Gawa Tafe Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 13

21K to 24K   out of 39K words

sai gawar wani D'an Sanda dake gefe, da alama tashi ce Bindigar. Zombies sunma gawarsa wani mahaukacin kisa babu kyan gani.

Motsin Zombies da suka ji a inda suka ja suka tsaya ne yasa su fara zare ido, da sauri Faruk ya niyar kamo hannun Jasmin domin subar wajan yaga ta fisge ta nufi inda ta hangi Bindigar nan.

Rufe bakinsa yayi yana girgiza ma Jasmin kai hankali a tashe su duka suke girgiza mata kai, hatta Farida data fi shiga halin rud'ewa kuka kawai take tana faman girgiza mata kai kamar k'adangaruwa.

D'aukar Bindigar kawai tayi tana saita dai-dai saman kanta, tana rik'e bakin Bindigar.

Ga Zombies data basu baya hawaye na shatata akan fuskarta.

Gaba d'ayansu ja da baya suka kama yi gudun kar Zombies d'in dake gaf da isowa inda suke.

Hanan ce ke kuka da k'arfi take kiran sunan Jasmin tana cewa.

"Dan Allah Jasmin karki yi haka, ki dakata daga abunda kike k'ok'arin aikatawa babu kyau hakan da kike k'ok'arin yima kanki dan Allah Jasm...

Ai kamin ma ta k'are maganar kawai suka ji k'arar Bindiga ta tashi, kusan gaba d'ayansu ne suka runtse idonsu da sauri, zuciyoyinsu na harbawa da k'arfin gaske.

A hankali suka bud'e idon nasu, Farida ce farkon sakin wani ihu domin idonsu yayi masu tozali da Gawar Jasmin data sakar ma kanta harsashi akanta nan take ta fad'i babu rai a jikinta.

Wani gigitaccan kuka Farida ta saki tana fad'uwa k'asa, kuka take tana rufe fuskarta da tafukan hannunta, kuka take tana ganin Zombies duk da Jasmin ta mutu sun haye ruwan cikinta sai bidiri suke.

Hankali a mugun tashe Anjali ta rarumo hannun Farida ta tayar da ita tsaye taja hannun suna niyar barin wajan.

Gaba d'ayansu ne suka bar wajan jiki a mugun sanyaye.

Farida ko tana kuka tana waigen gawar Jasmin da Zombies suka gama yima kaca-kaca.

Airport Rd Dabolim Goa

Jirginsu Harun ne ya fara dira a Babban Airport dake K'asar Goa.

Ya sauka da y'an mintoci nasu Anam ya dira shima.

Sai dai har yanzu suna a cikin jirgin ba'a basu damar fitowa ba.

Harun tsaye a tsakiyar jirginsu kowa ka kalla yayi shirinsa hatta kayan dake jikinsu na bada kariya ne daga farkin abun cutarwa.

A hankali yake masu wani jawabi kamar haka.

"Ya kamata mu natsu muyi nazarin irin illar da wa'innan Zombies d'in suke dashi idan suka ci karo da wadda yake mutum normal, muyi taka tsantsan mu kula, an bamu damar harbi ga duk lokacin da muka ci karo da wadda ya gama komawa Zombie, fatan kun gane abunda nake nufi?".

Kusan gaba d'ayansu ne suka sara masa suna basa amsa a tare.

Abubakar dake gefe ya wani k'ame sai sakin wani murmushin mugunta yake na gefen baki, Joha duk yana ankare dashi, kuma ya tsorota da ganin murmushin daya saki, ya zuba masa ido ne kawai yaga iya gudun ruwansa, da miye yake son aikatawa?, tabbas yasan akwai abunda ya taka har yasashi wannan munafikin murmushin nasa.

A hankali cike da takatsantsan suka fara sakkowa daga cikin Jirgin.

Wasu daga cikinsu zuciyoyinsu ne suka fara bugawa, ganin yadda Airport d'in kanta ta hargitse kota ina gawar mutane ne birjit a wajan, motoci gasu nan duk sun faffashe gilassansu wasu sun kama da wuta suna ci, jini ko kota ina takasa kike.

Kai gaba d'aya yanayin garin ya koma kamar wadda akayi yak'i aka ci garin da yak'i.

Bin K'asar Goa kawai suke da kallo.

Tunda suka fito dai basu ci karo da Zombies ba, hasali ma babu kowa a falin Jirgin.

