Author : Hassana Bamalli Oum Aphanan Category : Tknovels
ɗin 7782217014 , Mohammed Hassana ,fcmb Évidence of payment 09065990265 ,ƴan nijer Artel 500f regular ,vip 700f special 1000f*
Oum Aphnan✍️
[7/1, 10:42] 😘😘😘: 24
Ta hantsale muka dingayi shi Allah ya taimake sa ya riƙe ƙarfen ,kafin nan Ni har na kai ƙasa sai ji kake rammmm na ƙwalu akan bayana ,wani ƙwarzababben ƙara na saki mai Amsa kuwwa wanda sai da duk gidan ya Amsa ,da gudu Adams ya gangaro benen ya ciccoɓo Nadiya cikin tashin hankali ,tuni jini ya fara fita mata ta hanci da baki idonta a lumshe jikinta ya saki ,sa hannunsa yayi a ƙasar bayanta ya ɗagata cakk yayi hanyar ƙofa da gudu kamar ya ɗauki er tsana ,momy da ta idar da sallah a goje ta fito da hijabin sallan ta ,faɗi take lafiya lafiya ? Amma ina Adams har ya fice binsa tayi da gudu ,a compound sukaci karo da Hajiya mama itama ,nan suka ɗunguma hanyar parking lot ,tun kafin ya ƙarasa wajen yike kiran ,gate ! gate Open the gate "
"Je fata yayi a motar ya shiga gaba da sauri mom ta shiga bayan ko tsayawa ta rufe baiyiba ya figi motar ,Hajiya mama da take takowa da ƙyar ,saida ta iske ɓurɓushin ƙuransu ,samun gefen flowers tayi ta zauna tana salati da salallami
A asibiti yina parking mom ta fita da gudu kiran nurses suzo da abun ɗaukan mara lafiya ,shikam sunkutarta yayi ya shiga reception ɗin da sauri yina ware ware ,ganin an rubuta accident and Emergency Female section a saman wani ƙofa yasa ya cusa kansa da sauri ,da sauri
Wata attendant ta sha gabansa ta babbake jikinta a jikin ƙofar "Malam ba'a shiga bakaga ɗakin mata ba ne ko baka iya karatu bane,kalli nan " ta nuna masa inda akai rubutun a saman ƙofar ,bakinsa rawa ya kamayi kamar me in Ina ,ya ma rasa mai zai ce mata don takaici kawai sa ƙafa yayi a wajen ƙafarta ya taɗiyeta ,sai gata rimmmmm! Ta damfaru a ƙasa kanta ya ƙwalu da tiles ,ƙaran Azaba ta fashe dashi ,shikam ko a jikinsa ,haka ya tsallake ya shige ciki ya kwantar da Nadiyar akan bed ɗin da ya gani empty ,sai sannan momy ta shigo da sauri bayanta likitocine mata sai namiji ɗaya wanda ga dukkan Alamu shine Babban gabaɗaya ,haka suka rufu akan gadon Nadiyar ,ana haɗa lines da sauransu ,sunyi kusan 2hrs Adams na tsaye ƙeƙam kamar icce anyi anyi ya fita waje ya zauna yaƙi hakanan suka ƙyaleshi har suka gama aikinsu ,a hankali matan suka ringa sulalewa saura mace ɗaya da take tattara kayan da sukayi amfani dashi sai kuma doctorn da ya kafe ƙirjin Nadiya da ido bako cire kai ,itakam a hankali take sauke numfashi take mayarwa
Adams yayi second biyar yina son karantan inda likitan ke kallo ,saida ya gama haɗa zarginsa akan lallai ƙirjin Nadiya da ko shi kansa kallo ɗaya da yayi ma wajen Saida yaji yarrrr wai shine shi yake kallo ,bai tsaya sanyaba ya ɗaga hannu ya tsinke kumatun likitan da mari ,Ji kake "Ɗauuuuu!" dafe kuncinsa yayi kana ya ce "Ahhhh" ganin Adams tsaye a gabansa yina huci ya sa ransa ɓaci "kai daƙiƙin ina ne da zaka ringa kallon jikinta banza ɗan iska ,kwarto ai shiyasa naƙi fita saboda na daɗe da sanin gaba ɗaya ku likitocin nan ƴan iskane " Duk da Likitan ransa yayi ƙololuwan ɓaci amma saboda yasan a aikinsa ba faɗa da mara lafiya ko ƴan uwan mara lafiya yasa ya girgiza kai ya ɗanyi tsaki kana ya maida ƙwarar idonsa akan ƙirjin Nadiya daya gama cika ya batse da dukiyoyin Fulani
Adams kallon sashen Nadiyar yayi ya ga cikakkiyar mace kwance samɓal cinyoyin nan santala² farare sol sai manannen bomshort ,ga cibinta a waje ,ga nonuwanta hanƙar cikin er rigan ,wani ƙara ya saki a take yaji ƙwalla na shirin zubo masa ,da sauri ya shaƙo wuyar rigan likitan ya haɗashi da bango ,Daƙyar yake iya magana saboda yanda numfashinsa ke gaurawa kamar yayi gudu "Ɗan fita mana "
A gadare yace "Bazan fitaba ina kan aiki nane,kasan kana kishin matar naka uban wa yace ku kawo ta haka ,bata da kayane?Nafika ƙaryan baƙar kishi"
Dukda yina cikin ɓacin rai saida ya maimaita "Mata??
