Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
koda bangon duniya ne indai zata bar K'asar Goa, indai Allah ya taimake su ya fitar dasu daga cikin annobar nan bata jin zata sake barin K'asarta Nigeria, ko za'a kasheta kuwa dan hakan.
Wani irin murmushi Anjali ta saki tana nuna masu wata y'ar k'aramar Mota dake can gefensu, sai dai motar a bud'e take duk anci uwarta gilassan Motar duk a fashe hatta gaban motar yayi raga-raga, duk da haka su dai idan zata tashi tayi tafiya ai tafi tafiyar k'afar da zasuyi, domin tafiyar k'afa tafi hatsari sosai a cikin wannan hali da suke ciki.
Da sauri suka k'arasa gaba d'ayansu, suna cire gawar wani mutum daya mutu a cikin Motar.
Gaba d'ayansu suka hau Motar, Faruk ne yasa key d'in motar cikin ikon Allah motar ta tashi, murmushi ya saki shima kansa kamin ya tayar da ita suka fara tafiya.
_____________________
Tafiya suke a k'afa mai wahalar gaske domin Kai tsaye taswirar nan nuna masu hanya take can k'arshen garin Goa.
Ga wata rana da safiyar aka tashi da ita mai cizo ma kuwa.
Shi yasa idan ka kallesu tafiya kawai suke a sukwane.
Sauk'in su d'aya da sunci k'aro da Zombies akwai Bindiga a hannunsu harbi kawai suke d'auke su dasu, shi yasa tafiyar tasu babu gargada.
Farida ce ta saki y'ar k'arar murna tana nuna wata bos d'in mota mai d'an girma kamar ta d'aukar lemo domin bayanta a bud'e yake.
Da d'an gudu ta k'arasa inda motar take parking babu kowa a cikinta sai wasu Gawawwakin mutum hud'u yashe a wajan Motar a k'asa.
Izuwa yanzu ta saba ganin gawawwakin mutane, dan haka suma da murna suka rink'a shiga bayan Motar sai Captain Harun da Joha suka shiga gidan gaba sauran kuma suka shiga baya.
Captain Joha ne yayi k'ok'arin tayar da Motar amma tak'i tashi, hankalin su ya soma tashi ganin mota taki tashi kwata-kwata.
Yayi-yayi amma tak'i tashi, Captain Harun ne ya ce ya basa tokin ya gwada ko zata tashin.
Captain Joha ya basa wajan tokin shi kuma ya koma wajan mai zaman banza.
Yana zama ya fara k'ok'arin tayar da ita, sai tayi kamar zata tashi sai kuma ta mutu, sun kai minti ashirin ana abu d'aya.
Waro ido Farida tayi suda ke bayan Mota suna hangin abunda ke faruwa a waje a bayansu .
Wasu dondozen Zombies ne suka shawo wata kwana suna tafiya akan titin da motar nan ta mutu, tafiya kawai suke suna nufo motar duk da basu ji motsin wani abu ba, to amma har sun fara d'aga hanci suna jiwo k'amshin mutane.
Ganin Farida na neman fasa masu ihu yasa Captain Abbakar saka hannunsa yana toshe mata baki da k'arfi, domin yaga har yanzu basu san ainafin inda suke ba, lalube kawai suke suna tafiya.
Wata uwar harara ta b'alla masa tana kiciniyar kwacewa daga rufe mata baki da yayi.
Doctor Anam zatai masa magana Asiya ta rigata matsowa inda suke tana saka hannunta wajan kwace bakin Farida da Abbakar yasa hannunsa ya toshe mata baki.
Fisge ta tayi daga hannun Abbakar d'in tana d'an harararsa itama ta ce.
"Kai naji da mutum dan Allah, ya za'ai ka wani toshe mata baki baccin Allah ya halitta mata bakin sakin ihun, ko ni ce na fara cin karo dasu wallahi ihun zan saki".
Wani irin kallo ya bita dashi zaiyi magana kawai suka ga an figi motar da k'arfi har wasu daga cikinsu na zubewa k'asa a cikin Motar, wani irin gudu suka ga anayi dasu.
Sauke ajiyar zuciya Asiya tayi tana kallon yadda Zombies suka biyo su sunyi masu nisa a yanzu da motar tashi.
