Author : Zahra Muhammad Surbajo Category : Arewa Pen
rai da rayuwa seta ɗauko fansar mahaifiyarta,akanku tunda abun naku ba mutunci"cewar inna tana share hawaye.
"inna kiyi haƙuri ni bada wata manufa nace haka ba gaskiya kawai na faɗa miki,kuma Aisha tace maryam taba deeyanah,duniya da lahira,dan haka kiyi haƙuri don Allah ki kwantar da hankalinki"Abubakar ya faɗi hawaye na biyo idanunsa.
"au ita Aishan ina raye zatai kyautar ƴar bata ban ba to bakomai ga ƴarku nan habubakar"ta ajiye deeyanah ta juya ta bar gurin.
Duk yadda Abubakar yaso bata haƙuri amma taƙi yarda,haka ta bar gidan tai tafiyarta.
Abubakar dawowa yayi ya ɗauki deeyanah yashiga mota ya nufi asibitin da maryam ke kwance wacce a yanzu tana amfani da dukka hannunta ƙafarce de har yanzu da saura.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[6/6, 11:32 AM] Zulaihat Musa p: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Na kuɗine ki biya kamin ki karanta min,in kika karanta baki biyani Allah yasaka min*
*Zahra Muhammed Nasir 2084024749 UBA*
*A turo shaidar biya tanan,ɗari biyar ne kacal 07044600044*
*21*
Maryam lokacin da Abubakar ke shaida mata wasiyyar da Aisha ta bari na bar mata deeyanah kyauta,rasa inda zatasa kanta tayi dan farinciki yayinda gefe ɗaya kuma rashin Aishan ke taɓa zuciyarta,dan har zuciyarta take son Aishan.
Amsar deeyanah tayi ta rungume ta fashe da kuka,da kyar Abubakar ya rarrasheta,cikin muryar wanda yay kuka Maryam tace"komai nada dalilinsa ashe Aisha ta shigo rayuwarmu da gaggawane sabida bazata jimaba,ta shigo rayuwarmu ta bamu farinciki da bamu da bakin godiya sede mu bita da addua"ta ƙarasa maganar tana share hawayenta.
Rungumeta yayi ya sumbaceta a goshi,har ranshi mutuwar Aisha ya taɓa wani sashi na rayuwarsa,sabida Aisha ba macen da ake saurin maye gurbinta da wata bace.
Maganin ruwan nono maryam tasa anemo mata,ayko haka akai ta kawo mata kuma cikin hukuncin Allah nonon yasamu ta fara shayar da deeyanah,wannan abu ba ƙaramin faranta ran Abubakar yayi ba.
Kwanci tashi maryam ta samu sauƙi har an sallameta ta dawo gida,koda ta dawo sosai take kukan rashin Aisha bada wasa ba.
Deeyanah ta taso cikin gata da kulawa irin ta uwa mahaifiya,maryam na sonta har ranta ko kaɗan bata son damuwarta,
Shekarar deeyanah ɗaya amma zaka ɗauka takai biyu,gudu take ko ina,
Shekarar ta biyu maryam ta yayeta,lokacin Abubakar yasamu ƙarin girma zuwa mataimakin supeto ganar arziƙi ya ƙaru deeyanah sosai take ganin gata bada wasa ba.
Kaita suka shirya zuwa kaiwa inna ziyara,dan tun bayan rasuwar Aisha bata sake zuwa ba,sede Abubakar yaje shima da faɗa suke rabuwa,dan ta kafe se ya kawo mata deeyanah mafarkin Aisha takeyi.
Sun isa kaita lafiya,ko kaɗan maryam bata samu karɓuwa agun inna ba,se habaici take mata,kan ta kashe kishiyarta,
Maryam bata iya kare kanta sede zuciyarta na mata zafi Abubakar ke rarrashinta,
Satin su guda akaita sukayi shirin komawa,nan ko inna tai tsalle ta dire se an bata deeyanah.
Zo kuga kuka gun maryam kamar an mata mutuwa,tsugunawa tayi gaban innar tana kuka tace"kimin rai inna bazan iya rayuwa me daɗi ba ba deeyanah,kitausayamin don Allah inna karki rabamu"
"wallahi ko mutuwa zakiyi sede ki mutu amma jikata tazo kenan bazata koma ba"cewar inna lokacin data kwace deeyanah a hannun maryam.
