CUTA TA DAU CUTA COMPLETE BOOK BY BILLYN ABDULL.txt

Author :  BILLYN ABDULL Category :  Hausa Read

Chapter   20 / 38

57K to 60K   out of 113.7K words

yace yazo Kano suna buƙatar ganinsa daga nan zuwa gobe. Zai kuma riƙe iyayensa a station ɗin har sai yazo. Bai jira cewarsa ba ya yanke kiran. Matuƙar tashin hankali Dafeeq ya shiga kuwa. Duk ya wani gigice da ruɗewa kamar wanda ya zare. Kuma shi a karan kanshi bama zai iya fadin abinda ya sakashi ruɗewar ba ma dan bai taɓa hasashe ko tsammanin Khadijah zata iya sanarma su Baba Hakimi abinda ke faruwa ba balle komawa gida a wannan halin, sakamakon imani da yay da ɗunbin soyayyar da take masa.....

__________★


“Kamar yanda nai alkawarin sanar muku wacece ni? Sunana shine Alimah kamar yanda kuka sani. Sai dai ni ba mutum bace kamar yanda kuke tunani...”
Babu wanda baiyi zaburar firgita ba a ɗakin, itako cikin rashin damuwa ta cigaba da faɗin, “Kamar yanda kuke rayuwa a gidajenku haka muma wasu a cikinmu nan ɗin ne wajen rayuwarmu. Dan haka na kasance ɗaya daga cikin masu rayuwa a gidan su Anoosh. Na shigo rayuwar ɗanku ne dan rama cuta da cuta. Saboda na fahimci bazai daina abinda yake ba cikin sauƙi. Na tsara shiga rayuwar ƙanwarsa Rabi'ah ne domin cimmasa ta inda bai zato ko tsammani ba. Dan haka ni da shi *_CUTA CE TA ƊAU CUTA_*. Abinda nai masa a baya kuma ba komai bane face sharar fage. Dan sai na sabauta rayuwarsa fiye da yanda ya ruguza ta ƴaƴan jama'a. Sai na bar babban gargaɗi wa ƴan baya masu irin halinsa a kansa ta yanda idan suka tinashi zasu shiga hankulansu yayin aikata makamancin abinda ya aikata. Dan haka JJ muje zuwa mataki na biyu dan yanzu ne wasan zai fara na gaskiya tsakanina da kai”.
Wani irin gigitaccen ihun tashin hankali JJ ya buga, jikinsa na wata irin jijjiga da magiyar dan ALLAH tayi haƙuri, ya tuba ya tuba ta taimakesa tayi haƙuri. Ina ko saurarensa batai ba tama ɓace ɓat a ɗakin. Daga iyayensa har ƴan uwan nasa suma a rude suke ta yanda bama fahimtar ihunsa da magiya suke ba. Dan tuni wasu ma sun bar ɗakin a guje. A ƙanƙanin lokaci labarin JJ ya fara zagaye anguwa da ga bakin waɗanda suka jiyo komai a gidansu. Dan danan ko'ina ya ɗauki zance, har aka samu mai ƙarfin halin zuwa anguwar su Anoosh ya fesa labarin da ya zarce cikin anguwa ya fara zagaye gari har kunnen ƴan jarida sai ga zance a gidajen rediyo. Yayinda wasu ma suka fara zuwa gida wai jin ta bakin JJ.
Hakan kuwa bamai yiwuwa bane, dan ganin JJ ya zama abu mafi wahala, wanda ma sukai ƙarfin halin iya juriyar ganin nasa da sun shiga ɗakin suke dawowa hankali a tashe sakamakon abinda idonsu ke gane musu. Dan batare da cin wuta ko ƙuna na gaba ɗaya fatar JJ tai wani irin saluɓewa kamar wanda ya ƙone a cikin man gyaɗa ko wata gagarumar wuta. Babu abinda yake a kwana da yini sai kuka da ihun magiyar a taimakesa jikinsa na ci da wuta. Sai dai abin mamaki a zahiri babu abinda ake gani sai jajur da jikin nasa yayi kawai. Tausayin rai duk da ana ALLAH wadai da abinda JJ ya aikata malamai suka haɗu ana masa addu'a da fatan Alimah ta bayyana kanta. Amma ƙiri-ƙiri babu Alimah babu dalilinta. Sai nau'o'in azabar da take ganama JJ kawai ke bayyana kansu. Dan bayan ƙuna sai ga JJ kuma na kukan son yin fitsari amma yaƙi fita. Ranar ma sunga tashin hankali akan wannan matsalar dan sai da dai takai an ɗaukesa zuwa asibiti. Shi kansa bai taɓa tunanin fitsari zai iya zama azaba ga mutum ba sai a ranar. Iya ƙoƙari likitoci sunyi dan ganin JJ yayi fitsari amma abu ya gagara, sai da takai har suma yake sannan aka samu ɗan kaɗan ya zuba, sai kuma zubar kaɗan ɗin ta sake zame masa wata sabuwar azabar data nema zama fin ta farko garesa har yana gigicewa kamar wanda ciwon hauka ke neman kamawa.
Mutane ƙalilan ne ke tausayin JJ, amma mafi yawa sai ALLAH ya ƙara da ALLAH wadai sukeyi. Lokacin da hotunansa da labarinsa suka fara zagaye social media batare da an san wanda ya ɗora su ba sai wasu a cikin ƴammatansa daya lalatama rayuwa da irin yaudarar da yay ma Anoosh suka shiga binsa da mugayen addu'a suma. Harda masu zuwa dubashi har gida ko asibiti. Abin kamar wata almara labarin JJ ya zama latest a yanzu musamman a media da gidajen rediyo..
Bata canja ba kuma akan abokansa suma nasu ya fara fitowa duk da dai bai kai ta'addacin na JJ ba da ya haɗa harda kisan kai....