Dan itama sosai abun ya bata tsoro ganin Zombies d'in nan da Farida ta fara gani, ga Mota tak'i tashi.
Abbakar bai sake magana ba ya wani koma daga gefe yana wani basarwa.
Kusan su duka suka bisa da harara daga doctor Asiyar har Farida.
Wani munafikin burki Captain Harun ya ja saboda saura kad'an su had'e da wata k'aramar Mota dake a gabansu.
Suma na cikin motar da sauri suka ja suka tsaya.
Su Anam ganin anja wannan uban birki yasa su sakkowa jikinsu na rawa kar dai Zombies ne suka tare masu gaba?, to amma idan sune ai zasu iya bi ta kansu su wuce, kai akwai matsala shi yasa kowa dake bayan Motar yayi hanzarin fitowa, domin kar wani abun cutarwar ya k'araso inda suke ga bayan Mota a bud'e.
Da d'an mamaki su Harun ke kallon Motar data sha gabansu tana shigowa tsakiyar titi babu kulawa shine yasa Harun ya kusa yin ciki dasu.
Gaba d'ayansu sun tsaya suna jiran ganin su waye zasu fito.
Hanan ce farkon b'alle marfin Motar ta fito gaba d'ayanta.
Wani irin zare ido tayi tana nuna wa'inda take gani a gabanta da zallar mamaki take son furta wani abu amma ta kasa, haba hawaye ne kawai suka fara rige-rigen zubo mata akan fuskarta.
Da wani irin gudu Anam ta kwace hannunta dake cikin na Doctor Fahat nufi inda Hanan take tsaye.
Wata wawar runguma tayi mata har suna k'ok'arin zubewa k'asa wani irin kuka suka fashe dashi suna sake k'ank'ame juna kamar ance za'a sake rabasu.
Su Faruk ne suka fito suma cike da tsananin murna suke kallonsu suma wani irin annuri ne ke fita daga kan fuskar tasu.
Sakinta Anam tayi tana tattab'a ilahirin jikin Hanan d'in tana kuka take fad'in.
"Dan Allah ki ce min kece a tsaye a kusa dani, kar kice gizo ne kike min, ki ce kece K'anwata dan Allah kamin magana na gasgata zance na".
Itama cikin muryar kukan ta ce.
"Wallahi Aunty Anam ni ce ba gizo bane".
Hawayen dake zubo mata tasa bayan hannun tana d'auke su wasu na sake zuba.
Jikinta na kyarma na tsananin murna ta sake rungumeta, sakinta ta sake yi tana sake shafa fuskarta duk ta rud'e. Hango su Faruk yasa ta saki Hanan da sauri tana matsawa kusa dasu, kawai alama tayi masu da ware hannunwanta alamar suzo gare ta.
Da d'an sauri suka k'arasa inda take basu tsaya ba suka rungumeta, wani kalar kukan dad'i ne Anam ta sake rushewa dashi na ban tausayi.
Hatta su Captain Harun dake tsaye wasu y'an guntun hawaye ne suke sharewa abun ya tab'a ransu.
Hanan hango Farida na jifanta da murmushi yasa ta zaro ido waje da mugun mamaki ta ware baki tana kiran sunanta cike da tsananin mamakin gaske.
Jikinta na rawa had'e nufar inda Faridar take tsaye.
Ai tana zuwa ta fara shafa fuskarta tana kuka da hawaye sai kawai ta saki dariya mai sauti tana sake kallonta, bata san lokacin data jawota jikinta ta rungume ba.
Kuka Hanan take a jikin Farida tana cewa.
"Dan girman Allah Farida ki yafe min, nasan duk ni ce silar shigarki cikin wannan hali da muka tsinci kanmu a ciki, da ban matsa dole sai dake zanyi tafiyar nan ba da baki kasance a tare damu a nan ba, ki yafe min kinji?".
Itama Faridar na hawaye ta d'an saki Hanan d'in tana kallonta ta ce.
"Na yafe miki ranki ya dad'e Allah ya yafe mana baki d'aya".
Girgiza kanta Hanan tayi tana sake cewa.
"Karki sake ce min Ranki ya dad'e daga rana irinta yau mun zama d'aya, ke kinma koma y'ar cikin ahalinmu gabai d'aya, daga yau kece Auntyta ta biyu, daga yau kin zama y'ar Familyn B Radda".