Abubakar ya rasa me zece kawai hannun maryam ya kama ya ɗagata,yafara janta su tafi ayko nan fa ta shiga kuka iya ƙarfinta tana zillewa itama deeyanah kuka take tana miƙawa maryam hannu tana "mummy na"cikin kuka.
Abubakar cak ya ɗaga maryam yayi mota da ita,da ike da direba suka taho,suna shiga direban yaja suka bar ƙofar gidan.
Maryam har lokacin kuka take iya ƙarfinta.kamin suzo kaduna tuni jikinta yayi zafi,dole asibiti yasa suka wuce,
Gwaje gwaje aka mata inda gwajin farko likitan yay musu albishir da cewa tana da ciki har na tsawon watannin uku.
Daga Abubakar har maryam jin abun suke kamar a mafarki murnar da sukayi bazata faɗu ba.
Wannan shine maƙasudin riƙon diyana daya koma hannun inna,inda tayi iya ƙoƙarinta ta cire son maryam da IG a zuciyar deeyanah kamar yadda tasha alwashi.
har zuwa yanzu da maryam keda ƴaƴa biyar,ba abinda ya sauya,duk da maryam ta samu nata ƴaƴan amma hankalinta nakan deeyanah kullum seta yiwa IG maganarta.
*CIGABAN LABARI*
Cikin sheshsheƙar kuka inna tace "kinji gaskiyar abinda ya faru abaya deeyana duka nayine bawai dan ban sonki ba,so ne yasa hakan deeyana"cewar inna tana fyatar majina.
"kin cutar da mahaifiyata inna hakan be gamsar dake ba seda nima kika cutar dani,"cewar deeyana tana kuka.
"haba deeyanah ta taya zan cutar dake?"inna ta tambaya tana kuka.
"Kin cuceni mana inna da mahaifiyata kika rabani da ita,baki barni nasamu ladan biyayya ga uwata ba meyasa inna?"ta tambaya cikin ƙaraji.
"mahaifiyarki ta mutu Deeyana ko baki fahimci labarin dana baki ba"cewar inna cikin yanayi na firgici.
"ƴarki ce ta mutu a duk labarin da kika bani inna banji inda kikace mamana ta mutu ba"cewar deeyanah tana kuka.
"Deeyanah Aisha itace ta haifeki kuma ta mutu"
"bani da mahaifiya sama da Maryam inna,Aisha ƴarki ce,Allah yajiƙanta,amma uwata maryam ce ta shayar dani inna menene ake kira da uwa,?in baki san maanar kalmar ba ki dubi maryam itace maanar sunan uwa,inna nayi danasanin duk abinda nakema mummyna batare da sanina ba,kuma inde dan ni kike zaune a gidannan inna ki tattara ki tafi,matar da bata kasheni ina tsimman goyoba bazata kasheni lokacin dana isa moruwa ba inna,kitafi ki barmu mu sami fahimta da shaƙuwa tsakanina da iyayena,zamanki cikimu takurace inna"deeyana ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka.
Inna ta kasa cewa komai se kukan nadama da take tayi,deeyanah ta juya mata baya.
Itako deeyanah dataga zaman gun inna baze fishsheta ba da gudu ta tafi zuwa falon hajiya maryam dan ta nemi gafarar ta.
Muje zuwa agyara zama yanzu ƴan wasan zasu dunga bayyana ɗaya bayan ɗaya,har maana da sunan littafin ya bayyana.
Surbajo for life.
[6/6, 11:33 AM] Zulaihat Musa p: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*karki karantamin batare da kin siya ba,500 ne,inkin karanta kuma ke da Allah*
*Zahra Muhammed Nasir 2084024749 UBA*
*A turo shaidar biya tanan 07044600044*
*22*
Zaune suke a falo IG na matsawa Hajiya ƙafafunta suna hira cikin kwanciyar hankali,tayi sallama ta shigo falon.
Babu wanda beyi mamakin ganinta ba,hajiya maryam a ruɗe take faɗin"deeyana dear me yasameki a fuska naga ta kumbura,"ta tambaya cikin kulawa.
