Author : BILLYN ABDULL Category : Hausa Read
ya bushe.....
_________★
Ƙarfe biyar da kusan rabi motarsa ta shigo gidan. Kamar kullum yana tare da Awwal. A yanda ya fito motar a kasalance zai sa ka fahimci a gajiye yake. Dan hatta ƴar saman suit ɗinsa riƙe take a hannunsa ya ɗan sagalata a kafaɗarshi. Kai tsaye sashen Mamy ya nufa, ya bar Awwal na tattare masa tarkacensa kamar yanda ya saba.
Sassanyan muryarsa ta fargar da su Mamy dake hira zuwa garesa. Duk da tunkan ya shigo dama ƙamshinsa ya musu sallama. Cike da girmamawa ya gaida gwaggonninsa biyu da suka rage basu wuce ba. Sai wasu mata biyu da suma suka gaishesa cikin girmamawar. Sai Noor da itama ta gaishesa, sannan shima ya maida hankali ga Mamy dake binsa da kallon tausayi, dan gani taima kamar ya ɗan rame mata yau ɗin. Amsa masa tai da kulawa, tare da ɗorawa da faɗin, “Baffah kaci abinci kuwa yau ɗin nan?”.
Murmushi yay mata mai sanyi, sai kuma a hankali ya ce, “Mamy naci snacks da drink....”
“Baffah na drinks da snack aiba abinci bane. Shiyyasa naga ka rame min a ido wlhy. Kaga maza jeka wajen matarka an kai muku abinci dan ALLAH ka zauna kaci, sannan itama ka tabbatar taci kaga baƙuwace ita”.
Murmushin ya sake yi nan ma yana miƙewa, sallama ya musu ya fice dan shima dai yasan yana matuƙar buƙatar hutawar kam...
Tsaye take gaban mirror tana fesa turare dan kammala gyara jikinta kenan kamar yanda su Aunty Firdausi suka gargaɗeta da yi. Ratsa kunneta da sassanyar muryarsa tai yasata ɗan daburcewa, cikin sauri ta ɗauki ɗan kwalinta da bata kai ga ɗaurawa ba ta shiga ƙoƙarin warwarewa tana amsa sallamar tasa. A hankali ya janye idanunsa da ga kan gashinta dai-dai tana ɗora ɗan kwalin da faɗin, “Sannu da zuwa ina yini”.
Rigarsa dake saman kafaɗa ya sauke a ɗan kasalance ya amsa da, “Ya baƙunta? Badai kiyi kuka da zasu tafi ba dai ko?”.
Kasa bashi amsa tayi, sai ma idanunta da suka ciko da ƙwallan, amma tai dauriyar riƙesu. Freight ɗin dake ɗakin ƙarami ta nufa, ruwa ta ɗakko da kofi ta nufesa. Yanda ta zuba ruwan a nutse da ɗan rissinawa yayin miƙa masa ya sashi sakin siririyar ajiyar zuciya. Jin kaifin idanunsa a kanta ga shi ya haɗa hannunta da kofin ruwan ya riƙe yaƙi ya saki ya saka tsigar jikinta fara tashi yaam. Ji tai ta kasa daurewa ta ɗago a hankali itama, kai tsaye cikin idanun nasa natan suka shige, ji tai ta ƙara rikicewa ma, dan mijin nata akwai kwarjini da cika idon mai kallonsa.
Ganin yanda tayi ɗin ya sashi sakin murmushi, magana ta gaskiya yana matuƙar son mace mai kunya da sanyin hali irin na Khadijah, dan haka komai nata ke birgesa kai tsaye. Yanda baida hayaniya haka yake son mace mara hayaniya da rashin kauɗi. Kofin ya kai bakinsa batare daya sakar mata hannunta ba, sai da ya shanye duka batare da ya saki hannun nata ba dai ya jawota zuwa jikinsa a hankali ya zagayeta da ɗayan hannunsa, cikin kunneta ya raɗata mata “Haka ake tarbar miji dama Baddo?”.
