Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Usman Sufi.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Hausa Read

Chapter   6 / 12

15K to 18K   out of 34.1K words

daf da ita sai ya kawai ya miƙa hannunshi da niyyar ya cakume ta.amma
sai ya ji wani irin tiririn zafi ya tunkaro shi tamkar an yana kusa tanderun wuta.
Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya fusata ainun, kawai sai ya buɗe
baki da nufin ya karanta waɗansu dalasiman tsafi.
Kaico! haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, in da ace Yasiran ya san abin da zai faru da bai yi
gangancin karanta dalasiman tsafin ba, domin kuwa yana cikin hakan ne wata irin gagarumar
wuta ta kama a jikinshi tana ci. Nan fa magajin gari ya shiga kurma wawan ihu yana mai kai
komo a cikin turakar domin ganin ya kashe wutar, amma duk sa'adda ya zuba ruwa sai wutar da
ƙara ruruwa.
Ita kuwa amarya munirat koda ta ga wuta ta kama a jikinshi, sai ta ci gaba da karanta
waɗannan kalmomi na larabci da taga ni a jikin fuka-fukan tsuntsun nan a cikin zuciyarta, kuma
ta miƙe tsaye zumbur ta rugawa izuwa ƙofar fita daga turakar.
Bisa mamaki duk ƙofar da ta tunkara sai ta ga ta buɗe da kanta, wani abu da ya bata mamaki
kuma ya ɗaure mata kai shi ne, gashi dai ƙiri-ƙiri dakaru suna kallon ta ta tsakiyar su take
ratsawa, amma babu mai ɗaga mata yatsa ballantana ya ce mata uffan.
Haka dai amarya Munirat ta cigaba da tafiya a cikin gidan sarautar, zuciyarta cike da
matuƙar farin ciki maral musaltuwa gami da imani da ma'abocin waɗannan kalmomi da ta

karanta suka ce ci rayuwar ta. A dai-dai wannan lokaci ne dakarun dake gidan sarautar suka
dunga tuttɗowa suna zare makaman su suna rugawa izuwa ɓangaren sarki, bisa jin ihu gami da
kururuwar magajin gari Yasiran da suka yi.
kafin ƙiftawar idanun gidan sarautar ya hargitse da guje-gujen jama'a gami da ifice-ifice
tamkar an busa ƙahon BUSAR MUTUWA.


BABI NA TARA

A can birnin muridai kuwa, sarki Zammar mahaifin gimbiya Mashlira ya ga dukkanin abin
da ya wakana tsakanin yaro Imran da aljani Durusul-fannar.
A cikin halarar tsafin shi a lokacin da yake zaune a fadar tare da 'yan majalisar shi.
Ko da ganin hakan sai ya cika da matuƙar baƙin ciki maral-musaltuwa.
Wata rana sarki Zammar na kwance a cikin turakarshi da ta ƙawatu da kayan alatun more
rayuwr duniya, sai ya yi mafarki da yarshi Mashlira tana cikin ƙoshin lafiya.
Kuma har ta gaya mashi cewa bata guje mashi domin ta ci amanar shi ba, sai domin ta
shiga duniya ta samo masu maganin lalurar da ta addabe, su tun daga wannan rana Sarki
Zammar ya kasance cikin matuƙar farin ciki, ya yiwa 'yarshi fatan alheri da samun nasara.
Wannan shi ne abin da yafaru acan birnin muridai.


Babi na tara

Tafiyar daƙiƙa latalin kacal aka yi aka iso ƙofar shigowa birnin Istanbul, sa'adda aka yi arba
da yadda ƙofar birnin takasance sai kowa ya cika da matuƙar mamaki, katangun birnin sun
kasance masu matuƙar tsawo, a sama da ƙasan ƙofar birnin miyagun dakaru ne na mutum da
aljan ga su nan birjik shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayen ɗauke da waɗansu irin
masifaffun makamai
Kai koda tsuntsu ne ya zo giftawa ta wannan waje waɗannan dakaru ba zasu bar shi a raye
ba, tsananin kwarjini mayaƙan ya isa ya ɗimauta duk wata halitta mai numfashi.
Idan har ƙofar birnin Istanbul takasance haka, to ya tsaron gidan sarautar birnin zai kasance
kuwa?
Sarki Lazwar ne ya yi wa kanshi wannan tambaya a cikin ranshi ba tare da ya furta wani ya ji
ba.
Wani narkeken sadauki mai matuƙar muni da kwarjini ya matso daf da inda su sarki Lazwar
su ke ya kare masu kallo da yan mini-minin idanuwanshi jajaye tamkar garwashin wuta, cikin
wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya ku waɗannan baƙi shin daga ina
kuke, kuma mene ne ke tafe da ku izuwa birnin nafi daraja a duniya?. Ko da jin wannan tambaya sai zuciyar sarki Lazwar ta kama tafarfasa tamkar zata
ƙone.
Bakomai ne ya sanya hakan ba, sai bisa jin badakaren ya ambaci birnin Istanbul da suna mafi
daraja a duniya.
Amma koda ya tuna cewa shi fa a halin yanzu sunan shi bawa ba BASARAKE ba, sai ya
danne zuciyarshi, ya dubi badakaren ya ce "ya kai wannan badakare ka yi sani cewa ba komai

