GIDAN DADI BOOK 2 END BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS.txt

Author :  Hassana Bamalli Oum Aphanan Category :  Tknovels

Chapter   10 / 16

27K to 30K   out of 46.1K words

. Nikuwa nace don ma bakuje gidan Adams bane da tabbas cewa zakuyi banki kuka shiga ko wani fitinannen hotel don sam tsarin ginin bai kama da gida .

Sai bayan kwana uku lokacin Nadiya har ta soma sabawa da rayuwar kaɗaici ya siyo mata kaya akwatu guda ,in ya fita sallar asuba kafin ya dawo za tayi wanka ta saka turarensa in ya dawo yayi ta jaraba ,in dare yayi yina tafiya sallan isha kafin ya dawo zata rigashi hayewa gado tayi kwanciyarta ,don haka saidai ya kwanta a Sofa shikuma ,don shi har yanzu bai gamsu tama iya saɓa sabulu a jikinta ba bare har tayi wankan da zata fita ,dazai haɗa makwanci da ita ,Nadiya kam a daɗinta haka zata bubbuɗe ƙafa taita juyi a makeken gadon shikuwa yayi ta tsaki kenan ,a dare ya farka so nawa kafin 2.30am yayi lokacin sallar darensa kenan wanda in ya farka sai asuba ,Ran Nadiya ɓaci yakeyi idan ya tashi wannan sallar ,haka zatayi ta tsaki ko ta zauna dingirgir taita rusa masa kuka ,kashe kunnensa yike baya ce mata komai

Abinci kuwa tuni ta waye ,tunda ta gane yanda ake odan abincin a wani abune dake ɗakin kamar POS machine ,Aikuwa lafiyayyen oda takesa ana mata abincin ciman mutum uku kaji kuwa ba'a magana ,tafa saki jikinta tana danƙaran abinci kwana uku bata ganin hasken waje don haka ta kara mulmulawa ,naman wuyarta ya haɗe da gemunta tayi jajir kamar jini ya ɓulla dama ga gyaran Amare da tasha ,Adams kam in ta juya tana tafiya ya doshi satan kallonta kenan cikin tausayawa shikam ya takeyi da wainnan manyan ɗuwawuka ,wai batajin nauyi ne?
Nikuwa nace uhm uhm malam Adams ko dai Admiring kake?

A ranar da suka shiga kwana na huɗu ,A ranar yace su fito su tafi .
Wani murna ne ya baibayeta tanaso suna fitowa daga mota zasu shiga jirgi sai ta gudu ta tafi gidansu

Har sun kai airport ,kawai yanda yike Kallon ta ya tabbatar ba wani damuwa a jikinta , a take ƙwalwarsa ya juya ya tabbatar guduwa take plan ɗin yi ,magana yayiwa driver ɗin sa ,wai su bar airport ɗin su wuce gida a mota

Haɗe fuska tayi kamar zata ƙwalla ihu
"To wai me yasa? "
Banza yayi mata ,kawai sai hawayen takaici ya shiga zubo mata a fuska
Juyowa yayi ya kalleta
"Ke banson shashancin banza ya zaki cika ma bawan Allah kunni da ihunki kamar na tsadda? Gwara Ni na saba ji" banza tayi masa ta cigaba da kukanta ,kimun shiru nace wai meye haka? Me na maki kike mun kuka wai?" Ya magana cikin hargagi da tsawa da saida taji jikinta ya mutu ,tsit tayi kamar er yaye ,duddulo mata da ƙwala²n idonsa yayi "meyeeee?!" Ya sake tambayarta
"Banson tafiyar mota ne " banza yayi mata bai sake ce mata komai ba ,haka ta ƙarace ƙuncinta barci ya kwasheta ,saida sukaci rabin tafiya yasa aka tsaya a wani food palace mai kyau yasa aka kawo mata gasashen kaza mai kyau da madara da Ice cream da ruwa ,gefen Ƙafarta ya ajiye mata suka cigaba da tafiya ,sanyin ice cream ya sata farkawa ,aikuwa cikin sanyin jiki ta jawo ta hau ci ,ranta wasayau ,basu ƙara tsayawa ba sai a gida.........