Ji Khadijah tai inama ƙasa ta buɗe kawai ta shige dan kunyarsa. Yanda yake tafi da ita nasata mance ta taɓa aure, dan kunyarsa take irin sosai ɗin nan, kodan ya girmi Dafeeq a shekaru ne, ko kuwa yanayin kamewarsa da cikar kamalane ke sata jin hakan ita bata sani ba. Sun yi kusan minti biyu a haka kafin ya saketa, sai kuma a ɗan kasalance ya ce, “Bara nayi wanka na zo nai sayen bakin amarya dan naga dai take-taken ki kenan”.
Da sauri ta juya masa baya tana ɗan murmushi. A ranta tana jin mutumin nan nadabanne a cikin daban. Komansa na tabbatar mata lallai a duniya akwai maza akwai kuma mazaje. Jin yana ƙoƙarin fita muryarta acan ƙasan maƙoshi ta ce, “Mamy ta aiko da abinci a kawo maka?”.
Sai da ya kalla ƙyaƙyƙyawan agogon hannunsa da ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci ɗaya shima murya can ƙasa ya bata amsa da, “Zan dawo anan naci after isha”.
Kanta kawai ta jinjina masa batare data iya kallonsa ba. Sai da taji ya fita ta ɗan sauke ajiyar zuciya tare da ɗagowa, idanu ta ɗan tsurama inda ya tsaya ɗin sai kuma ta saki murmushi, ita kanta tana mamakin yanda take tsintar kanta a wani shauƙi da kunya mai tsanani a duk sanda suka kasance tare. Ga wata kasala dake saukar mata da jin nutsuwa. Bayi ta shiga tai alwalar magrib duk da da ɗan sauran mintuna, amfani tai da sauran lokacin da ya rage tai zaman karatun Alqur'ani har sai da lokaci ya cika ta tashi ta gabatar da magrib, koda aka idar karatun ta cigaba dayi har isha'i. Ta jima tana addu'oi sannan ta tashi, gaban mirror ta koma tai ɗauri mai ƙyau tare da sake gyara kwalliyarta simple data sake fidda mata ƙyawunta. Ta sake saka turare sannan ta ɗauka mayafi ta yafa kamar mai shirin fita. Tayi ƙyau sosai, sai kwalliyar tata ta sake tabbatar da ita a amarya. Falo ta fito ta saka turaren wuta a kusan burner uku data gani, duk da kuwa falon yana ƙamshinsa abinsa. Kitchen ta shiga ta haɗa abincin dan tunda aka kawo anan aka ajiyesa. Ta kawo kulolin ta koma ɗakko sauran ta samu ya shigo. Sai dai waya yake yi, yana zaune a kujera sanye cikin milk jallabiya datai masa ƙyau sosai kamar wani balaraben Saudiyya. Ga ƙamshin turarensa mai daɗi ya cika falon. Yanda yake wayar cikin yaren filatanci haɗe da turanci dolene ya birgeka. Duk kai kawon da take tsakanin kitchen zuwa dining idonsa na kanta, ta masa ƙyau sosai, haka kawai sai wayar da sukai da Doctor Giɗaɗo ɗazun ta faɗo masa a rai, wai Kainaat nada ciki. Da sauri ya ture tunanin gefe cikin halin ko'in kula, dan shi ko kaɗan baiji wani abu na kishi akan hakan ba, shi yama manta da wata Kainaat can a babin rayuwarsa, yama yi zaton ta koma ga iyayenta tuni ashe wai tana Adamawa harma ta sake wani auren, gaskiya bai taɓa sake tabbatar da Kainaat kidahuma bace sai yanzu, yayi nadamar auren yarinyar nan a rayuwarsa, amma ba komai ai yayine domin Mamynsa, gashi kuma yaci ribar biyayyar da yay mata a farko tunda gashi a karo na biyu ta sake haɗashi aure da choice ɗinsa, hakan kaɗai garesa Alhmdllh. Isowar Khadijah wajen ya sashi yin sallama da wanda yake wayar tare da ture batun Kainaat gefe, cikin ɗan risinawa kanta a ƙasa ganin ya kammala wayar ta furta, “Hamma ga abincin (yanda taji Noor na kiransa). Wani kalar ɗan waro idanu yay waje, sai kuma kamar a ɗan shagwaɓe ya ce, “Hamma kuma baddo! Wannan ai salon hanani rawar gaban hantsi ne”. Cikin rashin fahimta da jin yanda yay maganar a wani can ƙasan maƙoshi ta ɗan ɗago ta kallesa. Manyan danunsa ya lumshe mata tare da wani kalar ɓata fuska a daƙile ya ce, “Eh mana, miya haɗa ango a daren farkonsa da wani Hamma can. Inama laifin irin su kankanar zuciyata, madarar raina, gobar ruhina haka sai na san ango nake.”
