Author : Hassana Bamalli Oum Aphanan Category : Tknovels
[6/21, 12:05] 😘😘😘: 11
Hajja Safiyya Sam Abun yaran ya fara damunta ta rasa wani irin abune wannan wanda ko sanda maman little keda rai basa irinsu l da Adams a matsayinta Na mace saƙonsa ,sai yanzu yikeyi da Nadiya ? Sam basa jituwa kamar masu ganin cikin juna ,tunani take mai zurfi amma ta kasa gano ina matsalar take daga ƙarshe kawai sai ta yi watsi da tunanin ta shiga sabgar rayuwarta
Nadiya kam tana saka kaya tana kuka wannan wani irin rayuwar yahudanci ne ,namiji yaga tsaraicinka? Ai dole mutum ya bar gidan nan don tsira da mutuncinsa,a take taji ranta ya cushe zaman gidan tama tsaneshi ,a hankali ta soma har haɗa kayanta a akwatinta ta kwashi littafanta ta goya a jakan baya ta jawo ta fito falo ba kowa sai ƙaran AC haka har ta fice wajen tsakar gidan batayi karo da kowa ba har masu aiki.
Adams kamar wanda aka mintsinesa ya zabura ya sauko daga kan gadon jin zai fara mugayen tunanin jaravansa da zasu dawo masa da ciwonsa ,lemon drink da kullum yake reserving Wanda tunda suka haɗu da Nadiya ya manta when last yasha ,shi ya tsiyaya a cup ya fito gaban ɗakinsa ya tsaya ya dafa ƙarfen benen yina kallon tsakar gidan yina sipping.
Ba zato ya ganta saye da baƙar wando falazo da top mai sake tayi rolling da Black veil rataye da jakar baya ga wani ƙaton akwatin kayanta tana ja ,wani yarrrr yaji a ransa yanda yaga ɗuwawukanta sun matse a saman wandon daga ƙasa wandon ya buɗe kamar siket ,atake yaga she look sexy a idonsa ,lumshe ido yayi ya buɗe ya mata ƙuri da ido ,yinason ya dakatar da ita amma yasan sam bazata fuskancesa ba ,sannan a ransa yace "ka kuskura kai mata magana ma zata ɗauka ita ɗin wata tsiyar ce ,gwara ki cigaba da ganawa juna azaba"
Wayarsa ya je daki da sauri ya kira security ya basu umurnin karsu bar Nadiya ta fita ya sama kujera ya zauna yina hango wajen
Nadiya kam juyin dambu da taliya security sun hanata fita dagewa tayi "To wai me yasa nan gidan mu ne,da kun Sanni? To zan tafi gidan mune iyayena sunce in dawo"
"Hajiya ba laifinmu bane umurnine daga sama ,ko kirasa ki tambayesa in ya amince shikenan"
Tsaki ya bashi Amsa ta ja akwatin ta dawo ranta na baƙi ,tana tunanin way out ,ƙurrrr ya kasheta da ido kamar ance ɗago mana suka haɗa ido aikuwa ta banka masa harara , fuskar shanu yayi mata kamar sai yanda yike Amma deep inside daɗi yaji tana wucewa shima ya bar wajen.
Gaba ta ɗauka da kowa har dare ba wanda ya ganta ,in momy ta leƙa sai tayi barcin ƙarya
Suna dinner ne momy ta kalli Adams taga yina cin abincinsa hankali kwance "Sweetheart me kayiwa Nadiya?" Gabansa ne ya bada damm!
Momy tace nayi mata wani abu ne kuma?"
"Kawai tambayarka nayi don na lura kamar fushi take damu " caɓe baki yayi cikin halin ko'in kula
"Ban mata komai ba Ni meye haɗina da wannan gajar ƙazamiyar dama za ta dinga isolating kanta haka to da mun ji daɗi"
"Hummm ba'a zagin mace ,mace tanada power sosai ,kuma akoda yaushe in zakayi wa mutum tsana kayishi a hankali ,saboda karya cutar dakai da yawa"
Ajiye fork ɗin hannunsa yayi
"Mom kina tunanin akwai ranar da ,don naci ƙaniyar waccan dunƙulalliyar ƙatuwar zan dawo inji haushi ..hu'um"
"Aah ha Adams bani a wajen sulhu ina gargadinka" miƙewa yayi ya kurɓi ruwa yayi mata saida safe
Murmushi tayi ta miƙe itama ,taje ta kai little wajen nannynta ,ta dawo ta shiga ɗakin nadiya ,tana zaune tana waya tana kuka ,amma tana jin motsin mutum tayi sauri ta kwanta ,taja bargo .