Wata iska ce ke hurowa shuuuuu sai wasu y'an k'ananun koke-koke had'e da d'an ihu dake fitowa nesa da Airport d'in.

Su Anam ma sun gama fitowa, abunda suke jiyowa ne yasa ma zuciyarsu rauni had'e da wani tsananin tsoro da ya gama rufe masu jiki.

Domin su ba'a basu wata Bindiga ba, sai dai abubuwan kare kai kamar su k'arfe ko rodi, wadda idan Zombies sun kawo masu hari su kare kansu.

Gudu-gudu sauri-sauri suka shiga wata babbar mota, bayanta dogo ne, gaba d'ayansu har Sojojin a motar suka shiga.

Ganin sai tafiya ake dasu yasa Anam cewa.

"Wai ina muka nufa ne yanzu?, ba cewa akai za'a fara kaimu fad'ar shugaban k'asar Goa d'in ba?".

Matuk'in Motar ne yayi gyaran murya da harshen turanci ya fara cewa.

"Ai yanzu haka Fad'ar ta gama gazawa, tun kuna hanya Zombies suka gama fasa Fad'ar yanzu haka shima shugaban yana can yana gudun cuton ransa, muma nan da kike gani zamu ci gaba da gudu ne har lokacin da zamu ga miye Allah zaiyi.

Amma akwai wani asibiti dake K'asar nan ance shine kad'ai har yanzu Zombies basu shiga can ba, amma zuwa Asibitin yanzu shine Babban hatsari a garemu, domin nesa da cikin gari aka yisa, kamin ma muce munje garesa za'a iya rasa rayuwaka da dama".

Tofa gaba d'ayansu ido waje suka sauraron abunda driver nan ke fad'a.

Captain Harun ne ransa ya soma b'aci, jin kamar an kawo su ne dama dan kawai ayi anfani dasu, idan ya so su mutu ma babu ruwansu, duk manyan k'asar su ne suka ja masu ai, domin yasan da babu Y'ay'ansu a ciki wallahi ko Goa zata tashi baza suyi maganar cewa zasu basu taimako ba.

"Miye kike fad'a haka?, mu ai ba haka aka ce mana zamu zo mu iske ba, ko dai dama akwai wata manufar turo mu K'asar nan ne bamu sani ba?".

Cewar Harun.

Wata Soja ce ta tashi tsaye tana duban Harun kamin ta ce.

"Ai Sir baka da labarin Y'ay'an Gwamna suna K'asar nan, harda ma Y'ay'an shi shugaban k'asarmu, shi yasa basu gaya mana ainafin abunda yasa suka turo nan ba, sun turomu ne kawai don mu ceto Yaransu da abunda ya rutsa dasu a K'asar nan".

Idan ka kalli Harun a lokacin tabbas zaka san ransa ya b'aci, danmi shugaban Sojojinsu bai gaya masa hakan ba?.

Doctor Anam ita kam ko a jikinta domin tasan da manufar zuwansu.

Doctor Asiya ce ta kalli Doctor Halisa tana d'an tab'e baki ta ce.

"Au dama akwai Y'an family d'in Doctor Anam, da abun ya rutsa dasu a K'asar nan?. To ya ma za'ai mu fara nemo inda suke ne?, wama ya sani ko sun mutu?, nifa wallahi baccin naji ance za'a bamu kyauta da number yabo babu d'an iskan shugaban da zai sani zuwa K'asar Goa d'in nan wallahi, ba'a haife ubansa ba bare shi kansa ma.......

Doctor Anam ce ta mik'e tsaye a zuciye ta nuna Doctor Asiya wadda yasa Doctor Asiyar katse maganar data ke son idasa fad'a tana cewa.

"Karki sake ki sake anbatar sunan Iyayena kina zagi, wani ya ce dole sai kin zo ne?, akwai wadda akai ma dole a cikinku gaba d'aya?"

"Kuyi ma mutane shuru a nan wajan, kuna abu sai ka ce k'ananun Yara"

Fad'in Doctor Fahat.

Harun ne ya d'an saki tsaki yana nuna Doctor Fahat domin yaga alamar kamar shine Babba a cikin Doctors d'in.

"Doctor ya kamata kaja masu kunne, bama son hayaniya muna cikin neman mafita, so please su san miye suke yi".

Tab'e baki matan sukai wasu najin zafin Harun dake nuna kamar yafi kowa.

Muryar Harun suka sake ji yana driver motar magana yana cewa.