Dariya sosai Khadijah keyi, dan harga ALLAH ya bata matuƙar dariya, irin waɗan nan sunaye haka. Ganin yanda take dariya har fararen jerarrun haƙoranta na bayyana ya sa ya saki murmushi shima. Haka yake son ganinta cikin farin ciki, dan yasan ya tsamota cikin danginta tana cike da damuwar kewarsu dannewa kawai take. Miƙewa yay har sannan fuskarsa da murmushi ya nufi dining ɗin, hakan yasa itama haɗiye sauran dariyar tabi bayansa. Ita da kanta ta zuba masa abincin, sai dai kaɗan ta saka kamar yanda ya buƙata. Ganin ta zauna bata da niyyar zuba nata ya sashi kallonta da fararen idanunsa masu maruƙar rikita mata lissafi. Ƙasa tai da kanta tana wasa da yatsunta. Komai baice da ita ba ya ɗauke idanun, sai kuma ya ɗauki spoon ya saka a plante ɗin nasa a bincin. “Bismilla muci”. Ya faɗa babu alamar wasa a tattare da shi. Ji tai gaba ɗaya ta kasa musa masa. Dan girmansa da kwarjinin sa a idonta bana wasa bane. Kasa sakewa taci abinci tayi, sai juya spoon take a ciki da tsakura kaɗan-kaɗan. Shiko bai mata magana ba yana cigaba da ci a nutse rabin hankalinsa akan tvn dake dining ɗin yana kallon news. Ya ɗan ci sosai ya ajiye cokalin sai kuma ya zari tissue ya goge bakinsa yana kallonta. Tana jin yanda idanunsa ke yawo a jikinta amma sam ta kasa ɗagowa, har sai da ya fara ƙara mata abincin sannan ta ɗago da sauri. Kansa kawai ya ɗan ɗaga mata alamar taci yana miƙewa yabar dining ɗin, can falo ya koma ya sake zama a inda ya tashi yana buɗe laptop daya ajiye ya shiga aikin gabansa da duk bai wuce bincike akan noma ba dai. Dan in dai ka gansa da laptop aikin kenan kawai.
Tashinsa a wajen ya ɗan taimaka mata taci abincin, bayan ta kammala ta tattare wajen ta kai kitchen, sauran abincin take ta tunanin yanda zatai da shi, dan bata son barinsa ya lalace babu daɗi. Gashi ita ba waya ba balle ta kira Noor tace a zo a ɗauka. Ta manto wayarta a Kano, tun ɗazun take son magana da su ma hakan ya gagara. Rashin mafita ya sata fitowa, kanta a ƙasa ta nufo inda yake. Sai da ta ɗan saci kallonsa, ganin hankalinsa gaba ɗaya a screen ɗin laptop ɗin yake ta sauke ajiyar zuciya can ƙasa. A hankali ta ce, “Hamm....” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa. Murmushi ya ɗan saki batare daya kalleta ba, idanunsa akan screen ɗin laptop ɗin ya ce, “Uhumm ina jin ki! Batun Hamma kuma zan canja shi ai da kaina dan ni dai ba Hammanki bane”.