__________★

Kamar yanda d.p.o yay alƙawarin riƙe iyayen Dafeeq haka kuwa akayi, dan saurayin Zuhrah da ke tsaye akan case ɗin ya nuna suma bazasu yarda ba har sai Dafeeq yazo ya bayyana gaskiya wa mutane sannan domin wanke Khadijah. Hankali tashe Dafeeq ya iso Kano tare da Kainaat daya taso gaba. Da farko batai niyyar zuwa ba, sai dai bisa ga tunanin shukama Dafeeq tsiya a Kanon ta yanda zai saketa ya kuma bata takardunta kan dole yasa ta yarda ta biyoshi. Kusan ƙarfe sha biyun dare suka iso Kano, dole yay haƙuri suka wuce gidansu dan su kwana. Sai dai Kainaat nata yamutse-yamutsen fuska wai tana ƙyanƙyamin gidan tsabar iskanci. Ba itace a gabansa ba dan haka ya watsar da ita. Washe gari daga sallar asuba a police station yay masa, sai dai kuma bai samu ganin iyayen nashi ba ance sai d.p.o yazo ƙarfe goma.
Hankali tashe ya juya gidan su Khadijah, inda ya tadda su Baba Hakimi da suka kwana anan. Sai dai ƙiri-ƙiri Baba Hakimi ya nuna shi bazai sauraresa ba sai sunje gaban d.p.o. dan gaskiya labarin abinda Dafeeq ɗin yazo ya aikata na ɓata Khadijah anan Kano ya matuƙar girgizashi da mamakin yaron. Yaso ganin Khadijah amma sai hakan ya gagara gareshi nan ma, sai ma wani abin mamakin daya sake cin karo da shi, wato ganin Kainaat ta fito a gidan ita da wata yarinyar makwaftansu da alama itace tai mata rakkiya. Wani shegen murmushi take masa cike da salon iskanci da nuna halin ko ina kula da mamakin da take karanta a saman fuskarsa........✍️


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na ashirin da huɗu_


__________


*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥


*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K'ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

____________


......Wani irin duka zuciyarsa keyi matuƙa da ganin Kainaat ɗin. Dan duk yanda yaso dakewa yay fuska hakan ya gagara gareshi. Cikin ɗan rawar harshe da shan jinin jikinsa ya furta, “Mi kikeyi anan haka Hajiya?”.
“Zuminci”.
Ta bashi amsa a gadarance a kuma taƙaice. Batare data jira cewarsa ba tai gaba abunta ƴar rakiyarta biye da ita. Sosai yaji kansa yana juya masa, dan magana ta gaskiya ya fara tsoron shegiyar matar nan. Dan ya fahimci dole akwai abinda take ƙullawa, kai anya ma ba'itace ta saka aka kawo Khadijah da su Baba Hakimi Kano ba? Lallai biri yayi kama da mutum, dan ya kamata ma ace yay wannan tunanin, to amma bai zama lallai ita ɗin bace tunda yasan in har Khadijah gidan Baba Hakimi ta tafi a safiyar daya saketa dole Baba Hakimi zai iya cewa zai rakota gida. Gaba ɗaya kansa ya kasa haska masa komai game da abinda Kainaat take son shiryawa, bai da zaɓin kuma daya wuce tafiya su haɗu a police station ɗin kamar yanda akace masa.
Koda ya koma gida duk haukan daya dinga yi akan Kainaat ta sanar masa mitaje yi gidan su Khadijah ko kallonsa batai ba balle ma ya samu wata amsa. Hasalima ta tattarashi ta watsar ne tai kwanciyarta. Cikar lokacin tafiya station ya sakashi ƙyaleta ya wuce yana rayama ransa dole zai yi maganin ta ne.

