Author : Pinky Darling Category : Tknovels
dinshi tayi bayan ya chanza outfit dinshi zuwa na asibiti anatse ta taimaka mashi ya shiga cikin body scanning machine din, saida ta tabbatar ta duba lafiyarshi tukunna tayi mashi sallama, zata wuce Kenan yace ‘’ right now at this moment I want to be the only man in your life that will love and take care of u’’ ita abima har mamaki yake bata shiko wannan daga haduwa da ita bai santa ba bata sanshi ba kallonshi kawai tayi sai tayi murmushi ta fita. Koda badaru ya koma gida hankalinshi sam baya jikinshi tunanin shuwaira kawai yake yi ta tafi da imanin shi yanda take magana da yanda take al’amuranta gaba daya ya tafi dashi, haka dai ya lallaba kullum saiyaje asibitin nan, da farko shuwaira bata amince mashi ba daga baya kuma ta fara tausaya mashi harta fara sonshi. Ganin irin soyayyar dake girma tsakanin shuwaira da badaru yasa iyayenta wanda suke riketa suka zauna da badaru domin yayi masu bayanin asalinshi,koda yayi masu bayanin asalinsa Sai uncle ya aminta dashi kuma yayi alqawarin aura mashi shuwaira tunda itama ta nuna tanaso, dukda anty dinta matar uncle bata soba,bayan Yan watanni uncle ya aura ma badaru shuwaira amma da sharadin bazai koma gida ba zai zauna da ita ah Morocco, nan take badaru ya amince da sharadin su.
antyn ta bataso hakan ba sbd tana tsoron gujewa matsala don lokacin da akayi auren babu wanda yazo daga bangaren badaru. Badaru kuwa babu wanda ya fadamawa cewa yayi aure saida suka shafe shekara kunsan biyar alokacin ko batan wata shuwaira bata samu ba suna zaman lpy sosai da ita da badaru dukda maganar danginsa yana damunta sosai, tunda sukayi aure saidai ya shirya ya je Nigeria yayi yan kwanakinsa ya dawo. Lokacin da badaru ya sanar da Mustapha auren da yayi a morocco ba karamin zafi Mustapha yaji ba ayanda ya dauki dan uwan nasa har yayi aure amma bai fada ma kowa ba aciki kuwa harda mahaifiyarshi larai wadda suke zaune anan katsina da ita da binta sai kaninsu badaru aliyu haidar.
Bayan komawar badaru da wata daya yaji duk zaman morocco ya chanza masa yaji baya qaunar zama ah garin haka yasa ya samu shuwaira da batun komawa Nigeria, duk da shuwaira tana shaáwar ganin dangin badaru amma hakan bai sata jin babu dadi ba zatabar uncle dinta, bayan yan kwanaki badaru ya lallabata suka shirya sukayima su uncle sallama sannan suka taho Nigeria. Dirar su Kenan ah aminu kano international airport kano badaru ya dauki waya don ya kira dan uwansa, nan ya sanar dashi sun iso, minti kadan saiga Mustapha, Mustapha yaji dadi ganin badaru da iyalinshi, direct gidan Mustapha suka wuce inda anan suka huta sannan sukaci abinci aka kaisu dakin da zasu zauna, shuwaira dai taji dadin tarbar da akayi masu amma duk bata cikin natsuwar ta domin tunda suka iso ta fara jin fargaba hankalinta duk ba ajikin ta yake ba amma dai haka ta daure bata nuna ba, bayan yan kwanaki suka shirya harda iyalan Mustapha wato haj kareema da yayanta uku, wahab, Ibrahim da Muhammad.
Koda suka isa katsina ba karamin mamaki Mustapha yayi ba ganin yanda larai batayi ma badaru fadaba akan auren da yayi, abunda baisani ba ashe ya riga da ya fadi ma mahaifiyarshi komai agame da batun aurenshi kuma tasaka mashi albarka sannan ta umarceshi da ya dungo boye duk wani abun alkairinsa da zai faru dashi, bai dauki zancen baba larai da komai ba shiyasa bai nuna damuwa ba kuma shiyasa bai fadama kowa ba ciki kuwa harda dan uwansa Mustapha.
