Bariki Gadona Book 1 Compelet Oum Aphnan

Author :  Hassana Bamalli Oum Aphanan Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 13

36K to 37.8K   out of 37.8K words

Zobban gwala-gwalai ,hujin kunnuwana ma ,haka na maƙala masu zinaren, na saka leg chain a ƙafar hagu ,da zogen ƙafa ,dukdai na zinare .

Ban ɗibi kaya da yawa ba ,don a jakar baya irin na student na zuba suturuna da zansa ,motana Kuma na jera firgitattun turarruka na da nike alfahari dasu da takalmana masu asalin tsada ,sannan na ɗauki hanya ,Shabiyun rana na shigo garin Kaduna ,saida nayi branch a wani Restaurant mai kyau naci abinci ,a lokacin kansa saida nayi new crush Amma haka nayi ignoring ɗinsa na saita akalar mota ta zuwa Zaria ,na isa gidan bayan azuhur ,don haka gaban gidan danƙam yike da maza dangi da ƴan cikin gida dama maƙofta ,ga rukunin yara matasa ,a can gefe ga na iyaye , Danno hancin motata nayi a 360 na fakata a tsakanin rukunan mutanen biyu ,kowa saida hankalinsa ya dawo kaina ganin watannan lafceciyar motar sai walƙiyar sabunta takeyi ,saida na nutsu na hura iska a bakina ,na shiryawa rashin mutunci sannan na buɗe Aljihun motata na fiddo chewing gum mai daɗin ƙamshi na jefa a baki ,na ɗauki glasses ɗina na sakaya idanuwana gudun sun burn,saida suka gaji da jiran mallaki motar kana na fito ,sam sun kasa ganeni saboda na ƙara kyau ,ga shigata ya saɓawa na Hausa Fulani ,da cat walking na ratsa ta cikin iyayena na tunkari ƙofar gidanmu ,ganin haka Baba muntari ya ce "Baiwar Allah wa kike nema ? Ko baƙin Ango ne?" Kallonsa nayi da tsummokaran rigansa kawai sai na tuno sanda yike cin zarafin mamana yina jifana da mugun baki "Ai dai kin haihu ,zaki gani a ƙwaryanki bazaki ɓatawa yayana suna ba ,amma da idon ganinki zakiga yanda ƴarki zata zama riƙaƙƙiyar ƴar duniya na bugawa a jarida wacce sai ta fiki ....... " Wani abu mai ɗaci ne yazo ya tokare mun a ƙirji ,jin maganganun sa nike a kwanyar kaina kamar yanzu abun ke faruwa ,idona a take ya kaɗa yayi ja

"Dalla matsa bani waje ,yanda kake da gado a gidan haka nima "

Sakin baki yayi sagaga ,tabbas idan ya manta kamannina ai bazai manta muryata ba ,da ƙarfi ya ƙwalla kiran sunana ya dafe ƙirji "Bilkisu!!!"

Jan tsaki nayi na sake maida kai zan shige aikuwa mutanen wajen sai ɓuuu suka yo kaina
"Wata bilkisun ,ina bilkisun?"

Zare gilashin fuskata nayi na tsaya ina kallon su ɗaiɗai ba alaman tarbiyya bare ta ido ,har baban nawa haushinsa nike don shine silar faɗa wata wannan halin

Ibro cikin fushi,ƙyashi ,Hassada da baƙin ciki ya ɗaura hannunsa a kaina zai fincikeni baya
"Zo ki wuce bazaki ɓata mun taroba ace ga ƴar kanta a cikin gidanmu ,a bikina ana nuna ki "

Kallon ido cikin ido nayi masa wanda saida ya sashi sauke ƙwarar idonsa cikin nawa

"Ci ka Ni Alade"

"Ke kinci ubanki baza'a saken ki ba ,bakin iyaye kawai...." Ai bai rufe baki ba yaji na dunƙule hannu na sakar masa Naushi a tsakanin hanci da baki ,a take kuwa hancinsa ya fashe ya kama jini

"Banza ɗan baƙin ciki harsadanka kai zai kashe ,nan gidan ubana ne inga ɗan kutumar uban da zai dakatar dani "
"Ni kika fasama hanci?"
"Na fasa"
"Ni kika fasa ma hanci? Wallahi yau sai na lahira yafiki jin dadi "
Tsaki naja

"Yayin da ma kenan ,kai bari kaji bakaiba wallahi innaso a sabauta mun kaf mutanen dake wajen nan waya kawai zan kira sai duk kunci ubanku" riƙe baki tsoffin sukayi yanda sukaji lokaci ɗaya na ɗage hannu na nuna su duka na danna masu zagi