Baƙar kishi ?? Nike ma wa? Watannan ƙazamar?" Girgiza kai yayi da sauri a take ya ƙaryata zancen zuciyarsa ,saboda sam Nadiya batai kalan matar da za'a tozarta ba ,amma shi yasan ba kishinta yike savoda soyayya ba kawai yina kishinta ne saboda ita ɗin ,macece a ƙarƙashin kulawar su take
"Sai akace ka kafe mata ƙirji da kallo kwartoncin naka har a gaban mutane ? Subhanallh ƙarshen duniya dama ance za'a ringa zina akan titi" dakatar dashi yayi da hannu
"Aah kaga dakata malam ,ka mareni bance maka komai ba ,kasha kwalata bance maka komai ba ,kar kayi mun ƙazafi saboda ina ƙoƙarin taimakon matar ka ,me zan kalla ?wai nono ? To Matana biyu,in abunda kake zargine to bashi bane ,Ni gudun numfashinta nike ƙirgawa Inaso insan zuwa yaushene zata farko amma kai sai hauka kakeyi ,still on my point wayace ka fito da ita da kayan baiwa me gida shayi ?"
Tsaki yaja "malam kabar danganta ta dani Ni ba Matana bane" ya fada kansa na sunkuye a ƙasa duk yaji kunya ,shi ya manta za'a iya bincikar breathing pattern nata through sternal area
Likitan Jan kujera yayi ya zauna ya cigaba da rubutu akan file ɗin nadiya ,ana haka saiga momy ta shigo da wata Nurse a bayanta riƙe da baƙar ledar doguwar riga da ta aiki wani cleaner ya siyo masu a boutique d'in dake wajen asibitin
Ɗaure fuska tayi ta kalli Adams "To hakimi zoka fita kana sane dai haramun ne ka tsaya Nadiya na kwance a haka kuma kasan inda idonta biyune ai bazataji daɗi ba ko?...sister ɗan sa mata rigar Plz,muje dayallah" ta tasa ƙeyarsa yina "Mom zata warke kuwa ,mom Ni naja ta faɗo daga stairs ɗin nan" tsaki tayi ta cigaba da tafiya shikuwa yina Binta kamar bindi duk ya ruɗe "mom haba ke kuwa naga ke kamar ma baki damu da ciwonta bane ,ko don ba ke kika haife ta ba?" Waigo wa tayi ta kallesa sannan ta girgiza kai "Cashi!! Sannu Adams lallai nine kake sa idonka cikin nawa kake yaɓawa magana son ranka akan nadiya?,bakada laifi amma dai ka taka a sannu don Dama na fada maka akwai ranar nadama yau gashi yazo nadaɗe ina zargin son Nadiya shi yake sawa kake kwarzaban er mutane ,to na ganin ma idona ,saidai ina gargaɗin ka don ka dade da saka mata tsanarka a zuciyarta ,bakinsa rawa ya kamayi "Mom Ni bance Ina sonta ba" tsaki taja ta shige mota ta zauna
Gaba ya dawo ya zauna shima yayi shiru yina tunanin maganar mama ,kiran likita ya sashi fita da sauri har yina buga tuntuɓe
"Wai gaskiya mutunina ka kamu da yawa ,son ma irin makahon son nan kake mata ,sai da na fito nikejin labarin wai da zakashigo fyallar da Attendant ɗinmu kayi tana nan tayi tsagewar ƙashi,har tafi mara lafiyar da ka kawo jin jiki ,me kayi kenan wannan?"
Zuwa yanzu ya fara jin haushinsu kowa yace yina sonta ,wani irin so daga taimako ?
