CUTA TA DAU CUTA COMPLETE BOOK BY BILLYN ABDULL.txt

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   37 / 38

108K to 111K   out of 113.7K words

nan suka gudu zuciyata zata iya bugawa. Na fiki jin wannan tsoron, dan tun daga jiya zuwa safiyar yau hatta da bugun zuciyata ba dai-dai yake ba. Ni bazan iya jure abinda su Baba suka jure akanki ba Khadijah, dole ne na ɗauki matakin da zai zame min masalaha dan bazan iya jurar rasa yarinyata ba, zan aura masa ita, suje hakan zai fi bani kwanciyar hankali akan ace sun bijire mana zuwa wata duniyar..” hawayen dake neman zubo masa ya sashi kasa cigaba da maganar. Sai kawai ya juya ya shige bedroom dan dama a tsaye yake, ya shige yana ƙoƙarin maida hawayen.
      Da kallo Khadijah da tun furucinsa na (Ni bazan iya jure abinda su Baba suka jure akanki ba Khadijah) hawayenta suka tsaya cak. Illahirin jikinta ya shiga rawa. Dan ba ƙaramin ratsata waɗan nan kalaman sukai ba. Sai zuciyarta ke gaya mata kamar fa gori mijin nata ya mata. Gori yake mata akan abinda ta aikata da ya zama ya shafi ƴarsu a yanzu. A take ta sake fashewa da wani matsananci kuka. Domin wannan shine karo na farko da irin wannan babban saɓanin ya shigo tsakaninsu. Bawai basa samun saɓani ba. Wannan dole ne a gidan kowane aure na kowace ƙabila. Amma a tsahon shekaru goma sha takwas da aurensu bata jin Abaan ya taɓa ɗaga mata murya irin haka, dan shi ko faɗa zaiyi yakanyi ne cikin yanayin sanyinsa da rashin hayaniya. Amma a yau yanda yake ihu mata akai ta tabbata hatta yaransu dake ƙasa duk suna jiyosu...
      Ilai kuwa hasashenta yay dai-dai, dan ta iske Auta da Fharooq na kuka sosai a falon ƙasan. Yayinda take jiyo muryar Muhammad a ɗakin Mimi yana mata masifa yana kuka da ƙalibalantarta akan yau a dalilinta ga iyayensu suna ɗagama juna murya. Yayinda ita kuma take kuka kamar ranta zai fita. Ji Khadijah tai hajijiya na neman kwasarta, dan komai ya gama rikice mata tama rasa ina zata dafa.