A sanyaye ta shigo ta haura har kan bed ɗinta "Me nayi maki Daughter ?"
Shiru Nadiya tayi ta ɗauke numfashi saboda karma ta Gane idonta biyu
"Nadiya idan nayi maki wani abu to ki daukeshi bjsa rashin sani,ina sonki sosai kamar maman little ,idan kuma wani yayi maki wani abu shima kizo ki fada mun still matsayinki na daban ne a raina zan ƙwatar maki encinki "
Cikin kuka ta miƙe zaune ta yaye bargon ,saida ta tsorata ganin yanda ta rame in just 1 day
Fadawa cinyar ta tayi ta fashe da kuka
"Mom ki cewa Ya Adams ya ƙyaleni ya fita harkata kinga yau saida yayi mun wankan dole...." Dafe ƙirji tayi "wankan dole? Ya cire maki kaya ya saɓeki da soso da sabulu? A gidan nan ina ciki ake wannan abun ban sani ba?" Yanda ta furgice saida ya bani tsoro
"Aah mom hankadani toilet yayi yasa wani na'ura yamun wankan da ya gama ya hankaɗoni waje" sassanyar Ajiyar zuciya ta aje
"Ohooo na gane to shikenan zan raba tsakaninku ,ba shi ba ke ko?" Jinjina kai tayi Alamar eh
"Tom Angama amma kema zan roƙeki wani Alfarma "
Shiru tayi mata sai daƙwaƙo mata ido da tayi "Plz Nadiya ki ringa wanka ko sau daya a rana ,Adams ya rainaki ne saboda yina ganinki kamar ƙazama ,amma yanda kike jinki big girl dinnan idan kina wanka wallahi sai ya ringa shayin yin maki maganar raini ki gwada tsafta ki gani sai kince na fada maki"
Narai² Nayi da ido "Mom ko nace zanyi tsafta l kasawa nikeyi wallahi nima inason Inyi wankan amma sai inji nauyin jikina sai in fasa kuma ai yanzu inasa turare"
Dafa kafaɗana tayi tana murzawa a hankali "Kinajina ,warin jiki dabam na rashin wanka ,kazalika koda kasa turare rarrabuwa sukeyi ƙamshin turaren dabam tsamin datti dabam ,saidai tunda ya saka maki abunda zai ringa maki wanka inajin komai yazo da sauki ,ki ringa shiga kina daga tsaye zai wankeki ki fito koba shine ba ƙyauya ai yike hanaki ko?" Jinjina mata kai nayi sai kuma naji kunya ,hakuri na soma bata cike da nadama,itakuwa sosai ta ke sake jina a ranta kawai komai nawa burgeta yike "Shikenan a tashi aje aci abinci"
"Uhm uhm mom na fara diating " yamutse fuska tayi cikin rashin fahimta "Fofo zagina yike yinacemun mai ƙiba mummuna ,kuma inacin abinci kamar na kafurai so shi nake so na daina"
"Come on jorrrr wuce muje kici abinci inga gari"
Miƙewa nayi a hankali na bi bayanta ,da kanta ta haɗa mun abinci inacewa tabarshi tana bankamun harara ,kasa ciki na uku nayi naci plate daya gefin kashi daya na cikina kenan na ɗan sha ruwa da lemu na mike na mata saida safe ,na saita alarm na kwanta
[6/21, 12:05] 😘😘😘: 12
Washekari 5am alarm ɗina ya ringa mun kukan zakara ,juyi nayi tayi na kasa miƙewa ,wohoho Ni Nadiya wannan wani kalar masifa ce ,kayi barci 9pm ka tashi 5am duk saboda kar a zage ka? This life no balance. Da wani azababben ciwon kai na farka haka na ƙururuta naje toilet na zauna na zabga tagumi ko kaɗan banason ruwa ya sauka a jikina ,anan wajen na soma gyangyaɗi ,kamar saukar Aradu naji ance "Ki tashi kiyi wanka ki shirin school olodo kawai" firgigit na farka ,kawai sai na dafe kai na yanka ihu ina addu'an shiga toilet duk zatona ,gamo nayi ,Adams dake saye da jallabiya zai shiga Masallaci guntse dariya yayi yina kallonta ta kafan cameran da Aka manna masa da ɗakinta ,wanda ya saita shi in tana wanka ko canja kaya ko wani abu ko ya kalla blank zai gani
A hankali ya latsa jan madallin dazai disconnecting da ɗakin ,ya wuce masallaci ransa fes yasan yanda ya firgitata ɗin nan bata ba saurin barci kuma .
