Author : Mansur Usman Sufi Category : Hausa Read
za
a gabar da bikin bauta zaka sha mamaki da idanunka, na mai tabbatar maka da cewa a ranar
zai zamto gawa dama dukkanin wanda ya kwaɗaitu da shiga addinin shi.
Sa'adda da muryar ta zo dai-dai nan azancen ta sai matsafi Shamrul ya cika da matuƙar
farin ciki ya sake yin sujjada a karo na biyu ga gunki Zallas. Sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin
bautar.
Wannan shi ne abin da ya faru da matsafi shamrul bayan ya rabu da yaro Imran.
Lokacin da su sarkin yaƙi Darusu suka cigaba da tafiya a cikin birnin Istanbul ɗauke da
sarki Lazwar, ɗaure a kan doki cikin halin suma sai suka ci gaba da tafiya babu sassauci, tafiyar
daƙiƙa latalin kacal kaɗai su ka yi suka iso kofar gidan sarautar birnin.
Gidan sarautar yakasance mai dogayen gine-ginen zamani masu ƙayatarwa, koda isowar
su sai waɗansu irin girɗa-girɗan samudawan dakaru dake shirye cikin gagarumar shigar yaƙi
suka wangame makekiyar ƙofar shiga.
Inda za'a sanya katti majiya ƙarfi mutum saba'in ba za su iya ture kofar ba,
Kai tsaye Sarkin yaƙi Darusu ya kunna kai izuwa ciki dakarun shi na biye da shi, duk inda ya
gifta a cikin gidan sai di ka ga dakaru, kuyangi, barori, bayi na zube ƙasa suna kwasar gaisuwa
a gare shi
Daga cikin gidan sarautar ya kasance ƙasaitacce tamkar aljannar duniya, babu wata
halitta walau mutum ko aljan da za ta tsinci kanta a cikin wannan gida face ta tabbatar wa da
kanta cewa gaba da gaban ta aljani ya taka wuta.
Shin yanzu idan har gidan sarautar birnin Istanbul ya kasance haka to ya y turaka, da
fadar sarki Ladiyas za su kasance.
Tambayar da gimbiya mashlira ta yi wa kanta kenan wacce ta saje cikin dakarun ba tare da
an gane ta ba
Aka cigaba da tafiya har aka iso wani ɓangare a gidan sarautar, kawai sai sarkin yaƙi
Darusu ya yi umarni aka shigar da sarki Lazwar izuwa ciki sannan ya dubi waɗansu dakaru
mutum biyar daga cikin su ya ce da su "ku tsaya anan har izuwa lokacin da wannan baƙon
jarumi zai farfaɗo, ku tabbatar da cewa wani abu mai taɓa lafiyar shi ba". Koda gama faɗin hakan sai sarkin yaƙi Darusu ya juya ya nufi hanyar da za ta fitar da shi daga
gidan sarautar sauran dakarun suka mara mashi baya.
wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a lokacin da su sarkin yaƙi Darusu suka
ɗauke shi a cikin halin suma.
Al'amarin abokan tafiyar sarki Lazwar sarkin yaƙi da bawa Shamsal kuwa, koda ficewar su
daga masaukin sai sarkin yaƙi ya dubi bawa Shamsal ya ce dashi "wai kuwa me ka fahimta
game da hadima khadijat akankallon da naga tana yi maka?
Koda jin wannan tambaya sai Shamsal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu, daga can sai ya
ɗago da kanshu ya dubi sarkin yaƙi ya ce "ya sarkin yaƙi ka yi sani cewa haƙiƙa ban fahimci
wani abu ba game da kallon da khadijat ke yi min ba,
sai dai a lokacin da muka haɗa idanu na ji zuciyata ta buga da ƙarfi".
Da jin wannan batu sai sarkin yaƙi ya yi murmushi ya ce "ai kuwa dukkanin ku kun faɗa
tarkon so ne ba ku sani ba, lallai nan da wani lokaci za ku cigaba da kasance a kogin
SOYAYYA, amma wani hanzari ba gudu ba kai a yanayin da kake kallon khadijat kana ganin
cewa halin talauci ne ya sanya ta yin aikatau a ƙarƙashin sarkin kasuwa Sha'aran? Jiki na ba ni cewa tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari a tare da ita.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai bawa Shamsal ya yi shiru karo na biyu sannan
ya dube shi ya ce "tabbas maganar ka akwai ƙamshin gaskiya a ciki, domin a lokacin da muka
sauka a rumfa su muna cin abinci na ga kallon da khadijat ke yiwa yaro Imran ya zarta misali.
Bisa nazari da nayi haƙiƙa kallo ne mai ɗauke da tsantsar tausayi irin na 'yan uwa na jini. Amma
dai ko ma dai mene ne komai zai bayyana domin masu iya magana na cewa, komai nisan jifa
ƙasa zata faɗo, kuma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe.
