AUREN KATIN KASA BOOK 1 PDF HAUSA NOVELS BY PINKY DARLING

Author :  Pinky Darling Category :  Tknovels

Chapter   15 / 16

42K to 45K   out of 46.7K words

kara da cewa ‘’are you deaf? Don’t you dare ignore me’’…cikin tashin hankali da fargaba yasa amra zubewa qasa kawai ,gwiwoyinta sun gaza daukanta, hankali atashe ta soma Magana ‘’dan allah kayi hkuri bazan kara ba sir’’ tunawa da yaran da tayi magana dashi yasa tayi sauri juya harshe zuwa turanci shikuwa mamaki yayi wannan mai Zubin baqaqen larabawan ya akayi ta iya hausa dukda ba wani kallon kirki yayi mata ba… bai kuma cewa komai ba kusan minti talatin,

gwiwoyinta duk sun sage sunyi tsami gashi shi baiyi Magana ba bai dago ba kuma baice ta tashi ba, kamarma bacci yake yanda ya lumshe idanunshi, ahankali ta soma dago kanta sai kuma ta sauke, tsinkayar muryashi tayi yana cewa ‘’you’re dismissed’’ da kyar ta iya tashi tace ‘’thank you sir’’.. sannan ta fuce harda saurinta, tana fitowa ta fara jero nunfashi kamar wadda tayi gudu,ahankali ta fara sauka kasa, kodata koma office dinsu hafiza na ganinta ta tambayeta ko taje kiran da ake mata tace eh taje, wunin ranar babu abinda tayi tana zaune har time din tafiya gida yayi.

Koda ta koma gida saida ta shafa man zafi sosai akafanta, nan ta tsaya jikin mirror tana karema kanta kallo, ta chanza sosai, tayi wani haske skin dinta luwai luwai, ko ina bulbul, shape din jikinta kam har tsoronsu takeji dan yanxu ko fita tayi sai an kalleta an kuma kallonta, komai zan zan…….ayanzu batada damuwa saita yan uwanta, sau daya take samun suyi waya a wata, abin yana damunta, anan ta fara tunanin ko wayar aka kwace masu, ganin batada mai bata amsa yasa kawai ta bar zancen ah ranta, itama kanta kwana biyu bata jin dadi, wani irin ciwon gefen ciki take jifa jifa gashi bana period bane amma haka take daurewa tunda zuwa yake time to time.

Bangaren su salima ashe kwace wayar daddy yayi wanda duk Khadija ce tayi sanadi saboda tasa salima tayi mata wanki ita kuma ranar batajin dadi bata samu tayi ba, ay ko daddy na dawowa ta kala mata sharri cewa tana waya da samari da daddare,ganin idan aka kwace wayan hannun salima zaisa taji zafin abin shine ta hada mata wannan bomb din, sukuwa sunyi kukan rashin yar uwarsu kamar me, gashi salim ciwonshi yana dawowa kadan kadan, kullum cikin ciwon kirji yake yana kukan zuciyar ci zata fita, itama salima ciwon ciki dai gaba yake karayi babu mai kawo masu agaji sai Allah, tun suna daure kuncin gidan har sun saba sun zama wasu shiru shiru, basa Magana, makaranta kuwa suna zuwa kuma mrs abida tana yi masu kokari sosai matar kirki. Haka babbar sallah tazo suna kallo yayan gwal suna sha’anin su, sukuwa ko mayafi ba’a saya masu ba, salima tayi kuka harta godema Allah.

Kwanaki sunata tafi yau watan ta biyu da fara housemanship ah (UAF Specialist Hospital), kamar yanda hafiza ta taba fada mata tayi kaffa kaffa da kowa haka kuwa ta dunga lallabawa babu ruwanta da kowa, ayyukanta takeyi hankali kwance, tun haduwar ta da general sau daya bata kuma sanya shi a idonta, kuma ba a nemeta ba daga headquarters hakan ba karamin dadi yake mata ba, babu abinda ke kaita wajen sojojin nan saidai idan sunzo monthly check up wanda sakeyi duk wata, hafiza kuwa duniya tayi mata dadi sbd an bata office din ogar team dinsu sbd zataje parental leave temporary, cikin aikin ogar tasu kuwa harda handling health checkup din generals da manyan sojojin headquater din, duk wata zataje har office dinsu domin diban jinin su sbd test don su basa zuwa hospital din, duk sanda wata ya zagayo kuwa har rawar kafa take wajen zuwa

