CUTA TA DAU CUTA COMPLETE BOOK BY BILLYN ABDULL.txt

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   24 / 38

69K to 72K   out of 113.7K words

ALLAH gaba ɗaya ma ta gama ruɗewa da gigicewa. Itafa aka ɗaurama aure a yau. Ya arrahaman ya akai haka ta kasance? Rashin amsa yasata ƙara daurewa, dan tayi alƙawarin a wannan gaɓar, koda mijin nata zai kasance gurgu ne. Makaho ne. Zata zauna dashi kasancewar su iyayenta suka zaɓa mata shi. Kai koda ace ƙazami ne, ko da ace jahili ne. Kai koda ma ace yanada wani mummunan hali in har bazai sakata saɓama UBANGIJI ba, zata zauna da shi. Ta kuma san ma iyayenta bazasu taɓa aura mata wanda zai ɗorata a hanyar zuwa wutar jahannama ba.
Nasiha sosai akai musu a ɗakin har iyayensu mata suma sun shigo suka ɗora nasu kafin a fito dasu saboda kiran sallar la'asar. Cikin gida aka shiga dasu wajen Mama. Kasa daurewa Khadijah tayi ta faɗa jikinta tana hawaye mara sauti. Rungumeta kawai mama tai batace komai ba. Dan harga ALLAH tana tausayin ƴar tata. Amma tana mata fatan alkairi a wannan auren. Suma su Ni'ima jikin Maman suka shige suna kuka. Hakan yasa dangi abokan wasa sukai musu caa da sheri wasu na karesu....

Bayan idar da sallar la'asar duk aka ɗunguma babbar harabar islamiyyar su da za'ayi taron. Komai an gama shiryawa manyan baƙi kuma duk sun iso dama sallar dai ake buƙatar fara gabatarwa sannan. Zaman amare da aka sakema shiga cikin dogayen rigunan abaya farare da adon golden da mintuna kaɗan tawagar anguna ta iso wajen. Nan take wajen ya ƙara cika taf. Sauka aka fara gabatarwa, inda komai ya tafi a cikin tsari da birgewa. Yayinda bakunan anguna ya kasa rufuwa. Sai dai babu wanda yasan wanene angon Khadijah har zuwa yanzu idan ka cire iyayenta maza. Sun sami ƙyaututtuka da suka bada mamaki musamman wanda suka fito da ga ogan abokan ango Abaan Omar Modibbo. Dan kuwa mukullayen motoci har uku ƙanana dai amma masu ƙyau da ɗaukar hankali ya bama amaren su duka ukun dan sun birgesa matuƙa. Bayan wannan ma wasu ƙyaututtukan sun biyo baya dan islamiyyar sun gayyaci manyan mutane sosai, hatta da su Baba Hakimi da suka taso tun daga Adamawa basu wuceba suma sun tsaya domin saukar, kafin a fara gudanar da lectures masu ratsa jiki ga anguna da amare. Har zuwa yanzu bawai Khadijah ta fita a ɗimuwar da take ciki bane ba. Dauriya kawai take da son tilasta kanta zama a dake, amma duk da haka jikinta zazzaɓi ne mai zafi sosai dan tunda suka zauna a wajen ma kanta na a kafaɗar Ni'ima kasancewar duk sanda ya ɗago sai ta kama ogan anguna da ake kira Alhaji Abaan Modibbo na kallonta, sai ta daina ɗagowar har sai da aka kirasu wajen sauka. Suna dawowa bayan an kammala ma dai kwance take shiru a jikin Zuhrah data koma kusa da ita a yanzun. Sauka ta ƙyatar sosai. Ansha hotuna kamar babu gobe. Anan ne ma dai mutane suka fara tsarguwa da hasashen wanda kowa kema kallon angon Khadijah ganin duk sanda za'ai hoto yana a kusa da ita ne, amma kuma basu da tabbas har aka tashi gab da magrib.