"Zaka iya yi mana jagora har iya zuwa wannan asibitin?".

Zaro ido waje direban yayi hankali a tashe yake fad'in.

"Gaskiya ranka ya dad'e akwai babbar matsala idan muka ce zamu nufi asibitin nan yanzu, ba lallai mu duka muje a raye ba, gaskiya ni dai daga nan zan iya sauka na zan baku wata taswirar da zata nuna maku hanyar zuwa asibitin da nake maku zancensa"

Doctor Asiya ce mik'e tana fad'in.

"Banga dalilin da zaisa dole sai mun nufi Asibitin nan ba, mi ya kawo mu?, ba taimako ba?, kawai mu shiga mu fara neman wa'inda aka kawo mu dominsu mana?".

Wani kallo da Harun ya wurgama Asiya yasa ta shan jinin jikinta.

Zabura sukai jin k'arar bugun motar da suke ciki had'e da girgiza motar.

K'ara su Anam suka saki ganin Zombies ne suka yayyab'e Motar tasu, duk da tafiyar da suke yi sai wani gunji suke had'e da gurnani suna son fasa gilashin Motar.

Tsakiyar motar suka dawo jikinsu na d'aukar rawa. Duk abunda ke faruwa Harun yana inda yake tsaye ko a jikinsa, sai ka ce baiga abunda suka gani ba.

Su Abbakar ma abunda suka gani ne ya d'an tab'a zuciyarsu, amma suka dake a matsayinsu na Sojoji.

Doctor Asiya bakinta na rawa take nuna jikin window tana fad'in.

"Innallihi wa'inna alaihir raju'on, dama haka mutum yake komawa kamar wani horror?, mukam mun shiga uku, ku duba yadda suke son fasa gilashin Motar nan, ya Salam mun bani mun shiga uku, Allah ya kawo mu lahira, mun kawo kanmu makasa da kanmu wallahi".

Wata uwar harara Fahat ya watsama Asiya, itama kuwa ta banka masa tata a fakaice.

Gaba d'aya hankalinta ya gama tashi.

Suna ganin yadda direban ke bi ta kansu yana latsewa suna iya jin ihunsu marar dad'inji.

Tafiya kawai suke Zombies na sake mak'ale Motar, wasu na fad'uwa k'asa ana latsesu, wasu na tafiya daga nesa dasu suna hangen yadda suke tafiya a lauye kai a jirkice.

_____________________

Suna uban gudu kawai Hanan wani dutse ya tab'iyeta ta fad'i k'asa.

Ihu ta saki ganin wasu Zombies guda biyu na gaf da isowa inda ta fad'in.

Da gudun masifa Farida ta nufi inda Hanan ta fad'i tana kiran sunanta.

"Wayyo Allah Hanan ki ta so da sauri".

So take ta mik'e amma yadda kasan ansa wani maganad'ison k'arfe an danne ta.

Kuka take sosai su Faruk da sukayi nisa suma dole suka tsaya.

Kamo k'afarta sukai Zombies d'in guda biyu, sai janta suke tana ihu tana kuka.

Da k'arfi Farida ta rik'e tsintsiyar hannun Hanan d'in tana ja itama suna ja.

Gaba d'aya hankalin Hanan ya gama tashi, k'irjinta sai dukan tara-tara yake, tsoronta d'aya karsu kai mata cizo ko su karceta.

Tana kuka tana ihu saisa k'afar take tana harbinsu suna gunji suna sake manne mata.

Wani dutse ne Farida ta hanga da sauri ta saki hannun Hanan d'in ta d'akko dutsen ta shammaci Zombies d'in tasa k'arfinta tana bugama d'aya daga cikinsu.

Wani ihu ya saki marar dad'i, ya zube wajan yana shure-shure.

D'ayan ne yak'i sakinta sai so yake ya kai mata baki a k'afar tata, so kawai yake ya cijeta.

Jikin Farida har yanzu na rawa zata sake kwad'ama wadda ya rage kawai itama wadda ta kwad'ama daga farko ya mik'e ya shammaceta ya cafke k'afarta.

Ihu ta saki tana salati jikinta na sake d'aukar rawa zufa ta wanke mata fuska.

Al'ameen ne ya rugo da gudu yana zuwa yasa k'afarsa da k'arfi ya danne fuskar Zombie d'in da ya kama k'afar Farida, wani irin ihu ya saki da gunji, yana sakin k'afar tata.