ne ke tafe damu izuwa wannan birnin na ku ba face sai domin mu gudanar da kasuwanci, kuma
a halin yanzu mun fito ne daga nahiyar ƙasashe larabawan gabas.
Ko da jin amsar wannan tambaya sai badakaren ya bushe da dariya sannan daga bisani
ya murtuke fuska ya ce "Za mu ba ku izinin shiga wannan birnin saboda muhimmancin abin da
ke tafe da ku. Sai dai wani hanzari ba gudu ba idan muka samu ɗayan ku ya karya dokokin
wannan birnin namu, to zamu ƙwace dukiyarku gami da tusa ƙeyarku izuwa gidan kaso. Ko da jin wannan batu sai hantar cikin kowa ta kaɗa da karfi tsoro ya kama shi.
Kawai sai badakaren ya yiwa waɗansu dakaru inkiya ta wutsiyar idanu take dakarun suka
shiga wangame kofar birnin, ƙofar na kammala buɗewa su sarki suka kunna kai izuwa cikin
birnin zukatansu cike da matuƙar farin ciki.
Lokacin da su Sarki lazwar suka tsinci kansu a cikin birnin Istanbul sai suka kama
kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni, kuma suka cika da matuƙar mamaki
gami da al'ajabi, bisa ganin yadda birnin ya kasance mai matuƙar kyawun gine-gine tamkar
aljannar duniya. Kai tsaye yarinya Shuraiba ta durfafi hanyar kasuwar birnin, amma sai sarki Lazwar ya yi
caraf! ya dubi yarinya Shuraiba ya ce "ya ke Shuraiba shin mene ne dalilin da ya sanya za ki kai
mu kasuwa? Bayan cewa ba kasuwanci ne ya kawo mu wannan birni ba?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai Shuraiba ta bushe da dariya ta ce "ai bakomai ne
yasanya na kawo mu kasuwa ba sai domin kar ka manta cewa ka faɗawa dakaru masu tsaron
kofar birnin Istanbul cewa kasuwanci ne ya kawo mu, tabbas dola ne a kowa ne lokaci dakarun
sarki su kawo ziyarar bazato, domin binciken gaskiyar maganar abin da ka faɗa masu, Abu na biyu kuwa shi ne a lokacin da muka shigo wannan birni 'yan fashi da makami gami da
'yan damfara sun shaida shigowar mu, a koda yaushe za su iya kawo mana farmaki domin a
tsammanin su za su samu dukiya mai tarin yawa a wajen mu.
Waɗannan dalilai ne suka sanya na kawo mu kasuwa domin babu wani waje mai ɗauke da
cikekken tsaro fiye da kasuwa".
Ko da jin amsar waɗannan tambayoyi daga bakin Shuraiba sai kowa ya gyaɗa kai alamar
gamsuwa gami da samun nutsuwa.
Lokacin da aka shiga kasuwar sai aka tarad da takasance maƙiyaya mai faɗin gaske, tana
ɗauke da gine gine cikin tsari, rumfunan masu siyan da tufafi dabam, kayan masarufi, komai dai
an yi bisa tsari mai ƙayatarwa.
Kai tsaye aka durfafi rumfar wani dattijo, da ta ƙawatu da kayan alatu na hatimin sarauta,
da alama shine shugaba kasuwar.
Tun daga nesa Shuraiba taga ya ƙura mata idanu ko kiftawa ba ya yi.
koda shugaban kasuwar ya yi arba da su sai ya miƙe tsaye zumbu! Ya tarbe su cikin matuƙar
farin ciki yana yi masu lale marhaban da zuwa, tamkar ya sadu waɗansu yan uwanshi na jini da
ya jima bai sadu da su ba.
Bayan shugaban kasuwar mai suna Sha'aran ya sauke su a bakin ƙofar rumfar, sai ya yi
umarni aka kawo musu abincin kalaci aka jera a bisa wani dogon teburi, nan fa su sarki Lazwar
suka shiga kimtsa cikinsu, har suna hannu baka hannu ƙwarya, domin rabon su da cin irin
abincin yau wata huɗu kenan cif. Kuma suna mamakin irin karamci da shugaban kasuwar ya nuna masu.
Shi kuwa yaro Imran da aka fara cin abincin sai ya yi bisimillah, loma bakwai ya yi sannan ya
zare hannunshi ya kurɓi ruwa maƙwarwa huɗu sannan ya koma koma gefe gudal.

