Bariki Gadona Book 1 Compelet Oum Aphnan

Author :  Hassana Bamalli Oum Aphanan Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 13

21K to 24K   out of 37.8K words

maida numfashi
"Wash Umma na gaji"
Wani murmushin cinyewa ɗin nan tayi
"Hmmm kice Ansha rawa "
"Wallahi umma kedai bari ,saima kinga ƴarki a fili ,ki bari in Mahmud ya turo mun vid ɗin Ni zan nuna maki ki gani "

Kayan da na samu muke buɗewa wasu in tsaki wasu ina ɗauka in rungume wasu in fashe da dariya ,na Mahmud ne a ƙarshe ,a hankali umma ta ɗauka so careful ta ɗaye duk ta ƙosa taga meye a ciki

Subhanallh diamond ne ta ganin kwance sai walwali yike yina kashe ido tamkar rana ,sai a gefensa aka nannaɗe cheguk ɗin kuɗi aka sagale kamar abun ɗan kunne

Ɓangarowa tayi ,cheque ɗin 1million ne ,in siya Tulare

Kuka mamana ta fashe dashi ta rungumeni
"Oh Allah Ni Fatima nayi farin Haihuwa ban taɓa kaɗa maki ko ruwan tawwada ba bare in kaiki wajen wani malami ba ,ya baki maganin farinjini amma ahhhhh ,Baby kina ganin abunda nike gani kuwa?"

Caɓe baki nayi saboda raina ya ɓaci banga ya saka mun Zobban zinare ba kamar yanda yayi mun Alƙawari

"Umma yau ɗaya na fara jin haushin Mahmud zobunan zinare fa mukayi zai zuba mun"

"Ke jacan wainnan wuce zinare ,kinga a cheque ɗin nan kaɗai ,zan shiga kasuwa in siyo maki ƴar madaidaiciya daidai yatsarki kamar gram 8 nasan bazai wuce 300k ba ,sauran dubu ɗari bakwai ɗin mu cigaba da shagali dashi ,na lura kwanannan zan siya mota ,wannan kuɗi haka gwara mu fara ajiye kadara ,muyi mu yagi rabonmu"

*****
Labarin wagga abun arziƙi har ya kaima uwata ta biyu ,masu karatu kundai san wacece ? To Hajiya Lady police ,kuma ta ƙara mana ƙwarin gwuiwa sosai kan mu yagi rabonmu


7dayz later (Bayan kwanaki bakwai)
Ranar muna gidan Hajiya ladi ,saiga kira a wayar mamana ,kamar arziki aka fara gaisuwa can kuma sai ya zarce da tsiya aka shiga musayar yawu faɗa faca²

Hajiya ladi miƙa hannu tana shafa kafaɗar ummana "haba calm down baby girl ,keda wacece,wata er tashan ke damunmu ?"

Miƙa mata wayar tayi ta kanga a kunne itakuma tayi baya tana maida numfashi ,nidai kin ganni saidai in kalli waccan da wannan in cigaba da shafa Samsung galaxy ɗina ,don a yanzu ita ake yayi .

"Au uwar Mahmud kike? Wani bola kenan ? Ni ɗiyata ma bata sanshiba kece shashasha kika kasa baiwa ɗanki tarbiyya ki ka bar turawa sukamasa tarbiyyan soyayya ,to bari kiji hurrrr ki raba ɗanki da yarinyana in ba haka ba dake dashi zan muku mummunan tijara "

Ta ɗaya ɓangaren ne aka cigaba da hurgo zafafan maganganu
"Kar ki manta ban fara magana dake ba saida nasan ubanki ba kowa bane face Sarkin Dogarai masu yiwa sarki gadi ....ban samu numberki ba saida nasan ke ɗin ba kowa bace face matar wani hussusukakken talaka ,wai makama ,kuma shine uban yarinyar da ta damfari yarona da sunan soyayya ta kwashe muna kuɗi ...to kinga cikin ruwan sanyi zansa a danƙe mun ku ayi mun maganinku" duk zatonta still da Hajiya Binta take fada batasan ladice ta karɓi wayarba