A kiɗime Nadiya take Kallon saman toilet ɗin ,tabbas wannan Muryar ya Adams ne to Aljani ne ? Gashi dai ko ina na toilet ɗin sealed ,sai raga ragan abubuwa da taga an ƙara kuma tasan wannan zai yuwu toilet heater ne dasa sauransu .
Tsaki taja ta cire kayan jikinta cikin wauta ,ta danna inda ta danna jiya amma bai fito da ruwanba ,a hankali ta ke karantar abubuwan A nutse kafin ta tattaɓa wajajen saiko ga ruwa yina mata feshi ta bangwayen ɗakin soson ya fito ya wanketa fes tana gama fita ya hankaɗota waje
Tsaki taja "Na lura wannan na'uran shegene in ya gama mai makon ya kashe kansa sai ya hankaɗoni waje ? ,Zan studying ɗinka kafin ka hankaɗoni sai in kasheka banza kawai"
Gogaggun uniform dinta ta saka ,ta wuce ta shafa turare a jikinta ,nan taga fuskarta ya mata wasakayau ita kanta sai taji ta rage nauyi ,a caji ta makala wayarta ta ɗauki school bag dinta ta fito
Lifter section ta nufa ,tanason kawai yakaita down floor ba tareda taga kowa ba ta sauka saboda batason ma dalilin da zai hada su koda yazo gayar da momy
Ba zato ta ji muryarsa "Ina zaki anan wajen ko salar kije lifter ya bugoki ,ki ja Mana bala'i"
Harara na banka masa na murguɗa masa baki "Nikam in na raina kasuwa shiga cikinta ma banayi,in mutu ma ai ba damuwarka bane ,kuma taya zan san lifter ? Bayan gida babu "
"Ok nima dai Koda naji ,to bi tana normal path ,Wanda gidansu akwai zasu koya maki yanda ake operating ɗinsa a hankali " ya bata amsa cike da gatsali kamar baisan baƙar magana ta jefesa dashiba
Tsaki taja kawai ta danna ya rufeta ta sauka inda zata taje school Bus wanda yanzu ya zama nata ita da little ,takai 15 minutes tana jiran drivern da da su suke jiranta ,amma yau gata da wurwuri ,ɗan duba littafinta ta soma yi ,na rage lokaci kafin daga nan barci ya sureta ,bata farka ba saida taji bude kofar motar little ta shigo ta faɗa jikinta taja mata kunci "Anty kumatu good morning yau kin rigamu zuwa , why?" Murmushi tayi "I wake up early ne shiyasa little,ya akayi kikasan ina nan ,kinje ɗakina baki ganni ba?"
Girgiza kai tayi zaro halshe cikin wasan yara "Fofo ne yace ma momy kinyi breakfast kin tafi school Bus" shiru nayi ina mamakin yanda Adams ya gwanance da ƙarya ,ya sani sarai ban karyaba amma saboda rashin cin abincina da ldi yike masa shine harda girba mun ƙarya?
"Anty ya naga fuskarki yayi wani iri ko Fofo ne ya doke ki" dariyar yaƙe na mata sannan na girgiza mata kai
"Nayi barci kaɗan ne shiyasa "
"To meyasa?" Dafe kai nayi da sauri "little Ina ciwon kai ki shiru " sauka tayi a jikina a hankali ta koma daya siɗe ɗin ƙofar tana kallon waje ,alamu dai taji haushi ,sai kuma naji banji daɗi ba ,a hankali na matsa jikinta
"Kinyi fushine?" Girgiza mun kai tayi ,Banda mood din magana da yawa don haka kawai na ƙyaleta ,saida aka saukeni a school ɗina sannan na tsaya na ɗan rungumeta na bata sumba a saman goshi "Take care baby"
Washe baki tayi har kuncinta na dimpling "bye ...." Da ƙarfi tace "I love youuuu"
"Your anty love you more"nima na bata amsa da ƙarfi ina ɗan tafiya saboda na kusa latti .
