AUREN KATIN KASA BOOK 1 PDF HAUSA NOVELS BY PINKY DARLING

Author :  Pinky Darling Category :  Tknovels

Chapter   9 / 16

24K to 27K   out of 46.7K words

farin balarabe ya fito sannan ya sara mashi,hannu kawai amar ya daga mashi sannan balaraben ya bude mashi kofar seat din baya, anatse amar ya shiga ya zauna suka ja moton.

Koda ya zauna lumshe idonshi kawai yayi sbd tsayuwa daya danyi acikin ranan yasa yadan fara jin head ache kadan kadan, kida nadan tashi na slow music babu hayani ga kuma sanyi aircon ga kamshi turarenshi na réo pefume mai sanyin kamshi, ahankali ya soma bude idonshi wanda suka danyi jaa, eyeball din looking so sexy kamar wani wanda ya shawu, Magana ya fara ‘’M-5 whats the situation of the mall today? Kasan banason hayaniya sosai ko’’ ahankali wanda aka kira da M-5 yace, ‘’’there will be no issues sir, today’s not a day.’’……maida idonshi kawai yayi ya rufe, yanajin dama ya koma gida amma kuma yanason zuwa mall din sbd akwai kayayyakin da yakeso sbd private training din da zasu fara on Monday,.. shi mutunne mai son yima kanshi hidima da kanshi bai yarda da sako ba gwamma yayi abu da kanshi,…. Ahankali motor dinsu ya tsaya a acikin mall parking slot, saida ya dauka almost 10minutes kafin ya bude idonshi, gyaran murya yyi wanda yasa M5 bude mashi kofar shi da hanzari, face mask ya Makala a fuskan shi sannan ya fara tafiya bayan ya dakatar da escort dinshi, anatse yake tafi harya shiga cikin dubai mall din sannan ya fara waige waige don neman hammam dama da sukayi waya sunyi dashi cewa zasu hadu anan inda yake ce mashi zai kawo sabuwar babe dinshi shopping, saida ya kirashi sannan ya fadi mashi inda zasu hadu acikin wasu Aclass private restaurant acikin mall din. … inda hammam yake a last floor ne hakan ya sashi tsayawa nike shop yayi yan sayyayn shi anan ground floor, daman yana buqatan new set of shorts da activities clothings, yana nan zaune acikin shop din attendant mace tazo, ganin special customer dinsu yasa ta juya ta kira namiji acikin attendant don yayi attending dinshi… yana zaune kuwa

suka dinga fito da latest edition din abubuwan da yake buqata har wanda baizo da niyar sayaba saida ya dauka musamman kaya marasa nauyi wanda shi ne favorite dinshi all the time,tashin farko ya kashe millions of dollars anan wajen sannan ya karasa hermes ya tsaya ya karo perfumes dinshi sannan ya kira m-5 akan ya kwasa yasasu acikin motor… anatse ya fito lokacin ya maida mask dinshi sannan ya saka bakin glass wanda ya karama fuskarnan Tashi kwarjini, anatse yake tafiya gwanin burgewa kamar baya son taka kasa, ahankali ya shiga corner din da zai sadashi da lift domin hawa sama,… bum yaji abu ya bugi kirjinshi nan take wayan hannunshi ta fadi kasa allah yaso bata fashe ba, rufe idonshi yayi aranshi yana ayyana wani irin blind stupid fool ne ya bugeshi, gashi daman bashida hakuri,,, saida ta dago kanta daya bugu da abinda ta kasa tantance rock ne ko bango yasa ta dafe goshin ta tace ouchhh sannan ta fara murza wajen kwallan azaba na shirin zubo mata… nan take yaji kamar ya taba jin muryar da yaji tace ouch but tabbas koma wanene tunda har ya iya jin kamar ya gane to tabbas basu hadu ta dadi ba hakan yasa azafafen ya bude idonshi yana cije lips dinshi sannan ya fara magana ‘’who d hell do you think you are ? are you dumb? Are you blind?’’… gaban amra ne yayi wani mummunan faduwa kanta a sauke, ashe jikin mutun ne ya bugi goshin ta nan take kafarta ta fara rawar dari, ta kasa cewa komai sai hawaye, ganin yanda tayi banza dashi yasa ya harzuqa kamar zai bugeta anan take yaji muryar abokinshi asanyaye yace ‘’amarrrr!! Dudue’’ da sauri ya dago ya kalleshi, karasowa hammam yayi sannan ya dan dafa amar ya matso kusa da kunnenshi sannan yace “we’re in public don’t tell me what you have never done in your entire life shi kake kokarin yi, calm down mace ne fa wannan’’’tamke fuska amar yayi ko wayan shi daya fadi bai kalla ba ya taka har bakin lift ya tsaya ,