Daga inda take tsaye ta fashe da kuka,ta ruga da gudu jikin hajiya maryam,ta rungumeta tana kuka,sosai kukanta ya kiɗima hajiya maryam,duk da ciwon da jikinta ke mata sakamakon faɗuwar da tayi ɗazu,amma ƙoƙarin kamo ta takeyi,duk ta ruɗe ganin deeyana na kuka.
"mummy ki yafemin don Allah ki gafartamin nagano gaskiya,kuyi haƙuri keda daddy ku gafarceni wallahi rashin sanine"cewar deeyanah cikin matsanancin kuka.
Wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar IG da ta hajiya maryam,lalle sun yarda Allah baya zalunci se wanda ya zalinci kansa,wai yau deeyana ke neman yafiyarsu kan ta gano gaskiya,rungumeta hajiya tayi tana faɗin.
"na jima da yafe miki deeyanah dear,uwa ay bata riƙe ɓacin ran ƴarta a zuciyarta,farincikina ɗaya deeyanah ta ta da ta dawo gareni"cewar hajiya cike da farinciki.
IG ma murmushi kawao yake da ke nuna alamun jin daɗinsa Dan aduniya deeyanah da inna ne kawai matsalarsa,kuma yanzu Alhmdllh tunda deeyanah tata matsalar ta kau.
Shima yafiyarshi ta nema kuma take ya yafe mata gami da sa mata albarka,
Ranar tare da mummy ta kwana,rungume da ita,ita kanta mummy batasan tayi kewar ƴar tata ba se yanzu da take kwance gado ɗaya da ita.sosai take godewa Allah daya dawo da ƴarta gareta.
Rayuwa me cike daso da ƙaunar juna deeyanah da sauran ƴan uwanta da mahaifiyarsu suke gudanarwa acikim gidan,wanda hakan sosai yake faranta ran IG.
Inna ko bata shiga sabgarsu sabida ita har ranta bata son hajiya maryam,shiyasa ko deeyanah dake hulɗa dasu yanzu take ɗaukar abin a mazaunin asiri maryam tayo ta rabata da deeyanah.
Suna wannan halin ne hutun deeyanah ya ƙare ta koma makatanta cike da kewar hajiya maryam da sauran ƙannanta.har kuka tayi da taga dare yayi bata gansu ba.
Jameela ma sosai tai murna da komawarsu makarantar,dan ta ƙosa dama su haɗu da deeyanah akwai tarin maganganun da takeson sanar da ita.
Yau da wuri aka tasosu daga class dan haka hostel kai tsaye suka wuce,wanka sukayi sukaci abinco sannan jameela taja hannun deeyanah zuwa cikin lambun hostel ɗinsu inda keda ƙarancin ɗalibai suna zama deeyanah tace.
"wai ƙawata meyene tun muna class kika damu da mu taso,duk kin ɗagamin hankali"cewar deeyanah tana diban jameela.
Cikin yanayin damuwa,jameela tace"ƙawata ina cikin damuwane sabida mahaifiyata da sauran ƴan uwana duk acikin damuwar suke"
Cike da kulawa da nuna tausayawa deeyanah ta ruƙo hannun jameela tace"wacce irin damuwace wannan ƙawata da zata ɗaga hankalinku gaba ɗaya?"
Ajiyar zuciya jameela tayi sannan tace"mahaifina shine sarkin garinmu me daraja ta ɗaya,mahaifiyata itace matarshi ta farko,kuma ƴaƴanta goma dashi biyar maza biyar mata,se kishiyarta ita kuma ɗanta ɗaya,kuma yayyena maza uku ma sun girmeshi,shine mahaifinmu yace shi zeyi murabus ya ɗora yaron kishiyar maman nawa,bayan ga yayyena da suka girmeshi,wannan shine abinda ke damun mu deeyanah kuma ke kaɗai zaki iya taimakamin in rusa wannan magana ta mahaifina"Jameela ta ƙarasa maganar hawaye na biyo idonta.
Cikin yanayin ban mamaki deeyanah tace"ni kuma jameela?tay zan iya taimakonki kan abinda yafi ƙarfina ba ikona ba bana mahaifina ba?"cewar deeyanah tana ware ido.
"deeyana kina da kyau matuƙa,Allah ya kyautata surarki ta yadda duk namijin da ya ganki zeso ko yaudararsa ce ma kiyi,"ta ƙarasa maganar tana kamo hannunta.
