CUTA TA DAU CUTA COMPLETE BOOK BY BILLYN ABDULL.txt

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   19 / 38

54K to 57K   out of 113.7K words

tunanin sanarma wani shima zai sanarma Abaan ɗin da take harin komawa komai, ya ɗan balgata mata wani sirrinta daya ɗauka a cikin waya daya shafi Abaan ɗin.
Matuƙar tashin hankali Kainaat ta shiga. Gaba ɗaya ma ta rikice. A take ta shiga bincike sosai a ɗakinta. Tako samu ya yashe komai harda kuɗin dake a cikin bank nata duka biyu. A takaice dai bata da wani ƙarfi ma da take tunani na dukiya da zaisa ta iya masa rashin mutunci ko gayyato hukuma cikin al'amarin nasu. Sannan maganar zai kaima Abaan wani yankin sirrinta ma wani tashin hankali ne gareta da bazata taɓa fatan ya kasance ba. A cikin ƙanƙanin lokaci komai ya canja a gidan. Ta fahimci hatta wayarta idan tai kira ko aka kirata shima tana zuwa cikin tashi wayar. Sai ma tarasa ina zata kama taji daɗi. Gashi ƙiri-ƙiri ya kulle ƙofar gate yama sallami Dauri maigadi da kuɗi masu yawa wai yaje ya huta zai nemesa. Yayi magana da Manager na Companynta da wayarta cewar a cigaba da al'amura shi da Madam sunyi tafiya zuwa Lagos honeymoon. A haka suka kwashe sati ɗaya a gida babu wani cigaba sai na tafka rikici da masifa. Kowa kuma yaƙi zuwa gidan sakamakon bin duk wanda yasan zai iya nemanta a waya ya tura masa text message cewar sun tafi honeymoon sannan ya kashe wayar ma gaba ɗaya. Tayi masifar tayi zagin tayi kurarin amma yaƙi bata wayar. Ta nema iya nema amma ta kasa gano a inda ya ɓoye. Shi kuma wayar hannunsa babu ma wanda yasan layin sai iyayensa kawai balle wani ya kirashi yasan suna gari. Tun Kainaat na ɗaukar al'amarin wasa harta fahimci yafi ƙarfin wasan fa yaron nan da gaske yake shirin mata ɗibar albarka yake da gaske. A yau suna cikin rikici ta maresa ya rama. A take dambe ya nema harƙumewa a tsakaninsu. Sai dai ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba, ya bubbugeta dan Dafeeq dai akwai zuciyar banza. Sannan duk da ƙananun shekarun nan nashi baya ƙaunar raini kowa ya sani tunma bai kai haka ba. Itama dai ta samu nasarar ƙwala masa plate a goshi harta jimasa ciwo. Hakan yasa shi nufar bayi domin wanke jini batare da ya lura da wayarsa data faɗi ƙasa ba. Yana shiga kira na shigowa, dan haka Kainaat ta ɗauki wayar da sauri, a mamakinta sai taga mamansa ce. A take zuciyarta ta bata shawarar ɗagawa, dan ta fara zargin lallai uwar tasa tasan komai dake faruwa tunda ita kaɗai ke kiransa a layin nan sai babansa. Ɗakin da Khadijah ta zauna ta shiga, ta maida ta kulle ƙofar sannan ta ɗaga wayar tana gab da tsinkewa. Tana kaita kunne Maman Dafeeq na kwaɗa sallama.......