amra kuwa ido ya raina fata, allah ya ceceta daga hannun wannan rock din, anatse hammam ya tsugunna yakwashi ledodin ta da wayan amar sannan yace mata ‘’so sorry for his behaviour’’… kan amra dai akasa ta kasa dagowa sbd tsoro daga zuwa gari ko sati batayi ba ta hadu da bala’I shima ko bai wani damu ba ya wuce wajen abokinshi, saida suka shiga lift din hammam ya kalleshi yace ‘’ haba dude, ka dunga kokarin danne saurin fushin nan naka,’’ ko kallonshi amar baiyi ba ahaka har sukazo last floor, ganin yanda amar yyi banza dashi ya nuna masa cewa aqule yake kuma miskilancin ya matso… har seat din da hammam yayi masu reserving suka zauna inda hammam ya bar babe dinshi balarbiya mai shegen kyau tasa abaya sai gashinta dake lilo don batasa mayafin abayarba amma tayi matukar kyau, sosai…kallonsu Haifa tayi tana murmushi cikin harshen larabci tace ma hammam wannan ne “aminin namu” girgiza kai kawai yayi sanan ta kalli amar tace ‘’Assalam alayk khayf haluk afdil sadik?’’(how are you our friend)…kawar da kai kawai amar yayi sannan yace “hamdullah”

Tundaga wannan bai kara cewa komai ba har aka kawo masu ordern da hammam yayi wanda amar ko tabawa baiyi ba sai dan cocktail da aka aje yadanyi sipping sannan suka tashi suka fita, awajen parking space sukayi

parting ways inda kowa ya hau arniyan motor shi… direct gida amar ya wuce while hammam ya sauke Haifa a gidansu sannan ya taho gidan amar don yau basu samu damar yin Magana sosai ba.

Bangaren amra kuwa harta fito hankalinta atashe yake tama manta da requesting ride saidatazo waje sannan ta samu taxi din malls din, anan ta fada mashi inda zai kaita….

Bayan ta isa gida wanka kawai tayi don har yanxu tana period sannan ta chanza zuwa kayan bacci lokacin wajen karfe tara, anatse ta dunga sorting out kayayyakin da ta sayo, na fridge ta aje sannan tayi sorting kowanne wajen ma’ajiyarsa… standing broom, mop dasu bucket, kitchen ta nufa ta aje yar tukunya data sayo da frying pan dasu cups, plate, saida tayi sorting komai tukunna ta dawo parlor ta zauna,wayan ta ta jawo sannan ta fara kiran su salima ah Nigeria… sun dade suna waya sosai inda salima ta shaida mata yanxu suna dan sakewa sosai wanda har mamaki amra tayi wai harda daddy ah masu sake masu, sannan last weekend ma dasu aka je shakatawa…hmm kawai amra tace aranta tana tunanin duk wannan dalilin da yasa dady yake abubuwan… sallama kawai sukayi taso su gaisa da salim amma yana bacci.

Kallo kawai ta kunna ah tv inda take ganin al’adun kasar daban daban gwanin burgewa, anan barci ya kwasheta…

