GIDAN DADI BOOK 2 END BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS.txt

Author :  Hassana Bamalli Oum Aphanan Category :  Tknovels

Chapter   11 / 16

30K to 33K   out of 46.1K words

tsiya na roƙeki" nadiya hawaye take shararwa Allah ya bata Sa'a ta saka kafaarta ta angajeta ta kuwa kifa saboda Batada ƙwari gashi tana jinyan son Auren celeberity

Taso mata sukayi duka suka rufe ta da bugu harda masu zaro muciya suna muƙa mata a jiki ,ihu take da dai Ummu taga an haɗesu duka ana jibga daƙyar ta ƙwaci kanta tayi waje da gudu kiran Security

Sukuwa sai Batula ma ta saka bidan ƙofa ,yanda zasu daketa da kyau ba me ƙwatanta ,Nadiya data fincika kanta daƙyar tayi hanyar ƙofa da zammar guduwa kawai ta gani garƙame da bida ta ƙoƙarin zarewa ta kasa saboda hannunta dake rawa ta lallasu sosai ,waigoawa tayi kawai taga kausar ta biyota kamar zakanya ga faratanta zaƙo zaƙo ,wani yarrr taji tsikar jikinta ya tashi bata fatan ta sake kafa mata ƙunban nan masu dafi a jiki ,wai gawa tayi tana neman abinda zata kare kanta dashi kawai sai idonta ya sauka akan tukunyar man da take soya Irish gayinan dankalin ya ƙone mururus

Kama tukunyar man tayi ta runtse ido ta Antaka mata a jiki
Wani ƙara suka tsage dashi saboda yanda gabaɗaya tabasu sadakan mangyaɗan suda suke ta bayan Kausar ,amma kausar gabaɗaya tayi mata wanka da mai kamar ruwa a jiki .sakin tukunyar tayi a ƙasa ta ɓalle ƙofa a yanda take daga ita sai singlet ta fyallo da gudu security ta riketa kawai sai ta faɗa jikinta ta some saboda furgici da tashin hankali.
[7/5, 10:42] 😘😘😘: 33
Adams wajen Doctors parking lot yaje ya parka motarshi ,saidai ya kasa fita a motar ,ƙamshin turarenta da ta bar masa a wajen da ta zauna kawai yike bi yana sansana , a haka Doctor jabeer ya zo yayi knocking ƙofar motarn ya fara attempting buɗe ƙofar da Nadiya ta zauna ,irin in an buɗe ya zauna a wajen me zaman banza ,inda ta tashi kenan .
Adams firgigit yayi ya fito daga motar ɗin gabaɗaya ya dawo ya buɗe masa gidan baya ,saboda yanda yakeji tsinannnen kishi bazai bari wani ya zauna a wajen da Nadiya ta zauna ba bare ya naɗi ƙamshin ta ya tafi dashi ,mamakine ya kama Jabir "Bros kuna tare da wasu ne ?" Girgiza masa kai yayi "Aah mai ka gani ?" Ya fada shima yina dawowa kujeran bayan ya zauna "Bakomai na daiga mun dawo bayane kamar kana expecting zuwan wani da zai zauna a wajen ,cikin rashin tauna magana yace "wajen yarinyar can ne " cikin rashin fahimta yace "wata yarinya ?" A take ya daburce "uhm ai dama ,mtsewww share kawai"
Sosa kai Jabir yayi don ya manta ance fa Adams yayi aure "Oga Adams yau kuma wani counselling zan baka ?"Dalla dalla ya fara jero masa irin feelings din da yikeji a kanta
"To ai level yanzu ya sauya ,kaje mata da buƙatarka mana ko taƙi yarda ne? In taƙi yarda zan baka tips ɗin da zakayi ta ƙarfi kaga ita ta siya kenan da kaje dai ka fada wani hali gaka da mataa....." Shiru sukayi saboda ihun ɗalibai da sukaji da gudu da Nadiya a hannu dasu kausar ,kamar ance ɗago kai ,Adams ya ɗaura idonsa akan Nadiya unconsciousness a hannu securities wani ƙara ya saki ya ɓallo ƙofar motar ya bi bayansu da gudu yina dakatar dasu ,shi kaɗai yasa hannu ya karɓeta suka shiga Emergency ,Saidai Koda aka kaisu triage ,ko kallon Nadiya baayi ba aka fara wawware su kausar dasu Batula ana duba wanda sukafi jin jiki kausar ana zare mata kayan jikinta ya biyo da fatanta ,Adams da ya kasa jurewa zuwa yayi zai ɗauki nadiya wai a canja mata asibiti ,tunda ita da bata a hayyacinta ba'a duba ta ba
Fafur sukace bazai ɗauke ta ba saboda case ɗin su yina wajen hukuma ,zaro ido yayi "Hukuma? akan cin mene? Ku bani matata mu tafi tunda ita da ranta ke wani hali baku duba ta ba kuke duba wanda ga idonta biyu"
Likitocin da suke triage and filtering ɗin ne suka roƙi a fitar da Adams saboda dai sunsan aikinsu Kausar itace wanda ya kamata a fara bawa kula ,ita kawai ta sumane saboda tremor to an samu ta farko me za'a yi mata kuma ?