Wasu irin hawayen murna suke sake b'alle ma Farida bata san lokacin da itama ta sake jawota ta rungume ba.
Anam ma dake jinsu yanzu taje garesu ta had'a ta rungume suna ma Allah godiya buwayi gagara misali, wadda cikin hikimarsa ne ya had'asu.
Ganin abun nasu bamai k'arewa bane yasa Captain Harun yi masu maganar murnar ta isa haka su shiga mota d'aya a yanzu ko sun samu su kai inda suke son kaiwa.
Cike da tsananin murnar ganin junansu suka shiga babbar motar da su Captain Harun ke ja.
Sun cika da murna sai labari suke ba junansu bayan rabuwa, idan ka kallesu sai ka rantse da Allah sun fita daga masifar da suke ciki ne, ji suke kamar komai ya kusa zuwa k'arshe tunda dai gashi suna shirin zuwa inda cutar bata gama zuwa wajan ba, k'ila ma sukai sa'a a cikin Asibitin su samu waya su kira Nigeria a turo jirgi yazo har asibitin a kwashe su subar Goa su dai shine burinsu kawai a yanzu.........
EPISODE 17TO18
Wani irin gudu yake da motar a tsiyace, domin koda Zombies ne suka shige masu gaba ta kansu kawai yake bi ya latse su ci gaba da tafiya.
Basu tab'a tunanin Motar nan zata tsaya masu ba kawai suna cikin tafiya Mota ta kakare tak'i tafiya.
Kusan gaba d'ayansu ne suka rink'a sakkowa k'asa gabansu na fad'uwa.
Captain Harun ya kallesu yana d'an buga jikin Motar cike da taikaici ya ce.
"Motar nan ta tsaya, dama kuma can da alama ba lafiya ce ta isheta ba".
Captain Harun ya k'are maganar yana wani irin kallon gefen da Farida take, tare take da Hanan manne da juna sai kace y'an biyu.
Lura tayi dashi suna had'a ido ta shagwab'e masa fuska, bai san lokacin daya saki wani munafikin murmushin gefen baki ba, yana d'an shafa sumar kansa.
Abbakar dake ankare dasu komai zasuyi yana nan idonsa akansu, wani irin haushi ne ya kuma rufesa sosai ji yake kamar yayi Bindiga.
"yanzu a k'afa zamu ci gaba da tafiya har Allah yasa muga k'ara samin wani abun hawan idan akwaisa".
Cewar Joha.
Tafiya suka somayi ga dare ya fara kutsu kai, ganin dare ga duhu dake neman rufe garin yasa suka yada zango a bakin wata bishiya mai tsawo da kauri, saboda tunda suka fara tafiyar k'afar nan basu had'u da wani gida ba a gabansu ko inda zasu d'an shiga su kafe.
Hura wuta sukai tana ci a gabansu a inda suka yada zango, kowannan su ya zauna wasu na d'an tab'a fira, wasu ko baccin wahala ne ya fara d'aukarsu.
A hankali a hankali dare ya fara tsalawa sosai baka jin motsin komai sai na kukan wasu tsintsaye, sai kuma kukan wasu halittun daban ga wata irin iska dake busu su kota ina.
Su dukansu bacci ya fara figarsu, basu aune ba suka ji ihu ya k'arad'e wajan gaba d'aya.
Wata wawar zabura sukai gaba d'ayansu suka mik'e zuciyar kowa na tsananin bugawa da k'arfi.
Kusan matan curewa sukai waje d'aya sai kyamar tsananin tsoro suke, sunma kasa magana.
Ta cikin hasken wutar da suka hura da bata idasa mutuwa ba, suka hango Abbakar ne ke wannan ihun, domin suna cikin bacci kawai yaji kamar ana ja masa k'afa, tun yana d'aukar ko a cikin mafarki ne har dai yaji abun yayi yawa ya farka a zabure.
Yana bud'e idonsa kawai yayi tozali da wani mutum ya koma Zombie sai jan k'afarsa yake yana neman inda zai kafa masa cizo.
Ai bai san lokacin da yayi wata irin muguwar zabura ba had'e da sakin gigitaccan ihu.
Abun nashi kamar dambe haka ya farayi da Zombie d'in nan mai nacin tsiya.