"look jameelah kin barni a duhu ki fitomin a mutum insan inda kika nufa pls"cewar deeyanah cikin yanayin dake nuna ƙosawarta.
"so nike in anyi hutu kizo gidanmu ku haɗu da ya hydar so nike in ya ganki ya kamu da sonki ta yadda zaki bashi umarnin ke bakya son yayi sarauta yacewa mahaifinmu baya so"cewar jameela cike da zullumin me deeyanah zata ce.
Muje zuw
Surbajo for life.
[6/6, 11:33 AM] Zulaihat Musa p: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*na kuɗine ki biya kamim ki karantamin 500,in kuma kika karanta min baki biyaba na barki da Allah*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*A Turo shaidar biya tanan 07044600044*
*Masu buƙatar a tallata musu hajarsu zasu iya yimin magana akan farashi me sauƙi*
*23*
Dariya deeyana keyi harda hawaye kamim ta natsu tace,
"amma jameela gaskiya kanki da motsi aciki,taya ni zan iya hana bada sarauta,karfa ki manta abincin wani gubar wani,in wasu zasu soni dan kyauna,wasu a me aykinsu ma bazasu yarda dani ba,kinga mubar maganar nan,kisa haƙuri kawai azuciyarku shi Allah ya zaɓa shiyasa yabasa,haka ya hukunta,ja da hakan kuskurene"cewar deeyanah cikin yanayin dake nuna zancan na jameela be samu karɓuwa agurinta.
Ran jameela yayi matuƙar ɓaci dan bata ɗauka deeyana zata watsa mata ƙasa a ido ba amma a fili se tayi yaƙe tace"haka ne deeyana to Allah yasa mudace"
Ta amsa mata da "Ameen ƙawata"tana murmushi.
Tun daga wannan lokacin jameela ta ƙudiri aniyar sa rayuwar deeyanah cikin garari,amma ko so ɗaya bata taɓa nuna mata a fili ba.
Rayuwa suke kamar ba komai aranta har zuwa lokacin da suka kammala makaranta,inda a wannan lokacin sun ƙara zama cikakkun ƴanmata,dama jameela ta girmi deeyanah da shekaru uku,
Deeyanah Abubakar Adamu Kaita,matashiya me jini ajika ƴar kimanin shekaru goma sha bakwai,fara ce data sirka da ja,hakan yaba fatarta damar yin kala ta musamman,ita ba doguwa ba ita ba gajera ba,maana medium size,tana da diri na kuzo ku gani,ga shafaffen ciki da mara,ga fararen idanuwa,manya wanda take yawan lumshesu kamar tana jin bacci,bakinta ɗan madaidaici ɗauke da laɓɓa masu tudu da taushi,koya ta motsa bakinta gefe da gefen kumatunta na lotsawa,da zaran tayi murmushi ko dariya kyakkyawar wushiryar dake tsakanin fararan haƙoranta na bayyana,wanda hakan ke ƙara mata kyau,ga gashi baƙi me tsayi da sheƙi da taushi.kai abun se wanda yagani.
Zaune suke a falo ita da mummy tayi matashin kai da cinyar mummyn,cikin shagwaɓa tace "nummy nifa wlh,ba na son BUK gaskiya," ta faɗi tana turo baki gaba.
Dariya mummy tayi ta shafo gashin kanta tace"kin cika rigima deeyanah,tunda mahaifinki yace ita zakiyi base kiyi biyayya ba,ni banason gardamar nan taki,meye aybun BUK ɗin"
Miƙewa zaune tayi sannan tace"mummy bata da aybu,ni kanon ne tayimin nisa wallahi,bazan iya jure tsayin lokaci ban ganki ba"ta ƙarasa maganar hawaye na biyo idonta,
Sosai tausayinta ya kama mummy,janyota jikinta tayi ta rungume,sannan tace cikin sigar rarrashi"karki damu,muna tare deeyana dear a waya,kuma zan dinga yawan zuwa ganinki,"
"mummy bafa wanda nasani a garin,taya zan rayu ni kaɗai se escote?"
"Kede akwai shashanci, ita hajiya umman fa,ko bazaki dinga zuwa gunta ba?"