Al'amarin daya bawa sarkin kasuwa Sha'aran mamaki kenan, ya ƙurawa yaro Imran
idanu yana so ya tuna irin mutanen da ya taɓa gani suna irin wannan dabi'a wajen cin abincin
su, Shi kuwa aljani ZA'ARATUN-LAYAL, da a halin yanzu sarki Lazwar ya canja mashi siffarshu
dagaaljan ya koma bil'adama, cin abincin ya yi yana santi kamar tsohon mahaukaci. Bayan kowa ya kimtsa cikinshi ya dawo hayyacinshi, sai sarki Lazwar ya zira hannunshi a
aljihun rigarshi domin ya ɗauko dinare domin ya biya kuɗin bincin da suka ci, da kuma kuɗin
hayar gidan da za'a ba su.
Amma sai kawai ya ga shugaban ya dube sa fuskar sa cike da annuri ya ce "ya ku waɗannan
baƙi masu daraja ku yi sani cewa, ganin ku da nayi ya sanya jikina ya ba ni cewa ku mutanen
ƙwarai ne. Yanzu ina buƙatar ku gabatar min da sunayen ku.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa, sarki Lazwar ya shiga gabatar da
sunayen su ɗaya-bayan-ɗaya,
Amma koda yazo kan yarinya Shuraiba sai sarkin kasuwar ya dakatar dashi ya ce "ba sai ka
gabatar mini da ita ba.
Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan, har Shuraiba ta ce a cikin ranta shin me shugaban
kasuwar ya sani game da ni. Kuma me ya sanya yake ƙura min idanu tun da muka shigo
kasuwar?
Ina dalilin rashin karɓar haƙƙin aikin shi daga gare mu.
Amsar tambayoyin da yarinya Shuraiba ta kasa bawa kanta kenan.
Shugaba sha'aran na gama faɗin hakan sai ya ƙwallawa wata budurwa kira.
Budurwar ta bayyana a gare shi sanye da tufafi masu yalwa, tun daga ƙasa har sama, kuma
fuskarta rufe da rawani mai ɗauke da wani hatimin sarauta idanuwanta kaɗai ake gani,
ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa, sannan ta buɗi baki cikin wata irin lallausar
murya mai daɗi tamkar sarewa ta ce ''ga ni ya shugabana me ake da buƙata?
Shugaba Sha'aran ya dube ta ya ce "ya ke khadijat ki yi sani cewa bakomai nake buƙata a gare
ki ba, sai domin ki yiwa waɗannan baƙi jagora izuwa unguwar Madinatul-dinar, masaukin
manyan baƙi, ina so ki ba su dukkan abin da suke bukata na kulawa".
Koda jin wannan umarni sai B
Budurwa khadijat ta mayar da duban ta ga su sarki Lazwar tana ƙare masu kallo
ɗaya-bayan-ɗaya.
Ya yin da ta haɗa idanu da yaro Imran sai taji zuciyar ta buga ƙarfi kuma tsikar jikin ta ta
tashi, kamar yadda ya faru gare ta shi ma haka yaro Imran ya ji wannan yanayi a tare da shi,
amma saboda kada wani ya fahimci abin da ke faruwa sai khadijat ta kawar da idanuwanta a
kan shi, a ɓangaren bawa Shamsal kuwa, tun sa'adda da ya kalli idanuwan budurwa khadijat
sai ya ji hantar cikinshi ta kaɗa da ƙarfi, sannan wani abu ya ɗar su a zuciyarshi da ya kasa
gane ko mene ne.
Ita kuwa gimbiya Mashlira cikin idanun khadijat kawai ta kalla taji kishi ya kama ta, domin koda
cewar fuskar khadijat a rufe take da rawani idanuwanta kaɗai ake gani, ta tabbatar cewa ta
shafe ta a kyawun sura ne sa ba kusa ba.
Tabbas idan masoyin ta sarki Lazwar ya yi arba da ita zahiri zai iya karkata zuciyarshi izuwa
gare ta.
Khadijat ta miƙe tsaye ta shige gaba, tana mai yafito su sarki da hannunta, tana mai yi
masu nuni da su biyo bayan ta.