*****

*Uzurinku nake nema fitan gaggawa ya kamamu wallahi ,ban daɗe da shigowa ba ai haƙuri da typing ɗin yau*
[7/4, 08:10] 😘😘😘: 31
Tana shigowa Hajiya mama da sauri ta tararraƙo ta ɗaga mata hannuwarta biyu bakinta a washe har kunne ,wai irin su kashe ɗin nan ,kauda fuska Nadiya tayi itama ta miƙa mata hannuwarta suka tafa ,Hajiya mama haka ta ɗaɗa ma hannuwanta duka ta ɗauka da Ihun "Ƙawaaaataaaah, Ikon Allah gani ga ƙawata matsayin kishiyoyi?" Wuceta tayi tana kumbure²
Da sauri Hajiya mama tabi bayan Nadiya "ke wannan zuƙeƙen mijin namu kike wa yanga? In bacin ciwo ke kin isa ,ina shan gayena ina sa bar baɗa kumatu da ashado ,ina masa girki mai daɗi ai saidai kiji labarin" yanda take yarfe hannu saida yaba kowa dariya ,itakuwa Nadiya ta haɗa rai ,jan hannunta tayi suka wuce sashenta ,tunda suka doshi sashen nata take jin ƙamshi kamar mene, mamaki bai gama kasheta ba ,saida ta ga ba wasu turare akayi ɓannansu ba ,face wata dattijuwar mata ce ,da ganinta kinga shuwa amma akwai mugun tsafta ,a jikinta ne da kuma tarkacenta suka waɗe sashen Hajiya mama da ƙamshi ,zaunar da nadiya Hajiya mama tayi sannan ta ƙwala ma mairo mai kula da ita kira wai aje a kawo ma Nadiya Abinci ,da sauri nadiya ta tari numfashin Hajjaju "wallahi Hajiya na ƙoshi naci abinci a mota "
"Tuwon jiƙaƙƙar masarane fa da miyar shuwaka " siririn tsaki taja a ciki ² tace "Ai kaji irinta ba,Hajiya na ƙoshi kawai"

"To ai anjima kya buƙata " shiru nadiya tayi mata tajuya suka gaisa da matar ,Hajiya Falmata washe baki tayi "Barkana da ganinki amarya mai ƙyallin goshi ,har na tsufa da zaman jiran isowarki" zaro ido tayi "Niɗin kuma ? To me zakiyi mun ?" Hajjajune ta amshe "Gyara ,Gyara zaai maki ,Hajiya don Allah ki girka mun ita dakyau waccan yaron da kike gani majanuni ne ,banson ko kallon banza ya iya mata bare suyi husuma " murmushi tayi nikuwa na haɗa rai wai auren da sunanshi ɓalalle suke wahala? To bari in ƙyallesu badai ƙamshi bane ? Ai nayi tayi "

Nadiya na komawa ɗaki ta fara da kiran momy wai zata gudo ranar Monday daga school ta dawo ,aikuwa ta balbale ta da masifa ,har tana cewa zata kira a soke mata fita kwatakwal. Tana kuka ta kira Nusaiba ,suna can suna shan Amarci da Hisham don haka bata kusa da wayar ,Dady ta kira tun kafin tayi masa ƙorafi ya fara zumbuɗa mata Albarka ,saida ya kashe mata jiki tsaf da nasihohinsa wanda ya sata kasa masa complain ɗin dawowa gida wannan yasa ta kashe wayar a sanyaye ta fake da cewa ta kirane su gaisa .
Tunani tayi to kenan ba ranar komawarta gidan iyayenta da gaske Adams yayi nasara a kanta? Gashi idan tayi masa zancen saki sai yace ta biyashi sadaki ? Mom ta tafi wajen ta ta tuntuɓeta da maganar amma sai murmushi tayi karki damu Ni banda haƙƙin in sakeki Nadiya da na sakeki ,Amma shawara ɗaya zan baki ki daina masa tsiya ki kwantar da kai yaga kin zama salaha ,in yaga ko ya takale ki da fitina baki biye masa shi da kansa zai baki takardanki tunda dama can ya aureki ne don yaga iyakanki to be gani ba ,kinga me ya rage?" Da sauri Nadiya ta fashe da dariya ta amshe da "Saki momy!" Ta sake tuntsurewa da dariya "Shikenan mom ki barni dashi zaiga biyayyar ƙarya ,Allah dai kasa in iya "
Ƙasa tayi da murya "Ahab zaki iya Ni kizo ma zan ta baki shawarar abunda zaki ringa masa yaji ya tsaneki saki kawai" ajiyar numfashi tayi "To shikenan momy nafa gode " ta suri takalmarta ta fita tana murna ,Her Excellency dariya tayi "I like your frankness my baby" ta miƙe ta ɗauki remote ɗin AC tana stabilizing ɗin shi yanda take so.