Dafa kafadansa doctor Jabir da ya zagaya wajen en uwansa likitoci yaji kan case ɗin yayi ya fara shaida masu fada sukayi aka babbaka kausar
So dole sai hukuma ta shiga ciki

Fututtukewa yayi shi matarsa tafi ƙarfin doka ,matarsa Amarya ce...Matana kaza Matana kaza ,a take ya fara kiran Commissioner of police da sauran manyan lawyoyi wai su tsaya akan Kausar har a gama bata duk kulawar da za'a bata sannan a tafi masa da ita da sauran masu hannu a dukan nadiya

Nadiya lafeewa tayi a bayan mota dukda jikinta duk yayi tsami ga yakushi duk yayi mata luɓu luɓu kamar zane amma dukda haka batajin zafin ya tankacin na kausar da aka kwailayewa gabaɗaya fatar jikinta saboda ya ɗago gabaɗaya ,Tundaga fuskarta wuya zuwa hannaye da ƙirji ,in kaga yanda tai ja aka naɗeta da bandeji to kai kanka sai ka firgita ,bare yaro da ganin irinsu a asibiti ke haddasa masu tsoron wajen ,amma wai a haka en sanda da lawyoyi sun cika asibitin ana jiran a gama dasu a basu su
Nadiya kam yina shiga motar ya fara hura hanci ,lumshe ido tayi da sauri tana tsalalo da hawaye
Kallo ɗaya ya mata yaja wani mugun tsaki ,ganin sun ɗauki hanyar asibiti yasa tace "Foufuu naji sauƙi muje gida " banza yayi mata ,a asibitin ne aka tsitsireta da allurai aka ja mata hannun da ya ɗan taɓu saboda muƙar muciya da ta sha .
Sun kai dare a asibitin kafin a sallame su su dawo gida ,Hajiya mama kam fada kamar taci baki ,harda su kuka wai bazata yafe ma wacce ta zalunta Nadiya ba

Saida suka dawo gida sannan saiga jiki ya ɗime da zafi ta kwanta jinya sosai amma bata bari kowa ya sani ,Shikam Adams baya awa sai ya shigo har ɗakin ya dubata abinda bai taɓa ba kenan tunda nadiya tazo gidan ,itakuma tana ganinsa sai ta lumshe ido tayi pretending barci take
Sai safiya ne ta tashi tai warmth wanka ta saka kayan shan iska amma sai muku² take da mayafi saboda Adams da yike yawan shigowa ,duk in ya fita sai ya dawo mata da Abunda takeso ,Ice cream dai da su tarkacen chocolate ,kaji kuwa sau biyu yina shiga kicin yina mata ,da chips Amma ƙinci takeyi yina fita sai taje taci abincin gida ,shikuma yina sake dawowa yaga duk abinda ya aje bata ciba,haka hankalinsa zai ƙara ɗugunzuma "Yarinya maciyya amma yau saboda Ni an mata dukan da ta kasa cin abinci? "
Sai ya sake fita biɗar wani abun da zata so ,kai ƙarshe ma cewa yayi a tasheta barcin ya isa haka ,ya zauna akan gefen gadonta yace ta shiga tai wanka suzo ya fita da ita maybe in ta ɗan je yawo taga gari ,tafi jin daɗi then zama waje ɗaya
A hankali ta sakko tana jefa ƙafa a hankali shikuwa sai tausaya mata yike a kunyace taje tayi wankan tana ta cikuiciku da towel kawai yaje ya buɗe wajen kayanta ya nemo mata Abaya mai er ciki mara nauyi Armless mai abun samarshi shigen Alkyabba amma shara shara kuma ba nauyi ,ya ajiye mata yayi ficewarsa don ya lura shiryawane bazata iyayi a gabansa ba ,a hankali ta ke shiryawa tanajin wani daɗi yau tana wahalar da Adams
Shikam harda ƙamshjn turarenta yike sashi nacewa yadai shigo kuma sosai yike tausaya mata duk in ya zauna shiru tuno ta yike tana kwance a bayan motarsa tana zubarda hawaye wanda yasan shi ya ja mata .