Tana jan lumfashi da k'arfin hali ta sake kwad'ama wadda yake ta k'ok'arin sai ya ciji Hanan d'in.

Yaja jin saukar duka a kansa ya saketa yana zubewa a sume.

Da mugun sauri ya mik'e jikinta na mugun-mugun rawa kamar mazari, ga wata uwar zufa data gama jik'e mata jiki.

Bata tab'a d'auka zata tsira bama, ta d'auka shikenan zasu cijeta itama.

Rik'e hannun Farida tayi da k'arfi tana sake k'ank'ameta.

Ai bata san lokacin data fad'a jikin Faridar bama, tana rushewa da wani irin azababben kuka, mai tafe daga can k'asan zuciyarta.

Itama Faridar kuka take sosai, da sauri Al'ameen ya kallesu yana sauke lumfashi shima ya ce.

"Ya kamata ku daina kukan nan haka nan, mubar wajan nan kawai, tunda Allah yasa babu abunda sukai mata".

D'an sakin juna sukai suna ci gaba da tafiya gaba d'ayansu jiki a sanyaye..............

EPISODE 12

Wata shopping mall ce suka ci karo ta da ita dan haka da sauri su Faruk ne farkon idasa shigewa cikinta.

Kallon-kallo aka tsaya yi daga shigowarsu ganin dondonzon Zombies da suka ci karo dasu, suna shiga k'aton shagon sayayyar.

Da mugun Tashin hankali suka fara ja da baya, da baya, suma Zombie d'in na sake kusanto su.

Da k'arfi Faruk ya rik'e hannun budurwasa wacce ta sake damk'e hannun nasa kamar zata b'allasa, tsabar kid'ima da razana.

Su Farida dama sune a baya dan haka da sauri suka juya domin ficewa daga cikin shigon, suma kamar saukar aradu haka suka ci karo da wasu Zombies a bayan nasu, amma su mutum biyu ne, d'aya ma baida hannuwa gaba d'aya an cire tsintsiyar hannun nasa, sai baki da fuska da k'afa kawai, a haka yake tafiya a lauye yana karkace kai k'afafunsa kansu d'aya a karye take, a haka yake janta tsabar masifa sai wani gunji suke suna wani irin gurnani.

Sake ja baya sukai suna sake duban gabansu, hankalinsu ne yayi mugun tashi.

Hanan ko k'ank'ame take da Farida, Ahmad d'inma ta kyalesa waje d'aya, tsabar halin data tsinci kanta.

Wata muguwar sufa Hanan tayi ta zame daga k'asa tana jawo Farida suka fad'a tare, kamin ka ce mi sun fice daga cikin Shagon, sun shammaci na gabansu Zombies d'in, tunda d'aya dama bai da hannu.

Su Faruk da mugun sauri yasa k'afa yana tab'iye d'ayan dake gabansu, ya fad'i yana sakin k'ara.

Na bayansu ko ganin yawansu yasa shi jan hannun budurwasa da k'arfi, sai dai yana janta sulb'in wajan ya kwasheta, gashi dama ta sanya wasu y'an iskan takalmi ji kake timmmmmmmmm, ta fad'i k'asa.

Bakinta ya fashe amma bata ji zafin fashewar bakin ba, sai ma wani ihu data saki lokacin data jita kasan da kuma jin ta bayanta an rik'e mata k'afa ana ja.

Ihu take tana wurwurga k'afar tata tana hankade Zombie d'in dayayi nasarar cafke k'afar tata.

Ba abunda Faruk yake sai waige-waige zuciyarsa na bugawa.

Muryar Hanan ce sukaji tana cewa.

"Anjaliiiiiii kuyi saurin fitowa daga Shagon nan, gaaaaa wasu Zombies nan tafe zuwa cikin shagon, muyi saurin barin wajan nan akwai matsala babba, saboda zombies sunyi yawa a wajan nan, zasu iya halakamu gaba d'ayaaaaaaaa".

Da ihu take maganar.

Anjali ce ta nufi inda Faruk yake rik'e da hannun budurwa tashi yana ja, Zombies kuma najan k'afarta har yanzu a kwance take data fad'in sai ihu take tana kiran, dan Allah kar su barta a nan su ceceta.

Amma ina da k'arfi Anjali ta fisge hannun Faruk dake jan hannun budurwasa, suka ruga da mugun gudu suna niyar fitowa daga cikin shagon sayayyar gaba d'aya.