"Malam ka kirani ka fada mun me ke cikin zuciyata ne ko kuwa ,rashin lafiyar waccan yarinyar "
"Yarinya ai ta rigada ta samu sauki ko yanzu ta farka daga barci da take zamu baku sallama ku tafi gida ba abunda ya sameta tsorata tayi sai ɗan buguwa "
A takaice ya masa godiya ya mike ,bayan ya ajiye masa cheque na 250k ,ɗauka likitan yayi yina karantawa ,baki sake saida ya kai ƙofa ya ga tabbas fita zaiyi sannan yace "Na miye wannan ?"
"Aikin ku na marasa lafiyan biyu ,ina mota ina jira a sallameta mu tafi"
"Zaka iya shiga ka ganta ai " wucesa yayi a ransa yina cewa
"Ba bukatar hakan,daga taimako sai raini ya shigo dole in ƙara matsatsi akan yarinyar nan kar taji sauƙi ta daɗa rainani
[7/1, 10:42] 😘😘😘: 25
2days Later
Tunda Nadiya ta dawo gidan suke er kunya da Adams ,shikam ko jin muryarta yayi sai hankalinsa ya tashi ya ringa ganin zanen nonuwanta ,ƙugunta da kuturinta a cikin idonsa ,ya sakawa ransa tunani wannan yasa maganarsa ya ƙara raguwa zirga²nsa ya ragu a cikin gidan duk wani abu da zaisa su haɗu da ita yina ƙoƙarin kiyaye masa ,yau daga wajen exercise wanka yaje yayi ya shige sashen Hajiya er tsohuwa ,yina tahowa ita kuma tana tahowa saye take cikin Jump suit ,mai jikin roba ² ya fidda sirrin mazaunan ta sosai sannan da yake a haɗe rigan da wandon yike saidai in zaa saka kayan a saka ta wuya wannan yasa zanenta ya fito ƙwarai ,ga wani bura uban hips da suka baje ,dukda tanada tumbi amma kadan ne don haka faɗin ƙugunta da tudun nonuwanta da suka fito sosai ta V neck ɗin rigar ya ɓatar da cikin gabaɗaya,gaskiya she look so sexy, ta gyara gashinta sai sheƙi yikeyi ta ɗaura P_cap
Tafiyarta ne taji ya sarƙe sam kaucewa haɗuwa dashi take tun abun nan da ya faru
"Shan gabansa tayi ta danna kai ɗakin Hajiya tsohuwa,bin mazaunanta dasuketa rawa cikin rigar me roba² yayi kamar an cusa balo balo ,dasauri ya saisaita muryarsa da yaji ta shaƙe
"Ke baki iya gaisuwa bane?" Yi tayi kamar bata jishi ba ,ta wuce kujeran Two setter ta harɗe ta gyara zaman p_cap dinta ko kallonsa batayiba
Gabanta ya tsaya ya shiga surfa mata masifa "Dayallah jibeki ?a haka kike yawo sai kace ashawo lady..." Sauri yayi ya bige bakinsa da kansa ,daidai sanda ta watsa masa narkakkun idanuwanta da saida sukasa tsikar jikinsa tashi
Kafeshi ta cigaba dayi da ido bako ƙyaftawa a hankali wasu kyawawan hawaye suka shiga layi a kuncinta ,a take yaji jikinsa yayi mugun sanyi ,amma sai ya wani basar ya fara kaɗa ƙafa
"Nice Ashawo Babes? Kaga nayi maka kama da karuwa?" Daidai nan Hajiya mama ta fito ,dasauri ya fara in ina "No...No...I mean bitch!!" Fiddo ido tayi waje ta dafe ƙirji sai ga wasu hawayen Bil! Bil! Bil!
"Ni ce bitch ? Ni zaka kalla ka cewa bitch saboda ka ganni a gidanku ? "
Duk ruɗewa yayi musamman yanda yaga Hajiya mama ta dogare a bakin ƙofa da alamun neman ƙarin bayani "A'a'a'a'ah ina nufin kalan shigar not you,kuma abinda ya ɓata mun rai..."kafin ya ƙarashe magana Hajiya mama da ta datsi maganar a sama tace ta zauna maka a kujera ko? Wai in tambaye ka Adamu ka saka ƙwai ne a kujeran nan da kowa ya zauna sai ransa ya ɓaci?ehem kujeran ka ne ,naga dai kujeran nan nawa ne ,to kar inji kar in gani ahir dinka Adamu ka kiyayeni akan yarinyar nan zan ci mutuncin ka zaka bar shigo mun ɗaki Adamu" sosa ƙeya ya shigayi yina ƙunƙunai "Adams dai...Adams dai ba Adamu ba" buɗe masa ido tayi ta wullo masa mahucin da ta ɗaura akan telebijin wanda zai tabbatar maka ɗakin tsoffi ka shigo "Kaci gidanku zagina kake yi?"