Ba tare da gardamar komai ba, suka mara mata baya har suka ƙule a cikin kasuwar, duk inda
suka gifta sai jama'a su bi su da kallo, haka suka wanzu suna ratsa saƙo da lungu na
unguwanni, har suka iso wani ƙasaitaccen gida.
Kai tsaye khadijat ta durfafi kofar gidan ta na isa dakarun dake gadi suka wangame
makekiyar kofar shiga gidan suna masu risinawa a gare ta cikin girmamawa.
Khadijah ta kunna kai izuwa cikin gidan, su sarki lazwar na biye da ita cike da matuƙar mamakin
yadda masaukin ya kasance.
Kowanne su ɗaki aka ba shi daban mai ɗauke da gado, kushin da kewayen wanka da sauran
kayan more rayuwa.
Kuma khadijat ta shaida masu cewa duk mai buƙatar wani abu ya sanar da ita har izuwa lokacin
da zasu tafi.
kasancewar a wannan lokaci duhun dare ya fara kawo kai, sai khadijat ta yi umarni aka kunna
dukkanin fitulun dake gidan.
A lokacin da dare ya tsala sai sarki Lazwar ya shiga izuwa masaukin kowanne ya bayyana
masa cewa, dole ne su kasance cikin shiri, domin a kowannnen lokaci za a iya kawo masu harin
bazato, kuma ba su da tabbacin cewa sarki kasuwa Sha'aran ba shi da wata mummunar
manufa akan su, kuma a gobe da duku-dukun safiya za su shiga cikin garin domin gudanar da
abin da ke tafe da su.
A can masaukin yaro Imran kuwa bayan gabatar da kalacen dare, sai ya shiga izuwa
kewayen ya ɗaura alwala ya dawo izuwa turakarshi ya shiga gabatar da Sallah isha'i yana cikin
hakanne ya ji an turo kofar shigowa, sai da ya idar ya yi addu'a sannan ya juya domin ya ga
kowane ne ya shigo ɗin. Koda ya yi arba da wanda ya shigo ɗin sai ya yi turus!, Ba wani ya gani ba face khadijat
hadima ga Sarkin kasuwa Sha'aran, tana durƙushe a gefan shi na hagu ta yi zama irin na
sallah.
Cikin matuƙar mamaki Imran ya du be ta cikin girmamawa ya ce "ya ke hidima Khadijat shin ina
dalilin shigowarki wannan masauki nawa a dai-dai wannan lokaci bakya tsoron sauran abokan
tafiya za su zargi wani abu?
Sannan jikina ya bani cewa kina kwaikwayon yadda nake gudanar da ibadar Ubangiji na.
Shin baka tunanin hakan zai jefa rayuwarki da tawa a cikin haɗari ba?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai khadijat ta yi murmushi mai taushi, sannan ta dubi
Imran cikin murya mai daɗin saurare ta ce
"ya kai wannan yaro ka yi sani cewa tun sa'adda nayi arba da kai a lokacin da ku ka sauka a
rumfar mai gidana, naji ka burgeni sosai a zuciyata tamkar ina tare ɗan uwa na jini, kuma
lokacin da ku ke cin abincin na lura cewa duk dabi'un cin abincin naka ya bambanta da nasu,
wato naka irin na ma'abota addinin Musulunci ne, tun daga lokacin na ji cewa na samu ɗan
uwa.
Bisa wannan dalili ne ya sanya na biyo ka izuwa masaukin ka domin na bika sallah. Fiye
da shekaru goma sha biyu kenan tun sa'adda an fito neman ɗan uwa na, wanda shi ne kaɗai ya
rage mini da a duniya rabon da a ce na samu jam'in sallah sai a yau,
Tabbas ina cikin matuƙar farin cikin da ba zai musaltu ba. Haƙiƙa da zaka zauna a tare da ni da
ka ɗebe mani kewar mahaifina da na rasa.

Tsawon shekarun da na shafe ina aiki tare da Sarkin kasuwa Sha'aran ban taɓa bayyana addini
na a gare shi, saboda gudun matsala, domin duk wanda aka samu yana gudanar da wani addini
saɓanin na birnin Istanbul hukuncin kisa ne a ƙanshin shi.
Bisa wannan dalili ne ya sanya kai ma nake baka shawara da ka guji bayyana hakan, har ku
kammala abin da ke tafe daku zuwa wannan birni";
Koda jin amsar waɗannan tambayoyi sai yaro Imran ya cika da matuƙar farin ciki yaji ya
yi matuƙar shaƙuwa da hadima khadijat, kuma mamaki ya kama shi bisa jin cewa ta fito neman
ɗan uwanta ne.
Shin khadijat ita ce 'yar uwar shi da ya fito nema ?
Amma ta ya zai iya gasgata hakan bayan cewa koda yaushe fuskarta a rufe take da rawani.
Amsar tambayoyin da Imran ya kasa bawa kanshi kenan.
Khadijat ta katse shirun da wanzu a tsakaninsu ta hanyar buɗar baki ta ce "ya kai ɗan
uwa na idan ba za ka damu ba, ina neman alfarma a gare ka da ka amince min kullum na
dunga zuwa wajen ka muna yin fira gami da ɗebe kewa
Koda jin wannan batu sai

6 / 12