Momy kam ko fitowa taƙiyi ,tanata jin daɗi yau Adams ɗin ta ne yike kulada mace? Kai Alhamdulillah Allah ya daidaita yaran nan"

Sunsha yawo sosai dukda baya iya mata magana gashi dai ko yinason ya mata magana amma Muryar sai ya tsaya a maƙoshi ,kawai dai miskilanci ke ɗawainiya dashi

Suna hanyar dawowa gida ne yayi parking a gefen hanya ya kasheta da ido ,itama dai a mamakance ta kallesa
"Me yasa ka tsaya ?" Yanda yaji muryarta a yanzu sai yaji kamar muryarta kansa ya rage karsashi ,ji yayi kamar ya fashe da kuka saboda tausayi da ta bashi ,ya lura yarinyar tanada batsa² da rawan kai amma tanada kirki kuma tanada dauriyar ciwo if not baici ta saki jiki haka ba ,kuma da alamu asibitin ne batason kwanciya shiyasa tanuna taji sauki
Shiru sukayi ba wanda ya cewa kowa komai ,ita har ya fara bata haushi ,ta tsani tai tayiwa mutum magana yayi banza da ita ,don haka tace "Uhmmm" ta turo baki ta juya masa ƙeya

Gyaran murya yayi "Ahmmmmm " sai kuma yayi shiru yina tunanin taya zai fara sai cewa yayi "Wa ma kike ?" Cikin mamaki ta waigo kafin ta jinjina kai "Nadiya Nike,da naso Inyi mamaki sai naga kuma ai ba abun mamaki bane saboda baka taɓa kirana da suna na va bien sai ke kuma a haka nike amsawaaa" yanda taja amsawar ya tabbatar abun na ƙona mata rai sosai ɗaga mata hannu yayi a hankali "Asshhh ,I spoiled again,Naaady plz I'm sorry ok?" Ji tayi ba wanda ya taɓa kiran sunan ta da style irinsa ,ada takanji ta tsani sunanta amma yau sai taji daɗin sunan a bakinsa "Nop ni banso babba yina bani haƙuri ya zanyi da kai don ka cemun ke ,amma dai kawai atimes banjin daɗine" ta ƙare idonta na tara hawaye

"Shiyasa nace ai kiyi haƙurin Plz ,sannan kuma Zan baki haƙuri na abunda ya faru da en ajinku nasan Ni na ja maki,Amma na cireki a makarantar bazasu sake ganinki ba ,zanyi tafiya Turkiyya akwai wani companyna da nike buƙatar zan kula dashi ,amma sai nan da wata shida zan tafiyar ,kin yarda innema maki makaranta acan sai ki bini ?"
Shiru tayi tana murza yatsun hannunta ,ita a duniya batada buri irin tayi karatu a ƙasar waje saidai zaman ne har na wata shida mate ɗin ta zasu wuceta da yawa

Sosai yaga fuskarta ya ɗan sauya kamar bataji daɗi ba"Shikenan to zan maidake Abuja kusada su mama ki karatu hakan yayi maki?"

"Aah inason can inda zaka ɗin amma Ni bazan iya zama har wata shida bane ƙawayena zasu wuce Ni"

"No su koda yaushe suna Admission ,in kinaso Zaki iya fara e-learning ,kinga a ɗaki Zaki karatunki in zakiyi practical suyi posting ɗinki asibitin da kike so "

Sa haƙorinta na ƙasa tayi taja leɓen ƙasan bakinta tana tsotsa ,cikin shagwaɓa tace "Saiii" kuma sai tayi shiru

"Sai me kuma?"
"Bakomai"
"Aikuwa sai kin fada ko mu kwana"
"Sai kuma Ni ya zanyi in tafi dakai wani ƙasa mu kaɗai?" Dariya ya saki ,har hawaye na taruwa masa a ido ya daki sitiyari a hankali

Itakuwa ƙur ta masa da ido tana mamakin wai dama ya iya dariya bare kuma dariyar ƙeta haka har da hawaye? Wai ma me tayi da ya bashi dariya?"