Suna iya jiyo yadda budurwar Faruk d'in ke ihun neman taimako, tana kwala kiran sunayensu da duk wadda ta sani.

Anjali tana gudu jaye da hannun Faruk d'in tana waigen budurwar da Zombies suka gama yayyab'eta suna cin naman jikinta, a sadda ta waiga dai-dai lokacin da wani yasa bakinsa a k'afad'ar hannunta kamar asiri abun taga kawai ya cire hannun nata ya fita daga gangar jikinta.

Runtse idonta tayi hawayen tashin hankali na b'alle mata, bata tab'a zubar da hawaye ba sai yanzun.

Danji ji take kamar baza'a koma gida da ita a raye ba itama.

Abun ya fara bata tsoro, yanzu suna tare da mutum sai kawai wata masifar ta kunne kai su rasa wani, zuciyarta ta fara karaya da wannan iftila'in da suka shiga, bata jin suma zasu tsira, domin babu wani taimakon kai da kai da aka turo masu a Goa d'in, bare susa ran wata rana zasu tsira daga wannan annobar.

___________________

Kiiiiiiiiiiiiiiiiiii

Yaja birki wadda yasa gaba d'ayansu fad'uwa a cikin Motar, da sauri wasu suka mik'e, sai Harun dake tsaye ya dafe wani abun Motar bai kai k'asa ba, saboda birkin da direban yaja.

Zasuyi magana kawai kamar ance su waiga gabansu suka hangi wasu uba-uban Zombies sun kusa wasu mutanan gari guda, a gabansu yadda kasan an jera su, kamar jiransu suke dama su iso wajan.

Ji kake muk'utttttt, Doctor Asiya ta had'e wani miyau a mak'oshinta bata shirya hakan ba.

Ido a waje take zaro su tana dafe da k'irjinta dake bugawa sosai.

Ba ita kad'ai ba hatta Anam abunda suka gani a gabansu yayi mummunan tada hankalinta, daka kalli fuskarta zaka shaida hakan.

Garama Doctor Fahat da wani maze kamar ba tashin hankali a ransa, amma can cikin ransa abunfa ya so basa tsananin tsoro, dan har ya fara karaya da wannan tafiyar.

Muryar Doctor Halisa k'asa-k'asa take magana.

"Innallihi wa'inna alaihir raju'on, mima ya kaini baro mahaifata k'asata na biyo ku wannan tafiya wacce zan iya kiranta data ajali ko na ce bak'ar tafiya?".

Kana iya jin yadda y'an hanjin cikinta ke bada wani sauti na tsananin razanar data yi ce kawai ta haifar mata da hakan, ga wata zufa dake tsatstsafo mata ta ko ina a jikinta.

Captain Harun ne kawai yake iya kame ganshi baka isa ka gane tsoro ne akan fuskarsa ko akasin hakan ba.

Su Abbakar ko dole K'anwar nak'i yake mazewa domin wai dai shima kar aga gazawarshi, shima so yake wannan tafiyar da zasu dawo a basa number yabo na farko, a lokacin da aka sami labarin babu Captain Harun ya mutu, yana da tabbacin shine zai maye gurbinsa.

Tunaninsa ne ya katse jin muryar Harun d'in yana kallon direban Motar yana cewa.

"Ya akai ka tsaya?".

"Ranka ya dad'e baka ganin masifar dake a gabanmu ne?".

D'an dafe kansa Harun yayi yana sake d'agowa cike da tafiyar k'asaitarshi, ya nufi wajan da direban yake, da yake motar irin wacce zaka iya tsallakawa ka nufi gaban motar ka shiga ba tare daka fita waje ba.

A hankali ya amshi tokin Motar shi kuma direban ya koma baya, domin ya ce yana gaf su sauke shi su ajesa bazai iya binsu tafiyar da zasuyi mai nisa kuma mai cike da had'ari ba.

Zan iya cewa sadda Harun yaja Motar a mugun tsiyace sai da yasa su Anam wintsilawa tsabar yadda ya figi motar a tsiyace.

Bai wani tsaya gargada ba ya bi ta kan Zombies d'in da suka tare masu gaba.

Wasu dan naci sun haye saman motar wasu sun rik'e abun jikin Motar sun mak'ale, suna jin k'amshin Bil Adam a ciki, shi yasa sai hauka suke suna gunji marar dad'in sauti, sai kartar

8 / 13