____________★


Abubuwa sun rincaɓe sosai a gidan su Khadijah yau ɗin nan. Dan har dare an hanasu ko ganin Baba. Sai da Zuhrah da taga basu da wata mafita tai kiran saurayinta da zata aura. Hankali tashe ya zo station ɗin. Abinka da mai kuɗi a hannu, cikin ƙanƙanin lokaci da ya ga d.p.o aka basu Baba. Sai dai zuwa safe zasu koma da shi wai za'a turasu kotu dan laifin bin mutum da makami ba abune na wasa ba tunda mutane da yawa sun shaida hakan a cikin anguwa shima kuma baba bai musa ba.
Kusan ƙarfe sha biyu da rabi na dare suka dawo gidan. Idan kaga Khadijah a wannan lokacin dolene ka tausaya mata. Idanunta sunyi masifar kumbura saboda kuka. Gaba ɗaya ta gama fita a hayyacinta fiye da kowa na gidan. Tunda suka shigo ta zube a gaban Baba kawai tana kuka da roƙon dan ALLAH su yafe mata. Ba su Baban kaɗai ba, hatta da ƴan uwanta roƙonsu ta dingayi akan su yafe mata duk laifinta ne, duk a dalilinta ne komai ke faruwa. Babu wanda dai ya iya cemata komai, sai maƙwafcinsu da aketa kai kawo da shi ya ce, “Suje su kwanta da safe koma minene ayi yanzu dare yayi Baba na buƙatar hutu. Dole duk suka shige ɗaki, sai dai sam Khadijah ta kasa barci, daga ƙarshe ta fito ta ɗaura alwala ta shimfiɗa ɗan kwalinta anan baranda ita kaɗai a tsakar gida ta fuskanci UBANGIJI mai share kukan masu kuka. Mai jin roƙon bayi da rahamarsa da jin ƙansa. Yanda take jero addu'oi da magiyar nan gafara a gun UBANGIJI cikin harshen larabci a cikin sujuda ɗinta ya jawo hankalin Baba da ya kasa barcin shima. Tsaye yay a jikin ƙofa kawai yana kallonta. Shi shaida ne duk cikin yaransa Khadijah dabance a fagen ilimi da ƙarancin kwaramniyar, tanada kaifin basira matuƙa, duk da suma sauran nada ƙoƙari amma tata basirar daban ce. Sai gashi ƙaddara da son zuciya ya ɗebeta aikata abinda ta aikata. Dan ALLAH shine shaidarsa yayi iya ƙoƙarinsa akan Khadijah hakama mahaifiyarsu. Sunbi duk hanyar data dace matsayinsu na iyaye domin dawo da ita hankalinta, nasiha, lallashi, kurari matsayinsu na iyaye duk sunyi amma duk da haka basuci nasara ba, ba kuma kowa zai fahimci ƙoƙarin su ba, wasu ma kallon sune masu kuskure sukeyi....
Khadijah da bata san da ana kallonta ba kuka take sosai bayan idar da sallar tana addu'a da roƙon ALLAH gafara da fatan ya ɗauki ranta a tsakanin nan, ya kuma saka iyayenta su yafe mata koda bayan ranta ne, ya wanketa da ga aibatantata da Dafeeq yayi a idon al'umma. Ta jima tana addu'ar anan ma kafin tai yunƙurin miƙewa tana layi dan ta gama yanke shawarar abinda zuciyarta ke ayyana mata. Daga baba har Mama dake bayansa tana hawayen tausayin ƴar tata binta da kallo sukai. Ganin ta nufi rijiyarsu gadan-gadan yasa Baba zabura cikin jan ƙafarsa da bai iya takawa. Tuni Mama ma ta rufa masa baya. Da ƙyar ya iya kaiwa dai-dai Khadijah ta tafi gaba ɗayanta zata afka kanta a rijiyar. Wani irin fisgota Baba yayi ya rungume a jikinsa dake rawa hawaye masu zafi na kufce masa. Mama ma ta haɗasu su duka biyun ta rungume itama tana mai fashewa da kuka. Sai ga Ni'ima da Zuhrah da ashe suma dai ba barcin suke ba a guje suma suka rungume iyayen nasu.
“Baba dan ALLAH ku barni na faɗa, ku yafe min kuma dan girman ALLAH. Nasan na cutar da ku, kuma bazan iya yafema kaina ba. Kun haifeni, kun raineni cikin ƙyaƙyƙyawar kulawa da nagarta da bajinta irin ta jaruman iyaye da duk ɗa na gari zai so samu a duniya. Amma son zuciya da wata baƙar soyayya mara amfani da amfanarwa ta ruɗeni na bijire muku. Kaicona ni Khadijah, kaico da haihuwar ɗiya irina. Wlhy Mama naga illar saɓama iyaye, naga illar ƙuntata zuciyar Iyaye. Inama ace jiya zata iya dawowa a duniyata na goge da shafe abubuwan dana aikata a gareku. Sai dai kaicona, hakan bazai taɓa kasancewa ba. Na riga na ɓata sunana, na goga muku baƙin fentin da bazai taɓa gogewa a tarihin wannan gida ba. Dan ALLAH Baba, Mama, ƴan uwana ku yafe min ku barni na faɗa cikin rijiyarnan. Maybe idan na mutu ba'a gani na baza'a sake tuna muku da abinda na aikata ba balle a aibantaku da wanda ban aikata ba. Wlhy gara na mutu, gara ace mutuwarma nayi ko Baba?...”
“Muna son ganinki a raye Aunty Khadijah. Dan ALLAH ki daina faɗar zaki kashe kanki. Muna sonki muna sonki sosai”. Zuhrah ce ta faɗa cikin kuka da sake ƙanƙame hannun Khadijah data kamo. Ɗagowa tai da sauri tana girgiza ma Zuhrah kai, sai dai kafin tace wani abu baba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaura yatsarsa akan lips dinta ya ce, “Shiii!! Ya isa haka. Ku zaunar dani kun san yanzu babanku babu ƙafa.”
Da sauri suka kakkamashi zuwa baranda, Ni'ima ta kawo tabarma da sauri ta shimfiɗa masa. Duk zama sukai shiru sai Khadijah dake durƙushe gabansu ta kama kunnuwanta har yanzu tana hawaye. Kusan kallon mintina uku Baba ya mata kafin ya ce, “Bamu labarin miya faru kika iya barinmu Khadijah? Miya faru a inda kuka je? Ya akai Dafeeq ya dawo ga iyayensa bayan watanni da barinku gida amma ke mace kima kasa hakan? Da gaske ne Dafeeq ya jima da sakin ki kika tafi wani waje daban saboda tsoron kar ki dawo garemu ai miki dariya?”.
“Sam ba haka bane Baba. Wlhy ba haka bane ba. ALLAH kuma shine shaidata duk abinda zan faɗa muku shine gaskiya. Sannan inada shaidu akan abinda zan faɗa mukun tun daga wanda ya ɗaura auren mu har zuwa inda muka zauna da dalilin farkawata a barcin kuskuren bijire muku na dawo gida. Duk da wlhy tunda na barku ban taɓa jin salamar haka ba a raina. Kawai ina dannewa ne dan kar naima Dafeeq laifi a wautata da son zuciya. Amma kullum a cikin mafarkinku nake, nakanyi kuka a ɓoye da jin kamar na dawo na baku haƙuri, sai dai ina jin tsoro, ni burina da nawa hangen shine idan na haihu zan zo muku da yaƴan maybe kufi yafe min kuskurena. Sai kuma aka samu akasin hakan abinda nake burin ya zamar min jagoran zuwa gareku ya gagara samuwar.......”✍️