Gossip centers ɗin da ɗalibai suke zama anyi cincirindo kamar ba aji ake dashiba by 8am haka na rarraɓa na wuce kamar majununiya ko daga kaina banayi bare inga ko nasan wasu daga cikin student ɗin
Ina wucewa aka soma hirana kuwa ganin Government car ke dropping ɗina kuma in an tashi shi yake zuwa ya ɗaukeni
"Wai yarinyar nan mai take takama dashine kanta na cizga fa ko don taga ita ɗin ƴar governor ne shiyasa take iskanci? An mace barci take ko tazo aji ko?"
Kausar ne tayi tsaki cike da harsada "waya faɗa maku ƴar gomna ne agolace fa ,shishigi ya kaita gidan da a Hostel take zaune yarinyar da a Abuja take...munsan komai ai"
"Ai ashe kice kin santa "
Teemah ce ga carke "Roomy ta ce ɗakinmu daya ,kuma har yanzu in akwai evening class a ɗakin take zama kafin a shiga "
****
[6/21, 12:05] 😘😘😘: 13
Aji naje na zauna acan back seat dama Ni a baya nike zama ,na zauna ba daɗewa barci ya sureni ,har ƙarfe 10am malamin da ya shigo ya fita wani zai shigo ,zafine da yunwa ya gallazeni a hargitse na mike naje da master card ɗina na siyo egg roll biyu da maltina 2 ,zan shiga kenan wata wulakantacciyar malama ta shiga aiko ta hanani shiga ban damu ba na ja gefe na sama cement chair na zauna na cinye tas na shanye malts d'in n'a watsar da gwangwanayen ,nayi miƙa na ɗan jingina a jikin body ɗin kujerar na fara hamma zan barci naji an dafa mun kafaɗa ta baya ,tsaki naja na hau masifa saboda da fari na tsorata "Dayallah waye ,in zakai magana da mutum sai bazaka fuskanceshi ta gaba sai ta baya " fara'a tane ya dadu ganin umma ce "Laaa ummu kin ɓace"
Zama tayi jiki a sanyaye tana mun kallon tausayawa "wai lafiyarki"
"Nadiya kinga result kuwa?" Yamutse fuska nayi cikin rashin fahimta " "Result ? Wani result anyi jarabawa ne a makarantar nan?"
"Au baki san ana mana jarabawar tantancewa ba ,to duk wainnan tests din jarabawa ne gayi can alika wanda sukaci fail sai suma sukeyi,saboda in kaci fail ,yina nuna next in za ayi asalin semester exam da wuya ba koranka za'ayi ba" jan tsaki nayi "to saboda jarabawa sai su suma halan jarabawar lahira ne ,Ni wallahi kin bani haushi ma,hope dai kinci "
"Naci kije ki duba naki "
"Baida amfani tun da nasan tests uku nayi ,baki snapping result din a waya ba in Gani" girgiza mun kai tayi "presdo dinmu yina nemanki"
"Me zan masa?"
