CUTA TA DAU CUTA COMPLETE BOOK BY BILLYN ABDULL.txt

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   28 / 38

81K to 84K   out of 113.7K words

nake jin na yarda dake. UBANGIJI ya yafe mana kurakuran mu baki ɗaya. Baba ya sanar dani komai akanki, ina son ki manta da abinda ya faru baya domin kuwa ƙaddararki ce, ita kuma ƙaddara duk iya gudunka baka isa tsere mata ba. Tun randa muka tsinceki a bakin hanya tabbas naji tausayinki sosai a raina, duk da kuwa ban san minene dalilin shigarki a halin da muka gankin ba. Bayan mun kaiki gida na tafine da tunaninki a wannan yinin, sai dai kasancewata mutum mai yawan sabgogi ina komowa Abuja namance komai daya shafeki na cigaba da harkoki na. Kasancewar irin rabuwar da mukai da matata ta farko Mamy kullum cikin roƙona take kan na fidda matar aure. Nakan bata amsa da cewar ba yanzu ba, idan kuma naga ta damu sai nace mata ta zaɓamin kamar yanda ta zaɓa min ta farko. Hakan kansa ta ƙyaleni, dan tana ɗaurama kanta laifin a kan yanda matar data zaɓamin ɗin ta kasance a baya. Sam lokacin da muka kaiki gida ban san su Adams nada alaƙa da gidanku ba, duk da nasan an saka musu date ɗin aure kuma zasu auri yara ƴan gida ɗaya ne. Ban taɓa maganarki kuma da su ba duk da su ɗin sun wuce yarana na business sun zama tamkar ƴan uwane gareni saboda gaskiyar su da riƙon amana. Dan sukan iya zuwa cikin gidan nan suci su sha suyi hira da Mamy harma suyi kwanaki, haka nima nakan ziyarci iyayensu a duk sanda na samu dama in har na shiga Kano. Mamy itace ta haɗa lefensu su duka, bayan ta kammala haɗawar ne tai kiransu dan su gani, sannan baifi saura sati uku bikin nasu ba, ni lokacin ma bana ƙasar. A randa sukazo ɗin ne Ibrahim na waya da ƙanwarki sai maganarki ta shigo ciki akan miki ɗinkunan fitar biki, alokacin Mamy na tare dasu, dan harta gaisa da Ni'ima ma. Bayan ya gama wayar yake cewa Mamy zai bada a saya miki kaya kema kamar kala biyar haka dan kayan lefen nan sun masa ƙyau, anan ne Mamy ke tambayar wacece ke ɗin kuma, dan duk zatonta wata budurwarce kuma daban, shine suke bata labarinki. Mamy macece mai tsananin tausayi, sannan da kike ganinta nan ƴar gwagwarmaya ce akan mata, a take ta nema ganin hotonki, tare da alƙawarin tsaya miki kiyi ilimi. Su Adams duk basu da hotonki sai da suka kira su Zuhrah suka tura musu. Ta jima tana kallonki fuskarta da murmushi, a bazata sai ji sukai ta ce, “Ni dama ɗan rigimar ogan nan naku zai amince ai da sai yay mana wuff da wannan black beauty girl ɗin kawai. ALLAH yarinyar ta shiga raina matuƙa”.
A take maganar tata ta ɗauki hankalinsu, musamman ma Noor da tai ta zigawa akan a min magana akuma turamin hoton. Tun Mamy bata ɗauki zancen serious ba harta amince a washe gari tai kirana, kai tsaye tace tamun mata na duba ga hoto nan ta tura min ta email ɗina na gani idan tamun. Duk da maganarta ta shigeni, kuma ba auren ne a gabana ba sai kawai na amsa mata da cewar na amince in har yarinyar ta mata. Harga ALLAH banga hotonki ba, dan ko buɗesa ma banyi ba na goge. Farin cikin da naji Mamy da Noor na