Domin kayar dashi yayi k'asa suka fara artabu sai k'undun bala suke a k'asa yana kiciniyar kwace kansa amma kamar k'arfi ake k'arama Zombie d'in nan ya dage iya k'arfinsa sai ya ciji shi.
Abbakar fa anga haza domin k'arfinsa ya soma k'arewa, Bindigar dake cikin aljihon wandonsa ma suna birgima ta fad'i bai sani ba, sai lalubarta yake son yi amma ya kasa.
Saura kad'an Zombie d'in nan ya kai masa cizo akan wuyansa, kawai yaji k'arar Bindiga an harbi Zombie d'in dake jikinsa, fad'owa yayi a jikin nasa baya motsi dan haka jiki na rawa ya hankad'asa gefe ya fad'i k'asa.
A mugun tsorace ya mik'e yana kallon wadda ya cecesa, mamaki ne ya kashesa ganin Captain Harun ne tsaye a wajan akansa, d'an tab'e baki yayi hakan baisa yaji wani abu ba, hasali ma wani haushinsa ya sake ji. Ko a jikin Captain Harun saima ya d'an d'aga k'afad'arsa ya bar wajan, ko godiya Abbakar bai masa ba.
Kamar jira ake a kashe Zombie d'in nan suka fara ganin kota ina b'illowa suke, dole tasa su Captain Harun fara harbinsu kota ina, da gudun masifa suka bar wajan.
Tunda suka bar wajan nan da suka yada zango basu tsayaba har asubahi tayi.
A gajiye suke gaba d'ayansu tafiyar ma har sun fara sarewa da ita, jan k'afa kawai suke Captain Joha na rik'e da Taswirar nan shike nuna masu hanyar daya kamata subi.
Ruwa suka samu sukai sallah ita ta sake basu kwarin gwaiwar ci gaba da tafiya, domin suna yin sallar nan suka ji wani d'an k'arfi yazo masu, dan haka basu tsaya wata sanyawa wajan ci gaba da tafiya ba.
Sun fara karaya tunda suka taho Motar nan ta lalace masu a hanya har yanzu basu ci k'aro da wata ba ko wani abun hawa da zai d'an taimaka masu.
Sai dai Allah gafurin rahimu ne domin suna cikin tafiya kawai suka ci karo da wata Motar Asibiti babba a tsakiyar titi anyi mugun hatsari da ita.
Kusan GAWA biyar ce a yashe a k'asa an masu mugun kisa babu kyan gani, a ciki ma sai da suka fitar da Gawar direban Motar.
Yanzu ma Captain Harun ne ya ja Motar sauran kuma suka shige baya.
Cike da tsananin murna suka fara tafiya Taswirar nan na nuna masu hanya sosai suna ganewa.
Allah mai iko kuma buwayi ne gagara misali, domin tafiya kad'an ce suka sha wata uwar kwana sai gasu sun b'illo asibitin da aketa basu labarin shine cutar bata shiga cikinsa ba.
Sai dai fa akwai wani babban tashin hankali da suka ci karo dashi a bakin asibitin.
Domin wasu dondonzon Zombies ne gaba d'aya sun gama zagaye k'ofar asibitin, kai gaba d'aya ma sun kewaye asibitin. Sai dai an riga da an rufe ko wacce k'ofa dake a cikin Asibitin, Zombies d'in nan sai gunji suke suna kokowar shiga asibitin da tsiya.
Domin yawansu harya zarce masali.
Tofa su Hanan suna hangen abunda ke faruwa da irin abunda ke gabansu.
Zuciyarsu sai bugawa take Asiya ta kasa hakuri ta rik'e baki jikinta na rawa take fad'in.
"Yau munga samu ga kuma rashi, Innallihi wa'inna alaihir raju'on, kai jama'a, yanzu ya ma za'ai mu fara tukarar k'ofar shiga asibitin can?, ai ko Karen hauka ya cije ka wallahi baka fara kai kanka wajan can, dubi ku gani fa, irin uban yawansu a bakin k'ofar shiga asibitin, yadda kasan gaba d'aya wa'inda suka zama Zombies na garin Goa ne fa a bakin Hospital d'in nan, yo ai yawansu yayi yawa, wai Allah nah".
Asiya ta k'are maganar tana tashi tsaye sai sake lek'en su take.
