aya, domin K'asar ta tashi aiki babu yadda za'ai ta dawo dai-dai.
Sun rink'a bi sak'o-sak'o lingu-lingu suna neman wadda bai zama Zombies ba koda akwaisa, shela suka rink'a da lasifika mai k'arar gaske, daga sama a cikin Jirgin Helicoptern suna sanarwa idan akwai sauran D'an Adam da ya rige a cikin Garin Goa d'in.
Ba laifi sun sami jama'a masu yawan gaske wa'inda suka b'oye gudun farkin Zombies wasu kuma an riga da an cijesu haka aka rink'a kwasarsu ana fita dasu daga K'asar Goa, dama Doctors sun taho da allurar da aka fara gwadata akan Abbakar duk wadda aka lura an cijesa allurar kawai suke masa nan take zai tafi dogon bacci kamin ya farka da amai nan take kuma ya warke daga mummunan cutar.
Wasu aka rink'a aje su duk K'asar da suke da wasu y'an uwa ko ahali a haka duk aka sauk'e kowa ya kama gabansa, K'asar Goa kuwa sai dai aka rink'a sakar mata bama-bamai suka rink'a tashi suna kashe ko wanne Zombies dake cikin k'asar, kota ina sakin bama-bamai suke Sojojin da aka turo gaba d'aya Goa ta zama tarihi an shafeta ta kuma kamar Mak'abarta.
Umaru Musa Yar'Adua Airport Katsina State Nigeria
Gaba d'ayansu ne suke sakkowa kowa ya kalli fuskokinsu sai ya shaida suna cikin farin ciki dawowa K'asarsu.
Airport d'in cike take damk'am da jama'a, wasu hawaye suke idan suka ga da Y'ay'ansu a cikin wa'inda suka dawo a raye, wasu kuwa nan take suke sumewa ganin babu Y'ay'ansu a cikin wa'inda suka dawo a raye.
Kusan gaba d'aya Family d'in B Radda ne suke zo tarbar Y'ay'ansu, idan ka kalli fuskokin Iyayen gaba d'ayansu a mugun tsorace suke domin ji suke kamar Yaran nasu baza su dawo a raye ba.
Mom ce farkon fara hango Y'ay'anta su biyu Anam da Hanan, sai dai Hanan tayi wata irin shegiyar rama tayi bak'i duk ta canza kamar ba ita ba, yadda kasan an sauya mata halitta duk tayi zuru-zuru da ita sai ido kawai da take ta zarewa.
Wani irin kuka Mom ta fasa da sauri ta k'araso inda suke Hanan na ganin Mom da Dad bata san lokacin data saki wani uban kuka ba tana fad'awa jikin Mom, Mom d'inma kuka ta rushe dashi tana jawo Anam ta rungume su a tare Dad dake gefe shima hawaye yake sosai, domin sai yau ne aka samu Mom ta iya tashi sai yaune aka sallamesu daga asibiti domin rashin lafiya ta rink'ayi kamar zata mutu, domin gani take yaranta shikenan sun tafi bazata sake ganinsu ba, hatta ruwa da kyar take shanshi, abinci kuwa sai dai aka rink'a bata shi ta hanci da wata na'urar da akasa mata a asibiti.
Abbie ma dake kyarmar jiki ganin su Faruk Momma kuwa jikinta na rawa tana kallonsu bakinta na kyarma wajan fad'in.
"Al'ameen kune kuka dawo a raye? Ina Amal d'ina take?".
Ta fad'a kamar wacce ta samu tab'in hankali.
Sai lokacin ne gabansu yayi wata irin mummunar fad'uwa.
An rasa waye zai fara sanar dasu Amal ta mutu a can.
Farida da Anjali suna gefe su babu iyayensu a wajan suna dai kallon family guda cike da tausayinsu.
Lokacin da Momma ta anbati sunan Amal Farida ce ta fashe da kuka.
Momma ta zaro ido tana kallon Farida hankali a tashe, hankalinta bai sake tashi ba sai ganin su Faruk na hawaye.
Ai kawai saita fara ja da baya tana rufe bakinta da tafukan hannunta so take ta saki ihu amma ta kasa girgiza kai take kamar wata k'adangaruwa tana fad'in.
"Karku sake kuce min Amal bata tare da ku, ina kuka baro min Y'ata?, ku fito min da ita dan Allah karku ce min wani abu ya sameta dan Allah".
Ta k'arashe maganar had'e da rushewa da wani irin azababben kuka wadda ke tafe can k'asan zuciyarta na tsananin tashin hankali.
Abbie ne yayi saurin tare ta a jikinsa ganin tana neman zubewa k'asa, shima zuciyarsa ce ke neman daina aiki domin yama fita shiga fargaba da tashin hankali tsananin yadda zuciyarsa ke bugawa harta wuce misali.
Al'ameen na kuka ya ce.
"Abbie mun rasa Amal har abadaaaaaaa".