ciki ya samun jin zan iya amsar auren koda bazan soki ba, dan matata ta baya ta gama ciremin sake jin son wata mace a rayuwata. A ranar Mamy ta aika su Adams Kano domin yin magana da Baba, ban san hidimar da suke ba dan tun a ranar na manta da batun wani tayin aure da Mamy tamun, ashe su suna nan sunata kai kawo dan da farko Baba yaƙi amincewa har sai da Mamy taje kano da kanta sannan, lokaci baifi saura kwana takwas bikin su Adams ba aka tsaida namu zancen. Ban dawo Nigeria ba sai ana saura kwana uku, na kuma zo ne da shirin bikin su Ibrahim. Sai kawai na samu an gyara gidan nan tsaf harma wasu a baƙin Adamawa sun fara isowa. Humm abin yaban mamaki, amma yanda naga mamy ta ɗauki abin da muhimmanci ya sakani danne zuciyata na cigaba da binsu da ido. Sam banyi niyyar zuwa dinner ɗin nan ba amma Mamy ta matsa tare da magiyar su Adams dole nai shiri aranar nabi jirgin ƙarfe shida zuwa Kano. Kin san wani abu?”. Yay maganar ƙarshe cikin sigar tambaya yana ɗan matsa hanunta dake cikin nashi da ɗan ɗaga ido ya kalleta. Kanta ta girgiza masa a kasalance.
“Tun kafin mu shigo cikin hall ɗin nan na fara cin karo da zazzaƙar muryarki da tai matuƙar ratsani kina addu'oi. Jinai na kwaɗaitu da son ganin mamallakiyar muryar tunkan na shigo ciki, sai dai muna shigowa muka samu kin gama. Ni ne na turama Awwal saƙo cewar a sake sakaki ki fito kiyi addu'a.....” da sauri ta waro masa idanunta alamar mamaki, murmushi ya sakar mata da cigaba da faɗin, “Lokacin da kika miƙe jinai kamar na zama tsuntsu naje naga fuskarki, dan sam bana ganinki da ƙyau, har sai da kika kammala kika koma mazauninki. A lokacin ne na iya ganin fuskarki, ji janai zuciyata na neman fitowa ta baki, da ƙyar na iya controlling kaina, abinda zai kuma baki mamaki har lokacin banfa gane ki ba, dan kin canja gaba ɗaya daga waccan ranar. Sannan kuma ban san kece matar da Mamy ta zaɓamin ɗin ba har sai da aka sake kiranki matsayin yayar amare da zata bada tarihinsu. Anan ne zuciyata ta shiga waswasi har lokacin da tsageran yaron nan ya fito ya fara miki liƙi, kawai saina samu zuciyata da shiga ƙunci harna kasa dannewa na turama Ibrahim saƙo, amsar daya bani ta sakani miƙewa zimbir na nufeku, sai kuma ga Awwal yazo min da batun wai kece ai muka kai gida watanni takwas da suka wuce. Bayan mun kaiki gida na koma masauki ban iya barci ba Khadijah, kwana nai ina jerama UBANGIJI godiya dan wlhy a ƙanƙanin lokaci ya dasa min ƙaunarki a zuciya irin wadda ban taɓama wata ɗiya mace da sunan soyayya ba a rayuwata. A washe gari na matuƙar jin ƙagara a ɗaura mana aure, dan kawai saina samu kaina da tsoron karfa tsohon mijinki ya dawo yace bai sake ki ba, ban samu nutsuwa ba har sai da naji an ɗaura mana aure. Ina sonki Khadijah, ina matuƙar sonki har cikin jinina, ina fatan nima zaki soni ki ƙaunaceni koda ƙanƙanine dan ALLAH. Karki wahalar dani domin ni mai rauni ne akan soyayyarki”. Hannunta dake a cikin nashi ya ɗorasa saman ƙirjinsa, cikin sake raunana murya da kafeta da mayun idanunsa masu matuƙar haske da girma ya furta......✍️