Bayan sallar isha'i akai shirin miƙa amare ɗakunansu. Sai dai kuma banda Khadijah. Ayanzu ne fa sukai asalin kukan rabuwa. Dan da ƙyar aka raba su Ni'ima da ga jikin Mama da Khadijah. Da aka kaisu yima Baba sallama ma nan ma ansha ɗan ƙaramin bidiri kafin. Har ƴan kai amarya suka je suka dawo Khadijah na kwance a ɗaki zazzaɓi yay mata rijif. Koda mama ta bata magani ma fakar idonta tai ta ajiye ta koma ta kwanta. Anata sam barka da gidajen amare. Abin farin ciki kuma suna a jere da juna ne komai nasu kuma iri ɗaya kamar wanda suka aura tagwaye. Koda yake Ibrahim da Adams kowa na iya kallonsu da tagwaye saboda shaƙuwarsu da ƙaunar fa sukema juna. To sai muce ALLAH ya sanya alkairi ya kuma basu zaman lafiya mai ɗorewa....


*_WASHE GARI_*

Duk da yanda Khadijah ta tashi a yanayin rashin lafiya Baba ya tabbatar da yau za'a wuce da ita nata ɗakin mijin. Dan kuwa ya tabbatar da ƴan uwan ango da motocin ɗaukar amarya tun jiya suna Kano yau kuma zasu wuce da ita. Dan haka ƙarfe goma duk wanda zai rakkiyar Khadijah ya shirya tsaff. Dan motocin har sun iso tare da masu amsar amarya. An musu tarba ta mutuntawa kamar yanda suma suka shigo da dattakonsu. Matane guda biyar sai abokan ango da galla-gallan motoci har kusan ashirin. Al'amarin ya bama kowa mamaki daya kawo maganganu suka fara tashi a anguwa. Kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Ƴan ɗaukar amarya ke sanar da amarya ita a jirgi zata wuce tare da mutum biyu, dan haka motocin da suka ɗauki dangi tuni sun ɗauki hanyar Abuja.
Bayan kammala shirya Khadijah dake ta faman kwasar kuka aka kaita ga baba. Sai da ya sanya mata albarka tare da nasiha mai ratsa jiki da addu'a kamar yanda yayma ƴan uwanta jiya sannan ya ɗora da faɗin, “Naso ace na baki damar zaɓar Miji da kanki Khadijah domin ki tabbatar da na huce na kuma yafe miki. Sai dai tsarin UBANGIJI ya banbanta ne dana kowa. Amma in sha ALLAHU idan kikayi haƙuri a yanzun ma zakiyi farin ciki fiye da zaɓin da zaki iyama kanki. Dan mutumin nan mutumin kirki ne da tabbas aurenki da shi wata hikima ce ta UBANGIJI. Naso na faɗa miki dukkan yanda al'amarin ya kasance haka. Sai dai ya roƙi alfarmar na barsa ya sanar miki da kansa. Dan haka dan ALLAH ina roƙonki kije kuyi haƙuri a gidan aurenki Khadijah. Kima mijinki biyayya, ki ƙyautatama ƴan uwansa da maƙotanki. Ki manta da abinda ya faru baya sunansa ƙaddara. Ita kuma ƙaddara ai babu mai iya tsallaketa. ALLAH yay miki albarka ke da sauran ƴan uwanki”.
A tare aka amsa da Amin. Yayinda Khadijah ta sake fashewa da kuka da faɗin, “Baba in sha ALLAHU zan kasance mai biyayya a gare ku. Kuma dan ALLAH ku yafe min ku yafe min. In sha ALLAH zan tabbatar muku da ni ɗin ɗiyace tagari akan wannan auren”.
“Mun yafe miki tuni Khadijah. Fatanmu dai ki bama mara sa ɗa kunya kawai. Ki zauna lafiya ki kuma ringumi sabuwar rayuwarki ta yanzu da hannu biyu da kuma haƙuri”.
“In sha ALLAHU Baba”.
Sauran ƴan uwa sun sake mata nasiha sannan aka fito da ita zuwa motar da zata kaisu airport ɗin ita da wasu dangin angon 2 da aka bari, sai Inna Zulai da Gwaggo Safina da zasu mata rakkiyar suma. Har suka isa airport kuka sosai Khadijah keyi Inna Zulai dai na lallashinta. Sun ɗan yi zama saboda kai kawo da jiran lokacin daya rage dan sai 12:30 jirginsu ya ɗaga. Khadijah ta sake hawa jirgi a karo na biyu. Yayinda su Gwaggo Safina ya kasance musu na farko. Cikin mintuna ƙalilan suka iso Abuja. Anan ma sun tarar da motoci na jiransu har guda biyu. Ɗaya Khadijah da iyayenta suka shiga. Ɗayar kuma ƴan uwan ango biyu dake tare da su ne. Khadijah dai na kwance jikin Inna Zulai har suka iso inda taji suna faman santi ƙasa-ƙasa, duk da dai dama tunda suka fito airport bakinsu bai huta ba sai faman ƙus-ƙus sukeyi.
Tun daga gate su Gwaggo Safina suka sake tabbatar da ƴarsu Khadijah ta sake shiga cikin zuri'ar fulani kamar dai mijinta Dafeeq na farko. Banbancin kawai shi Dafeeq sun jima a birni a yanzu ko fillancin ma babu maiji a iyayensa. Suko wannan sunata yara yarensu a baki tabbacin basu bar gida ba. Tarba akai musu ta girmamawa da mutuntawa. Yayinda suma suka nuna nasu dattakon. Dan duk da an nuna musu sashen amarya basu yarda sun nufi can da ita ba suka buƙaci a kaisu sashen mahaifiyarsa tunda ance suna tare ne a gida ɗaya. Aiko sunji daɗin wannan ƙarancin.
An fara kai Khadijah wajen surukata. Katafaren falo na gani na faɗa da yaji kayan more rayuwa kamar ba'asan ciwon kuɗi ba. Kai tsaye suka gane wacece mahaifiyar angon. Dan dai-dai Khadijah da fuskarta ke lulluɓe da mayafin da aka rufa mata na kaiwa duƙe kamilalliyar dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 2sitter ta kamo hannunta ta zaunar a kujerar kusa da ita tare da rungumeta. Ta tsufa kam, sai dai ba wani tsufa ba irin na takwarkwashewa. Dan akwai jin daɗi sosai tattare da ita. Kasa daurewa Khadijah tai ta zamo ƙasa kusa da ƙafafunta ta zauna. Hakan datai ya sake birge ƴan uwan ango dama mahaifiyarsa sosai..........✍️