Cigaban labari…….
Sallan asuba da aketa kirane ya farkar da amra wadda ke kwance a kasa miqewa tayi sannan ta tattare kayan shimfidar datayi ta ninke komai sannan ta wuce toilet koda ta fito kwance ta tarar da salima sai salim agefenta, ahankali ta tako ta fara tashin salim…,’’salim salim tashi lokacin sallah yayi”.,..tashi yayi ya zauna sannan ya fuskance ta, yace ‘’ adda amra kin tashi ashe good morning bari na tashi salima’’ dakatar dashi amra tayi sannan tace ‘’ kyaleta zan tashe ta, ka wuce toilet kayi alwala saikazo muyi sallah ko”,
mikewa yayi sannan ya bude kofar toilet, saidata jirashi ya fito tukunna ta shimfida masu sallaya sannan suka tada kabbara, koda suka idar addua sosai sukayi dashi da ita, kallon salima yayi wadda ke baje tana barci sannan yace adda maisa salima bazatayi salla bane ita,? Kallonshi amra tayi sannan tace
‘’salim I will explain to you why salima is not praying but please not now saika girma for now idan nayi maka bayani bazaka gane me nake nufi ba but idan har kaga nida salima bamuyi sallah ba we have our own reason kuma addini yasan da haka kaji ko’’ nodding kanshi yayi sannan yace adda let be get back to sleep,’’ tashi yayi ya kwanta gefen salima itakuwa amra tattare kayan sallan tayi sannan ta wuce wardrop din su ta aje, doguwar rigace ta barci har kasa ajikinta sai hula, fitowa tayi direct daga dakinsu fitilun ko’ina a kashe yake ahankali ta karasa wajen switch din wutan ta fara kunnawa saidata tabbatar ta kunna wanda zata buqata domin gyare gyaren da zatayi sannan ta wuce cikin kitchen, kodata shiga kitchen din yana nan yanda ta bari fess fess,karasawa har cikin kichen din tayi sannan ta wuce store ta fara dibo abinda zata buqata wajen yin breakfast, saidata fara fere irish da doya sannan ta dora shi akan gas, fita tayi backyard ganin gari har ya fara haske yasa ta kwaso tsintsiya da mopper, sannan ta wuce cikin parlor, duk girman parlor nan haka ta share shi tsaf duk da babu wani datti saidata tabbatar ta gama sannan ta fara mopping din ko’ina.
Anaste ta kammala aikin ta sannan ta koma kitchen anan ta fara yan soye soye abubuwa data dafa sannan ta hada masu custard saboda tasan kananu yaran zasu buqata, sannan ta dafa ruwan tea. Wajen karfe 9 daidai suka fara sakko daya bayan daya, Khadija ce ta shugo kitchen jikinta sanye da kayan bacci riga da wanda kanta da ribbom kalar kayan jikinta ta daure yar jelar gashin nata, siririya ce batada haske sannan hancin ta yana nan anane kamar gutsirarren dankali, kodata shigo ko kallon amra batayi ba ta wuce wajen tabkeken fridge dinsu ganin haka yasa amra cewa good morning khadi, ko kallonta batayi ba ta bude fridge din ganin bataga abinda take nema ba yasata cewa, “ina avocado smoothie din danace ki dunga hada min duk safiya kina ajewa”??, kallonta amra tayi sannan tace, ‘’avocado dinne yakare shiyasa ban hada ba’’ ..tsaki kawai khady tayi sannan ta dauki bottle water ta wuce dining, ita kuwa amra qannenta ta zubama akula sannan ta aje agefe, mugs din shan tea ta kwasa sannan ta wuce dashi dining room, duk kowa ya hallara amma banda iyayensu mata, daga kan khady, Muhammad, amina, ishaq, jabir,jalal sai khamis da Khalil, halim ce kawai babu acikinsu sai kuma manyan yayyi wahab da Ibrahim wanda basa kasar ma kwata kwata.
