Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Usman Sufi.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Hausa Read

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 34.1K words

da
makami ya dawo yaƙar su da ƙarfin sihirin tsafi, domin wani lokacin idan Imran da Khadijah
suka sare shi ta takubban su sai su ga raunin ya koma ya haɗe sumul, wasu lokutan ma sai ya
rikiɗa ya zama haske.
Sarki Lazwar, gimbiya Mashlira da aljani Za'aratul-layal kuwa sun wanzu suna masu
kaiwa sarkin yaƙi Darusu hare-hare cikin gwanintar yaƙi tamkar za su cinye shi ɗanye.
Amma bisa mamaki sai ya zame masu ƙadangaren bakin tulu suka kasa samun nasarar
koda lakutar jikinshi, duk kuwa da cewar ƙarfin mutum biyu ne da aljani ɗaya akan mutum guda.
A ɓangaren bawa Shamsal da sarkin yaƙi ku wa sun wanzu suna ragargazar dakarun
dake fadar duk inda suka sanya gaba sai ka ga dakarun na zubewa ƙasa matattu, nan fa ƙarar
karafniyar ƙarafa, ihun mazaje hade da hargowar aljanu gami da ifice-ificen jama'a ya cika
dodon kunne, ƙura ta turnuƙe fadar baki ɗaya tamkar haɗari zai gangamo a kece da ruwan
sama.
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin manyan sarakuna biyu, aljanu
biyu, gami da jarumai shida sai yaƙin ya zamto tashin hankali gami da ban tsoro ga yan kallo.
Sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan ɗauki ba daɗi tsakanin jaruman ba tare da
ɗayan su ya samu nasarar hallaka ɗaya ba.
A bangaren sarki Ladiyas kuwa ya zamewa su gimbiya Lamrat ANNOBA ƊARI domin
duk da cewar Hadimul-kahiri na amafni da addu'o'i domin su hallaka sarki Ladiyas amma sai
hakan ya gagara domin sai sun datse wuyanshi suna tunanin ya mutu sai kawai su ga wani
ruhun ya keto daga cikin ƙarƙashin ƙasa ya sake shiga jikinshi. Sai kuma a ɗora wani gumurzun, nan fa ya zamana cewa su Hadimul-kahiri sun kashe fiye
ruhika arba'in na sarki Ladiyas.
Al'amarin da ya sanya su duka ukun suka samu miyagun raunuka musamman yarinya
Shuraiba. Haƙiƙa sarki Ladiyas bakaramin hatsabiba ne domin ya yi nisa a halarar tsafi wanda
cimma mashi abu ne mai matuƙar wahala.
A dai-dai wannan lokaci ne yaro Imran da hadima Khadijat suka samu nasarar hallaka
matsafi Shamrul, ta hanyar amfani da takubbansu suka soka mashi akan ƙawon zuciyarshi, ya
yin da suka hango su yarinya Shuraiba kuma suka ga irin mugun halin da suke ciki sai suka kai
masu ɗauki. Nan fa ya zamana cewa labari ya sha bamban domin a wannan karon sai ya zamana tasirin
sihirin dake tare da sarki Ladiyas ya fara karyewa, domin duk sa'adda hadima Khadijat da yaro
Imran suka kai mashi hari da makamansu duk inda suka sara sai su ga sun tsarga jikinshi.
Bisa taimakon Ubangijin halitta daƙyar da siɗin goshi suka samu nasarar hallaka sarki ladiyas,
ta hanyar sare mashi hannaye da ƙafafuwanshi suka jefar da gawarshu a ƙas.