Tsaki Hajiya ladi taja "Tom ina jiranki ,Allah yasa kar ƙilu yaja bau garin neman kuɗi labari yasha banban da mijinki ....shashasha" kafin ta kuma magana tayi maza ta kashe wayar ,.
Da sauri ta daɗa kira amma anƙi ɗagawa

Hajiya Adama ƙawar maman su Mahmud ɗin fushi tayi ta hau zage²

"Wainnan ƴan iskan matane ,kowa yinada labarinsu, amma naji labarin mijinta dukan tsiya yike mata gashi yina son sarautarsa don haka shirya mu tafi in rakaki wani waje "

*****
Ƙarfe uku na yamma sai ga kiran jakadiyar mai babban ɗaki ta wayar Hajiya ladi police ,wai ga mata nan sun kawo ƙarar Hajiya Binta da ɗiyarta fadan mai martaba ,har ma an aika a kirawo mijinta wato makaman gari .

Luffff Hajiya Binta tayi akan sofa ɗin ɗakin ranta in yayi dubu ya ɓaci ,wai wannan matar wani irin rashin mutunci take taƙama dashine da zatakai ƙararta inda ake ganin mutuncinta ?

Shiru itama Hajiya ladi tayi,cikin dogon tunani ,nikuma na tasasu gaba da ihu ina roƙon su ceceni kar Sarkin Dogarai yasa a kamoni a zaneni da wannan bulalan nasu na rashin imani.

Ba wanda yabi ta kaina duk sun ɗauke wuta cikin ɓacin rai da dogon nazari , ƙwafa Hajiya ladi tayi taje gaban telephone ɗin dake ajiye a gefen garun falonta ,ta daddana numbobi ta manna kan tarho ɗin a kunnenta ,daidai nan wayarta ya shiga tsukku Lamban Alhaji babba ya shiga karakaina akan screen ɗin..... A sarari ta furta "Alhaji babba !!!" Sai kawai ta furzar da wani irin huci a bakinta ,ta saki kan tarho ɗin ya shiga lilo a wajen da yike sagale ,ta haye sama da sauri ,ta faɗa bedroom ɗin ta ,tana haki take amsa wayar ,sai da ta gama sannan tayi cilli da wayar akan bed ɗin ta ta koma ta rafka tagumi ,tana ƴan tunane tunane

"Mtseww wai nawa yaron kaf ya kashe ma yarinyar nan tun daga haɗiwarsu zuwa yau da zasu nema ɗaga mana hankali wanda baza'a iya biyan sa ba ?! Amma wallahi tunda basu kwantar dakaiba ta ƙofar matsiyata suka biyo to bazamu biyaba ,kuma mu zuba " ɗan murmushin mugunta ta saki ,kuma sai Can kuma sai ta zabura ta buɗe kwabanta ta zaɓo wata tsadadden leshi fari kwatakwal mai ɗan nauyi an masa ɗinkin bubu ,ta maza ta saka kayan ta gingima ɗauri kamar jirgi ya tokari yamma ,ta kawo Tularuka masu ƙamshin gaske dasu sinadaran bita zai zai ta shashafa,sannan ta zura takalmi half cover kalar mayafinta .

A gurguje ta fito hannunta riƙe da key ɗin motarta ,waya da wani faskeken tabarau

Tundaga bakin ƙofa take kiran "Ina sojoji na??"

Wasu murɗaɗɗun maza ne maras Imani ,masu jajayen ido da baƙaƙen laɓɓa suka yo gabanta da sauri cikin baƙaƙen suit ,suna zuwa gabanta suka ƙame suka sara mata kamar ita ɗin wata komanda ce .