_____________

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na talatin da huɗu_


_____________


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

___________

.......“Taɓa kiji yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri. Na kuma fara fuskantar wannan yanayin ne tun a rannar dinner ɗin nan dana fara tozali dake. Ni na tabbata zaki iya juyani fiye da yanda kike zato saboda ƙaunarki Khadijah, abinda kawai na tsana shine cin amana, wulaƙantamin mahaifiya da ƴar uwa, duk a yanda nake jin ƙaunar nan taki bazan iya amince miki hakan garesu ba. Domin su ɗin rayuwata ne, fatana ke da su ku dunƙule ku zame min abu ɗaya dan ALLAH Khadijah. In sha ALLAHU zakuyi alfahari da ni, sannan zaku sameni fiye da yanda kuke zato da tsammani ku duka dan na kasance rawani a tsakanin kalluba ne gareku.”
A hankali hawayen da Khadijah ke riƙewa suka silalo, murmushi ta saki mai sanyi da raunana zuciya. Hannunta dake cikin nasa ta juya, sai nasan ya koma cikin nata. Kaɗan ta matsashi hakan ya sashi kallonta, ganin hawaye ya sakashi tashi daga kafaɗarta da sauri, hannu ya kai kan fuskarta amma sai ta kauce ma hakan, sai kawai ta sake saki kuka ta faɗa jikinsa. Baida zaɓin da ya wuce ƙanƙameta da ƙyau, ya wani lumshe idanunsa sautin kukan na ratsa masa zuciya. Kusan mintuna biyu ta ɗauka a hakan, jin bata da niyyar dainawa ya ɗagota daga jikinsa gaba ɗayanta, ƙoƙarin son kallonta yake amma taƙi yarda, sai da ya kamo fuskarta cikin tafin hannunsa duka biyu biyu. Yanda ya zubama fuskar tata ido ya sata rumtse idanun da sauri wasu hawayen na sake silalowa. Sake lumshe nasa idanun yayi yana jan numfashi da fesa mata akan fuskar, sai kuma ya matsar da tasa fuskar a hankali ya saukar da lips ɗinsa masu ɗumi kan nata da hawaye ya jiƙa sukai sanyi da santsi ga taushi. Ƙanƙame jikinta tai da farko gabanta na faɗuwa, sai dai yanda yake aika mata salon sumbatar yasa cikin ƙanƙanin lokaci ya birkita mata dukkan lissafi batare data farga ba ta fara maida murtani itama. Sake rikicewa Abaan yayi, dan baima san shi ɗin yana cikin kewa da buƙatar abokiyar halittar tasaba sai a yanzu. Tuni salon ya sauya da wani irin zazzafan yanayi mai ɗunbin tarihin da su kansu sun san bazasu taɓa iya mantawa ba har gaban abadan, dan wannan rana ta kasance musu ta daban a cikin daban a rayuwarsu. Dan ta kasance musu a mafi daraja da girman dare da kowaɗanne ma'aurata kan ƙalla kuma su rubuta su ajiye a kundin sirrinsu mafi zama ƙololuwar sirri da babu wani mahaluki dakan iya bincikowa, dan koda ace da bakinsu suka faɗeshi ga wani sai dai su kamanta badai lissafinsa dalla-dalla ba dan wannan wani al'amari ne mai girma daga ƙyautar UBANGIJIN al'arashi mai rahama da jin ƙan bayi...