*_POLICE STATION_*

Kowa da ake buƙatar gani ya iso, har D.p.o ya bada umarnin fito da iyayen Dafeeq da suka kwana a rufe. Sai dai abin mamaki sam hankalinsa ma baya kansu ya zubama Khadijah idone tamkar zai cinyeta. Shifa badan kar ace yay ƙarya ba sai yaga a kwanaki kusan goma sha ɗayan nan da rabuwarsu kamar harma ta canja. Tai masa wani irin fresh da ita, babu bandage ko ɗaya yanzu a jikinta sai ɗan alamun tabbunan ciwukan. Ga wani ƙamshi mai tada hankali da take zubawa. Tana sanye cikin doguwar rigar abayar Ni'ima baƙa da aka wadata da duwatsu sai walwali take. Shi shaida ne Khadijah ƙyaƙyƙyawace. Dan irin black beauty yaran nan ne masu taushin fata da ƙyalli tamkar ƴaƴan masu kudin na da rana bata ganinsu kullum suna ac. Gata da murzajjen jiki dan babu rama tattare da ita sam kasancewarta cikakkiyar mace da ALLAH ya wadata da komai dake tabbatar da mace a mace. Tunda suka haɗa ido tai masa wani banzan kallo daya girgiza zuciyarsa ta ɗauke kanta bata sake kallon ko sashen da yake ba. Amma shikam sam ya gagara daina kallonta. Jima yake kamar yaje ya rungumeta, dan wani irin mahaukacin sonta ne ke ƙara azalzalar zuciyarsa. Da gasken gaske yana matuƙar ƙaunar Khadijah, baima san miya shiga kansa ba ya saketa shikam, shiyyasa sam ba'a son yanke hukunci cikin fushi.....
Maganar d.p.o ce ta katse masa tunani, dole ya nutsu ya maida hankalinsa can. D.p.o ya fara bama Khadijah damar yin bayani akan duk abinda ya faru. Itako kanta tsaye babu ko shakka balle gargada ta shiga jero bayani tun daga marin da taima Dafeeq a makaranta har zuwa randa ya daketa ya kuma saketa bata ɓoye komai ba. Shima Baba hakimi ya maimaita tun daga randa sukaje wajensa har zuwansu nan Kano, wanda ke tare da shi suma sun tabbatar da hakan akai. Karo na farko ran mahaifin Dafeeq ya ɓaci. Bawan ALLAH muryarsa har rawa take wajen faɗin, “Amma kai ba haka ka faɗa mana ba Dafeeq. Yanzu nan kana tare da yarinyar nan tsahon shekara uku amma kazo kace mana ka saketa harma baka san inda take ba? Dafeeq wace irin rayuwa ce wannan ka zaɓama kan ka? Yanzu gatan da mukai maka a matsayinka na ɗa ɗaya tilo garemu domin nuna godiyarmu ga UBANGIJI kuma sai ya zama laifi kenan da ɗoraka akan wata hanya mara ɓillewa. Anji yarinyar nan itama nada laifi tunda bawai ka jata ta tsiya bane ka tafi da ita, da kanta ta zaɓi binka kuka tafi. Sai dai duk mai hankali da son faɗar gaskiya yasan Dafeeq ka fita laifi. Dan ita mace rauni ne da ita, sannan duk ƙanƙantar namiji a kanta zai iya yaudararta ya canja mata tunani, musamman ku yaran nan na zamani da kukai ma soyayya bahaguwar fahimta. Banji daɗi ba, dan kasa nida mahaifiyarka faɗa akan abinda ba haka yake ba. Duk da wlhy itace nidai ke zugani, koda naji bai kamata nayi abinda mukayi ba sai naji na kasa musa mata saboda soyayyar da nake muku kai da ita. Malam Muhammad dan ALLAH kayi haƙuri ka gafarcemu. Tabbas mun cutar daku kuma mun cutar da kammu. Dan kai mutumin kirki ne ka nuna mana dattako akan wannan al'amarin, saboda tunda aka fara bakace komai ba koda ɓatancine ga ɗanmu sai mune keta hauka a cikin anguwa batare da yin nazari da tunani irin na iyayen ƙwarai ba. Wannan shine mafi yawan kuskuren iyayen zamani akan kin amsar kuskuren ƴaƴansu saboda soyayya. Sai lokacin da abu ya ƙwaɓe yaro ya shiga cikin wani bala'i kuma mu kasa zaune mu kasa tsaye koma muce wani ne ya jefesa da asiri ko baki alhalin mune da kammu muka rusa masa rayuwa saboda gurguwar soyayya. Dan ALLAH ku yafe mana Malam Muhammad kai da iyalinka gaba ɗaya, yanzu da sanadin ciwon nan ka rasa ranka ina zamu saka kammu ne”.