*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥


*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K'ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na ashirin da tara_

______________


Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846

Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria

Ummu khalifa 01017018846

_______________


......Sunyi zama na kusan mintuna ashirin an gaggasa da ƙyau kafin ai musu rakkiya inda akace sashen amarya. Ai su Gwaggo Safina ma sai suka gagara cewa komai ganin daular duniya. Salla sukai zaman gabatarwa yayinda Khadijah ta kwanta dan zazzaɓi ne sosai a jikinta. Zuwa yanzu ma har ɗan rawar sanyi take yi. Amma tanata ƙoƙarin daurewa ta kuma ƙi sanarma kowa har sauran mutanen da suka taho a mota suka samu isowa. Anan fa gida ya sake ɗaukar harama. Ga tarin abinci iri-iri an kawo musu al'amarin dai sai sambarka kam.
      Aunty Firdausi ce ta fahimci Khadijah babu lafiya. Dan an zuba mata abinci tace ta ƙoshi. Tsoffin iyayenta suka mata caa da faɗa wai tana abu ita ba budurwa ba. Ya kamata ace ta haƙura haka ta kuma godema UBANGIJI da wannan ni'ima da yay mata. Taso matan da sukai ya tilastata yin lauma ɗaya ta abincin sai ga amai. A sannan ne Aunty Firdausi data kawo mata ɗauki taji jikinta da zafi sosai shine ta ke sanar musu bama ta da lafiya. Duk kuma sai jikinsu yay sanyi suka shiga mata sannu da jera mata kalaman lallashi. Dole wanka ta samu tayi da ruwa mai zafi ta canja kaya. Sai kuma aka shiga tunanin ina za'a samo magani, gashi su ba gama wayar ango sukai ba balle a nemosa ace amarya babu lafiya. Da kunya kuma aje wajen mahaifiyarsa daga zuwa ace mata amarya babu lafiya. Dole suka haƙura har zuwa yamma da aketa shirye-shiryen Fulani event ɗin da suka shirya zasuyi anan harabar gidan. Dan har an gama tsara ko'ina da adon fulani ma. Ana idar da sallar magrib aka kawo kayan da amarya zata saka itama.