      Al'amarin kamar wasa sai abu ya zama babba. Dan gaba ɗaya a cikin satin gidan dake kamar aljannar duniya ha ma'abota rayuwar cikinsa ya zama kamar wani gidan mutuwa. Magabatan Yazeed sunzo. Dan Ministar da kansa tare da vice president da ƙanensa biyu sunzo neman auren Mimi kamar yanda Alhaji Abaan ya basu dama. Bai kuma ja komai da nisa ba duk da raɗaɗin da yake ji a ransa na rabuwa da yarinyarsa da bata gama mallakar hankalinta ba suka gama komai hatta ranar ɗaurin aure. Dan gaba ɗaya wata biyu kacal ya saka musu a lokacin su Mimi na cikin hutu. Aifa ranar sosai Khadijah ta birkicema Alhaji Abaan akan itafa bata yarda ba, bata amince ama Mimi aure a wannan shekarun ba. Dan tana matuƙar tsoron ɗiyarta ta faɗa a makamanciyar rayuwar data faɗa itama. To anan nefa rikici ya ɓarke. Alhaji Abaan yace bata isa ba. Babu fashi zai aurar da Mimi dan haka shine kwanciyar hankalinsa. A gefe kuma Mimi na kuka da roƙon Daddyn nata akan yayi haƙuri kada yay mata aure. Ita wlhy bata son aure a yanzu. In dai Yazeed ne ta rabu da shi har abada. Ko saurarenta ma Daddy baiyi ba. Ranar ma data ishesa da magiya da kuka a karo na farko na tarihi ya faffaleta da maruka biyu da suka matuƙar gigita mata rayuwa. Dan abu ne da bai taɓa faruwa ba. Duk rintsi Alhaji Abaan baya dukan yaransa. Wani lokacin ma idan suka ƙure Khadijah ta dakesu har haushi yake ji. Yafi gane ya zaunar da yaro ya masa nasiha idan yayi ba daidai ba. Amma a ranar sai da Mimi ta samu rabonta har ana ganin shatin hannunsa a farar ƙyaƙyƙyawar fuskarta mai tsananin kamanni da tashi. Aunty Noor ta shiga zancen itama tana beging yayan nata. Amma a karo na farko yaƙi saurarenta akan shifa babu fashi akan aurar da Mimi. Idan sunga zasu je su fara shiri matsayinsu na iyaye suje su fara. Idan kuma bazasuyi komai ba daga an ɗaura aure zai ɗauketa shi kaɗansa ya miƙata gidan miji ne.
      Komai ya caɓe, ƙura ta tashi sosai da ya kai har rashin jituwa yasa a karo na farko Khadijah tai shiri ta wuce Kano. Kai tsaye kura ta nufa wajen dangin iyayensu. Inda takai ƙarar Abaan wajen kawunan ta. Aranar ta dawo cikin Kano ta yada zango a gidan Ni'ima. Inda suka tattauna tare da ita da Zuhrah da mazajensu dake tamkar ƙanne ga Alhaji Abaan ɗin. Basu ɓoye mata ba sun fito fili sun sanar mata kuskurenta na tun farko ko muce maimaita mata tunda kowa ya daɗe da tabbatar mata wannan tun iyayensu nada rai. Suka kuma nuna mata kar taga laifin Alhaji Abaan da yawa a tsorace kawai yake dan yana ganin tarihi zai fa iya maimaita kansa Mimi tabi Yazeed su gudu kamar yanda itama tabi Dafeeq a wancan shekarun. Bata ko musa ba wajen amsar laifinta, ta kuma yi kuka ta sake nadama da roƙon gafarar iyayensu da suka jima da kwanta dama. Haka dai washe gari suka ɗunguma suka koma Abuja wajen Alhaji Abaan, sai dai ita bata bisu ba nan suka barta a Kano ɗin.
        Suma dai sun je sun zauna da Alhaji Abaan tare da lallashinsa da ban haƙuri musamman ganin yanda Mimi itama ke kuka da magiya da roƙon yay haƙuri ta tuba. Dan yanda yarinyar ke a firgice har asibiti aka kwantar da ita na kwana biyu. Duk ta zabge ta rame ta sake yin haske abin tausayi. Ga ƴan ƙannenta ababen farin cikinta sun juya mata baya gaba ɗaya. Musamman ma Muhammad da yafi kowa ɗaukar zafi da ita kasancewar yafi sauran ƴan uwansa wayo. A su ɗin ma dai Alhaji Abaan ya murje idonsa, sai ma haƙuri da ya basu akan shifa yana akan bakansa dan babu fashi. Garama su faɗama Khadijah ta dawo in zata dawo. In ko ba hakaba za ai bikin Mimi ko bata nan. Waɗan nan kalamai nashi sun sake tada musu hankali. Dan dole fa suka komo Kano jiki a sanyaye. Sunta lallashin Khadijah akan ta haƙura kawai ta koma ta barsa yay abinda ya tsara akan ƴarsa. Dan ya riga ya hau sama irin yanda kowa bai san ya iya fushi haka ba. Kuka ta dinga musu dan gani take ita kowa fa baya hango abinda take lurar dasu. Tana tsoron a aurar da Mimi Yazeed ya dawo yaci dunduniyarsu kamar yanda Dafeeq ya mata. To bayan dai sun sake tattaunawa dabarar zuwa ga Baba Hakimi ta zo musu. Haka sukai shiri suka ɗunguma garin Adamawa. Inda suka je suka tattare komai suka sanarma Baba Hakimi daya ƙara tsufa sosai. Haka dai badan yana jin ƙarfi ba suka kwashesa zuwa Abuja. Shine yay zama da Khadijah da Abaan da Mimi, sai da ya gama jin komai sannan yay murmushin su na manya. Sannan ya sallami Mimi ya fara magana da Abaan da Khadijah. Sun tattauna sosai inda daga ƙarshe ya sa Alhaji Abaan ɗin kira masa Ministar da ɗansa Yazeed aka sake sabon zama harda Mimi. Wannan zama shine ya kawo masalaha a tsakani. In da Baba Hakimi ya kawo masalaha akan komai. Yazeed zai yi haƙuri Mimi ta kammala secondary ɗinta. A lokacin shima karatunsa yay nisa. Amma da sharaɗin bazai sake zuwa ya ɗauketa a school ba ko ya fiddata daga gida bada sanin iyayenta ba. Zai dinga zuwa hira wajenta akowane ranar juma'a da yamma, zakuma suyi hirar ne a nan falon gidansu.
      A take Yazeed ya amince. Dan shima hankalinsa a tashe yake sosai da yanda Mimi ta birkice masa tamace su rabu, ta kumayi blocking nashi a waya da kowanne account nata na media. Shi kuma harga ALLAH so da ƙaunarta yake na gaskiya. Ya kuma fahimci wawtarsa da kuskurensa saboda mahaifiyarsa ta masa faɗa sosai kasancewarta mace mai dattako. Anan dai aka sasanta komai aka dai-daita zancen biki ya fasu...