"Mummy kince fa gidan sarautane gidan kar inje amin kallon banza ni ko wallahi banda haƙuri ramawa zanyi,shiyasa ma banason zuwa"cewar deeyanah wacce har yanzu bakinta ke ture agaba.
"Hajiya Umma yayatace bazata wulaƙantamin ke ba ko kin manta kema ƴar waye,the whole IG na ƙasarki shine mahaifinki,har akwai wanda ze miki kallon banza"
Dariya deeyanah tayi dan tana alfahari da mahaifin nata bada wasa ba,shiyasa koya aka dan gantata dashi take tsintar kanta cikin farinciki.
Da haka mummy ta shawo kanta ta amince da tafiyarta jamiar Bayero dake kano,cike da kwarin guiwa.
muje zuwa
Wacce bata siyaba kibata shawarar ta siya dan littafinmu ya ɗauko hanya.
Surbajo for life
[6/6, 11:33 AM] Zulaihat Musa p: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*meso ki turo kuɗinki 500 na kuɗine karki karantamin in baki biyaba,inkikayi na barki da Allah*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*A turo shaidar biya tanan 07044600044*
*24*
Duk wani shiri da tanaji IG ya gama yiwa deeyanah na tafiyarta makaranta,ba abinda baa tanadar mata ba,gidan da zata zauna masu tsaron lafiyarta da direban daze dunga kaita ya dawo da ita.duka a unguwar nasarawa GRA dake kanon.
Da kuka suka rabu da mummy dan wannan karon IG ne da kanshi yace ze rakata dan yana so daga can ya wuce kaita yaga ginin da akewa inna,wacce ya shawo kanta da ƙyar ta yarda ya gina mata gidan.
Sun iso kano lafiya,inda suka samu tarba ta musamman daga sauran mahukunta,rakiyar girma aka yiwa deeyanah zuwa makarantar inda hakan sosai ya ɗauki hankalin sauran ɗalibai,ciki harda jameela ƙawa ga deeyanah,wacce itama makarantar ta shiga.
Bayan angama komai IG ya barta tare da masu tsaron lafiyarta shi ya wuce,sosai deeyanah tai kewar mahaifin nata.
Tana tsaye tana tunani taji ance "kamota nan"daga bayanta.
Da sauri ta waiga,carab tao ido biyu da jameela ayko wani ihun murnar ganinta ta saki sannan suka rungume juna.
Sosai deeyana ke murnar ganin Jameela,dan gaba ɗaya ji tayi damuwarta ta kauce.
"ƙawata ya bayan rabuwa,wallahi numbar mummy da kika bani a hanya ta faɗi,kuma ina ta so in mun shigo Abuja innemeki wlh Allah be nufa ba"cewar Jameela lokacin da suke takawa zuwa gurin wasu kujeru,yayinda ƴan sandan dake tsaron lafiyar deeyana ke binsu a baya.
Bayan sun zauna ne deeyanah tace"wallahi kullum cikin jiran kiranki nake amma shuru baki kiraba,gashi ni banida numbarki,haka na haƙura sabida kinga time ɗin bamu da phone namu"cewar deeyanah tana murmushi.
"ke dai bari ƴar uwa wallahi nayi kewarki,yanzu ina kika sauka?"jameela ta buƙata.
"wani gidan daddyna dake nasarawa gra nan na sauka,"cewar deeyanah.
"lah to ay muma unguwar muke,kai amma naji daɗi sosai yanzu tunda ba abinda zamuyi muje inga gidan naki in yaso gobe tunda ba school se kizo namu gidan ko?"inji jameela tana ruƙo hannun deeyanah.
Ayko cike da nishaɗi suka rankaya,zuwa gidan na deeyanah,matsakaicin gidane me ɗakuna uku,se kitchen da ɗan garden se masu gadi da dattijuwar da zata dinga yimata abinci,se ƴar matashiya me suna laraba dake mata wanke wanke da shara da gyaran gidan.
Sosai jameela ta yaba da gidan na deeyanah,inda seda taci abinci tukuna tayi mata sallama ta tafi gida bayan sunyi musanjen phone number.
Washe gari da yamma deeyanah ta shirya tasa direba yakaita address ɗin da jameela ta turo mata.
Tayi matuƙar mamaki da ganin girman gidan nasu jameela,kanta be ƙara kwancewa ba seda suka shiga cikin gidan.