Duk da zancen nasa ya sata jin kunya haka ta daure ta sanar masa batun abincin. Karan farko ya ɗago ya ɗan kalleta ya sake maida kansa, ji yay ta birgesa, dan ta sabbatar masa ita ba almabazzar mace bace ba. Gefensa ya nuna mata ya ce, “Bismilla zauna bara na kira Noor sai ta aiko a ɗauke”. Kanta ta jin jina masa itama kawai, dan har ya riga yakai wayar kunnesa. Dai-dai tana ƙoƙarin zama a ƙasa ya ajiye wayar yana kallonta, kansa ya girgiza mata da faɗin, “No akoda yaushe nafi buƙatar jin iyalina a jikina in har ina gida. Karki sake kwantanta cewa zaki zauna ƙasa dan ina kujera. Dan haka bissmilla”. Ya nuna mata kusa da shi, inda ta tabbatar idan ta zauna dolene a jikin nasa zata kasance kamar yanda ya ambata.........✍️
Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846
Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria
Ummu khalifa 01017018846
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na talatin da uku_
___________
Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846
Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria
Ummu khalifa 01017018846
______________
......Zama tai a ɗan takure, sai dai a bazata taji ya saƙalo hannunsa ta bayanta ya kwantota saman kafaɗarsa, batare da ya sake magana ba ya cigaba da aikinsa. Ta jima idanunta a runtse dan kunya, kafin ta buɗesu a hankali tana kallon abinda yake a laptop ɗin. A haka masu aikin Mamy da suka kawo mata abincin sukai sallama. Zata tashi ya sake maidata yana amsa musu sallamar, sai kuma yace su shigo. Kamar Khadijah zata fasa ihu dan kunya, amma shi sai taga aikinsa ma kawai yake. Ta gefen ido ta kalla masu aikin, sai taga tunda suka musu kallo ɗaya basu sake yi ba. Ko gaishesu da sukai kawunansu a ƙasa suke. Shi hannu ma kawai ya ɗaga musu, sai itace ta amsa musu. Koda suka shiga kitchen ɗin ma suka fito sam basu kallesu ba har suka fice, a hankali ta sauke ajiyar zuciya har yana iya jinta. Sai dai baice komai ba face ɗan murmushi daya saki kaɗan ya cigaba da aikinsa. Kusan awa ɗaya suna a haka, tun tana noƙe jikinta harma ta saki wani barci-barci ya fara rinjayar idanunta dan ƙamshin turarensa ba ƙaramin ratsata yake ba da saukar mata kasala. Laptop ɗin ya rufe ya ajiye tare da sauke ƙafafunsa dake a table ƙasa. Sai kuma ya ɗan kalleta yana mai kai hannunsa saman fuskarta ya shafa. Firgigit ta buɗe idanun, ganin yanda fuskarsa ke gab da tashi ga hannunsa akan tata fuskar ya sata ɗaga kanta a kafaɗarsa da ɗan sauri.
“Da'alama kin gaji da yawa, ansha rawa wajen party shekaran jiya ko?”.
Juyowa tai da sauri batare data tuna dawa ma take maganarba, idanunta a ɗan ware bakinta na nuna alamun ƴar shagwaɓa ta ce, “Ni wlhy bana rawa, kuma dai ai kowa yasan banyi ba”.
Wani irin harmutsawa jinin jikinsa yayi saboda yanda tayi ɗin, ga idanunta sun sake wani haske har ƙyalli suke, baƙin ya ƙara baƙi, lips ɗinta sun ɗan tattare kaɗan. Samun kansa yay da jinjina mata kansa, idanunsa na a cikin tsakkiyar nata idanun, kamar mai raɗa ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Uhmm nima shaida ne bakiyi rawan ba, amma yanzu zakiyi min nawa a ɗaki ko....”
“Rawan!”.
Ta faɗa cikin ƙara waro idanunta sosai waje, irin nuna alamun matuƙar mamakinsa ɗin nan.
A wani irin sake kasancewa a kasalance ya jinjina mata kansa yana lumshe idanunsa da buɗewa cikin nata ya furta, “Uhhumm Baddo”.