Mata dai mai gyaran jiki Tundaga Laraba,zuwa Lahadi matar nan tana ɗakina ,gyara take mun bilhaƙƙi ,gashi ana gyara ana isanka da baki ,surutu dai ,ana koya maka kisisinar kama miji ba boka ba malam, Gashi ba fita ,to dayike dama ba shiri muke da Adams ba ban ma son inga giftawarsa ,don haka nikuwa ko bakin ƙofa ban sake fitowa ba ,dama tace wai ba'a son rana ya taɓa Ni ,wasu jiƙo kuwa da take bani da yanda take sani ina zama a kujeran turare abun har ya fara isana kamar wata me jego kullum ina gasa ɗuwawu?.
Adams ma bai kuma neman Nadiya ba ,haka momy da Dady ba wanda yayi masu magana duk an zura masu ido ,saidai kawai ta samo wata mai koya girki in an gama mun gyara sai ta koya mun bakery drinks da abincin en gayu a cewar mama mijinta bayacin abincin kowa sai wanda yayi da kansa ko Ni ,don haka matarsa dole ta iya girki na musamman da wannan ma zasu samu zaman lafiya .


Monday morning
Zuwa nayi nai wankana saidai tara mun ruwa matar takeyi kamar kullum ta zuba turaruka a ciki ,ina fitowa na zauna zan shafa mai ,da uniform ɗina a gefen gado
"Hajiya badai fita zakiyi ba muna tsaka da aiki ?" Cikin hassala nadiya tace "me ya kawoni inba karatun ba ,this is my primary assignment ko so kike a koreni ?"
Shiru tayi ta fita ta tura ma her Excellency saƙo ta waya .
Ce mata tayi ta fito falon ƙasa ta sameta ,Adams ta gani cikin suit gray da alamu fita zaiyi suna sallama da maman "Me kike cewa?" Bayan ta gayar da Adams ɗin ne tace "Hajiya ce na ganta tana shiryawa zata tafi makaranta kuma zata ɓata muna shiri kar taje ta haɗu da maza suyi mata fyaɗe..." Adam bai jira ta rufe baki ba yace "Wannan ko wani irin shu'umin gyara ne marar amfani wayace to kuyi ..." A hankali momy ta kira sunanshi "sweetheart!" Ɗagowa yayi ya kalleta itama shi take kallo "ka koyi haƙuri akan sha'anin matarka ,sam kana nuna zaƙewa" sosai ta saka kansa a tukunya don haka bai fahimce ta ba kawai sai yayi shiru "Je kice mata ta fito mijinta sai ya kaita "
Juyawa tai tana mata godiya ,shikuma da sauri ya ɗaga baki zai tsiya tai saurin sa yatsarta a saman leɓe "shishh sai ka nuna wa duniya cewa bakason matarka? Bafa mu muka haɗaku ba ,sanda kaje ka nemi auranta ma Safiya bata sani ba so in zakayi hayaniyar ka ,ka bari sai daga kai sai ita kar in kuma ji bazaka ringa rabamun hali a cikin jama'a ba"
"Mom I'm not her driver "
"Kuma daga yau kullum kai zaka kaita makaranta kaje ka ɗaukota saboda tsaro ba"
"Tsaro? Nida nike Governor's son ban nemi tsaron kowa ba ina yawona simple Ni kadai sai ita?"
Banza tayi masa daidai ta fito ta saka uniform ta ɗaura Abaya ,ta rufe fuskarta da Nose mask ,gaisheda mom tayi sannan ta kalleshi ta watsar ta kalli gefe sannan tace "Ina kwana" bai kalleta ba bare ya Amsata ya wuce huuuu ,momy murmushi tayi "Nadiya kinji yanda daga sakkowanki kika addabemu da ƙamshi in anje a kula kinji? Kinada Number mijinki duk inda sararin rashin aji ya samu ki kira yazo ya ɗauke ki kinji?" Yi tayi kamar zatayi kuka "momy fufu fa kika kirashi da mijina kin manta plan ɗinmu ne? Jiba fa na gaisheshi ko amsani baiyi ba"

"Ayya na manta ne my Nady,Amma kema ai ba a haka zaki gaisheshi ba yanda kika gaisheshi da gatsali dole yaƙi amsawa kuma na faɗa maki in kina masa irin haka to za'a shekara bai sakeki ba ,amma idan yaga kina masa biyayya wata guda...." Kawai sai ta karkaɗe mata hannu ,alamun anyi an gama ɗin nan.