Sarkin yaƙi ya ce "tabbas zancen ka dutse ya abokina";
Daga wannan furuci ne kowannen su ya yi shiru.
Wannan shi ne abin da ya faru da tsakanin sarkin yaƙi da bawa shamsal a masaukin su.
Al'amrin yarinya Shuraiba kuwa lokacin da gimbiya Lamrat ta ɗauke ta a cikin keken dokin
ta suka durfafi hanyar da zata sada su da gidan sarauta, sai ya zamana cewa duk inda suka
gifta a cikin birnin Istanbul sai dai ka ga jama'a na faɗuwa ƙasa suna gaisuwa tamkar za su yi
mata sujjada. Haka dai aka cigaba da wannan tafiya har aka iso ƙofar gidan sarauta aka kunna kai izuwa
ciki.
Bisa wani ƙasaitacce ɓangare da yafi ko ina ƙawatuwa a gidan sarautar, keken dokin ya sauke
su gimbiya Lamrat, kai tsaye ta kutsa kai izuwa ciki, hannun riƙe da na yarinya shuraiba dakaru
na take mata baya, ɓangaren cike yake da kuyangi, barori, hadimai da bayi suna ta kai komo
suna ta hidima. Nan fa ya zamana cewa yarinya Shuraiba ta zamto cikakkiyar 'yar ƙauye, ta kama
kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni.
Wata kyakkyawar budurwa daga cikin kuyangin ta rugo izuwa inda suke ta zube ƙasa ta kwashi
gaisuwa ga gimbiya sannan ta ɓuɗi baki cikin ladabi da girmama ta ce "ya shugabata shin me
kike da bukata?
Gombiya Lamrat ta ce "ya ke Lazura ki yi sani cewa abi nda nake buƙata shi ne ki tafi da
wannan yarinya a tsaftace mata jikinta a sanya mata tufafi masu kyawu, sannan a haɗa mana
abin kalaci".
Ko da jin wannan umarni daga baƙin Lamrat sai kuyanga Lazura ta risina ta ce "an gama ya
shugabata"
Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta kama hannun yarinya Shuraiba ta shige da izuwa
wani ɓangare na daban.
Sannan gimbiya ta shige izuwa turakarta dakaru masu tsaron lafiyar na biye da ita.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya Shuraiba da gimbiya Lamrat matar sarki Ladiyas.
Al'amarin yaro Imran kuwa, lokacin da ya isa izuwa masaukin su sai ya shiga kewaye ya
watsa ruwa kuma ya ɗaura alwala, sannan ya gabar da Sallar magariba, bayan ya kammala ya
yi godiya ga Ubangiji
Koda gama aiwatar da hakan sai ya ji an ƙwanƙwasa Ƙofar dakinshi.
Kawai ya tashi ya je ya buɗe domin ya ga wane ne, sai ya ga a she hadima khadijat ɗauke da
abin kalaci da taceccen ruwan inibi bisa kofin azurfa.
Bayan ta ajiye a gaban shi sai ta samu waje ta zauna shi ma ya yi koyi da ita.
Khadijah ta dube shi ta ce "na samu wani labari dake yawo a gari akan abin da yafaru
tsakanin ka da matsafi Shamrul, tabbas idan hakan ya tabbata dola ne mu kasance cikin shirin
ko ta kwana domin a kowane lokaci dakarun farmaki zasl su dunga kawo mana ziyara don
ganin bayan ka". Koda jin wannan batu daga bakin khadijat sai yaro Imran ya jinjina al'amarin a cikin ranshi
sannan ya dubi khadijat ya ce 'tabbas maganar ki gaskiya ce ya 'yar uwanta, kuma Ubangiji
yana tare da mu a kodayaushe yanzu bari na yi kalaci sai ki dawo mu gabatar da sallar isha'i.
Da jin hakan saikhadijat ta miƙe tsaye ta juya ta fice daga ɗakin tana mai waigen Imran.
Wannan shi ne abin da ya faru da yaro Imran lokacin da ya isa masaukin su.
BABI NA SHA HUƊU
Lokacin da dare ya tsala sai sarkin yaƙi Darusu ya ɗauki sarki Lazwar ya gurfanar da shi a
gaban mai girma Ladiyas Ladiyas, a lokacin da ya ke zaune a cikin wata ƙasaitacciyar turaka.
tsayawa musalta tsaruwa da ƙawatuwar turakar zai iya zamowa ƙauyanci sai dai abin da idanu
suka gani kawai komai ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan dole
ne ya zamto bagidaje kuma cikekken ɗan kauye.
Bisa wata ƙasaitacciyar kejera wani mutum zaune a kai.