office din general, duk wannan abun da take ogan kuwa ko ta kanta baya bi, haka zatazo fess fess abinta amma ko kallo baitaba hadashi da ita ba, akwai ranar datazo bayan ta gama abinda zatayi ta tsareshi da ido, jin idon mutun akanshi yasa ya dago yayi mata kallon farko, abinda bata sani ba arayuwar shi yaki jinin a zuba mashi ido, nan take ranshi abace ya danna landline ya kira m-5, koda ya shigo office din, amar baiyi wata wata ba yace ‘’get this lady out of my office, as from now on, get someone else to do her job nonsense’’ yakai karshe yana kawar da kanshi.. hafiza kuwa wadda hankalinta ya dawo jikinta lokacin da yake Magana azafafe yasa ta fara matsa kwalla, kamar ta surfa ihu haka takeji,..hanya m-5 ya nuna mata domin ta fice, har ta koma office matse kwalla take, ta kasa gane taqamaimai laifin me tayi mashi, amma dukda haka tayi ma kanta alqawarin kota halin qaqa saita sameshi, koda ta shigo office amra ta tarar azaune tana duba wasu files, koda amra tayi mata sannu da zuwa banza tayi da ita, ganin yau an tabo sis hafiza yasa itama bata kuma cewa komai ba ta cigaba da aikinta hankali kwance…

Next day

Yau ta kasance farkon weekend, koda amra ta tashi yau saita jita cikin wani lullubabben farin ciki saboda on Monday Haifa zata fara zuwa asibiti itama, daman kadaici yayi mata yawa don hafiza yanxu bata yawan kulata sosai sbd damuwar da take ciki, gyaran apartment dinta ta fara, saidata wanke toilets ta sanya kayan kamshi sannan ta gyara dakinta, ta sanya sabon bedsheets din data sayo kwanakin baya sannan ta kunna bakhoor acikin burner daman ita ma’abociyar kamshi ce, saida ta gama komai tukunna ta fara kiciniyar dafa ma kanta abinci don kwana biyu kudinta yayi qasa sosai gashi batason taba savings din da takeyi, gashi shima daddy ya rage turo mata kudi, anatse ta soma girkinta, jollof din taliya tayi wadda taji kayan kamshi da fresh fish, bayan ta kammala ta gyara kitchen din tsaf sannan ta koma sitting domin bama cikinta hakinshi, anatse take cin taliyar wadda tayi mata dadi sosai ita kanta data dafa, wayanta dake gefenta ne tayi ringing tana ganin sunan Haifa akan screen din tayi sauri dagawa, ‘’hello babe ya kike’’ Haifa tayi Magana cikin wayan, gaisawa sukayi sosai sannan suka fara hirar idon sun fara aiki tare ba karamin dadi amra taji ba wayan datayi da Haifa.

Amar’s apartment.

Yau kusan wata biyu Kenan tunda yazo apartment dinshi bai koma penthouse ba, hankali kwance yake rayuwa agidan, bashida wata damuwa,daman shi ma’abocin zama shi kadai ne baya son hayaniya kwata kwata, shiyasa baida abokanai sai hammam, French fries ne agabanshi, da burger sai corn dog, anatse yake dauka yana kaiwa bakinshi, ga kuma laptop din shi kan cinyar shi wanda yake daddanawa, hankalinshi yayi nisa sosai yana research, rubutu ne manya manya akan system din nashi ya kurama ido, wanda aka rubuta MKS EMPIRE, yakai kololuwa wajen tunani, yau kusan shekara biyu Kenan, idonshi nakan