A yadda zancan ya daki zuciyoyin iyayensu kusan gaba d'aya jinsu da ganinsu ne ya d'auke, domin Momma dake jikin Abbie nan take ta fasa k'ara tana sumewa a jikinsa.
Shi kuwa Dad ne yayi hanzarin tarbosa Mom kuma ta tare Momma data dad'e da sumewa a wajan.
A gigice su Faruk suke kuka had'e da idasowa inda suke da sauri hankalinsu yayi mugun-mugun tashi ganin irin halin tashin hankali da rud'u da Iyayansu suka shiga lokaci d'aya.
Jami'an tsoron da suke ba mai girma Gwamna tsoro ganin abunda ke faruwa da Gwamna da kuma iyalansa yasa suka rud'e suna k'ok'arin sanar da a turo Motar asibiti da gggawa, jami'an tsoron duk sun gama zagaye su, sai ka ce za'ai masu wani uban.
Su Anam dasu Doctor Fahat da Asiya hankalinsu suma yayi tashi ainun nan take Doctor Fahat ya rik'e Dad da duk ya gama fita daga yaccinsa shima ganin d'an uwansa cikin wannan hali.
Motar Asibiti ta k'araso da hanzari ta iso gaba d'ayansu aka kwashe sai wani asibitin kud'i aka wuce dasu gaba d'aya harsu Farida da duk wa'inda aka dawo dasu daga tafiyar, domin suma kansu sai da aka kwantar dasu a gadon asibiti, saboda suma kansu suna buk'atar a duba lafiyar jikinsu.
Tun a filin jirgi su Captain Harun suka rabu dasu Farida saboda suma Hukumar Soja ce ta zo tarbarsu duk da sunga irin tashin hankalin da suka shiga, suma kansu suna zuwa Hukumar su ta Soja suna da komai da Doctors da suke duba lafiyarsu nan take aka fara basu kulawa ta musamman.
_________________
Sai da sukai kwana biyu a asibiti kamin su d'an dawo cikin yaccinsu.
Su Momma da Abbie kuwa wani mummunan hawan jini ne ya kama su nan take, dan haka kulawa ake basu ta musamman da kyar Likitoci suka shawo kansu.
Suma kusan kwanansu uku basu san wadda ke kansu ba, sai da suka farka ba laifi jikinsu yayi kyau, amma fa Momma na farkawa tayi kuka kamar ba gobe, tayi kukan bak'in cikin rashin Amal, kuma tayi wata irin muguwar nadamar barin Y'ay'anta a sangarce haka, shi kansa Abbie idonsa suka kad'a sukai jawur zuciyarsa na zafin rashin Amal d'in, domin duk cikin Y'ay'ansa yafi ji da ita, saboda ita kad'ai ce mace a cikin gidansa, ita kad'ai ce yake kallo yake jin dad'i, a wajan Momma ma kusan haka ne, tana mutuk'ar son Amal.
Ganin tashin hankalin da suka shiga yasa su Faruk basu fara gigin fad'a masu irin mutuwar da tayi ba, da irin iftila'in rayuwar da suka tsinci kansu a wannan tafiyar da sukayi. Kawai sai suka shanye abunda duk suka gani da irin wahalhalun da suka sha.
Suna k'ara samun sauk'i aka sallamesu gaba d'ayansu.
A wajan su Farida kuwa Mom ta mayar da ita kamar itama d'iyar cikinta ce, jin irin yadda Hanan ke yaba mata a bisa irin taimakon data irink'a mata a wannan tafiyar da sukayi.
Inda Farida ta fara zuwa gidansu kusan satinta d'aya da dawowa jin ba'a mata zancan gidansu yasa ita tayi, saima lokacin Mom duk taji kunya ta kamata, nan dai ta had'ata dasu Anam suka je raka Farida har gidansu.
Sai dai abunda Farida ta tarar ya mugun girgiza ta, domin ta tarar da makwaftan gidansu suke sanar da ita cewa Babanta ya rasu kwanaki kad'an da suka wuce, bak'in cikin rashinta da rashin sanin inda Inna Zubaida ta kaita ne yasa nan take ya fad'i hawan jini yayi masa mummunan kamu, babu wata kulawa da yake samu wajan Inna Zubaida d'in har Allah ya amshi ransa.
Ita kuwa Inna Zubaida kusan kullum sai taje gidansu Anam domin dai a bata kud'in albashin Farida na aiki amma jami'an tsoro ke korota suna hanata shiga, lokacin da duk take zuwa su Mom na asibiti lokacin da aka kwantar da ita babu lafiya, lokacin suna cikin tashin hankalin tafiyarsu Anam d'in.
Inda Inna Zubaida ta rink'a ciwo bashi wadda shine yasa aka zo da Y'an Sadda aka kamata aka kulleta a Ofishin Y'an Sadda, y'an bashin da take ci masu basu suka shigar da k'ara a koto, koto ta yanke ma Inna Zubaida zaman gidan Yari na shekara biyar, saboda taci bashin jama'a da yawa a bisa cewa da an bata kud'in albashin Farida wadda shine ta dogara dama can dashi, wai zata rink'a biyansu dashi, to lokacin idan taje gidan su Anam d'in ba'a ma bari taga mutunan gidan shine fa wa'inda taci ma bashin suka gaji da irin k'aryar da take masu a kullum suka makata a koto.