Shaƙar iska tayi a hankali ta firzar "Munada fita yanzu yanzu nan "

"Yes ma" ƴan sandan da take kiransu da sojojin ta suka haɗe baki wajen amsa mata

Kallonsu ɗaya bayan ɗaya tayi kafin ta wulla ma ɗaya a cikinsu makullin motarta

"Kai nikeso ka kaini yau "
Da sauri ya cafe ,itakuma tayi gaba yabi bayanta da sauri

Ɗaura jiniya sukayi a mota suka fice a motocin su duk inda suka wuce a motocin su raɓewa masu abun hawa suke suna basu waje saboda yanda suke gudu akan kwaltan ko'ina ya karaɗe da jiniya wui wui wui ,ka rantse da Allah wani babban ɗan siyasa ko wani mai faɗa a ji ne zai wuce.

©Alheri Writers Asso.
Oum Aphnan✍️
09065990265
[6/3, 00:31] 😘😘😘: *Don Allah in kinga Littafin nan ba na kyauta bane ,ki kauda idonki mu yaƙi ɓarayi ,ki biyo ki siya naki ,don Samun karatunki cikin salama ,ba haƙƙin wata ba... ngd*

25&26
Da taƙamarta da gadaransu na ƴan duniyan mata suka shiga cikin fadan kuma Tundaga ƙofar fada suke bin ƙananun dogaran da dubu ɗai ɗai ,aiko take aka shiga bunsu ɓuuuu ana zuba masu kirari ,duk sun amshe jakkunan Hannunsu ,basu shiga cikin gidaba suka yada zango a office ɗin Dakachi ,suka sa a kira masu Sarkin gida
Da rawar jiki Sarkin gida yazo inda suke ya zobe yina kwasan gaisuwa ,saida Hajiya ladi ta gama cika wuya sannan ta soma tambayarsa abinda ke faruwa a fada
"Wata Hajiya ce tazo ,matar comishina ne na ilimi wai ta kawo ƙarar Hajjaju Binta akan zargin ɓatawa ɗanta tarbiyya ,ta sa yaronta yina sato mata kuɗaɗe yina kai mata ,yanzu gashi ya tattare mata, gwala-gwalai masu tsada yayi ma ƴar Hajiya Bintan barde(birthday) to Ala ayyi Halin dai suna ciki suna jiran ,mai martaba ne ya fito sukai kokensu ,wai a raba mata ɗanta da ƴarki"

Jan iska tayi ta zubar sannan ta miƙe ta daki tebur ɗin office ɗin da ƙarfi wanda yasa dakaci dake gefe yina zuƙar sigarinsa jifa da sigarin ya miƙe a tsorace ,har yina ƙona leɓe da wutan sigarin

Ƙanƙance ido tayi "Majidaɗi? " Ta kira sunansa ,da sauri Sarkin gida yace "Na'am"

"Banson jin maganarnan kuma badai burinta a raba yaronta da ƴarmu bane ? To magana ta mutu anan imu imu zanje inja mata warning a cikin gida .....saidai fa ku sani sam ba wanda yasan zancen nan a mazan fada sai ku kaɗai wallahi maganar na fita zansa sojojina su banƙare mun ku su zaneku ,yanda sai kun wata kuna jinya " tana kai aya ta ciccilla masu rafan dubu ɗari ɗari kowa ɗaya

Jikinsu na rawa suka shiga zabga mata kirari "Matar ɗan sanda ƴar sandace ,Allah ya ƙara girma da basira ,lafiya da jajircewa ,mun gode Allah ya I da nufi"

Ko bi ta kansu batayi ba ta danna kai cikin gidan fadan ,barorine mata birjik cikin dark blue ɗin uniform sai shawagi suke tsakanin ɗakuna ,kicin zuwa bayan gidan ,sai masu hutawa ƙarƙashin bishiyoyi