Murmushi irin na dattako Baba ya saki, sai kuma ya nisa a hankali tare da furta, “Babu komai Malam Abubakar. In sha ALLAHU komai ya wuce a yanzu. Kuma dama can ni dai ban riƙe waninku ba face addu'ar kariya da nake bin su Khadijah da shi akan ALLAH ya hanesu aikata alfasha a ƙarƙashin inuwar shaiɗan. Kuma Alhmdllh na godema UBANGIJI daya kasance sun rayu ne a ƙarƙashin inuwar aure. Ko lokacin da kukazo kuke cemana Dafeeq ya saketa ta shiga duniya ban fasa gayama UBANGIJI na ba duk da mun shiga tashin hankali. Amma sai na dinga ganinta a mafarki cikin aminci akoda yaushe, na kuma dinga jin bana kokwanto akan tanada aure. Nayi imani da ƙaddara zata iya faɗawa akan komai, amma ina alfahari da fatan yanda ban taɓa taɓa ƴar kowa ba da nufin zina ko ɓata mata rayuwa nima in sha ALLAHU ALLAH zai bama nawa ƴaƴan kariya. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, ya kuma shirya mana yaranmu damu kammu dan aduk sanda suka aikata kuskure yakan zama wani lokacin muma iyaye da gudunmawarmu a ciki, duk da dai akwai tsayayyun iyaye da wlhy suna iya ƙoƙarinsu akan ƴaƴan amma zakaga abun sai dai addu'a kawai. Wasu kuma duk da suna ƙoƙarin zata iya yiyuwa suma sunma iyayensu wani kuskurene da suke girban abinda suka shuka akan ƴaƴan nasu kuma. Dan abinda muke mantawa idan fa ka aikatama iyayenka ƙyaƙyƙyawa kaima ƙyaƙyƙyawa zaka girba a wajen ƴaƴanka, idan mummuna ne kaima zaka girbi dai-dai da hakanne. Ni kaina ina danganta abinda Khadijah ta aikatamin da bijirewar da naima nawa iyayen akan auren mahaifiyarsu a farko, dan sai da takai bayan an aura min ita nai tahowata nan Kano kusan watanni biyar wai dan duk suji haushi su rabamu, amma koda na koma saina samu dai tana nan a gidanmu. Daga nan na karaya na sallama bayan ita da kanta tamun nasiha da tabbatar min itama ba sona take ba umarnin iyaye tabi, tana roƙona koda bazamu so juna ba muyima iyayenmu biyayya kodan darajar da ALLAH ya basu da fifiko a kammu na haihuwa. Wannan shine sanadin gyara komai harna ɗakkota muka dawo nan cikin Kano da zama. Duk da na roƙa iyayena gafara sun kuma yafemin gashi sai da na girba abinda na shuka ga ƴata ta fari dana ɗauki burin duniya na ɗaura a kanta da tunanin zata zama madubin ƙannenta a komai na rayuwa.”
Kuka sosai Khadijah ta saki hankalinta na ƙara tashi. Dan wlhy zuciyarta zata iya bugawa idan ƴaƴanta anan gaba akace zasu rama abin nan da taima mahaifanta. Cikin rawar jiki da kuka take roƙon dan ALLAH su yafe mata. Cikin murmushi Baba yace, “Ai komai ya wuce Khadijah na yafe miki. Mahaifiyarki ma ta yafe miki tun ma kan ki dawo garemu. ALLAH ya ƙara shirya mana ku”.
An amsa da Amin, yayinda Dafeeq ya durƙusa shima gaban Khadijah cikin sanyin murya ya ce, “Dan ALLAH nima kiyi haƙuri to ki dawo gareni Khadijah. Na miki alƙawarin wlhy zan koma miki kamar da yanda muke a farko. Abinda ya faru ma wlhy tsautsayi ne. Amma zan cigaba da riritaki fiye da yanda nai miki a farko”.
Wani banzan kallo ta masa hawaye na sauka mata. Sai kuma ta nuna kanta da faɗin, “Wai ni kake tunanin zan koma gareka Dafeeq? To kayi kuskure. Wlhy koda ace baka aikatamin komai ba hakan ta faru, zan hana kaina komawa aurenka saboda ya zama horo ga kuskuren dana aikata na bijirema iyayena. Koda ace kuwa ina jin soyayyar ka zata halakani wlhy. Balle ma a yanzu bana jin koda ɗigon soyayyar ka a raina. Kuma wlhy! Wlhy! Wlhy koda ace soyayyarka zata halakani, koda ace kaine autan maza na barka har abada Dafeeq.....”
Cikin rawar jiki da bugawar zuciya Dafeeq dake ƙoƙarin riƙo mata hannu ke furta, “Dan ALLAH Khadijah, dan ALLAH kada kice

20 / 38