wannan suna ya kasa gane komai babu clue, aqufule yayi wurgi da tsadadiyar macbook dinshi, idonshi yayi jaa sosai, ahankali bakinshi ya fara furta ‘’who are you, what is MKS why can’t i get a hint?’’..dafe kanshi yayi wanda yake jin kamar an daura mashi dutse, tsabar tururun bala’in dake cinshi yasashi fara karanto addua aranshi, babu wanda ta fado mashi rai sai Amma shi, yayi missing dinta sosai, harga Allah yana son ganinta, amma kuma gidan ne bazai iya zuwa ba, akwai tarihi da yawa kunshe agidan wanda yake fama mashi zafin rashin babanshi, ahankali zuciyar sa ta fara mashi sanyi, wayanshi ya dauka ya fara dialing AMMA NA.. kusan ringing biyu kafin ta daga da sallama abakinta,’’Assalam alaiku son, ya kake ya aiki kana lapiya nayi missing dinka sosai’’.. jin muryarta kadai ya sanyaya mashi zuciyar shi, yana masifar qaunar mahaifiyarshi, bashi da kamarta aduniya,shiyasa baya son bacin ranta ko kadan’..’’AMMA NA ina nan lapiya ya kuke?hope komai yana lpy nima nayi missing dinki sosai Amma, hope bakida damuwa?” ya kai karshe yana sauraron ta.. hira sukayi sosai dukda hiran akan maganar aure ne, tana fara wa kuwa yace ‘’Amma I’m very busy now, zamuyi Magana next time’’, ganin haka yasa ta gane bayason zancen ne, sallama kawai sukayi sannan ya kashe wayan gaba daya ma, anan zaune bacci ya daukeshi akan couch din bedroom.

Haifa’s

Akwance take kan makeken gadonta, kunnenta maqale da waya, murmushi takeyi sosai wanda ke nuna alamun tana jin dadin wayar, hammam wanda shima ya shagala da hirar tasu ta masoya yasa shi chanza tambayan ta maganar karatun, itako sai lokacin ta tuna bata fada mashi zasu fara internship ba, ‘’ohh babe kaga na so na manta ban fada maka ba, ay gobe Monday zan fara housemanship dina’’… sautin murmushin sa taji sannan yace ‘’ah ina zakiyi ne?’’…. ‘’ah UAF specialist hospital’’…mamaki ya gama cika hammam Magana chan yayi yace ‘’wait you mean the only uaf hospital that I know?” dariya tayi sannan tace ‘’yes daddy ne yayi min hanya sbd amra, ita already ta fara so ni kuma yanxu zan fara nima’’…. Murmushin yaqe yayi sannan yace ‘’well kice kin dawo kusa da babynki Kenan, ay nima ina headquarters ko kin manta boyfriend din naki army senior officer ne’’’jin tayi shuru yasashi cewa ‘’hello are you there?’’… gyaran murya tayi sannan tace, ‘’baka taba fada min ba sai yau, dukda idan na tambaye ka so many things about you Kaman wannan saikayi dodging maganan, anyway duk wannan baida amfani I’m happy cause I will get to see you everyday love’’..basu wani dade sosai ba sukayi sallama, jinjina lamarin hamman takeyi aranta, kwata kwata yaqi bari tasan duk wani abu daya shafesa ba kamar ita ba daya san komai game da ita, baima taba fada mata shi army officer bane kawai dai ta taba ganin hotonshi da kayansu kuma bata yi gigin tambayan shi ba sbd bata shiga abinda ba’a saka ta ba, da tunanin abin ta kwanta aranta.

***Auren Katin Kasa ***

(Unexpectedly falling)

Story and written by:

QueenMarh

Paid book 

Chapter44-45

Washe gari Monday da wuri amra ta shirya cikin manyan kaya irin namu, atamfa riga da skirt, wanda ta taho dashi daga gida, sun dameta sosai, kayan alatun jikinta kamar zasu farka kayan su fito lol… mamaki ne ya lulubeta sbd agida kayan kamarma yawa sukayi mata, amma yanxu skirt dinma da kyar yake shiga sbd ass dinta daya karu sosai, feshe jiknta tayi da turaren ta mai sanyin kamshi wanda suka taba saya itada Haifa, mayafin ta dauka ta yafa shi gefen kafadarta, ganin jikinta is too exposed yasa ta lullube bayan ta sai tabar gaban, flat shoes ta dauka na zara baki wanda ya fidda kyawun yatsunta wanda tadan goga masu henna kadan wanda ta sayo, chain bag dinta ta dauka ta sanya sannan ta zari wayanta da lap coat dinta da laptop ta fito, ahankali ta sakko ta shiga motorn da tayi requesting sannan suka fara tayi, adaidai gate din shiga head quarter wayanta yayi ringing, ganin number Haifa yasa tayi saurin picking, nan ta shaida mata ta iso already kuma tana cikin asibitin, ciki suka shiga kamar kullum sannan ta bada payment din ride dinta ta wuce direct cikin bulding dinsu, ahankali ta ke takawa harta isa reception, Haifa na ganinta ta taho da sauri ta rungumeta, saida suka gama rungume rungumensu sannan suka wuce office din su amra, babu kowa aciki da alamu hafiza bata karasoba, zama sukayi kafin amra ta fara shirinta, lapcoat kawai ta daura akan kayanta sannan tayi rolling veil din ajikin ta, morning round ta fara wajen sojojin da aka kwantar, saida ta duba daya bayan dayansu daman basuda wani yawa sosai sannan suka wuce wajen head of team office, basu kaiga karasawa ba sukaji hafiza na kiran amra, koda suka juyo suka gaisheta nan amra ta shaida mata zasuje wajen head ne, nan hafiza ta shaida masu cewa itace zatayi dealing da aikin head temporary, juyawa sukayi harda hafiza suka wuce office dinsu anan hafiza tayi ma Haifa komai sannan ta shirya mata nata office din wanda yake gefen nasu office din.

Haifa kam taso ahada su waje daya da amra amma ganin wajen nasu babu nisa Tsakani yasa ta hakura.

Lokacin sallah nayi suka wuce masjid na mata, salla sukayi sannan suka fito ajere ko wacce da lapcoat din ta ahannun gwanin burgewa, fitowa sukayi daga bulding din dama masjid din shine bulding next to headquater bulding, tafiya suka dan yi kafin daya bisani suka jiyo hayaniya, dagowa sukayi ganin waenda akema wannan salute din, wajen duk ya karade, general ne da na hannun damanshi m-5 sai kuma hammam sun fito daga masjid, kallon kallo amra sukayi

itada Haifa, kan kowa adaure, jawota gefe amra tayi sbd adaidai hanyar wucewar su suka tsaya, ganin Haifa ta qi motsawa yasa ta kura mata ido tace ‘’haifa lets go karki samu acikin matsala’’ itako Haifa mamaki ne ya cikata, hammam ne ya ganta har sunyi ido biyu amma ya kawar da kai kamar bai santa ba, mamakin hakan da yayi ne ya sata kasa motsawa, ganin sunzo dab dasu yasa cikin amra kullewa, hankali atashe ta duqar da kanta, tsinkayar muryar hammam sukayi wanda ke cewa ‘’get out of the way ladies’’… amar da baima san dasu awajen ba ya dago yayi masu kallo daya sannan ya wucewar shi.. da karfi amra ta janyo ta gefe tace ‘’haifa wai meke damunki, kinaso akoremu ne ko asamu tsallen kwadon da bamu shirya ba’’…asanyaye Haifa ta kalleta, fuskarta tap da qalla tace ‘’amra bakiga abinda ya faru bane? Hammam ne fa yayi kamar bai san da tsayuwana awajen nan ba, what is the meaning of that’’…sai yanxu amra ta dago zancen, wanda yayi masu Magana akan su kauce ahanya wato hammam ne…

Janta tayi suka wuce cikin asibiti, zama sukayi ah office din amra, saida amra ta bata ruwa mai sanyi tasha, har lokacin mamaki ne kwance ah fuskar Haifa, saida amra ta tabbatar ta ‘dan sauko tukunna ta fara mata Magana cikin nutsuwa ‘’Haifa bai kamata don hammam bai maki Magana ba kodan ya kau dakai don ya ganki kiji zafi ba, uzuri zaki mashi, kinga dai babban ne ah headquater kuma kinga wanda yake tare dashi general ne gaba daya na headquater, kuma kinsan yanda aiki yake anan, komai professional ne, ni ina tunanin yayi haka ne sbd kinga bayason asan cewa yana relationship da intern, yanxu haka ma qila bai kula dake ba, ke kuma duk kin wani damu, please karki damu kanki nasan cewa zai maki Magana, ki bari ku fara Magana ke dashi tukunna kinji kafin kiyi judging dinshi”.