         Sosai kayan sukaima Khadijah ƙyau tamkar ka saceta. Ga shi itama kuma ALLAH ya azurtata da gashi, dan har Aunty Firdausi na tsokanarta da ai da ansan zasuyi wannan wasan da an mata kitson fulanin itama tunda dai ta alaƙantu da su ta fannin uwa. Dariya wanda ke ɗakin sukayi kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Ita dai Khadijah bata tanka musu ba dan takanta take. Ga zazzaɓi ga fargabar tunanin kowane irin miji kuma zata tarar a yanzu. Shin shima irin Dafeeq ne ko yamafi Dafeeq abubuwan mamaki. Dan itakam a yanzu bata jin bayan mahaifinta al'amarin wani namiji na birgeta a wannan rayuwar. Kawai dai ayi sha'ani ne.
        Sai da aka yafa mata gyale aka rufe mata fuska sannan suka fito. Duk da ba ganin fuskarta akeba sai ambaton masha ALLAH dangin ango keyi ganin yanda kayan sukai matuƙar zama a jikin amaryar tasu. An zaunar da itane kusa da surukarta daketa faman jin daɗin sake ganin wannan rana da ranta, ta riƙe hannunta cikin nata. Zafi taji sosai da ya sakata ambaton “Ya Salam daughter baki da lafiya ne haka amma baku faɗa ba?”. Kasa cewa komai Khadijah tai, dan duk da bataga fuskar matar ba har yanzu wani kalar kwarjini da girmanta take ji cikin ranta. Jikinta ta ɗan saka Khadijahn tare da kiran wata ƙyaƙyƙyawar matashiya mai tsananin kamanni da ita. Gabansu ta tsugunna tana murmushi da dafa ƙafarsu su duka biyun, sai kuma ta ɗaga gyalen zata leƙa Khadijah. Harararta Mamy tayi da buge mata hannu. Tai ƴar dariya da faɗin, “Kai Mamy na ƙagarane fa naga amaryan Hamma”.
       “To bazaki gani ba”.
   Mamy ta faɗa tana hararta. Hannu ta ɗaga alamar surrender tana murmushi. “Shike nan na haƙura Mamy, amma kamar jikinta da zafi.”
        “Eh shine dalilin da yasa ma na kiraki nan ai. Yayanki basu iso ba har yanzu, inaga kiyi magana da Yafendo ayi komai a takaice Dota ta koma ciki, sannan ki nema min number doctor”.
    “Okay Mamy”.
   Ta faɗa tana miƙewa. Kamar jira tashinta babu jimawa aka wangale gate. Motace ta shigo, rashin wadatacce fili kasancewar sun mamaye harabar gidan yasa sukai parking can nesa. Kowa yasan ango ne ya iso, dan can Kano suka barsa sai yanzu yake isowa. Jirgin ƙarfe bakwai suka biyo alhmdllh kuma gashi har sun iso. Driver da yaje ɗaukarsu ne ya fara fitowa. Sai Awwal dake gefensa shima ya fito. Shiko yana baya bayansa jingine da kujera idanunsa a lumshe. A kallo ɗaya zaka fahimci a gajiye yake. Dan koda driver ya buɗe masa motar ya ɓata kusan minti ɗaya kafin ya fito. Cikin rashin hayaniyar nan tasa yacema drivern “Thanks you Baba. Mun hanaka barci ko”.
     Murmushi Baba yay da faɗin, “A haba Alhaji ai yima kaine. Sannunku da zuwa dai, ALLAH kuma ya sanya alkairi a cikin wannan aure. Yasa yanda muka taru anan baɗi i war haka muna nan muna shagalin suna kuma”.
        Awwal ne ya amsa da amin yana ƙumshe dariya. Shiko ya ɗan murmusa kawai batare da yace komai ba sai dai a zuciyarsa ya amsa da Amin. Dan sosai yake son yara shima, kawai dai ana ganin kamar bai damu bane saboda bai cika yawan furtawa ba. Idanunsa ya kai inda ake taron, hankalin wasu duk na garesu ne, yayinda wasu kuma ke hidimarsu batare da sun farga da su ba. Tunanin ta yanda zai shige sashensa batare da wani ya tsaida shi ba yake. Sai dai bai kai ga samo mafitarba ma ƴan uwa suka fara zagayesa ana masa sannu da zuwa da jera masa kirarin ango ango kasha ƙamshi. Kamar yanda ya saba ne, murmushi kawai yake musu a taƙaice. Ganin suna neman cika wajen ya zare jikinsa ya gudu ta baya zuwa sashensa dake manne dana amarya. Sai dai da yake akwai ƙofa ta gaba da baya da basai  dole yabi ta cikin falon Khadijahn ba yasa zaka iya ɗauka ma daban-daban ne. Shigewarsa babu jimawa Mammy tasa aka maida Khadijah ciki dan rawar sanyi take yi. An cigaba da gudanar da shagali Noor kuma taje ta sanar ma Yayanta amarya bata da lafiya a kira Doctor. Fitowarsa kenan daga wanka sallamarta ya sashi zira jallabiyya ya fito falon. Agogo ya ɗan kalla sai kuma ya dubi ƙanwar tasa ɗaya tilo a duniya. “Amma miyasa tun ɗazun k baki kirashi, yanzu fa kusan 10 ake tafiya. Sannan kun zo da ita a wannan sanyin ita da bata da lafiya kuma”.
       “Sorry Hamma Ab. Ai ba'asan bata da lafiya bane fa sai yanzu Mamy ta gane. Kuma yanzu haka ma an maidata ciki. Na kuma kira Doctor ɗin bai ɗauka bane maybe baya kusa”. Baice komai ba face ƙoƙarin sarrafa wayar hannunsa da ya ɗauka. Inda ya fito ya koma yana kai wayar kunnesa da yima Noor alamar taje kawai...