Ka’idar gidance duk yaran kowa sai ya sauko anyi breakfast dashi gudun samun misunderstanding kuwa iyayensu basa saukowa saidai ko wacce ta dafa a kitchen din part dinta asama.
kowannan su yana zaune haka amra tazo daya bayan daya tayi serving dinsu, ishaq ne kawai ya bude baki yace mata ‘’thank you sis amra,’’ murmushi kawai tayi mashi sannan ta juya zata koma kitchen, tana gab da shiga kuwa tajiyo muryar halma tana sakkowa daga stair tana sanye da pink riga iya gwiwa,kallon amra tayi sannan tace ‘’ zaki tafi baki bani nawa breakfast dinba kosai na kira mummy?“juyowa amra tayi sannan ta fara zuba mata, ishaq kuwa tsaki kawai yayi, amina kam ko kallon inda take batayi ba,dukda itace akusa da halma .
Saidata sallamesu sannan ta wuce kitchen abunta aranta tana mamakin isa da suke nunawa, kamar basune suke wasa tare ba lokacin da iyayen su na raye lallai baka sanin mai sonka saika rasa gatanka aduniya, murmushi kawai amra tayi sannan ta wuce dakinsu,
Tana shiga ta tarar da su salim har sunyi wanka sun chanza kaya ita suke jira, aikuwa tana shugowa salim jikinshi har rawa yake wajen karban kulan data shugo dashi, waje ta samu ta zauna salima nayi mata sannu da aiki. Kallonta amra tayi sannan tace ‘’salima ku fara ci, ni yanxu agajiye nake zanje nayi wanka idan na fito sai inci nawa nima’’…kallonta salima tayi sannan tace adda zamu jira ki kiyi wankan’’, qwalalo ido salim yayi yace adda gaskia nikam bazan maki karya ba yunwa nake ji,’’ dariya suka fara mashi saida suka tsagaita salima tace “kai salim akwai dan banzan ci”, tura mashi kulan salima tayi sannan tace karba ka ci ka rage mana’’ amra kuwa toilet ta wuce ta watso ruwa sannan ta fito ta bude wardrob dinsu, doguwar riga ta dauko baka mai yan duwatsu ajikinta sannanta ta koma toilet anan ta chanza kayan sbd salim yana cikin dakin sannan ta dawo ta wuce wajen dressing mirror dinsu, dan roll on kawai ta goga sannan ta wuce wajen yan uwanta anan sukayi zaman su daga bisani kuma suka fuce gaba dayansu zuwa kitchen din, nan suka taya ta daura lunch harta kammala sannan suka jera a dining, daki suka koma lokacin ana kiran sallar azhar, sallah sukayi koda suka idar anan suka dinga jin fitar motoci da alamu ko wacce cikin matan ta kwashi yayanta sun fice abunsu, sukuwa su amra da kanneneta da basuda gata sai aka barsu da gadin gida, ganin zaman bashida ammfani yasa suka fito suka wuce compound din gidan anan ne amra ta tsunko masu guava suka wanke sukaci sannan su salim suka fara wasansu shida salima yana gudu tana binshi abaya ita kuwa amra kallonsu kawai take tana jin dadi aranta daga bisani kuma ta shiga tunanin rayuwar su, harga allah tana son kannenta sosai har cikin xuciyar ta kuma batajin zata iya nesa dazu, suna nan har aka kira sallar magrib sannan suka koma cikin gida, daki kawai suka wuce sukayi sallah, amra bata mayi tunanin dora girki ba saboda basuci na rana ba sannan kuma daman yau Sunday ayaune kuma baba rabi zata dawo mai’aikin gidan gaba daya, daman tana zuwa gida friday da daddare sannan ta kwana biyu sunday ta dawo da yammata cigaba da aikinta.
***Auren Katin Kasa ***
(Unexpectedly falling)
Story and written by:
QueenMarh
Free page….