Washe gari ta kasance Monday, da wuri ta tashi ta shirya cikin wata abaya mai kyau, wadda tadan haskata sosai sai tayi kyau abinta, dan flat shoe dinta ta saka sannan ta kwashi duk wani document dinta da za ta buqata idan taje, tana sauka kasa ride dinta ya iso, cikin mintuna da bai wuce 20minutes ba suka iso, tunda ga bakin gate hankalinta ya tashi, wato wasu zabga zabgan motoci ne suke shiga cikin school din, tunda suka shiga ciki kuwa nunfashinta ya dauke, babu abinda take aranta sai addua,..wato makaranta ce babba mai dogayen buildings aciki harabar makarantar,ga blocks daban daban ko ina sheqin glass yake tsabar tsafta,ga bishiyoyi duk wani lungu da sako, abin saidai Masha Allah … parking drivern yayi sannan ta fito, parking space dinma abin kallo ne gwanin birgewa zabga zabgan motoci neatly anyi parking dinsu harda symbol din student a parking-space… daburcewa amra tayi sbd ta kasa gane inane ma hanyar reception, ahankali take tafiya harta tsaya wani bulding, ganin fitowa kawai akeyi ta ciki yasa ta kasa ganewa ko ta gaba ne nan kota baya haka yasa kawai ta tsaya abakin hanyar, mutane kuwa baqaqe da farare babu wanda yabi ta kanta, wani security ta gani da uniform hakan yasa ta matsa wajen shi ta tamabaye shi inda reception yake, nuna mata gabanta yayi yace ta shiga ciki, hakanan a tsorace ta kutsa kai cikin katon bulding din, kallon wurin tayi aranta tana cewa ‘’oh ni amrah ba yar uban kowa ba nice a makarantar yayan attajirai, a natse ta tako gaban kanta wajen wata baturiya wadda tasha suit ta yalce

gashinta, karasawa tayi har wajen ta sannan ta fara yi mata bayani, aikuwa baturiyar tana duba system taga sunanta nan take ta turata wani office, tafiya tadanyi mai dan tsayi kafin ta karasa office din, mutun biyu ne aciki duk maza, nanma saida tayi masu bayani sannan suka umarceta data zauna, tana nan zaune sukayi mata komai, suka bude mata portal, suka mata school identification card sannan sukayi mata registration sannan aka aikata wani office din again domin karbar school package, nanma dataje suman tsaye tayi, komai is organize, anan suka bata wani wrapped package wanda batasan mene bama, daganan suka hadata da wata mata domin yi mata school tour idan tana so, ganin sauki yazo mata har gida yasa tace zatayi nan kuwa suka fara zagawa ko’ina harda department dinsu na yan medicine, saida ta jigata tukunna suka gama,babu inda basu jeba, department daban daban, café, wajen activities, halls, kai ko’ina, gwanin burgewa.

note!! Pls ban iya larabci ba amma zanyi kokari Insha Allah…………

***Auren Katin Kasa ***

(Unexpectedly falling)

Story and written by:

QueenMarh

Free page….

Chapter 27-28

Amar kuwa tunda ya iso penthouse dinshi wanka kawai yayi ya shirya cikin wani lallausan shorts baki sai yar vest wadda ta kamashi sosai, daman shi ma’abocin kaya marasa nauyi ne lokacin har anyi sallan magrib, sallah kawai yayi sannan yaci dinner ya sauko parlorn kasa yana kallon world news, gefenshi kuma laptop dinshi ne yana dan ayyukan office wanda aka tura mashi ta email akan wasu yan ta’adda ta suka addabi wani sashe na kasar dukda kasar tasu akwai security mai tsauri amma wannan kungiyar babba ce wadda shekaru da dama suka dauka tun yana junior officer yake ganin manyan ogannin shi suna wahala akansu amma tun alokacin yayi alqawari komin daren dadewa saiya kawo karshen su, domin safarar kwayoyin da human trafficking da suke yi cikin sirrin abin kamar ba aikin bil adama ba amma shi yasan cewa mutane ne kamar kowa suke yi amma kasancewar su kwarru wajen kaucewa duk wani dalilin dazaisa agano su yasa suke kubuce masu kuma abin mamaki da’an yi sa’a za ah kamasu kuma shikenan sai komai ya ruguje.