"Nima ban sani ba"
Tsaki naja,na cigaba da harkata result ɗin da ban sake bi ta kansa ba kenan ,saidai gabaɗaya nature din ajin ya canja malamai sukazo aka zage en ajin tasss wai ba'a taɓa daƙiƙai irin wannan batch dinba nidai kam ko a jikina ,ana tashi na sunkuci jakata nayi gida
Da sallama na shiga,suna zaune ita da ya Adams "momy good evening" Kallon tausayawa tayi mun ta buɗe hannunta ,alaman inzo ta rungumeni ,da sauri na fada jikinta ta rungumeni tsam tsam "Sannu kinji duk kin rame a fuska dress up azo aci abinci yau nasa anyi maki girki mai nauyi nasan kin kwaso yunwa" ɗan murmushi nayi "thank you Mom" na gyara zaman jakata nawuce saɓal saɓal jikina na ɗan rawa saboda ƙiba . Ko kallonsa banyi ba ,kasa jurewa yayi saida ya daka mun tsawa "Keeee!" Ya ƙwalla mun kira sosai naji sunan a raina ,amma na cigaba da tafiyata "Keeee dake nike ko sai na kiraki da daƙiƙiya tankwala ,mai ɗumama benci anje an kwaso na kwantan baya ,wannan wani iriyar daƙiƙanci ne ace acikin daƙiƙan da suka faɗi wanda suke ta suma kece makinki yafi na kowa muni? Gaskiya Ina tausaya maki " cak naja na tsaya maganarsa bai dameni ba ya tankacin zagi
"Momy kin ganshi ko? Wai kai ina ruwanka da rayuwata shishigi ba kwarjini shiga kabari da kwabashu"
"Hmm dama Ni me yayi ruwana da daƙiƙiya momy ina fada maki wannan yarinyar tankwala ne kin kasa ganewa" juyowa nayi kawai saiga wasu hawaye suna tsiyayo mun a ido ,a take jikin mom yayi sanyi ta faɗa sa da masifa dukda taji haushin falling din da nayi kuma ita ta sashi ya caccakeni ko nayi serious Ashe zai mun zagine har hakan
"Nagode ka cigaba da zagina Ni ba daƙiƙiya bane ,kuma ai wannan ba jarabawa bane , fisabilillah na daina barcin da nikeyi silar hakan sai ciwo nikeyi ban cema kowa komai ba ,na daina cin abinci silar hakan en hanjin cikina sai kuka sukeyi still ban ƙorafi ba sai takan wani banzan jarabawar Nursing? Had it been architecture ne yawwa is my fav. Dole zan gane nasan in banzo na farko ba zan kasance a top ten..."
"Wooooohoooo yi Mana shiru daƙiƙiya wuce" yayi mun irin abinda ake ma yaran nan irin koran nan mai cin rai
Jinjina kai nayi na ɗauki jakata na wuce ɗaki ,ina shiga wayata na ɗauka in kira mamata ,na bar momy tanata masa masifa
Missed calls na gani tururu a wayata har da baƙin numbers juya wayar nike ina tunanin ta wanne zan fara kira ,wani kiran ne ya shigo wayata ,a sanyaye na ɗauka na kanga a kunnena raina a ɗatace
"Assalamu Alaikum"
Ban amsa sallamar ba sai a ƙufule nace "waye"
"President din makarantar kune"
"Lafiya?"
"Mun hada tutorial class ne na ku da kuka fadi za'a ƙara dandaƙe maku karatu yanda zaku samu damar cinma en uwanku na aji kar ayi jarabawa a koreku gashi the worse part din kece na baya "
Tsawa na daka masa "kai Dalla yimun shiru ,kai ka kawo Ni makarantar ? To in fadin ina ruwanka ? Ni ban iya karatu a cikin mutane da yawaba ,sam bazaka ɓata mun ƙwaƙwalwa ba mtsewww banzayen mutane ƙwarzababbu sai kace a kaina aka fara faɗuwa"
Na kashe wayar ma gaba ɗaya ba tareda najira mai zai ceba na koma na kwanta raina a ɓace
****
Month later
A wannan ritsitsin na samu walwala saboda Ya Adams yayi tafiya ,kuma mamana da Anty Nusaiba sunzo sun duba Ni sun kuma bani psychological reassurance ,sannan little tana ɗebe mun kewa ,saboda haka koda aka liƙa time table ɗin jarabawa banji na damuba ,na bi na samu kaf takardun mutane nayi photocopy ganin ana kwanan karatu a makaranta ,na roki momy ta Barni inzauna a Hostel kafin mu gama jarabawa zanfi karatu ,ba ja ta amince saboda itama tanaso in dage kuma karatun gida bai kai na makaranta ba ,A haka na soma TDB ,cofee mai ƙarfin gaske nike cakudawa da madara da suga sai in cika a feeding flask in na zauna a kan kujera dangwargwam har safe idona a soye ina karatu a masallacin department dinmu ,duk masu karatun nan tsorona suka faraji yanda zasu gaji da karatu suyi barci su Barni a zaune,sai in hardace handout biyu uku kafin gari ya waye ,safe nayi suka fara group discussion haka zan ringabin ƙungiya ƙungiya ina gallazarsu duk abinda na hardace sai nayi vomiting ɗinsa out ,saluting din ƙwaƙwalwata sukeyi shiyasa ake cewa bakasan capacityn kowa ba ,wato Ni ba karatun understanding nikeyi ba kamar na sauran masu tunani da suke son yin aiki ba ,A'ah Ni hardacewa nike wato inje in