Fita yayi da gudu yina ƙare haɗe hannu yina kallon sashen Nadiyar alamar kar ta faɗawa Hajiya mama zagin da yayi mata
Samun kujera tayi ta zauna ta miƙa ƙafa akan tebur ɗin gabanta "Ƴarnan kita haƙuri kinji du Allah du Annabi,bansan me nene a kujeran nan da ba wanda zai hau kaiba ba tareda sunyi tsiya ba " murmushi tayi amma binne cikin zuciyarta wani tsanansa ne take jin yina bijiro mata..
"Hajajju ikon Allah ,kinsan me na tuna? Sanda muna gida haka muke faɗa da sisters ɗin akan kujera ,lokacin momy na tana riƙon ƙanninta sadi ,in zamuyi Kallo kowa sai yace sai yayi kallo a kujeran dake kallon TV haka zamuyi ta faɗa ,sai momy ta kashe tvn ta kore mu ,ko In mutum ya zauna akan kujera yina tashi yin wani abu wani ya zauna sai muce ai lallai fa sai ya tashi muna a waje kamar irin ka saka ƙwannan,kai da faɗa ya ishi dady ranar ya rarraba yace 1-1seater nawane da Anty nusaiba ,2seater na ya sadi ,3seater nashi shi da momy ,sanan fa kowa yike zama a nasa ,idan kuma akayi baƙi suka zauna ma a kujera kayi ta tukufurci kenan ,ko kaje ka zauna ana momy kai Faɗa akan kujera Allah dai shi kyauta ,shiyasa a times Nike missing gida"
****
Nadiya daga wannan ranar ta koma saka hijabi ,ko a gida ko kicin zata ,wani abun takaicin ma suna zaune suna hira tanajin motsinta sai ta zabura taje ta sako hijabi ta dawo tana Harbin iska
Abun ciyosa har wuya yayi ranar suna zaune sunacin peanut ta wani zabura har tana tankaɗar da peanut ɗin taje ta sako hijabin ta dawo ,zata zauna ya ƙanƙance ido ya hau masifa
"Ke wai me kika mai dani kwarto ko mene? Taya kina zaune da kin ganni sai ki ruga da gudu ki sako hijabi kamar kinga wani fasiƙi"
Momy da abun ya mata banbaraƙwai kada baki tayi zatayi magana ,yayi saurin haɗe mata hannu alamar tayi shiru don Allah
"Mom let her confess ,meke damunki bakison in ringa shigowa cikinku ne ? am i did wrong to you? "
Shiru ta masa tana ɗiban iska wanda shine abu mafi takaici a halinta da yike damunsa ƙin masa magana
Ji yayi kamar ya fasa ihu "ke magana da nike maki" tuni ƙwalla sun ciko mata ido "Banso in zama Bitch..." Kawai sai ta fara alamun kuka
"Ya Isa...ya isa Yi haƙuri nadiya kina saka hijabinki All the time , sweetheart ka ƙyaleta mana kowa da kalar tsinin poverty nashi ,ita kalar nata kenan" ajiyar zuciya ya ajiye a hankali saboda yanda ya ga mom Bata Gane baƙar magana ta masa ba , juyawa yayi a hankali ya fita ,yina zuwa gado ya kwata yina juyi yana tunanin rayuwarsa na baya da na yanzu
Saboda gabaɗaya zai iya cewa nadiya tana ƙoƙarin goge masa harda ,wai sonta yike ko damuwa da ita ne kawai yayi shine abunda ya kasa ganewa ,momy ne ta turo ƙofar ya shigo ,da sauri ya fara ƙoƙarin goge ƙwallan da suka zubo masa a ido
"Sweetheart you are in love" girgiza mata kai yayi da sauri
"Mom me kika gani ?Allah shi kyauta " ƙyar ta kashesa da ido "Yaushe muka fara er haka da kai? "Mekenan mom ?"
"Kana son ta"
"Wa?"