     Bayan ɗan fushi da shashshare juna na kusan sati guda bayan sasantawa Alhaji Abaan da Boddonsa suka shirya kansu. Suka kuma sake ɗaura ɗammarar jan Mimi jikinsu. Yayinda a ɓoye Alhaji Abaan yay mugun sakama Mimi ƴan leƙen asiri ako ina da zata iya kasancewa. Haka itama Dr Khadijah ba'a barta a baya ba wajen sakama ƴar tata idanu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Mimi ta kammala karatunta na sakandare. Yayinda Yazeed ma ke cigaba da nasa karatun. Abin kuma birgewa bayan ta kammala ɗin koda aka tada batun aurensu sai sukace ba yanzu ba sai Mimi ta fara karatunta na Jami'a, shi kuma ya kammala nasa. Hakan yayma iyayensu daɗi sosai, musamman kasancewarsu duk ƴan boko dama. A haka Mimi ta fara karatu a jami'ar, tana lavel 200 Yazeed ya kammala nashi karatun. Ya shiga hidimar bautar ƙasa. Yana kammalawa Babansa ya sama masa aiki mai tsoka, bai zauna ba ya sake shirin joining masters nashi. Zuwa lokacin soyayya ce mai ƙarfi da shaƙuwa a tsakanin Mimi da Yazeed. Ga zuminci ya sake ƙulluwa a tsakanin iyayensu fiye da da. Dan yanzu in ma baka sani ba saika ɗauka Yazeed ɗin ɗan gidan ne. A dalilin Masters da Yazeed zai wuce abroad aka yanke shawarar saka bikinsu. Daya dawo za'a sha biki Mimi ta ƙarasa karatunta a ɗakinta.
      Haka kuwa ne ya faru, dan shekarar Yazeed ɗaya da wasu watanni ya dawo gida Nigeria. Inda aka shiga shirye-shiryen biki na ƴan gata. Dan daga ango har amarya iyayensu duk masu hannu da maiƙo ne. Kafin kace mi zance auren waɗan nan iyalai biyu ya karaɗe shafukan sada zumunta. Inda aka shiga biki na nunama tsara. Amarya da ango duk sun sha ƙyau. Komai suke zaka fahimci cike da so da ƙaunar juna ne. Hakama iyayensu na a cikin matuƙar farin ciki da ganin wannan rana a gare su. Dan Khadijah tayi kuka har bata san iyaka ba. Ansha shagali amarya ta tare ɗakinta. Inda tabar iyayenta da ƙannenta da kewa. Duk da ma zuwa yanzu duk ba zaman ƙasar yaran suke ba saboda karatu. Auta ne kawai a gida sakamakon bana ya kammala nashi secondary ɗin shi. Shima dai ana shirye-shiryen miƙashi abroad ɗin ne........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_



🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na arba'in da uku_



*_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._*


*_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_*


*_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_*


*_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_*


*_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*


_Littatafan sune kamar haka 👇🏻_.