Kamar wadda aka maido hayyacinta ta miƙe zabar, sai kuma cikin sassarfa ta nufi barin wajen da bashi amsa muryarta na rawa. “Ni ALLAH bana rawa”. Wuff ta shige ɗan lungu bedroom ɗin ta. Murmushi mai bayyana haƙora ya saki, sai kuma ya taune lips ɗinsa da ƙarfi yana ɗan kaima kansa ƙaramin mangari ya ce, “Abaan kai ɗin nan ko”. Sai kuma ya sake sakin murmushin da komawa cikin kujerar ya wani lafe. Shi gaba ɗaya ma ji yake yana neman rasa control ɗinsa akan yarinyar nan. Anya Ibrahim da Adams ba saida suka tofeshi ba kafin su kawo wannan batun ga Mamy. Abin da mamaki fa, sam mantawa yake da cewar Khadijah ta taɓa aure kafin shi ɗin, kallon wata ƙaramar yarinya budurwa sharaf yake mata, koda yake yarinyarce ai, 20years fa, ko ƙanwarsa daya bama shekaru masu tazara sosai ta girmeta fa. Ai dami a kala kawai ya tsinta...
Tafi minti takatin da shigowa sannan ya shigo, dan harta canja kayanta zuwa na barci. Wando da riga ne masu santsi da basu kama jikinta ba, sai hula data saka amma duk da haka kwantaccen gashin gaban kanta sai da ya fito. Zaune take a saman gadon ta jingina da fuskarsa littafin addu'oi a hannunta. Ta rage fitilar ɗakin sai lamp na side drawer kawai da take amfani da shi wajen ganin rubutun littafin. Shigowar tasa sai da ta ɗan sakata razani, dan duk ta saki jiki akan bazai biyota ba. Ta ƙasan ido take binsa da kallo har ya hawo gadon, ganin ya ɗan zuba mata ido ya sata ɗauke nata ta maida ga littafin. Tsahon wasu sakanni kuma sai ya matso jikinta gab. Wani yarr taji saboda jin saukar kansa a kafaɗarta amma ta dake. Hannunsa ya ɗaura saman nata dake riƙe da littafin ya ɗan jawo kaɗan shima yana kallon rubutun larabcin. A haka suka cigaba da karantawa a tare batare da yayi magana ba. Ganin sun kammala karanta na barcin tana neman buɗe wani shafin kuma ya sashi zare book ɗin a hankali, jikinta ya ɗan ranƙwafo har tana ɗauke numfashi ya ajiyesa a side drawer ɗin, sai kuma ya nufi sauka gadon yana faɗin, “Kina da alwala?”.
Kanta ta jin jina masa alamar eh. Shima sai ya jin jina nasa da bata umarnin ta sakko. Sun gabatar da salla raka'a biyu, ya kama kanta yay addu'a tare da yi musu addu'ar zamar lafiya da samuwar zuri'a mai albarka sannan suka sake komawa garon. Zama ta sake yi kamar ɗazun, batare da yace mata komai ba ya rage ƙarfin lamp ɗin ƙasa sosai. Sake maida kansa yay a kafaɗarta kamar ɗazun ya riƙo hannunta cikin nashi ya matse har sai da ta ɗan zabura kaɗan.
“Mrs Abaan Omar Modibbo!”.
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa idonsa akan hannunsu dake cikin na juna. Zuciyarta na bugawa da sauri-sauri a hakanli itama ta ce, “Uhmyim”.
“Thanks you Baddo da kika amsheni a matsayin miji duk da ban taɓa zuwa gareki na nuna kaina ba, bazan ɓoye miki ba kin matuƙar burgeni da kika amshi auren nan a yanda yazo miki batare da nuna koda a fuskarki an miki ba daidai ba. Lallai ke kin cika ɗiya tagari abin alfaharin kowaɗanne iyaye. ALLAH yay miki albarka, ALLAH ya yarda dake fiye da yanda ni mijinki