"Nadiya ,just strength to the point" fututtukewa yayi "Mom a tsarina ba auran ƙatuwa,bare wannan ga ƙazanta ga masifa"
"Wannan a da ka santa ,ina dai gargaɗinka in kana sonta gwara ka wanke kanka a idonta kafin wankin hula ya kaika dare don a bari ya huce shi ke kawo rabon wani"
Tana gama magana ta mike ta fita shiru yayi yina juya maganarta ,da ya rasa makama kawai sai ya mike ya shiga wanka
[7/1, 10:42] 😘😘😘: 26
A wannan tsinin su nadiya taje gida tayi wa su mom sallama zasu tafi Umrah ,nan ta tardasu anata shirin bikin Nusaiba ,nanda 1 month ,suna keɓewa ,Nusaiba ta ce "To ya?"
"Anty har yanzu ban samu saurayi ba ,wallahi ko sunce suna sona da sun karɓi Address ɗina bansan me yasa ba ,basu zuwa ,ko kuma suna zuwa sau ɗaya basu ƙara zuwa " shiru Nusaiba tayi cikin tunani "Wait ina Adams "
"Meye haɗina dashi ko kallon banza ma bai isheni dashiba bare "
"Baki tunanin shi yake koran maki samari ?"
Kai Anty Nusaiba banjin ba,nidai nace ƙila mu Munada nauyi ne mu daɗe a gida bamu samu tsayayye ba " nan ta kwashe duk irin abubuwan da ke faruwa tsakaninsu da rashin lafiyarta da yiwa Attendant tsagewar ƙashi da yayi duk sanadiyyar ta ,shiru tayi kafin tace
"Sisto ,Adams na mugu mugun sonki amma jin kansa da kuma tsoron masifanki da yikeji shi yake hanashi nunawa amma ga shawara...."
Bayan kwana biyu suka ɗage Ƙasa mai tsarki Sunyi umransu a gefe ta buɗe ido ta kuma siya kayan ƙawa da turaruka masu kyau ,bayan sati biyu suka dawo gida ,a ranar da zasu dawo a airport sun fito zasu shiga motocin su ,shikuma nuradden Yazo daukan kawunsa da shima ya dawo daga airport ɗin suka haɗe da Nadiya ,Nuradden Yarone da bazai wuce 26Years ba ,Tunda ya ga Nadiya ya susuce ya shiga famfa ta ,saida ya karɓi Adress dinta da number waya ,though yaji nauyi saboda baisan ta yanda zai shiga gidan gomnati ba amma hakanan ya daure ,bayan kwana biyu ya je .
Tun kafin yazo dama ya kirata a waya ,don haka ta sa su rabi suka haɗa masa abun tarban baƙo na musamman ,yina zuwa tasa aka saukeshi a falo itakuma sai ƙalkale jiki take a gaban mirror ,Adams da ya gama ganeta ta Camera ɗin ɗakinsa da yike kallonta ta wajen ,haushine ya ishesa yanda ta saka wani tamfatsetsen jallabiya ,sai juyi take a gaban madubi tana ɗaukan kanta hoto ,ga munafukin haƙorin gwal da ta sa a gefen hushiryanta kamar wacce taje hajji ba Umrah ba,wanann ya kara ma fuskarta kwarjini da kyau ,kishine yaji ya maƙurosa ,da sauri ya fice ya ga waye baƙon da take ma wannan rawar ƙafan
Yina shiga falon ya tarda Nuradden an buɗe jiki ana hira da aboki cikin gadara a dole ya samo er babban gida ,zuwa yayi bakin ƙofar ya tsaya ya rike labule ya ɗaura fuska
Kallonsa sukayi kafin sukace "Yallaɓai Barka"
Buɗe masu ido yayi "Kuzo ku fita ,shegu aure zakuyi? Wai dakata wa ya baku izinin zuwa cikin gidan nan" bakin Nura rawa ya kamayi "Eh dama Hajiya Nadiya ce ,to to "
"Yanzu ka kirata da Hajiya kai kuma alhajin Kano ko? Kai ajinta ne? Zo ka fita ko yanzun nan ku jiku a gidan maza(jail) " jikinsu na rawa suka zube suna bashi haƙuri suka saƙa suka fice yina rakasu da tsawa takalmansu a hannu suka fita harda ƙarawa da gudu ,sun fyallo da gudu itakuma ta fito cikin yauƙi ,sukaci karo ,buɗe murya tayi "A'a'a'a'ah lafiya ku tsaya mana " ko kallonta basuyi ba suka kwasa da gudu sunji ana zancen zasuyi gidan yari ,tana tsaye cikin mamakin abunda ya firgita su sai ga Isashshen yazo yina doro yina cika wuya ya