"Wai menene"
Turo baki yayi shima yana kwaikwayonta "ba komai bobi ,kawai ya kamata muje da Hajiya er tsohuwa ce ,kinga shine adalci tunda Matana biyu ne" ɗaure fuska tayi "ta yaya Hajiya tsohuwa ta zama matarka ? Ba maman babanku Bane? Kuma a ina aka ɗaura auren ? To ko nima nawa sakina zakayi mamane tace in maka biyayya in ka kasa cutana zaka sake Ni" shiru yayi na en sakonni kafin yace "Oh dama mom duk cemun da take Sweetheart Bata sona ,shiknn zamuyi maganar daga baya ,now can we set up mu tafi " gyara zama tayi cikin zumuɗi,ta faɗi da ɗan ƙarfi "Yes sir!" Murmushi yayi suka fara tafiya itakuma ta fara shan strawberry smoothie ɗin ta
[7/6, 13:54] 😘😘😘: 34
Momy tayi mamakin yanda suka dawo da barkwancinsu, suka shigo ɗakinta "Aah Nady jiki yayi kyau kin fara yawo? Ni ina nan na fara tunanin Musa cigiya?"
"Wallahi mom naji sauƙi don ma Foufou ne ya tsareni da hira da tuni mun dawo
Tsare shi da ido tayi irin yaushe aka warware ƙiyayyar ?sosa ƙeya yayi ya fara kame² kamar ta tambayesa "mom kinsan mara lafiya sai ana lallaɓashi bare kuma nasan Ni na ja mata "
"Eh hakane kam kuma ya kamata ka kula da ita ,nady tashi kuje ya kula dake" haɗe rai tayi "Ha'ah mom naji sauƙi ai " miƙewa yayi ya fita "mom bari in je sallah inada meeting by 8pm"
Dariya tayi "Ni ba ruwana zo ku wuce da matarka "
"Mom na barta wajenki" zaro mata ido nadiya tayi "mom matarshi kuma kin manta kince sakina zaiyi"
"Af suɓutal kalam ne Nady ,jeki Hajja na jiranki"

****
Kwanci tashi ba wuya yau satin su nadiya uku da Aure ,Adams kam zuwa yanzu baya iya ɓoye irin son da yike mata ko a gaban waye,dukda shi kansa bai sani ba ,a tunaninsa ɓoyewa yike,Nadiya kanta yanzu in ta wuni bataji motsinsa ba ta dinga tambayar wai ina yake ne?
Amma duk haukan nan kowa ana nashi zancen cigaban aurensu sai ya nuna kamar baya so ,gwara ma Adams akan nadiya shi baya magana ,amma itane me zaƙalewa

A kwanakin nan ba wani gyaran jiki da za ayiwa amarya wanda baayi mata ba ,don akwai wani man turare da matar ta bata ta ringa shafawa tana fitowa wanka kafin ta ɗaura ,body cream Wai shi indai ya washeta kayan da ta cire ƙamshi zai ringayi haka duk wanda sukayi mu'amala ,kai komai ta taɓa sai yayi ƙamshin nan,wai idan har miji ya maƙale mata to shi ake kira da sirrin mallaka ,don duk macenda ya raɓa tsami zaiji tana masa .

****
Adams tuni ya gama ma nadiya processing makarantarta har ta fara ɗaukan darasinta ta elearning ,along the process na neman makarantar ne ya karɓi numberta yina kiranta time to time amma dai akan magana ne masu muhimmanci baija da tsayi ,saidai in ya kashe zaita juyi yina tuna feelings ɗin