Tunda suka shigo duk kuyangan da zasu taɓa ta gabanta sai ta zube ta kwashi gaisuwa amma ko kallo Basu isansu haka zasu tashi da satattan gwuiwa su wuce

Sassan mai babbar ɗaki suka nufa ,gefe da gefen ƙofan kuyangine mata biyu zaune akan fararen kujerun roba suna ƴan hiransu ,suna ganin sun nufo ƙofan sukayi zumbur suka miƙe suka ɗan sunkuyar da kansu alaman girmamawa ,danna kai suke yunƙurin yi da sauri Salamatu mai baki kenan a kaf cikin kuyangin gidan

"Ranku shi daɗe mai babbar ɗaki tana ganawa da manyan baƙi na musamman don haka bazata samu zarafin ganinku ba ,saidai a nemo maku sarkin gida ku shigar da koken ku a baku lokacin dawowa "

Wani ƙasƙantaccen kallo tabita dashi ,a take ta ɗaga Tafkeken hannunta ta watsa mata yatsun ta biyar akan baƙar fuskarta ,ji kake fauuuuuuuh!

Wani ƙara ta saki ta kife a wajen dafe da kunci
Ɗaga murya Hajiya ladi tayi "Ina sojojina ?"

A ƙa'idar fada maza basa shiga sassan mata amma dukda haka saida zaratan dakarun Hajiya ladi suka tsaitsaya a bakin ƙofa suna jiyo muryarta suka amsa da "Yes ma!"
Fincikarta tayi kamar tsumma ta cilla masu

"Ku mata bulala biyar jan kunne na tuntuɓen halshe da tayi "

Aikuwa cafe ta sukayi wannan ya wulla ma wannan suka shiga tsatsatsauleta ,tuni kuyangin duk sun gudu kowacce taje ta manne a inda baza'a hangota ba suna kallon dukan da ake shugarwa Salamatu da bulalen da ake zanan ɓarayi dashi a police station ,duk saida suka gullar mata da ƙafa da kulki sannan suka ƙyaleta

Sukam kai tsaye suka shige ɗakin ba tareda shamaki ba ,ɗakine da ya amsa sunanshi ya ƙawatu da manyan dardumai da luntsuma luntsuman kujerun sarauta jajaye da adon zaiba ,ko'ina ya ɗauki raɓan AC har tiles ɗin ɗakin da aka rufe kusan duk ɗakin da wani irin lallausan jar carpet da kana saka ƙafarka yike nitsewa ,

Daga can gefen falon wasu shinfuɗun carpet ɗin ne hawa kan hawa an masu adon timtim ,nan Gimbiya take a kishingiɗe ,kuyangi na mata fifita da wasu faska ²n mafitai masu jikin gashin ɗawisu an masu fentin blue ,ja da kore

Gabanta wasu hamshaƙan matane da gani kuɗi da boko ya gama ratsasu ,amma dukkansu su biyun sun zauna luf kamar ruwa ya cinyesu Albarkacin shigowa fada da sukayi duk jin kansu ya sauke .

Sallama Hajiya ladi ta rangaɗa
"To dai ga baƙin da ake wa zaman makoki Allah yayi masu zuwa....(a ƙaskance ta watsa ganinta kansu nan take ta ƙyaro fuskar matar da take tabbata zaton itace uwar Mahmud ɗin) nan kuwa ta hau masifa

"AU Shema'u Tukur dama kece uwar Mahmud? Ah lallai dole muga jagwalgwalo ,To arzikin ba'a gada ba ,gani kike in ɗanki ya kashewa budurwa miliyon guda ,ƙarar wa mijinki arziƙinsa zaiyi ko ba haka ba ? To kasheji daga yau na jawa ƴata kunne kuma zaki gani ƴata bazata ƙara kula ɗanki ba ke ma in kin isa ki hana ɗanki tarayya da ÿata ,amma kuma in hakan ya cigaba da faruwa dukan haddi zansa sojojina suyima ɗanki bazan dubi babanshi komishina bane ko minista horasa zanyi a ɗa mara tarbiyya ,jikan Tukur mai facin keke!!"