Chapter9-10
Duk sanda mama rabi ta fi kuwa amra ce ke karbar duk wani aikinta harsai ta dawo sbd haj kareema ce ta shimfida wannan dokar akan cewa Yayan riqo bazasuyi zaman lalaci ba, ita kuwa amra ta gwammace tayi komai kannenta su zauna su huta kamar yanda sauran yaran gidan suma suke rayuwar su babu takura, shiyasa koda haj kareema ta kawo sabon rule dinnan ita kuwa amra dadin haka taji don kuwa ya taimaketa sosai, babu girkin da za ah nuna mata har matan gidan ma kuma bata sangarce ba itakeyin komai nasu a gidan, abu biyu ne kawai batayi musu, na farko bata zuwa part din kowa acikin su sannan kuma bata yi masu wanki kuma bata shiga part din mai gidan wato alhaji Mustapha, yaya awajen ubanta sannan kuma uba awajen su ayanxu ita da kannenta.
Suna nan zaune adaki ita da kanneneta suka fara jin saukan motocin gidan da alamu sun fara dawowa, har akayi sallan ishaï suna zaune ita da kannenta salima tana zanenta while salim kuwa books din shi ya dauko yana assignment,sallamar da akayi ne yasasu dagowa suna kallon kofar don ganin mai yin sallamar, mama rabi ce ta shugo da yar ledar kayanta ahannu fuskarta dauke da murmushi tace “salim na dawo”, da gudu kuwa ya tafi wajenta yana mama rabi allah yasa kin kawo min tsarabar raken danace maki,murmushi tayi mashi sannan suka karasa cikin dakin, kallonta amra tayi tare da salima sannan suka gaisheta, anan ta bawa kowa tsarabar shi ‘’kai salim ga rakenka, ke kuma salima dama goruba kikace min kina so toh ga naki’’ washe baki salima tayi sannan tace kaii mama rabi allah ya bar mana ke’’, …murmushi tayi sannan ta kalli amra
tace mutuniyar arziki matar manya ga farar kasar ki nan ke ko gajiya bakyayi duk sati idan zan tafi sai kin bani dari biyar na sayo maki saikace mai ciki ko gajiya bakyayi dashan wannan abar”…dariya amra tayi ta kalleta tace mama rabi ke bakisan kwanakin da nakeyi Ina tattala kudin break dina na school ba duk don na tara na baki ki sayo min farar kasar nan, aykuwa nagode yau naga har yafi na last week yawa, nagode sosai’’ karbar ledar amra tayi sannan ta bude ta dauka daya ta fara bantara tana wullawa abakinta, salima kuwa baki ya rufu sai faman gurzar goriba takeyi. Sallama mama rabi tayi masu sannan ta fice ta koma nata dakin dake opposite da nasu. Saida suka gama kusur kusur dinsu tukunna amra ta fita domin zubo masu abinci, anan ta tarar da ishaq, yana ganinta kuwa ya taho, kallonshi tayi sannan tace “bro ishaq yau baku wuni agida ba inata so ka koya min wani assignment da aka bamu a school kasan mun kusa gama exam din second term ni harna kosa wallahi na gama school dinnan wallahi wahalar damu suke yi sosai,’’ dariya ishaq yayi sannan yace sis idan kince kin gaji da school to ai kuwa daddy aurar dake zaiyi wallahi karma kiyi fatan ki gama school yanxu’’ turo baki tayi sannan tace ay kuwa babu auren da zanyi yanxu nida nake da burin zama babbar likita ay aure ba nawa bane’’
kallonta yayi sannan yace “nikam dan allah adama min oat mana dama mun dawo da yunwa naje sama don nayi wanka ina dawowa naga yarannan sun
cinye abinci da kikayi kinsan kowa baya resisting abincin ki sis” dariya tayi sannan ta shiga dama mashi oat din sannan ta bashi wucewa yayi yanace mata ‘’Thanks sis nagaji yanxu gobe idan za ah sauke mu a school zan koya maki’’ murmushi kawai tayi aranta tana mamakin mutuncin ishaq sam babu ruwanshi bashida halayyar sauran yaran gidan, juyawa tayi sannan ta fara zuba masu abinci ita da kannenta, daki ta koma saida sukaci abinci sukayi nak ita da kannen ta sannan suka kwanta sbd su tashi da wuri.