Sosai tsarin gidan da girmansa ya burgeta,se bi take da kallo,har aka kaita ɓangaren mahaifiyar jameelan.
Murna da farincikin da jameela keyi na ganin deeyanah ba'a magana.gurin mahaifiyarta ta kai ta,ga mamakin deeyanah setaga ashe mahaifiyar jameelan itace hajiya umma yayar mummynta,dan tasanta farin sani itama kuma tasan deeyanar.
"wa nake gani kamar deeyanar maryam?"cewar hajiya umma tana riƙe baki.
Da sauri deeyana ta ƙarasa jikinta ta rungumeta tana faɗin "nice mama,dama jameela ɗiyarkice?"
Rungumeta hajiya umma tayi sannan suka samu kan kujera suka zauna,hajiya umma tace"ikon Allah kice ku duk ƙawancen naku ma bakusan kuna da alaƙa ba dan shashanci bari inkira maryam ɗin ince naga ɗiyata agidana"ta ƙarasa maganar tana dariya gamida danno lambar hajiya maryam.
"gani ga deeyanah agidana yanzu haka,wai ashe sunsan juna da jameela tunda jimawa"
"au wai dama jameelar datake shaidamin dama tamu take nufi? ikon Allah bata yadda be faruwa"cewar hajiya maryam daga ɗaya ɓangaren.
Daga haka hira suka ɗan taɓa wacce rabinta akan jameela da deeyanar ne,daga bisani sukayi sallama.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka cika gaban deeyanah da kayan maƙulashe,jameela ko yaƙe kawai takeyi,dan ko kaɗan bataso ace akwai wata alaƙa tsakaninta da deeyanar ba,amma duk da haka bazatai wasa da damarta ba dole ta ida nufinta akan deeyanar.
Koda dare yayi hajiya umma hana deeyanah tafiya gida tayi dole ta kwana agidan.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[6/6, 11:33 AM] Zulaihat Musa p: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*ki siya ki biya ki karanta 500 ne kacal ba tsada,yafi asato abaki ki karanta na Allah ya isa*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*Aturo shaidar biyan tanan 07044600044*
*25*
Ga al'adar yarima hydar duk safiya yana shiga sashin hajiya umma ya gaisheta sannan ya shiga gun mahaifiyarsa.
Yauma da misalin ƙarfe goma na safiya ya shigo cikin ƙasaitarshi da cikar halitta ya shigo gaisheta.
Lokacin duk suna zaune a tsakiyar falon kan tabarmar ledar cin abinci suna karyawa,
Rusunawa yayi agaban hajiya umman kanshi a ƙasa yace cikin muryarshi me ɗaukar hankali"barka da safiya ummana"
Saura kaɗan deeyanah ta kware,sabida saukar muryarshi a kunnenta,dan bataga shigowarshi ba kanta na sunkuye tana cin abinci.
Bin shi tayi da kallo wanda shi bemasan tanayi ba,kanshi na ƙasa,cikin halin ko in kula hajiya umman tace "barka de yarima"daga haka bata ƙara cewa komai ba,
"zamu fita ummana asa mana albarka"cewar hydar kanshi a ƙasa cikin tsantsar biyayya.
"Allah mana"hajiya umma tace tana doka masa harara,
Miƙewa yayi a hankali ya gyara alkyabbarsa ya juya cikin takunsa na ƙasaita ya fice daga falon.
Deeyanah ko kasa ci gaba tayi da cin abincin, dan gaba ɗaya wata kasalace ta sauko mata sakamakon ganin hydar da tayi,ta kasa gane wanne yanayi ta shiga ne,bazata iya cewa ga abinda take ji ba,haka taita juya cokalin acikin abincin batare data ci.
Jameela wacce duk abinda deeyanar takeyi akan idonta ya faru,wani farin cikine ya kamata dam taga haƙarta zata cimma ruwa cikin sauƙi.
Haka suka gama cin abincin deeyanah babu ƙwarin jiki a tattare da ita,ta koma ɗaki ta kwanta.
Jameela ce ta shigo ɗakin ta taɓota tace"ya de ƴar uwata,naga tunda kikaga yaya hydar duk yanayinki ya sauya,ko da wata matsalane in sanar da umma"cewar