Cak ta miƙe cikin fitina
"Ni kike zagi? Ubana da shine rayuwata shi ya bani ilimi ya kaini makaranta da kuɗin facin keken shi kike zagi kika ƙasƙantani a gaban wanda basu san asali da tushe na ba?"

"Ahhh dakata Shema tun muna makaranta kowa yasan ke ÿar tijara ce ,akan Naira goma zaki iya dambe a tsakiyar titi ,namiji zai siya maki awaran hamsin ya ƙwaƙule ki tas a bayan ajujuwa ...Tarbiyyan da kika bawa ɗanki kenan? Wato yazo ya iskanta mun yarinya? Wallahi baki isa ba ,yoooo zancen usuli ƙaryane baban naki ba facin keken yike yi ba???"

Cacan bakine ya hargitse ,da ƙyar su jakadiya da manyan dattawan mata na fadan suka shawo kan Al'amarin akayi masu sulhu aka raba faɗan akan kowa ta jawa ɗanta kunne


*****
Hajiya Binta ta tsure ainun a hanya ne ta kalli Hajiya ladi
"Aminiya na saba da kashaman arziki yaron nan yina kashe ma yarinyar nan kuɗi.."

"Mtsewww farin jini a goshin ɗiyata yike ni na faɗa maki wanda ya fishi ne zai zo"

Daga wannan ranar aka rufe shafin Mahmud ,na shato wani sabuwar rayuwar tawa


*****
Ya labarin Sadik sarki fa???
Tun ranar da ya bar gidan ladi police rayuwarsa yaƙi tsayuwa waje ɗaya ,tunanin sa ta wani hanya zai ƙuntata rayuwar Balkisu ,bayan rantsuwa da cin layan tarwatsa mata rayuwa da yayi ? A gefe ɗaya idan ya tuna da innocent face ɗin ta da kukanta sai yaji kamar ya fita a rayuwarta saidai kuma in ya tuna da marukan da yasha wanda tunda yike a rayuwa ba mahaluƙin da ya taɓa marinsa,yina tuna abun sai yaji wani irin muguwar tsanarta ya maye gurbin wannan ƴar tausayin nata da yike ji


A gefe guda kuma duk wani faɗi tashin da mai babbar ɗaki ta dingi yi na ganin an samu an daidai ta case ɗin Sarki da NDA ya koma makarantar sa abun fa bai yiwu ba ,ƙarshe dai aka nema masa admission a jami'ar kamfala ya fara karantar civil Law ,saidai watansa biyu da tafiya yaji ƙasar ta ginshesa ,hakan yasa shi gudowa ƙasar sa ta gado (9ja)

A wannan karon kansa mai martaba saida yaji haushin Sadik kuma yayi masa faɗa fata² ,sannan ya ɗaura da masa nasiha ,ta yanda zai gane cewa ilimi abu ne mafi muhimmanci dake ƙarawa mutum mutunci da girma a cikin jama'a

Nasihan iyayensa sosai ya shigesa ,saidai a take ya roƙi iyayensa Alfarma da su barshi yayi distance learning ,kuma ya kafa masu hujja dashi bazai iya karatu a wata ƙasa ya bar iyayensa ba ,kuma bazai iya karatu a federal universities da suke 9ja ba saboda yawan strike sannan a tsarinsa bayason karatu a private universities ,hmmm lamarin Sadik akwai tsauri a ciki amma haka iyayen suka yarda aka naima masa distance learning a Oxford


Yaji daɗi sosai yanzu kuma ya fara tunanin dawo da martabar Masarautar sa da ta tafi hutun wasu watanni sakamakon baya nan ,masifa ya dinga yiwa Fagachi da yaje gidan ya ga har ya fara zama bushy ga Royal flowers ɗin da akai decorating wajen duk sun yi yaushi