Washe gari kuwa sunso su dan Makara, shaf shaf suka shirya cikin uniform dinsu iri daya suka wuce parking space koda suka iso babu wanda ya sakko acikin yaran gida ga bus din nan anyi parking driver din har ya gaji da zama ya fara barci abinshi. Salim kuwa ganin haka ya fara matse hawaye babu abinda yake tunanin face dukan lattin da kusan kullum sai anyi mashi shida sisters dinsa sbd lattin da yaran gidan suke saka su gashi su yaran gidan makarantarsu ta masu kudi ce ba a dukkan latti sukuwa su salim makarantar su batakai tasu jabir ba karatu ake sosai shiyasa ake dukan latti. Ganin haka yasa amra ta fara lallashin sa ‘’ salim idan kana cikin fargaba ka dunga fadin “nnalillahi wa inna ilaihi rajiun” acikin ranka kaji ko, kayi hkuri ka daina kukan, share hawayen shi yayi sannan suka shiga chan kuryar bayan moton suna jiran fitowar su, saida suka bata wajen 30mins kafin dukkansu suka fito kowa da irin nashi kalar rashin mutuncin shugowa cikin motor ahaka dai aka lallaba aka fara tafiya,anan ishaq ya taimaka ma amra da assignment dinta sannan aka sauke su ishaq, tsabar rashin adalci da akeyi masu kuwa sai an fara sauke yayan gwal tukunna sai asauke su, alhalin makarantarsu itace akusa kafin tasu jabir. Driver na parking ah Royal international school kowannen su ya sauka tukunna ya juyo da motar domin komawa school din su amra adaidai Ar Rahman international school, makarantar tasu babu laifi sbd makaranta ce ta masu hali ba laifi amma ko kusa bazaka taba hada ta da royal international school ba fitowa sukayi adaidai gate kuwa wani malami yasha suite da katuwar bulala ahannun yana tare Yan latti, koda salim yaga haka sai hankalin shi ya qara tashi, karasa wa sukayi bayan amra ta rike hannun shi, yara ne kusan biyar atsaye da uniform dinsu blue and white riga da wando sai hijab wasu kuwa riga da skirt ne wasu kuwa doguwar rigace kamar amra itama doguwar riga akayi mata yanayin jikinta, bayan anzo kan su anan amra ta kalli malamin sannan tace mashi ‘’sir we are very sorry for coming late Wallahi ba laifinmu bane,its not our fault but please sir don’t beat my siblings you can beat me and punish me instead,,’’ yakai karshe idonta tap da kwalla, kallonta malamin yayi sannan yace they can go in but you will have to face the purnishment after break for now zona maki bulala tunda kin fanshi yan uwanki.. salima najin haka hankalinta ya tashi tace ‘’sir I will also take the punishment along with my sister’’, kallonta yayi sannan yace okay you can come with her to my office during break”..Wucewa salim da salima sukayi anan kuwa saida teacher nan yayi ma amra bulala biyar sannan ta wuce class koda ta shiga har first teacher ta fita sai second teacher ta shigo. Anatse ta zauna a class har aka gama classes sannan aka fita break kodata je office din displine master
umarni ya bata data wanken toilet din section din yan nursery, fita tayi sannan taje ta wanke, Allah sarki amra baiwar allah tana wankewa tana kwalla toilet din yayi budu budu sosai dama abinka da shaänin yara duk sun bata toilet seat da kashi sosai, tana wankewa tana kuka ahaka harta gama sannan ta wuce class lokacin har an gama break, a wunin ranar batada wata walwala gashi babu abinda tasaka acikin ta inbanda farar kasar da mama rabi ta sayo mata, har aka tashi suna nan zaune har lokacin islamiyya yayi dama school din tasu hade take da islamiyya saida biyar tayi sannan aka tashesu, fitowa sukayi suna jiran habu driver saida suka dau almost 30 minutes azaune bakin gate tukunna sai