Yana cikin research dinshi aka danna bell, anatse Pablo yazo ya wuceshi ya danna pins sannan ya bude kofar, hammam ne ya shugo, fuskarnan tarr da murmushi gwanin burgewa, amar najin sallamarsa ya gane shine sbd babu mai

zuwa kai tsaye har gaban smart door dinshi ba tare da m-5 yazo ya sanar dashi ba, tun kafin ya karaso amar ya fara Magana ‘’dude meya kawoka gidana, na dauka ay kwana zakayi da babe din taka zaka zo ka kula,… dariya kawai hammam yayi sannan ya zauna kusa da kujerar sa ‘’guy ya gajiyan hanya ya kabar Amma da dan iskan qanin ka dinnan ko yayan ka oho de”.. yayi saurin kawar da maganr da amar yayi mashi… ‘’amma is fine, useless bastard dinchan kuma saboda shi na juyo kawai, because babu amfani zama gida daya da mara hankali, mutumin da girma baisan ciwon kanshi ba, kuma babu mai tsaya mashi kamar Ammaa, but dukda haka babu abinda ya dameshi da al’amarin ta…kasan stupid dinnan mai yayi kuwa? Gyara zama hammam yayi sannan amar ya cigaba… ‘’saboda bashi da kunya mace ya kawo cikin gida fa, kuma abin haushi Amma na kallonshi ta kasa cewa komai, duka ne kawai banyi mashi ba dukda ya girmeni da but babu abinda zai hana na zane shi, I was pissed and I confront him sbd bai dace duk iskancin da zaiyi yayi agabanta ba, atleast sai yayi respecting dinta tunda gidan mijinta ne dukda shima gidan mahaifinshi ne, ni I wonder why amma is living with babanshi, that man is worse anan danshi ya gado halayyanshi’’ …nunfasawa yayi yana furzo wata zazzafan huci, fatar jikinshi har wani jaaa tayi sbd yanda abin ya bata mashi rai sosai’’.. kallonshi hammam yayi sannan yace ‘’ come on man, kadaina barin matsalar shi yana damunka, kawai ka kula da Amma ka fita sha’anin su”….hira suka danyi inda ya jefi jefi hammam ke tambayan shi maganar binciken da sukeyi ko ya samu any update… shiru kawai amar yayi baice komai ba, ganin haka yasa hammam cewa ‘’nikam akwai wani hint dana samu, dagowa amar yayi ya kalleshi kamar bazaiyi Magana ba yace ‘’uhmm’’ kallonshi hamman yakuma yi sannan yes ‘’na saka secret agent as workers na dessert safari anan na samu labari tanan zasu fitar da sabbin kwayoyi but ina bincikawa saboda naga suna da wayo kuma akwai mai special brain acikinsu but I just hope mu samu yin nasara akansu yanxu kusan shekara biyar fa Kenan ana abu daya’’…. Amar kam shuru yayi yana sauraron shi chan kuma yace ‘’forward all the information to my mail, I will check it, ganin hammam zai sake mashi Magana yasa ya mike yace ‘’I’m sleepy guy, kasan gobe zamuje private training hope you’re ready’’… tashi hammam yayi yana nufar kofar fita yace ‘’yes man good night saimun hadu achan gobe’’ sannan yasa kai ya fice..nunfashi amar ya sauke, harga Allah yana son hammam aboki ne na kwarai sun taso tare but this time around bayajin akan wannan case din zai iya fada ma kowa nashi binciken saboda kusan sau uku saiyazo dab da cimma manyan drug dealers dinnan sai kuma su kubuce masa kuma yasan yan Nigeria ne kasancewar shi shima dan Nigeria abin yana damunshi ace wai daga kasarshi mahaifar sa ake wannan ta’addancin, wanda ya kasa gane daga ina aka tsaya masu da har suke kaucewa, dukda yasan gaba daya headquater dinsu wani irin standard tight security ne da babu ma yanda za’ayi ace akwai dan leken asiri acikin su, abinda yafi damunshi shine yanda harda trafficking yara ake yi daga kasashe daban daban kuma azo awuce ta nan abin yana bashi mamaki dukda yankin da akeyi is not popular but yasan manya

manya ne acikin wannan harkar, amma sbd kwarewarsu yasa suke duk wani abunsu ta inda ba’a bawa mahimmanci.

Shin waye AMAR????