Murmushi tayi zanyi fiyeda abinda kikace ma don Ni a sati ɗaya ma ko biyu nakeso a wuce wajen "
"Ya danganta da iya takunki sannan domin neman shawara ko hanyar da zamu gana masa azaba kizo da sauri ki nemeni in baki shi"
Thumb up tayi mata "Ina godiya momy tah shiyasa nike kara sonki" taje da sauri ta rungumeta
[7/4, 09:17] 😘😘😘: 32
Zama yayi a driver seat ƙofar da zata shiga ya rigada ya bude don baison ja in ja yina wayarsa
Tana tunkaro wajensa ya rufe ido da sari yaja numfashi ,turarenta yina haddasa masa wani irin kasala da mutuwar jiki ,har ta shigo ta zauna baima sani ba,saida ta rufo ƙofar ,sannan yaji a wayar Dr. Jabeer yina ta faman ce masa hello...hello
"Doctor ina daf da shigowa cikin asibitinku in nazo sai muyi maganar kawai"

Ya danna abun kunnen ya kashe ya tada motar ita dai tana zaune itama sai chating ɗin ta takeyi da wayarta ,ko bi ta kansa bata yiba ,ƙur yayi mata da ido yina kallon yanda jikinta ke leda leda kamar wata tarwaɗan kifi ga gashi duk sunbi sun kwanta a jikinta ,ƙamshi kuwa ji yayi kamar an jonashi da sifirin hannunsa na mazari yinason cafkota ya rungumeta ,zuciyarsa na dakar dashi .
Nadiya ji tayi kamar ana kallonta don haka ta ɗago da sauri cikin nose mask ɗin ,idonsu ya haɗu da na juna banka mata harara yayi ya kauda kai "draw your mask down " ba musu ba komai ta cire face mask ɗin gaba ɗaya a fuskarta ta saka a jaka ,baiji daɗin yanda batayi masa musu ba ,amma ya kanne ya cigaba da driving hatsabibin ƙamshinsa na daɗa turaresa ,suna zuwa school saida ya kaita gaban aji sannan ya faka ,rataya jakanta a baya tayi zata fita "Hey ji nan" cikin wani salo na jan hankali da batasan ta iyashiba taɗago ta kallesa "Put on your mask" idonta ne taji kamar zai kawo ruwa ,har ta ɗaga baki zatayi masa masifa sai kuma ta haɗiye ta ciro face mask din ta saka
"Gwara ki faɗi abunda ke bakinki don zai kasheki " itadai batace masa komai ba ,ta fito a hankali ai tana sako ƙafarta waje taga Idanuwar jama'a farrrrrr a kanta mata da maza a hankali tace "Wayyo Allah " tana fita ya jawo ƙofar ya sake rufewa saboda yanda ta shafa ƙofar a hankali ta rufe kamar mai tausayin ƙofar ,tafiyarta ne taji ya sauya sai kace wani sabon kamu ,shikam yina nan tsaye idonsa akan ta har saida yaga su Ummu sun fito da gudu sun rungumeta ,wasu sun amshi jakanta sannan ya figi motar da gudun tsiya ya bulbule wanda suke kallonsa da ƙura ,tashi sukayi farrr duk suka watse ana alawadai da halinsa .
Nadiya tana shiga ajin sai ihu "promotion surukuwar gomna A ajinmu Allah yaja da ran Her Excellency...wuwuwuwuw" itadai seat dinta ta zauna a hankali ta jawo hannun Ummu ta riƙe tsamtsam kamar zata karyata ,a haka aketa zuwa mata Allah ya sanya Alkhairi har wanda basu magana da ita
Saida malami ya shigo sannan ajin ya natsu
10am
Nadiya Kallon Ummu tayi "plz Ina jin yunwa kuma ina jin kunyar zuwa capteria siyan wani abu ko zamuje Hostel ki mana girki" Ummu kallon nadiya tayi "Ha'ah omolochamiyoni kyau ga mulki waneke da zuwa capteria ? Nadiya kinyi kyau ga ƙamshi duk inda kika zauna barin wajen kike da ƙamshi " murmushi tayi suka fice daga ajin suna fara tafiya saiga wata er gayun malamarsu da taga hotunan bikinsu a Tv CIKIN gadara ta tsayar da ita "Ke ,in our nursing profession Ba'a saka zobba ,so ciresu ki bani nan" kallon uku saura kwata tayi mata ,sannan ta kalli yatsun hannunta ,kana ta yarfe hannun a hankali "I'm sorry ma Golds ne bazan iya ciresu ba ,ai banda Zobban magani so idan performing procedures zanyi zan cire but now uniform ne"
Ƙanƙance ido tayi cikin masifa "Ke zo nan Ni nike magana kina yi" wuceta tayi ta bar Ummu a wajen tana bata haƙuri