Sai alaokacin Haifa ta dan ji daidai, don duk abinda amra ta fada haka ne, maybe ma she’s just over doing things, kuma dole wajen aiki kowa ya zama strictly professional babu wani nuna kusanci da juna.

Hira amra ta fara janta dashi sbd ta dan watsake,ganin ta dawo daidai yasa suka fara aiki, wasu abubuwan ma duk amra ne ke nunama haifan, daga bisani kuma suka fita don ganin wards din asibitin wanda duk amra ne ke nunama haifan.

Saida sukayi zagayen ko’ina sannan suka dawo office, nan suka tarar da hafiza tana ta sassarfa tsakanin offices din, ganin su amra yasa tayi saurin karasawa gabansu ta miqa ma amra wani file da wani dan box tace ‘’amra, headquarters zakije yanxu yanxun nan, urgent work ne wannan,time din appointment din yayi idan kika dawo zan maki bayani, office din general zakije zaki deba jininshi for monthly blood test, akwai duk wani abu da zaki buqata acikin box din, kiyi maza ki tafi yanxu saura 2mins’’ tana kaiwa karshe ta wucesu, amra wadda kamar ta kurma ihu takeji, ta dago ta kalli haifa sannan tace ‘’haifa na shiga

uku, ni bana son shiga headquarters wallahi, ni wallahi harda office din general dinma bansan zuwa’’ dafata haifa tayi don ita bama tasan waye general din dasuke Magana akai ba tace ‘’babe you got this, jini ne fah kawai zaki deba ki dawo’’…ganin time nata tafiya yasa kawai ta wuce headquarters, harda dan saurinta, saida tazo gaban lift ta kalli agogon hannunta, kusan minti biyun Ma ta wuce, nan take fargaba ta dirar mata tunawa da last time dataje office dinshi very late, da sauri tabar gaban lift din sbd bazata iya jira ba, sauri sauri ta dunga tafiya gashi skirt din jikinta ya dameta sosai,dakyar ta karasa 10th floor tana nishin wahala, ganin almost 5 minutes yasa tayi sauri ta karasa gaban office dinshi.

Tana zuwa dab da office din ta tsaya, kirjinta yana bugu dumm dumm, runtse ido tayi sannan ta fara knocking ahankali, kusan minti biyu kafin yace ‘’come in’’… anatse ta murda handle din ta kutsa kai, kamshin nan ya bugi hancinta anatse ta runtse idonta ta fara takawa har gaban tamkeken table dinshi, tsayawa tayi da box din manne a kirjinta batayi gigin dagowa ba ta fara Magana ‘’Good afternoon sir, I’m here for your blood sample’’ jin shuru wajen minti goma yasa ta dago, karaf idonta ya sauka cikin nashi da sauri ta sadda kanta kasa.

Shi ko kallonta yayi kallo daya from here to toe sannan ya kauda kanshi gefe, saida ya dauki kusan yan mintuna sa



nnan ya soma Magana ‘’what’the time now’’?

Da sauri tace ‘’its 2:35pm sir’’

Shuru yayi yana latsa laptop idonshi nakan system din sannan yace

‘’ke kinsan girman laifin duk wanda ya bata min lokaci na? you even have the guts’’ yakai karshe yana dago kanshi akanta,

Dagowa tayi da sauri tana kallonshi, mamaki ne dauke afuskarta, jin hausa radau abakinsa’’ ganin shima kallonta yake da idanunshi masu kwarjini da kashe jiki yasa tayi saurin sauke nata idon,

Anatse ta fara Magana, muryarta kamar ta fara shaqewa tace ‘’I’m very sorry sir, I.. i..’’ tama kasa kaiwa karshe sbd wani irin sarkewa da lungs dinta sukayi, ahankali ta soma tari.

Tsinkayar muryarshi tayi yana cewa ‘’come and do your job and get the hell out my office, bana son mutane masu sakarci, who even sent you here? Babu wani specialist dazai zo ya daibi blood sample dinba sai thrashs? Yana kaiwa nan ya miqe tsaye sanye yake da uniform dinshi wanda suka fiddo da kyawu da cikar haibarsa, shajenshi wanda suka zagaye fuskarshi sai

15 / 16