_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na ashirin da uku_


___________


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

___________


.......Tsaff ta basu labarin komai da ya faru tun daga randa suka bar gida har ɗaura aurensu zuwa samuwar cikinta da yayta zubewa dama daina samuwarsa duka. Shigowar al'amarin Kainaat da ya zame mata wata fitila data haska mata hanya a yanzu. Turke Dafeeq da tai da dukan da yay mata zuwa tsintar kanta da tai a titi bayin ALLAHn da suka kawota gida suka taimaketa. Komai bata ɓoye musu ba. Duk dauriyar Baba sai da yaji hawaye sun cika masa ido. Sai dai kiran sallar asubahi da aka fara ya sakasu kasa cewa komai dole duk suka miƙe domin ɗaura alwala kamar yanda Baban ya basu umarni. Kasa haƙuri Mama tai dan tana tsoron shiga ɗaki Khadijah ta sake tunanin jefa kanta a rijiya. Anan baranda ta shimfiɗa sallaya domin yin tata sallar yayinda su kuma suke cikin ɗakinsu. Baba da Kamal kuma sun fice massalaci......


__________★

Maman Dafeeq data rangaɗa sallama a waya batare da jiran Dafeeq ya amsa ba ta cigaba da maganarta a ƙugule Kainaat na saurarenta. “Duk inda kake kazo gida a gobe, dan wannan shegiyar yarinyar daka jajibar mana a cikin zuri'armu ta dawo gida tace ƙarya kake baku rabu da juna ba. Hasalima raunikan data dawo dasu a jikinta na duka kaine kamata su ka kuma zubar mata da ciki. To nadai taƙaice maka zance yanzu haka nasa an kulle ubanta saboda yasa yan uwanta biyoni da makamai wai su kashe ni. Dan haka kazo maza muna nemanka ni da Babanka dan wannan sharrin datai maka sai an zauna kotu. Wlhy bazamu yarda ba. Kama taho da matarka ƴar arziƙi irin albarka dan tai maka shedar itace matarka a yanzu ba shegiyar ba. Ato kaji sai kai azamar tahowa”.
Ɗiff ta yanke wayar tsabar bala'i da ke cinta bama ta gama tantance dawa take wayar ba. Harga ALLAH Kainaat ta razana da mamakin wai Khadijah na gidansu Kano. To ta yayama akai ta iya tafiya a wannan yanayin? Wama ya bata kuɗin motar tafiyar to?. Koda yake ita miye nata ma. Ai wannan wata damace itama gareta da zata jijjiga rayuwar Dafeeq. Murmushi mai ƙayatarwa ta saki, tare da saka wata number ta rubuta text message. Tana turawa ta goge shi akan wayar tana sakin wani lalataccen murmushi. Kafin a fili ta furta, “Yaro mu zuba mu gani. Ni da kai ɗan halak ka fasa, dan CUTA CE TA ƊAU CUTA...” daga haka ta fita a ɗakin, wayar ta maida a inda ya barta ta haura sama itama.....