Mutumin ya kasance mai ƙirar sadaukai ya tara ƙwanji, kyakyawa ne na gaban kwatance kuma
ma'abocin kwarjini da haiba, Sanye yake da tufafi riga da wando irin na hamshakan sarakai,
kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya
isa. Ba wani ba ne wannan mutum ba face sarki Ladiyas ibn Fairuz. A wannan lokaci yana
zaune yana hangen wani ɓangare na lambun shaƙatawar daga tagar turakar. Yana cin kayan
marmari dake ajiye akan faranti na zinare bisa wani madaidaicin teburi na azurfa.
Koda bayyanar sarkin yaƙi Darusu sai ya ajiye tuffa dake hannunshu ya juya yana mai
fuskantar shi. Gami da ƙarewa sarki Lazwar kallo a lokacin da suke durƙushe a ƙasa bisa
gwiwoyinsu kuma sun sunkuiyar da kawunansu ƙasa.
Lokacin da sarki Lazwar ya ji shi durƙushe a gaban sarki Ladiyas sai baƙin ciki da takaici
suka mamaye zuciyarshi, ya ji kamar ya ƙwalla ihu, wai yau a ce shi ne durƙusawa wani sarki
saboda kawai neman biyan bukata, a matsayin shu na hamshaƙin sarki mai cike da taƙama da
BAƘAR IZZA. Tsawon daƙiƙa ana cikin wannan hali, sai daga bisani sarki Ladiyas ya buɗi baki cikin wata irin
kakkausar murya mai tattare da jarumtaka ya buɗi baki ya ce "ya kai dirkar birnina alamu sun
nuna min baƙom bawan da ka zo da shi zai iya kasance ɗaya cikin masu tsaron lafiyar gimbiya,
amma sai dai ba zai yiwu na amince da hakan ba face ya shiga izuwa ɗakin duhu kuma ya
samu nasarar cin jarabawar FARAUTAR RAI, lallai ne gobe da safe ka gabatar da shi a fada
domin yi mashi jarabawar";
Koda jin wannan umarni daga bakin sarki Ladiyas sai sarkin yaƙi darusi ya risina cikin
ladabi ya ce "an gama ya shugabana".
Yana gama faɗin hakan ya tashi tsaye ya juya ya fice daga turakar sarki Lazwar ya yi koyi
da shi yana mai bin bayan shi, suka durfafi wani ɓangare daban.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a lokacin da aka gabar da shi a gaban
mai girma Ladiyas.
Al'amarin yarinya Shuraiba kuwa, lokacin da kuyangi suka kammala yai mata wanka da
ado kuma suka ciyar da ita daddaɗan abinci, sai barci mai nauyi ya ɗauke ta.
Ba ta farka ba sai da dare ya tsala, a wannan lokaci gimbiya na zaune a kusa da ita bisa kan
gadon da take kwance.
Sa'adda ta ga Shuraiba ta farka daga barci sai ta sanya hannayenta biyu tashe ta tsaye
ta ja hannun ta izuwa wata ƙasaitacciyar kujera, da a gaban ta aka ajiye wani teburin azurfa mai
ɗauke da nau'ikan abinci, bin sha da tanɗe-tanɗe.
Cikin matuƙar farin ciki gimbiya ta shiga ɗibar abinci da abin sha tana bawa Shuraiba a baki.
Nan take Shuraiba ta ji tamkar mahaifiyarta ce ke ciyar da ita, ita kuwa gimbiya farin cikin
ta ba zai misaltu ba, bisa ganin cewa yau ita ce ke ciyar da 'yarta da hannunta da ta shafe
tsawon shekaru tana kewar ta.
Bayan gimbiya ta kammala bata abincin, ita ma ta kimtsa cikinta, sai Shuraiba ta shiga
bawa gimbiya labarin rayuwar ta, tun daga lokacin da sarki Ladiyas ya raba ta da mahaifiyarta
ya mayar da ita baiwar shi, har izuwa sa'adda suka koma rayuwa a daji ita da mahaifinta, har
kawo lokacin da ta haɗu da su sarki Lazwar, tun daga farko har ƙarshe ta zayyane wa gimbiya. Sa'adda gimbiya ta ji wannan labari daga bakin yarinya Shuraiba ba ta san sa'adda ta
rungume ta ba su duka biyun suna masu fashewa da matsanancin kuka mai tsuma zuciya. sai
daga bisa ne gimbiya ta janye jikinta daga na Shuraiba suka fuskantaci juna.
Kawai sai gimbiya ta sanya hannunta ta ya ye mayafin dake kanta fuskarta ta bayyana a fili
ƙarara.
Sa'adda Shuraiba ta yi arba da fuskar gimbiya ba ta san sa'adda ta sake rungume ta ba a
karo na biyu tana mai fashe da kukan murna.