"Sannan ibro Kasan inada cikinka ko? Sanadiyyar ka abunda ya faru dani ya faru ko? To don Allah indai makama da A'i ba zina sukayi suka haifeka ba ka dakatar dani ga shiga gidan nan ko kuma ka sa naƙasasshen hannunka a lafiyayyen fatar jikina....wallahi kaji nayi rantsuwa sai na sa an kulle mun kai an maka dukan bala'i ,wanda yatsun hannunka sai sun daina motsi ,kaga angonci saidai kaji labari"


Saida n'a ƙarashi tujarata sannan na danna kai cikin gidan ,a tsakar gida na nemi kujera ƴar tsuguno na zauna ,na bada rafan dubu ɗaya ma matar babanmu na sa ta mun kwaleman ɗakin mamana da yanzu yaran ta ƴan mata suke kwana a ciki

"Haba balkisu ai ko ba kuɗi zan maki kwalema keda ɗakin uwarki? Amma dai ki ɗan bar yaran nan su raɓe zuwa a gama Biki ko juya tunda ke ɗin ba mazauniya ba ne "

"Nace maki komawa zanyi? Makira annamimiya baki kamar na jaɓa?"

Tsuke baki tayi saboda taji labarin tijaran da tayiwa en waje maza ma basu ba

Saida na gama mulkina kana na koma ɗaki na kai kayana ,na tasa yara suka kwaso tsaraba ,wanda shi kansa angon saida nayi masa akwati guda na kayan fitar Biki ,kai kuɗi yayi ne ,haka kowa ke nan nan dani ana samun Albarka a nemana kinji fa kamar na kasa abun siye ba gindina na kasa a kasuwa ba

Anyi Biki cikin kwanciyar hankali taro kuma ta watse kowa da guntun gulmarsa ya wuce gida nikuwan Banda lokaci su don innna fara waya tun safe sai in wuce azuhur to hira mai tsayi baya tsakanina da mutanen gidan bare maganan dukan ruwan ciki ya shigo

Ana gama Biki maye ya fara uzzura mun da kira ,lallai fa In dawo kamar wani mijina ,ai ba shiri na fara haramar komawa ,en gida na tsakar gida sai gani na fito da jakar bayata zan koma kamar er makaranta zata koma boarding ,da Allah ya kiyaye hanya suka bini nayi ficewata ,amma a waje saida na zage ƙannena tassss saboda naga an karyanmun cikin mota ,nan nace sune suka tsaga da ƙusa suna mun baƙin ciki

Ban karaya ba ,ban koma gidan mamana ba saboda banso ta dakatar dani in ki mata biyayya in lalace ,haka ne koma Abj cikin farinciki


Haka ta kasance ma rayuwata babu wani canji saidai Biki ko sallah inzo gida ayi dani in Angama in juya ,zuwa yanzu ma nafi ƙarfin maye nace na gagari maye ,garashi nakeyi ina ganin manyan masu kuɗin kasa na mun rawar ƙafa in ya kira wayata bana ɗauka ,wannan abu ba ƙaramin ɓata ran maye yake ba gashi ya saba da gindina sam ya kasa sukuni ya kuma kasa jure rashina

Yauma ina zaune a wani shahararren hotels nida wani mawaƙine da yanzu tauraron sa ke haskawa a Africa duk in yayi waka sai an bashi award har Ingila da America sun bashi award ,ynz haka shi yake dating ɗina ,koma ince Ni fiance ɗinsa ce don yace aurena zaiyi

Maye saka sabuwar layin da bansanshi dashi ba yayi a waya ya kira Ni ,Saida tayi ringing sau uku tana yankewa ban dauka ba ,a lokacin na shagaltu a kallon baby na ,muna hiranmu na soyayya

Shi ya soma Ankara da ana kirana ,a sanyaye cikin muryarsa mai daɗi yace "Babe your phone "

Hannunsa na hada da nawa na ɗan murza a hankali idona na cikin ƙwaran idonsa ,na motsa laɓɓana dasuke ta faman sheƙin man laɓɓa

"Babe pick the call for me" dauka yayi ya kanga mun a kunne ,saida shiru ya biyo baya kafin ta ɗaya ɓangaren ace "Hello"

Buɗe idona nayi gaba-daya "MAYE???"