_________★


Jikin doctor Giɗaɗo ƙalau ya sauke wayar daga kunnesa. Yayinda matuƙar mamaki ke ratsashi jin yanda Alhaji Abaan ɗin ya amsa masa batun albishir da yay masa kan batun cikin kainaat. Ba haka yay zato ba sam, tabbas bai yi tsammanin samun hakan ba. Dan a zatonsa idan ya sanar masa Abaan ɗin zai kasance cikin ɗunbin farin ciki tamkar ya fasa wayar dan daɗi, dan shi shaidane irin wahalar da suka dingayi da matar tasa akan neman irin wannan damar. Amma sai gashi yanzu yaji sabanin hakan. (ayyah) kalamarfa da Abaan ɗin ya amsa kawai kenan da ita lokacin daya sanar masa da maganar ciki a jikin Kainaat na kwakin da basu wuce sati ɗaya ba ma, daga ƙarshe kuma yace masa yanada uziri sai kawai ya yanke kiran. Shigowar Nadwa ya sashi jan ajiyar zuciya ya fesar, sai kuma yaji wani daɗin ganin nata dan koba komai zata fiddashi a duhun da yake ciki yanzu..
Sun gaisa da girmamawa, batare da ya jira jin miya kawota ba ya jeho mata tambaya. “Hajiya Nadwa nikam ko zan sami wata number ɗin Alhaji Abaan a hannunki, dan inata kiransa nai masa albishir amma yaƙi ya ɗagamin, kin san manyan nan da uzirori”.
Ɗan jimm tai, sai kuma can ta ce, “Wani abu ya faru ne kake neman number ɗin sa?”.
“A'a babu abinda ya faru sai alkairi, kawai ina son masa albishir ne game da rashin lafiyar Hajiya Kainaat”.
Da sauri cikin waro idanu ta ce, “Albishir ɗin mi?”.
“A ke kam na faɗa miki kuma na ragema kaina lissafi, ai nai alƙawarin sai mijinta ya fara sani kafin kowa”.
Kallonsa ta tsaya yi kamar bazatace komai ba sai kuma ta ja numfashi, cike da kissa ta ce, “Kasani ko idan ka faɗamin ɗin na zama silar da za'a ninka maka goron albishir ɗin naka. Common faɗa min mike faruwa in har kana son number”.
Yasan halinta, tunda tace hakan saifa ya faɗa, ƙasa ya sake yi da murya ya ce, “Dan ALLAH amana fa, dan nafi son ya sani ta bakina kafin kowa”.
“Baka da matsala ina dai wannan ne”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya matso da fuskarsa a cikin raɗa ya ce, “Na gano tana ɗauke da cikin kwanaki takwas ne”.
Sosai Nadwa ta waro idanu waje har tana ƴar zabura ta furta, “Ciki kuma doctor?”.
Da sauri yay mata alamar ta rage murya, sannan ya amsa mata da, “Tabbas kuwa ko tantama babu ciki, Kinga kuwa ai wannan albishir ni ya kamata na fara sanarma Alhaji Abaan”.
“Ai ba nashi bane. Domin kuwa kusan shekara ɗaya da wata biyu kenan da rabuwarsu. Wannan yaron da kaga ya kawota shine mai cikin dan shi ta aura. Idan kace zaka kira ABAAN maimakon goron albishir ɗan karen bugu zakaci ma. Sannan idan ka sanar da Kainaat ko mijinta batun wannan cikin ma komai zai iya faruwa. Dan haka inada da bara, idan ka bani haɗin kai ni da kai duk sai muci arziƙi mu bar arziƙi a inda yake, kadai san ni ai bana kawo maka aikin banza”.
“Tabbas hakane Hajiya Nadwa yanzu yaya kike son ayi?”.
Wani shegen murmushi ta saki da kashe mar ido ɗaya, sai kuma ta miƙe tana ɗan duƙawa saman decks ɗin ta yanda har yana iya ganin jikinta. Yawu ya haɗiye da ƙyar yana sake ware ido shi yaga banza. Cikin kunne ta gwargwaɗa masa maganar da nima banji ba, a take suka saki ƴar dariya, ta bashi hannu alamar su tafa, cikin rawar jiki ya miƙa mata nashi shima yana wani karkatar dakai da leƙata. Yi tai kamar bata fahimci ina ya dosa ba suka tafa ta koma ta zauna a mazauninta....


“Doctor har yanzu baka sanar min mike damun matata ba, ko result ɗin bai fita bane?”.
Kai doctor Giɗaɗo ya jinjina yana yana jawo wani file a gefensa. Sai kuma ya kalli Dafeeq yana ɗan murmushi. “Afuwan abokina, result ɗin matarka ya fito, sai dai muna jiran na ƙarshe ne shiyyasa bance da kai komai ba. Amma tunda ka damu bari na baka wannan ɗin. Alhmdllh ba wani abu ke damunta ba sai infection, yayi tsanani ne sosai da har yake sakata ciwon mara, sai dai kada ku damu yanzu haka mun fara treatment ɗinta kuma komai zai zama normal”.
Wani shegen kallo Dafeeq ke masa, dan abinda Doctor bai sani ba duk tattaunawar da sukai da Nadwa yaji ta, abinda kawai bai ji ba maganar datai masa a kunne, itama kuma ya gama tsara hanyar da zai san ko minene. Da yake makirine bai nunaba ko a fuska, sai ma damuwarsa daya nuna sosai akan ciwon Kainaat ɗin. Babu musu kuma ya amshi takardar magunguna yaje ya saya. Ɗakin da Kainaat ɗin take ya koma, ya samu Nadwa na bata shayi, zama yay a kusa da ita cike da kulawa yana jera mata sannu, ƙasan ransa kuwa ji yake kamar ya shaƙe banza dan ba abinda zancen cikin nan ya ƙara masa a zuciya face ƙara jin tsanarta. Da gaske shifa bai shirya haihuwa ba yanzu, koma zai haihu bada wannan tsohuwar guzumar ba mai bakin iyaye aka. Da Khadijah kawai zai iya yarda ya haihu, dan itace kawai ta dace da hakan.
Kulawa sosai da hidima yake mata har abin na bama Kainaat mamaki, harma tana tunanin akwai abinda yake shiryawa a ransa amma ta gagara gane komai. Kwanansu

28 / 38