A take ya ware kuɗi masu kauri yasa a canja furnitung ɗin gidan ,aka canja fenti ko'ina ya ɗauki ƙyalli ,ranar saturdae yace a shaidawa abokansa zasu hau doki a zaga gari ayi shagali murnar dawowarsa, sai kuma ya shiga fadarsa a cigaba da gudanar da iko
Kunji wani aiki fa makaranta🤔

*****
Yau Jumu'a a gajiye na dawo daga makaranta ,tun daga school da ɓingilar siket ɗina na dawo da er hula na da na kafa akan kitson kalbana en yiri yiri gwanin sha'awa ,dama yanzu inada me keke dake kaini yana ɗauko Ni a hakan ma ƙorafi nike ana ɗaukan ƴan ajinmu a tsadaddun motocin gidanmu ina fama da me keke ,wannan dalilin yasa kullum sai an watse nike fitowa in shiga keken kamar mara gaskiya wai kar a ganni ina hawa keke....tun direban keke na masifa har ya sallamama ikon Allah don koda yayima ummana ƙorafi haushinsa takeji ko kuma ma ta bashi rashin gaskiya ,wai yina damuna da ƙorafi da guyaba kar zullumin masifarsa ya sa in rinka rama in bazai iya jirana ba to zata canja shi da wani ,dole ya haƙura ta ƙara masa kuɗin kaini akan na da .

A gajiye nike sharɓa ƙafana kundai san zauren mu da azaban duhu koda da rana tsaka ne ,cikin rashin sani naji na bangaji mutum ,ƙara na saki da sauri ya kamani ya riƙe ,a ƙirjinsa ,wani sassanyar ajiyar zuciya na saki don na sadaƙar sai na sha ƙasa

Ha'ahhhh me zai faru jira nike mutumin da ya riƙe Ni ya cikani amma sai naji yina lalube mun ƙirji yina shafo ƴan Nonon ƙirjina da basu wuci curin ƙaramar fura ba .

Mutsu mutsu na shiga yi ina faɗin "Ha'ahhhh wani ɗan iskan ne ? Haaahhh wai meye haka ne ?"

Gyaran murya baban mu yayi cikin shirin tafiyarsa masallacin Jumu'a yasha naɗin rawani dasu malun malun

Dallaro mu da tocila yayi
"Meke faruwa ne anan iyeee?"
Zaro ido nayi ganin babbar yaya ne ke ƙoƙarin yi mun wannan aika²n

Sosa ƙeya yayi cikin jin kunya ya cikani na wuce ina ƙunƙuni,Ni ba abun ina zagesa ba ,ya biyoni har ɗakin uwata yaci uwata ba mai rama mun

Shi kuwa baba masifa ya hau yin masa bayan ganin na wuce "Dama ace dodo zai ci dodo?...kana babban wansu ,jinina Ni duk na haifeku shine zaka lalata mun zuriya? To bari kaji mummunan nufinka irin wannan in ya ƙara faruwa Allah ya isa ban yafe ba ,ja'iri lalataccen mutum wuceee" ya daka masa tsawa suf sum sum ya wuce cikin jin kunya .

*******
*Fada*


©Alheri Writers Asso.
Oum Aphnan✍️
09065990265
[6/3, 00:31] 😘😘😘: *Don Allah in kinga Littafin nan ba na kyauta bane ,ki kauda idonki mu yaƙi ɓarayi ,ki biyo ki siya naki ,don Samun karatunki cikin salama ,ba haƙƙin wata ba... ngd*

27&28
Kamar yau kamar kullum Sadik sarki mutum ne mai son girma don haka kullum yina cikin malum malum da Alkyabbu,tum Bama Jumu'a tayi ,yau hakan ne ta kasance cikin manyan kaya ya fito na sky blue din shadda an ɗaura masa ɗinkin Alkyabba irinsa ,yasha rawanin farin

8 / 13