___________★

Kamar yanda jami'an tsaro suka buƙata an maida baba police station. Sai dai yanzu ba'a kullesa ba an dai yi shirin miƙasu kotu ne. An gama komai suna shirin barin station ɗin ne sai ga wani maƙwafcinsu da baƙi a mota. D.p.o ya bada umarnin a shigo da su. Shi dai baba koda suka shigo kallon rashin sani yake musu, sai da Khadijah da kanta ke ƙasa tana hawaye ta ɗago ne cikin zabura ta ce, “Baba Hakimi! Baba Harɗo! Aunty Mariya”.
Murmushi duk suke mata, yayinda aunty Mariya ta buɗe hannu alamar tazo gareta. Babu musu Khadijah taje ta shige jikinta tana kuka mai ban tausayi. Sun jima a haka sannan suka kai zaune bisa umarnin d.p.o, daga haka aka fara gaggaisawa. Iyayen Dafeeq dai nata harare-harare tunda suma basu san su Baba Hakimi ba a zahiri sai dai a labari wajen Dafeeq. Shi kuma bawai ya taɓa zama bane wajen sanar musu komai akan alkairin su Baba Hakimi garesu. Bayan an lafa da gaishe-gaishe Baba Hakimi ya sanar musu shi wanene da dalilin zuwansa nan ɗin...
“A jiya da dare wani yaro ya samemu da zance akan Khadijah da mijinta. Al'amarin ya bamu mamaki dan bamu san mike faruwa ba duk da kuwa suna a ƙarƙashin kulawarmu ne. Da farko zan fara da bama iyayensu haƙuri akan kasa maidosu gida tun a lokacin da suka zo garemu kam mu ɗaura musu aure. Munyi hakanne saboda gudun kada mu dawo dasu su sake wani takun guduwa tunda sun ƙudiri aniyar hakan dan dan yau ka haifesa ne baka haifi halinsa ba, shiyyasa na ɗaura musu auren na kuma katangesu a kusa da ni duk da nakan basu shawarar ko zasu koma ɗin amma suce ba yanzu ba. Na barsu ne har zuwa lokacin da zasu ji babu wannan zaƙin soyayyar dake ɗibarsu ta ƙuruciya. Zasu fi sanin muhimmanci da martabar kuskuren da suka tafka fiye da su dawo a sanda suke jin zaƙin soyayyar. Tabbas gaskiya ne Khadijah matar Dafeeq ce kuma ni shaidane da mutuncinta taje gareshi kamar yanda iyalina suka sanar dani, hakan ya ƙara ma bani ƙwarin gwiwar rungumarsu dan na fahimci wautar ƙuruciya da son zuciya irin ta yaranmu na yanzu ya fisgosu aikata abinda suka aikatan. Amma alhmdllh tunda ma aure sukai tunanin suyi bawai wata masha'a ba kamar yanda wasu yaran kanyi domin neman mafita.......”
Tsaff ya kwashe komai ya sanar musu tamkar yanda Khadijah ta faɗa a gaban su baba, ta kuma sake maimaitawa a gaban su D.p.o yanzu babu jimawa. Tunda Baba Hakimi ya fara magana babu abinda Baba ke saki sai ajiyar zuciyar sake samun nutsuwa. Yayinda iyayen Dafeeq suka birkice da borin wai ƙarya ne duk shiri ne. Dan haka a take sukai kiran Dafeeq a waya suka sanar masa...


________★

Lokacin da kiran ya shigo masa yana gida kwance a falo, dan gama sa'insarsa da Kainaat kenan ta dinga masa dariya da faɗin ya gama da matsalar gabansa sannan yazo su ɗaura daga inda suka tsaya tai shigewarta. Shine ya kwanta a wajen yana tunani da nazarin son gano inda maganarta ta dosa. Kamar bazai ɗauki kiran ba sai kuma ya ɗaga. Jin abinda mahaifinsa ke faɗa kaɗan ya rage ya wantsalo ƙasa da ga kujerar. Baima san ya lailayo wata bagidajiyar ashariya ba da faɗin, “Baba Hakimi tare da Khadijah a Kano?”.
Kafin Baban nashi ya bashi amsa d.p.o ya amshe wayar. Cikin bada umarni

19 / 38