Ɗakinsu ta wuce direct ,tana tyra ƙofa wa zata gani ,Kausar kwance akan gadonta ta ɗashe sosai da ganinta kinga marar lafiya

Haushine ya tuƙeta ,a rasa wanda zai ringa kwanciya mata a gado sai taguwar mazinata ?

Abunda bata sani ba yanda take mata kallon banza itama haka take mata ,wuceta tayi ta samu waje a ƙasa ta zauna
Suna hararan juna ,su Batula ne suka kaɗa kai sukayi shewa kamar sunga mahaukaciya ,hakan yasa nadiya duk ta tsargu
"Kausar ga me ƙwacen saurayi ta barki Hostel da jinya ,gata ki kama shegiya kici ubanta ki mata raga raga " kallonsu duka tayi ta watsar ,ita bata ma gane Yaren da suke ba ,a hankali ta cire rigar makarantar ta ta bar doguwar farin vest da ya kawo mata rabin cinya ta fiddo ,irish a ƙasan gadon Ummu ta fara peeling ,sukam zaginta sike tayi da habaici ko kallo bata ishesu ba ,a cikin dai habaicin ta fahimci cewar Kausar Budurwan Adams ne ,Ummu a haka ta shigo taraddasu ita harma ta ɗaura pan a gas zata fara frying Irish ɗin ta
"Yauwa ga uwar gulma ,shegiya me ƙafan ungulu gatanan tazo ki haɗa su duka kici babanninsu"
"Barsu ku Barni dai Inyi lafiya hayan en daba zanyi su sassara mun su ,kuma dole sai na auri Adams don don Ni kaɗai uwarsa ta haifesa" tsaki nadiya tayi ,cikin rainaswa ta tamkata "Ji banza kina abu kamar wata ashawo don bakiyi kama da karuwan ma masu aji ba ,Ni ina ruwana da Fufu saurayinki ne ? sai kuma gashi bai aurenki ba ɗan malaminka da kuka da taro jamaa saida ya aura er lukuta ruwan masu manyan motoci maza ƙwalelen ƙananun en iska irinki" yaye bargo tayi ta duro akan gado
"Ke Ni zaki zaga ina wasa dake ne bar ganina a kwance dukan ban mamaki zan maki"
"Nunata tayi da ludayin da ta tsamo a zazzafan ruwan mai tayi "to me yasa kika tsaya magana ,aiwatar mana zoki taɓa Ni in kakkaryaki in nuna maki banbancin siriri da mai ƙiba banza kamar ai mata huuuuf ,a hureta ta kifa,sai iskanci ya cika mata ƙoƙon kai ko karatu baya shiga daƙiƙiya tankwala"

Shaƙo nadiya tayi da tunɗazu kyakyawar jikinta ke sata jin baƙin ciki ,ta kafa mata ƙunba ta fara kartar mata fatar hannuwarta ,a take jikin nadiya da bata iya dambe ba sai cika baki ya fara rawa ga raɗaɗi ya addabeta ,ko ina na jikinta da ta karta sai yayi pink ya tsatsage ya fara tsatso jini
"Bar ganin wannan ruɓuɓun jikin tas zan laƙumesa kamar wahalallen biredi ,don komin ruɓuɓun alade bai kai ya kare akuyanci ba" ƙara nadiya ta tsaga saboda yanda take yakusheta ta kasa kataɓus sukuma ƙawayenta na ihu "ki koya mata hankali kausar ki cicci mana bakin shegiya ,in kin zane mata jiki maga bodyn da zata sake buɗe ma en Hostel jiki ana jin sha'awa

Ummu da ita ma ba ƙarfin take dashiba ,jan hannun Nadiya take tana kuka "wayyo nadiya karki haɗa ƙashi da ita ta shafa maki

10 / 16