     Noor na zaune a bakin gadon da Khadijah ke kwance ƙudundune cikin bargo kiran Yayanta ya shigo mata. Tana ɗauka umarnin kawo Khadijah kawai ya bata sashensa ya yanke kiran. Koda ta sanarma su Aunty Firdausi cewar Hammanta yace ta raka Khadijah likita yazo babu wanda yay yinƙurin hanata. Sai ma sake birgesu da take dan Noor akwai surutu, tun ɗazun hira take musu abinta kamar wata ƙaramar yarinya. Khadijah ce ma taso taɗan turje Inna Zulai ta fara mata faɗa, dole ta miƙe Noor ɗin ta kama mata hannu suka fice tana tafiya cikin ƙarfin hali dan jikinta sai rawar sanyi take.
        A hankali ya ɗago idanunsa dake kan tv yana sauraren hirar da doctor ke masa ya zubama ƙofar tare da amsa sallamar Noor akan lips. Khadijah da ke tafiya a hankali ya zubama idanu har suka iso gabansa, sosai tai masa ƙyau a cikin kayan fulanin dan ma akwai mayafi jikinta. Kai tsaye Noor ta zaunar da ita a kujerar 1sitter da ke gefensa na dama. Itako da dama da rabin fuskarta gyale ya rufe bata yarda tama kalli ko ina ba sai sassanyan ƙamshin turaren wuta dana fresheners dana jikinsa harma dana doctor ke rige-rigen shigar mata hanci. Noor na zaunar da ita ta naɗe ƙafafunta zuwa saman kujerar ta wani irin dunƙule waje ɗaya kamar ƴar mage. Wani irin fisgarsa yanayin nata ke yi, amma sai ya

24 / 38