Farida sosai labarin da y'an unguwarsu da Makwaftan gidansu ke bata ya daki zuciyarta, kuka ta fashe dashi tana bak'in cikin yadda Inna Zubaida ta wulakanta Mahaifinta yayi mutuwar rashin gata da kulawa.
Da kyar su Anam su rink'a lallashinta suka dawo gida da ita, suna sanar dasu Dad abunda aka sanar dasu da sukaje unguwar su Faridar.
Sosai Mom da Dad suka k'ara tausaya mata inda kulawar da suke bata saita soma tafi ta da, babu abunda ta nema ta rasa a gidan su Hanan d'in.
Inda ba zato ba tsammani rana saka Iyayen Captain Harun suka zo neman auran Farida, kusan lokaci d'aya aka zo neman auran Anam itama da Doctor Fahat Iyayanshi suka zo shima.
Sosai Dad ya cika da tsananin farin ciki inda nan take ya shige gaba wajan bada auran Farida ya zama shine ubanta shine uwarta yayi ruwa yayi tsaki.
A tare aka tsaida ranar auran wata biyu masu zuwa, sosai Farida ta tsinci kanta cikin tsananin farin ciki marar misaltuwa, sai lokacin ne ta gane ashe haka ta kamu da son bawan Allahn nan dama?, tafiyar nan da sukai ita kam ta zame mata alkhairi ta wani wajan, ta wani wajan kuma sai dai kawai ta ce karda Allah ya k'ara mai-maita masu irinta har abada.
Hanan ma Al'ameen ya ce yana sonta, Iyayansu ba k'aramin farin cikin maganar suka ji ba, ba b'ata lokaci duk aka had'e bakin gaba d'aya.
A ranar da aka d'aura auransu a ranar kuma Gwamnan Jahar Katsina (Abbie) ya had'a taro na Musamman ga wa'inda akayi tafiya dasu zuwa taimako a K'asar Goa.
Gaba d'ayansu ne zaune a d'akin taro bayan an gama d'aurin aure motocin gidan Gwamnati ne suka kwaso su, tunda dama su Faruk sun san da cewa Abbie ya shirya wannan taron domin jinjina da kyauta da zai basu.
Gaba d'ayansu sai da yayi masu kyautar ban girma had'e da kujerar Hajji da yaba su Farida da mijinta Harun sai kuma su Doctor Asiya da su Doctor Fahat shida matarshi Anam, sai su Abbakar shima da Captain Joha duk wadda akai tafiyar dashi sai da aka basu kyautar kujerar Makkah, sai kuma aka sake basu kyautar Mota y'ar ubansu had'e gida je a cikin wani Estate mai kyan gaske, gidanjan naso a jere suke kowa da nashi.
Kai ranar Farida tsabar farin ciki kuka ta rink'ayi, ba ita d'aya bama hatta Asiya da Halisa kyautar da mai girma Gwamna yayi masu ta gigita Kwakwalwarsu, hawayen murna dana farin ciki suka rink'ayi, hatta mazan ma farin cikin dake akan fuskokinsu basa misaltuwa.
Haka wannan taro ya tashi zuciyar kowa cike da d'unbin farin ciki marar adadi.
Inda kowa ya wuce da Matarshi tunda dama an riga da an gama d'aurin aure. Da daddare Hukumar Sojansu Captain Harun suka had'a masu wani d'an kwarya-kwaryar party, dinner ce mai kyan gaske suka shirya masu a Munaj Event Santer dake cikin garin Katsinar.
Anci an Sha anyi rawa an zubar da Naira, Farida ranar ta zame mata ranar da bazata tab'a mantawa da ita ba, komai yanzu ta sameshi ga mijinta a gefenta ga kuma Iyayen su Anam wa'inda suka zame mata kamar sune suka haifeta, idan ta tuna da nata uban saita zubar da hawaye had'e da masa addu'ar samun rahmar Ubangiji............
Alhmdllhi Alhmdllhi Alhmdllhi💃🔥 duka-duka a nan na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai suna GAWA TAFE, kuskuren da nayi cikinsa Ubangiji ya yafe min, darasin dake cikinsa kuma Allah Ubangiji yasa mutane su anfana dashi.
Sai kun sake jina a wani book d'in nawa.
Idan wannan labari yayi kama da taka rayuwar kayi hakuri arashi ne kawai
Alhmdllhi Ubangiji na gode maka
Ni ce dai Taku
ZAHRA ROYAL STAR CE✍️
Littafin kud'i ne idan kika Karanta min book baki biya ni hak'k'ina ba, kije keda Ubangiji, ki biya ki karanta cikin salama
D'ari hud'u ne kacal #400
Phone number
08130479973