Ba komai ne ya sanya ta hakan ba sai domin arba da ta yi da fuskar mahaifiyarta Lamrat,
tana mai cewa ashe zan sake ganin ki ya ummina ashe daman kina raye?
Daƙyar gimbiya Lamrat ta lallashe ta tayi shiru ta share mata hawaye, bayan ta samu nutsuwa
ne sai ta dube ta cikin annashiwa da farin ciki ta ce "ya 'yata kuma farin zuciyata Haƙiƙa ina
raye ban mutuwa, a kowace rana idan dare ya tsala sai nayi kukan baƙin ciki tare da roƙon abin
bauta akan ya kare min ke kuma ya kawo min lokacin da zan ɗauki fansa akan BAKIN
AZZALUMI da ya lalata rayuwar mu wato sarki Ladiyas. Sai gashi abin bauta ya dawo min dake
cikin ƙoshin lafiya, ina so mu ɓoye sirrin dake tsakanin mu har izuwa lokacin da zamu ɗauki
fansa.
Saboda hakan ma ya sanya na ɓoye miki fuskata a lokacin da muka haɗu a kasawu, domin
matuƙar wani ya gane hakan har sarki ya samu labari tofa dukkan shirin mu ya tarwatse.
Sa'adda gimbiya ta zo dai-dai nan azancenta sai yarinya Shuraiba ta cika da matuƙar farin
ciki maral-musaltuwa, tana mai cewa tabbas na aminta da ke ummina kuma za mu ɗauki fansa
akan sarki Ladiyas.
Wannan shine abin da ya wakana tsananin yarinya Shuraiba da mahaifiyarta gimbiya
Ramlat.
Al'amarin yaro Imran kuwa tun sa'adda ya yi bankwana da hadima Khadijat bayan sun sun
tattauna akan abin da ya wakana tsakanin shi da matsafi Shamrul a cikin kasuwa, sai ya shiga
kimtsa cikin shi bayan ya kammala ne Khadijat ta dawo gare shi suka gabatar da sallar Isha'i
Bayan kammala wa ne ya kwanta domin ya huce gajiyar dake tattare da shi.
Wannan shi ne ya faru da yaro Imran ma'abincin addinin Musulunci.
BABI NA SHA BIYAR
BIRNIN ISTANBUL
Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar sarki Ladiyas ta cika ta batse da jama'a
maza, mata yara da manya, duk inda mutun ya duba kawunan bil'adama rututu babu masaka
tsinke, tamkar dandazon kiyasai.
Domin a yau ne aka samu labarin cewa za'a gudanar da gasar farautar rai, domin tsallake
matakin ƙarshe da zai bawa sarki Lazwar damar kasance ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar
gimbiya Lamrat.
Bayan jama'a sun hallara kuma sarki Ladiyas ya hakimce a bisa karagarshi ta mulki,
sanye cikin ƙasaitacciyar shiga ta kece raini. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka hango
sarkin yaƙi Darusu ya shigo izuwa fadar tare da dakaru sun tuso ƙeyar sarki Lazwar ɗaure a
cikin sarari na baƙin ƙarfe. Sa'adda jama'a suka yi arba da sarki Lazwar sai fadar ta kaure da shewa, sai da sarkin
yaƙi ya ɗaga hannunshi sama sannan fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara.
Sannan ya fuskanci mutane bayan ya yi gyaran murya sai ya buɗi baki ya ce ''ya ku jama'ar
wannan fada mai albarka ku yi sani cewa ba komai ne ya sanya muka tara ku anan ba sai
domin a yau ne mai girma Ladiyas ya bayar da umarnin a saka jarumi Lazwar izuwa ɗakin
duhu. Domin ya yi gwagwarmaya da miyagun halittun da suke ciki kuma idan ya samu nasarar
tsallake matakin zai zamto daya cikin masu tsaron lafiyar mai martaba sarki.
Sa'adda sarkin yaƙi Darusu ya zo dai-dai nan a zancen shi, sai fadar ta sake kaurewa da
shewa a karo na biyu, sai daga bisani ne sarkin yaƙi ya umarci waɗansu dakaru mutum hamsin
suka wangame wata makekiyar kofar dake jikin bangon fadar, take wani makeken ɗaki ya
bayyana mai ɗauke da waɗansu nau'ikan halittu dangin kuraye da zakuna gami da macizai. Cikin hanzari waɗansu dakarun na daban suka buɗe ƙofar ɗakin, su ɗauki sarki Lazwar
suka jefa shi izuwa ciki, kana suka kwance sarƙoƙin dake riƙe da halittun, suka mayar da ƙofar
suka rufe ruf!
Sa'adda gimbiya