****
Case ɗin su kausar kuwa an Gama rectifying ,an rubuta masu kashedi kuma a kan ko mummunan kallo yashiga tsakaninta da nadiya zata karɓa horo dukda ta bar makarantar ,aka kira nadiya tazo itama tayi signing a takardan kafin lawyer ya ajiye a foldershi na cikin chambershi ,don haka Adams yace ta shirya su je ,Atamfa super ja da yarfin green mai kyau da tsada ta saka ,riga da siket ,ta saka ,siket ɗin streght siket ne ya kamata sosai ,amma rigar a buɗe wakatata ,don haka ba'a iya gano shape ɗin mazaunan ta saboda rigar ya ɗan sauka tayi kyau sosan gaske ,ta murza ɗauri ,sannan ta saka plt takalmi fari,da jaka,da mayafi ,tana cikin fesa turare ya shigo ,ɗaure fuska yayi ganin yanda take wankan turare ,kallonsa tayi ta haɗe rai a zuciyarta tace "Nafika ƙaryar majanunanci ,yau kai dariya gobe ka ɗaure fuska mtseww" banza tayi masa shigowa yayi ya tsaya a bayanta ,tana kallonsa ta cikin madubi batace komai ba ,ɗaukan wani kwalbar turaren tayi da hankula yakai hannunsa ya warce tularen ya ajiye akan mirror ɗin ,waigowa tayi tareda turo bakinta da yike shaiƙe lip gloss ,da limsassun idonsa ya tallafo ƙeyarta ,kafin tayi wani yunƙuri ya danna bakinsa akan leɓenta ta haɗe duk leɓɓenta biyu ya tsotse for few seconds sannan ya janye ɗaurin da tayi kamar wacce zataje get together ,ya warware ɗaurin ya maidashi normal ɗauri kana ya cikata ,baya tayi da sauri cikin jin jiri taje ta dafe mirror hannunta akan goshi ,buɗe baki tayi tanaso tayi tsiya amma muryarta ya shaƙe saboda gabaɗaya bata taɓa jin ɗumin bakin wani halitta akan jikinta ba sai yau

Adams murmushi yayi ya goge mata gefen kunci da sauri ta juya fuskarta ta na harare ²

Kwabanta ya buɗe ya canjo mata farin mayafi lafcece ,ya janye mayafin kafaɗarta ƙarami ya sagale mata babbar ya lulluɓata

"Ni banson kana taɓa Ni meye haka?ka bani mayafina shi nake so"

Sauke muryarsa yayi kamar na me raɗa,ya daɗa matsowa kusa da ita ,matsawa tayi da sauri "Plz ka daina taɓani mana,kawai ka bani mayafina "

"Kina matar Adams kina saka ƙaramin mayafi?"
"To meye Ni ba matarka bace ,bakace jira kake mu gama settling case din su kausar ba ka bani sakina?" Ta faɗa tana gyara ɗaurinta cikin kumburo baki

Shafe gashin kansa yake yina wani kalar murmushi kamar na wanda yake wani irin tsantsan begen wani

"Allah sarki kausar budurwataaaa! Humm budurwata kausar kenan" haɗe fuska tayi kamar zata falla masa mari

"Waye budurwan taka?" Lashe leɓen bakinsa yayi yina Admiring kalar kishinta ta wani daddalo ido waje har sun kaɗa ya cika da ƙwalla

"Kausar dai dakika ƙonata ,kinga duk a kaina ta samu naƙasar nan shiyasa nace inason a gama case ɗinku sai inje gidansu in roƙi yafiya a bani aurenta in fita da ita India a chanja mata mataccen skin ɗin nan da kika babbakata saboda so na"

Buɗe baki tayi muryarta na rawa irin na masu kuka "Ni Allah shi kyauta in babbakata saboda kai ,Na ƙwaci kaina ne saboda kar su kasheni saboda kai"

"Auhoo ai na gane ,wallahi tsananin tausayinta nike yanzu waye zai aureta da soyayyen fuska??" A hankali yike zaro maganar ba damuwa ba komai kamar baisan halin da take ciki ba

Itakuwa numfashinta ne ya fara barazanar barin ƙirjin ta ,kwartukwar ta zaro sunanshi
"Adam kaje ka aureta mana Ni meye haɗina daku ,duka da zakuyi ta damuna ita ta dakeni kai ka zageni..." Shiru tayi daidai sanda hawaye ya fara zubo mata a fuska ,da sauri ya zo kusa da ita yina ƙoƙarin kamo hannunta

"Subhanallh meye haka ya da kuka? Yi hakuri bansan maganar budurwata zai ɓata maki raiba , inshallah bazan sake ba daga yau" wucesa tayi fuuuu zata fita ,da sauri yabi bayanta da mayafi

"Ma'am wait ga mayafin time is not by our side"

"Nafasa fita Adam bazan bika ba ,kaje wajen kausar in ka burgeni ka aurota ka kawo ta cikin gidan yau "

"Waikkk maganar yayi girma sai kwadamun Adam ake ba ko kunya ,Haka ƙawayenki zasu zo suji kina kirana da Adams a matsayina na yayanki ke kuma ƙanwata ?"

Banza ta masa ta wuce ƙasa ta sama kujera ta zauna

11 / 16