Hanan ma kasa hakuri tayi ta ce.
"Wallahi nima abunda ya ban tsananin mamaki da tsoro, dubi yawansu fa kamar yawan wani gari gudu, yadda kasan duk nan suka taho suka tare, ko shi yasa Direban nan yake ce mana akwai had'ari zuwanmu asibitin?, ai bama zuwan ba shiga cikinsa ne babbar matsala a gare mu".
Captain Harun ne ya fara sakkowa k'asa domin sunyi parking d'in Motarsu ne nesa da bakin k'ofar shiga asibitin.
Wata Motar ba shukoki ruwa ya hango daga can gefensu, murmushi kad'an ya saki yana anbatar.
"Yes zamu shiga asibitin nan amma fa akwai had'ari gaskiya".
Captain Joha dake dubansa ya ce.
"Tayaya zamu fara tun k'arar shiga cikinsa?, ka kalli irin yawansu kowa a bakin k'ofar shiga asibitin?, kuma idan ma mota muka ce mu shiga mu bi ta kansu da k'arfi da yaji ai su wa'inda ke cikin Asibitin bazasu bud'e mana k'ofar ba, sana idan muka ce zamu karya k'ofar kuma akwai matsala, za'ai biyu babu kenan fa".
Dafasa yayi Harun yayi kamin ya ce.
"Ba haka zamu shiga asibitin ba, jawo hankalinsu zamuyi garemu su bar k'ofar asibitin, ni zan shige mana gaba waccar motar ruwan da nake gani a gefenmu zan rik'e abun bada ruwan ina fyasa masu shi ta haka zansa bazasu tab'a k'arasowa inda muke ba, har kowa ya shige ciki".
D'an lumfashi kad'an ya sauke, yabi bayan Harun d'in, bututun ruwan suka jawo da kyar.
Captain Joha ne yaje ya basu umarnin cewa su sakko gaba d'ayansu.
Gaba d'aya sakkowar sukai kowa ka kalla fuskarshi cike da tsoron abunda kaje ya dawo.
Suna kallon yadda Captain Harun ya nufi k'ofar asibitin gadan-gadan gabansu ba abunda yake sai tsananin bugawa, Farida ko runtse idonta tayi zuciyarta na tsinkewa.
Suna gani ya jefa masu wani dutse k'arar dutsen ne da suka ji, gaba d'ayansu Zombies d'in suka wani juyo lokaci d'aya suna wani irin azababben gunji da gurnani kamar zaki gaya abun harinshi.
Gaba d'ayansu ne suka fara tahowa inda suke suna wani irin shinshine-shinshine gaba d'ayansu babu kyan gani jini duk ya gama b'ata masu jiki fuskar wani idan ka kalla baka fatan Allah ya sake had'aka dashi bare har kalleshi, wasu ma basa gani makafi ne saboda wasu an kwalkwale idon gabai d'aya, wasu sun rasa hannuwa wasu ko kafarce a karye amma tsabar jaraba a haka suke tahowa burinsu kawai suci naman Bil Adam susha kuma jininsa.
Gaba d'ayansu su Hanan suka fara ja da baya Captain Harun suna gaf k'arasowa inda suke ya kunna bututun ruwan nan ya fara watsa masu, wani ihu-ihu suka fara yi a haka ya rink'a watsa masu suna zubewa k'asa suna sake tashi, a haka ya rink'a baya dasu har suka dawo bayansa yana watsa masu ruwan nan.
Su Hanan dasu Faruk da gudu suka je bakin k'ofar shiga asibitin tunda gaba d'aya Zombies d'in Captain Harun ya d'auke hankalinsu daga bakin k'ofar.
Dama ta cikin Asibitin camare ta nuna ga wasu nan zasu shigo dan haka suna zuwa aka bud'e k'aramar k'ofar shiga ciki, wasu suka fara shiga d'aya bayan d'aya.
Captain Harun kusan shine k'arshe, domin ruwan k'arewa yayi sai dai ya rink'a anfani da bututun ruwan yana buga masu shi a saman kai.
Yana shiga ya hango Abbakar bai shiga ba, ga k'ofa da ake niyar rufewa, da wani irin mugun tsalle ya fita ya kamo hannunsa da k'arfi ya jawosa, sai