"Nace masoyiyata!"
"Bana sonka Ni ba masoyiyarka bace karka ƙara kirana ,banza bunsuru kawai maciyin durin mata ,banza a banza mai nacin soyayya"

"Dakata Bilkisu"
"A zaune nike uwar uban me zan maka ?"
"Aah fa bilkisu ,Aah fa zakiyi kuskure ba irin maye ake tanki in tanka dashi ba"

"Mtseww in bakada abjn fadi zan kashe wayata don ina tareda babyna kar ka katse mana muhawarar jindaɗi"

"Bilkisu ƴar gidan makaman Zaria ko? Shikenan ki tsumayeni zan kawo kayan auren ki ,nan da sati guda zaki zama amaryan Acisu Maye "

"Mtseww kasha giya kenan to zamu gani"

"Kina wasa dani Bilkisu ,wallahi saina aureki, ai ke ƙaramar ƴar Duniyace tunda kika kasa nutsuwa ki karanci waye maye? Meye dalilin da ake kirana da maye? ,Ina baki abun mamaki? To nasan inda kike ,kina Emaculate hotel tareda Wannnan famous mawaƙin ,da yake yaudaranki da sunan zai aureki bayan tsuliya yikeso ....Daga nan kuma shirya plan din zuwa Turai tare kuyi sati shida ,to zan baki saƙo ki faɗa masa ko da gayinan riƙe da wayarki yina jina ,ki faɗa masa zai mutu .......Nan da sati guda dole ya zaɓi ɗayan biyu inma ya mutu a sakashi a kabarinsa ,ko kuma ya mutu tauraronsa ya daina haske mururus,saidai kuma ya nemi wani sana'ar amma dole cikin biyu ayi ɗaya,ki basa zaɓi in ya zaɓa yanemeni ya shaida mun,idan kuma yaƙi nan da sati guda zan yanke masa wanda ta bugo a raina ,ke kuma a wannan satin ki shirya zama amarya ,don haka ki jiƙa mun kanki da magunguna Inaso ki haukatank da daɗin ki....."

"MAYE ?? Dama da gaske ne raɗe raɗin da ake maka kana da dodo?
MAYE dama da gaske ne kana kashe abokan adawanka???
MAYE no! No Bilkisu bazan taɓa aurenka ba karma ka kuskura ka aikata wannan kuskure kuma karka kashe mun saurayina don in ka kashe mun babe kaima zan kashe ka "

Muhsin da yaji ana taɗin za'a kashesa ,da yanda take wassafa halin muguntar mutumin a take jikinsa ya kama ɓari

"Waye my love ? Dawa kike waya ...na shiga ukuna"
Yin masa alama da hannu nayi irin ya dakata ɗin nan

"Acisu kana jina?"

Wani dariyar boss Maye ya saki ,a take bakinsa ya fara aman wuta ,idanuwarsa na sauya launi ,blue ,ja da kore

"Zan aure ki dole ne wannan Bilkisu ki shirya ,shi kuma na gefenki da yike tambaya ki faɗa masa ,yanzu ragamar rayuwarsa ya dawo hannuna daga yanzu Ni zan ina waina sa " kawai sai ya saki wani irin mugun tsawa mai tartsatsi ya ƙwalla kiran sunansa

"MUHSEEEEEN ?!!!"
Zumbur suka miƙa a tare ita kuma ta saki wayar a ƙasa ya tararratse saboda firgici ,suna waige ² ,cigaba da kiran sunansa a ka cigaba dayi cikin amsa kuwwa tamkar gashinan a gabansa ,dafe kai Muhsin yayi kawai ya sulale a wajen ya faɗi kansa na jujjuya masa jini na tsirtowa ta hanci ta baki

Ƙara ƙwalla masa kira maye yayi ,yina kallon inda suke tar a gabansa kamar yina wajen

Ai yina sake kiransa kawai sai ji kake ƙarararaaasssss ƙasusuwa wuyan Muhsin na ɓaɓɓallewa nan ƙafarsa ɗaya ta cirga jikinsa ya saki ya daina motsi

Hannuna ɗaura akai na fashe da ihu ,na ɗauka waya ina laluben Number Acisu in kira shi

"Acisu karka kashemun saurayi ,don in ka kashesa bazan aureka ba...."

"Ai kinja masa ya rigada ya mutu ,da kinbini ta lalama da ba haka ba ,A huta gajiya Amaryata ,ki tafi ki bar wajen zamuji da gawar,bazaki samu matsala da en sanda ba ,ke ataƙaice ba mai ganin komai"
Yina dasa aya ya kashe wayarsa

Kallon wayar nayi kawai na tsaga ihu ,na ƙawalla kiran sunan sa a jikin wayar "MAYE!!!!!!"



LITTAFI NA ƊAYA YA ƘARE,MU TARA A NA BIYU DA YARDAR ALLAH


Ki biya Littafinki don samun cigaban labarin ta wannan hanyoyin

7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb

Ko katin mtn ta
09065990265

Tsarin biyan sune
Regular 300₦
Vip 500₦
Special 1000₦

Ƴan Niger
Katin Artel Regular 500f
Vip 800f
Special 1200f


Oum Aphnan✍️

13 / 13