*_KWANKWASON JIMINA....._*
_(NA MSS XOXO)_


*_GUDUN ƘADDARA_*
_( NA SAFIYYA HUGUMA)_


*_TSUSTAR NAMA....._*
_(NA BILYN ABDULL)_


*_AMEENATU_*
_(NA MAMU GEE)_




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_



🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

_______________


.........A watan da su Mimi ke cika bakwai cif da aure iyalan Alhaji Abaan suka nufi Kano halartar auren yaron Ni'ima da ƴar wajen Zuhrah. Harda amarya Mimi mai fama da ciki ɗan watanni biyar. Sai langaɓewa take a jikin Khadijah tana tureta da mata faɗa akan ta dinga ƙarfafa jikinta. Shiko Alhaji Abaan na faɗan ta bar damar masa yarinya ta barta da abinda ya dameta. Ita daga uban ma har ƴar dariya suke bata. Dan bataga ƙyau a makanta ba sam. Da taga zasu isheta ta ce aiba dole bane zata kira Yazeed ɗin yazo ya ɗauki matarsa basai taje bikin ba ai. Aiko ta sanya ma Daddynta kuka akan ita dai tana son zuwa dan ALLAH. Aiko ya ɗaure mata ƙugu dole Khadijah ta kawo ido ta saka musu.
      Sun isa Kano ranar talata, inda suka tarar su ake jira da shirye-shirye musamman Khadijah da ayanzu itace matsayin uwa ga ƙannenta. Washe garin laraba suka shirya fita duba matar autansu da ke a asibiti sakamakon miscarriage data samu a daren jiya. Mota biyu sukayi, daka gansu kaga nagartaccen family na gogaggun ƴan boko da naira ta gama nuna kanta a jikinsu. Dan daga iyayen har ƴaƴan tsaf-tsaf suke kamar ka taɓa jin daɗi ya maka ihu. Koda suka shigo asibitin kwarjininsu yasa kowama ya haɗu da su sai ya kallesu ya sake kallo. Bayan sun duba matar ƙanin nasu da akama sallama suka ɗunguma suka fito. Autansun ne ya ja su akan su rakashi wani waje Please. Babu wanda yay musu sai ma Mimi dake faman masa rakin ita dai a koma gida barci take ji. Aunty Jamilah na riƙe da ita tana riritata kamar wata ƙwai. Yayinda Khadijah ke faman harararta.
       A gaban gadon wani yamutsatsen tsoho da wahalar rayuwa ta gama nuna kanta a jikinsa suka tsaya. Yana kwance sai idanu luƙu-luƙu da haƙora daka gansa kaga wanda yunwa ta gama cinyema hanji.  A yanda yake kwance kuma zai baka tabbacin yana tare da lalurar shanyewar ɓarin jiki ne. Dan bakinsa har ya ɗan karkace. Da alama kuma idonsa ɗaya baya aiki sosai. A gefensa mace ce akan tsohon wheelchair irin na ƙarfen nan da akeyi a Nigeria. Itama duk ta fita hayyacinta fatar fuskarta tai wani faci-facin nan baƙi nan jaa nan brown. Itama dai a rame take sosai, sai haƙora gayau na gaba ma guda biyu sun fita sai uban gate kamar ƙofar gari. Babu ƙafa a tattare da ita sai dungulmi. Sai wani kalar tsamin dauɗa take ga kayan jikinta duk a ciccinye saboda tsufa da gajiyar da sukai suma. A kaf su Khadijah babu wanda ya gane su wanene, sai dai sun gaishesu da tambayar mai jiki. Amma abin mamaki daga matar har mijin da alama su sun shaidasu musamman ma Khadijah da Mimi da suka tsurama idanu. Dan atake hawaye suka fara bin kumatunsu. Khadijah dai ta ɓalle handbag dinta ta cire rafa na dubu guda biyu 200k ta ajiye musu dan haka kawai suka bata matuƙar tausayi. Tasan kuma tunda auta ya kawo su nan ya san mutanen. Ƙoƙarin tafiya suke saboda naci da shagwaɓar da Mimi take musu kan a tafi ita bata son warin asibitin.