Muhammadu Taura, haifaffan dan kasar Nigeria ne cikin jihar adamawa yola shi kadaine wajen iyayenshi wanda mahaifiyarshi ta dade da rasuwa sbd cutar daji data kamata, almajiranci ya kawo shi garin Bauchi inda anan yayi karatun allo har ya girma kuma ya samu aiki gidan wani dattijan arziki uban gidan sa alhj kabiru, alhaji kabiru babban dan kasuwa ne wanda yake sayar da abubuwa da dama irinsu kaya na sawa har shago yake dashi babba a kasuwar bauchi mai ci, yanada yaya biyu mata wadda uwarsu ta rasu tun suna kananu wanda kanwarshi da mijinta ya rasu itama take zaune dasu kuma ta ke kula dasu, zama ne sukayi zaman mutunci tsakanin muhammadu da alh kabiru inda ubangidan sa ya bashi yarda da amana, zaman su yayi dadi har ya sanya alhaji kabiru dora Muhammad akan kasuwanci domin shima ya samu nashi, cikin ikon allah shima Allah ya dagashi tun yana saurayinsa har yazo yafi alhaji kabiru wanda yanxu tsufa yazo mashi, lokaci daya alhaji kabiru yayi rashin lapiya kamar bazai tashi ba hakan yasa ya damka amanar iyalanshi hannun muhammadu kuma ya bashi auren yarshi ta farko, sanin muhammadu yaran kirki ne yasa ya damqa mashi wannan amanar, bayan yan kwanaki akayi auren muhammadu da amaryarsa amina, watansu daya da aure rai yayi halinsa, alhaji kabiru ya rasu… bayan sadakar arba’in muhammadu ya dauka matarshi da kanwarta domin zuwa ganin danginsa, zuwansa Kenan ya tarar da mahaifinshi akwance wanda yayi mamaki sosai sbd yana zuwa ganinshi sosai amma wannan karan abin ya bashi mamaki sosai, basu jima sosai ah adamawa ba allah yayima mahaifinshi rasuwa, muhammadu yaji mutuwar babanshi sosai, ganin babu amfanin zamanshi ah adamawa yasa ya tattara ya koma Bauchi da matarshi amina da kanwarta,…rayuwa sukayi cikin aminci inda amina allah ya bata ciki ta haifi danta kyakyawa suna kiranshi da yunus wanda yaci sunan mahaifin muhammadu wato yunus taura bayan wasu yan shekaru Allah ya kara hore masu ‘da namiji shima kamar ubansa, inda yaci sunan sa kabir wato mahaifin amina… yaran sun taso cikin kulawar iyayensu inda muhammadu yayi alkawarin yayanshi ilimi zasuyi sbd bayason wani jininshi kuma ya dauko sahun daya dauka na alma’jiranci, girmansu yazo ta tangarda saboda amina ta daura kaunar duniya akan kabiru sabd sunan mahaifinta da yake dashi, ta sangartashi sosai wanda ya fara lalata rayuwar sa tun kankantarshi, muhammdu yasha wahala da ita akan abinda take amma ina, har ya hakura ya zuba mata ido, after 15 years kowannensu ya zama saurayi inda yunus taura ya dage da nemen ilimi har ya zama abin kwatance shikuma kabir tun bayan ya gama secondary school ya shiga kasuwanci daga nan ya fada siyasa, kwanshi tashi abin ba wuya, allah duk ya daukaka su inda kabiru yayi aurensa inda ya auri habiba matar arziki, habiba macece mai son mutane, ga hakuri..farkon aurensu kabiru ya nuna

mata soyayya sosai harta haifi danta wanda suna kiranshi da Aman daga lokacin da kabiru ya fara siyasa kuwa komai ya jagule, inda kabiru babu abinda baya yi, neman mata ne, bun bokaye wajen neman buqatunshi, idan kuwa akace ya kawo rai toh fah kabiru ya cire imanin shi babu tsoron allah haka yake yi, bayan yaci zabe har wata kungiya ya kafa wadda babu wanda yasan da ita inbanda shi da wasu makusantar aminan sa kuma babu wanda yasan menene ma’anar kafa kungiyar da kuma abinda take gudanarwa, asannu ahankali siyasar ta daina karbuwa awajen kabiru amma dukda haka arxikin shi gaba yakeyi, ganin tambayoyi da iyayenshi da wan shi yayi yawa akan cewa kodai sata yayi ma gomnati yasa ya tattara yabar musu Bauchi ya koma

9 / 16