       Cikin rawar muryar yamutsaten mutumin da ke fita gururu ya ce, “Khadijah!”. Cak Khadijah ta tsaya tare da juyowa a firgice dan jin ya ambaci sunanta. Hawayen dake bin kumatunsa masu zafi suka sake ɓulɓulowa kamar yanda na matarsa ke ɓulbulowa. Batare da ya damu ba ya cigaba da faɗin, “Nasan baki ganeni ba. Dafeeq ne.”
     Ba Khadijah ba kowa ma dake wajen sai da ya razana. Idan ka cire Mimi da sauran yaran da basu san komai ba. Sai auta da ya san wanene ɗin shi daman. Dafeeq dake kuka rurus ya cigaba da faɗin, “Kinga yanda ALLAH yay dani Khadijah. Kinga yanda Dafeeq ya koma. Tabbas nasan alhakinki dana iyayenki bazai barni ba Khadijah. Dan na zalunceku ƙwarai da gaske. Nayi wasa da zuciyar data soni don ALLAH. Na bar soyayya ta gaskiya da amana saboda kuɗi. Na ɓata miki suna da tunanin ni ɗin mai wayo ne. Amma wlhy a duk abinda ya faru ban taɓa jin rashin sonki kona daƙiƙa ɗaya ba. Dan ALLAH ne shaida ta son gaskiya ke kaɗai na taɓamawa bayan iyayena. Sai dai ban san wace wauta da son zuciya ne ya jagoranceni aikata miki dukkan abinda ya faru ba. Kaicona. Inama nayi haƙuri nabi shawarar Baba alokacin da yace na bari ki gama karatunki da kansa zai aura min ke. Inama nayi haƙuri da abinda yace. Da nasan har yanzu muna a tare cikin farin ciki da zuri'armu. Amma na biyema son zuciya da wauta na ɓata komai. Na zugaki, nai amfani da soyayyar da kikemin ta gaskiya na sakaki bijirema iyayenki. Na kuma dawo na shirya da nawa kika cigaba da zama cikin fushin naki iyayen. Hakan bai isheni ba na ɓata miki suna a wautata wai duk dan na samu damar nisantaki da kowa sai ni kawai. Kiji bazaki taɓa iya rabuwa dani ba. Duk da hakan kuma ban haƙura ba naje na kawo wannan ƙarfen ƙafar cikin rayuwar mu. Na ɗakkoma kaina CUTA da hannuna gashi nan na gagara warkewa daga gubarta, saima sake wargazani da tayi gaba ɗaya. Khadijah kamar yanda Kainaat ta bijirema iyayenta da ƙyamatarsu matsayin su na iyayenta ta ɗauki iyayen bariki tarihi ya sake maimaita kansa. Dan a yanzu haka muma tamu ƴar ta jima da jefar damu da nunama duniya mu ba iyayenta bane ba. Talauci baisa mun sakata a makaranta ba. Sai talla da suyar awara a bakin layi. A haka ta samu saurayi daya dinga jan ra'ayinta har ya sakata a makaranta. Bayan ta kammala karatu ya tsaya mata ta shiga jami'a. Acan ne ta haɗu da ƙawaye da sabbin samari. Shima ta butulce masa dan acewarta ta gama da ajinsa.

37 / 38