In da ace mutum ya na wannan waje a lokacin da sarki Ladiyas da matsafi Shamrul suka yi
mutuwar wulakanci dole ne ya yi farin ciki maral-musaltuwa. Bisa ganin yadda Allah Ubangijin
halitta ya kawo ƙarshen azzalumai.
A dai-dai wannan lokaci ne su gimbiya mashlira, Aljani Za'aratul-layal da sarki Lazwar suka
samu nasarar hallaka sarkin yaƙi Darusu.
Sa'adda al'ummar fadar da su bawa Shamsal suka yi arba da gawar sarki Ladiyas, da ta
matsafi Shamrul sai dukkanin su suka durƙusa ƙasa bisa gwiwoyinsu suka yi mubaya'a, suna
masu cewa "haƙiƙa mun bayar da gaskiya ga Ubangijin yaro imran
Cikin hanzari waɗansu likitoci suka shigo fadar ɗauke da kayan aiki suka shiga duba lafiye
yarinya Shuraiba, gimbiya Lamrat,da sarki Lazwar.
Sannan yaro Imran ya ruga izuwa inda hadima Khadijat take suka rungume juna cikin
matuƙar farin ciki maral-musaltuwa bisa sake saduwa da juna da suka tsawon shekaru.
Daga bisani yaro Imran ya janye jikinshi daga na 'yar uwarshi Sharifa.
Ya juya ya fuskanci jama'a sannan ya buɗi baki ya ce "ya ku al'ummar wannan birni mai albarka
haƙiƙa na tabbatar da cewa a halin yanzu zukatanku sun gamsu cewa babu abin bauta da
gaskiya sai Allah mai kowa mai komai.
Saboda haka yanzu ba tare da wani ɓata lokaci ba yaro Imran ya faɗi kalmar shahada, take
ɗaruruwan jama'ar dake fadar suka maimaita.
Sautin muryoyinsu ya cika fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin baki ɗaya.
Bisa mamaki sai Imran da hadima Khadijat suka ji sarki Lazwar da sarkin yaƙinshi haɗe da
bawa Shamsal tare gimbiya Mashlira sun amsa kalamar shahadar.
Nan fa suka cika da al'ajabi, sarki Lazwar ya tako da ƙafafuwanshi izuwa inda imran da
Khadijat suke ya dubi Khadijat cikin girmamawa ya ce "ya ke Sharifat Haƙiƙa rashin sani yafi
dare duhu, na zo wannan birni neman ki, ashe kina tare da ni ban sani ba, yanzu ga shi na karɓi
addinin Musulunci shin ina makomar tafiya ta izuwa nemo abubuwan da za su warkar da ni
daga sihirin da abokin gaba ta sarki Durwazu ya yi min, na karɓi Musulunci ne domin yadda a
zuciyata, na samu tabbacin ne a lokacin da nake fafata yaƙi da miyagun halittun dake cikin
ɗakin duhu, inda dukkan wata dubara ta ƙwace min na nemi taimakon Ubangijin imran".
Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan azancen shi sai Sharifa, yaro Imran da sauran jama'a
suka cika da matuƙar mamaki.
Sharifat ta ce ''ya kai wannan sarki mai daraja ka yi sani cewa ai shi addinin Musulunci yana
shafe duk abin da ya tuve, saboda haka a halin yanzu sihirin da sarki Durwazu ya yi maka ya
karye.
Babu buƙatar sai na taimaka maka wajen mallako abubuwan da za su warkar da kai daga
sihirin, domin abubuwan da za'a mallako dukkanin su na tsafi ne.
A halin yanzu zaka iya kusantar kowace irin 'ya mace kuma har ka samu haihuwa ka
yarda Ubangijin musulunci kawai a koda yaushe";
Koda jin wannan batu daga bakin Sharifa wato sai sarki Lazwar ya cika da matuƙar farin
ciki wanda bai taɓa yin kamar shi ba.
Daga wannan ne aka ɗunguma izuwa gidan sarauta domin kowa ya huce gajiyar dake tattare
da shi.
A cikin wannan dare ne hirar soyayya ta ɓarke tsakanin sarki Lazwar da gimbiya Mashlira 'yar
shugaban maridai, yaro Imran da yarinya Shuraiba, Sharifat da bawa Shamsal.
Kuma a wannan dare ne akayi shelar naɗin sarautar yaro Imran da wazirinshi Shamsal.

kafin wayewar gari ciki da wajen birnin Istanbul ya cika ya batse da jama'a baƙin
sarakuna daga kowa ce nahiya da 'yan kasuwa.
Tun lokacin da alfijir ya keto bayan an gabatar da sallar asuba sai jama'a suka yi tsinke a fadar
maza da mata yara da manya.
Sarakuna da manyan baƙi an ware masu wajen zaman su daban, haka ma na talakawa,
komai dai an yi shi bisa tsari.
Sarkin fadar birnin Istanbul wani dattijo ya tashi ya gabatar da jawabin maraba ga mahalar ta
taro. Sannan ma'ajin sarautar ya gabato da kayan sarauta da suka haɗar da alkyabba, rawani,
kwagiri, takalmi da sauaran su.
Sarkin fada Huzaifa ya ɗauki kayan ya shiga sanya wa yaro Imran a jikin shi, bayan ya
kammala ne sai ya umarci yaro Imran ya je ya zauna bisa karagar mulki ya hakimce, nan fa
tsananin kyawun surar Imran ya fito ƙarara yarinya shuraiba kuwa sai ta dunga satar kallon shi
tana yi mashi kallo mai nuna alamun tsantsar so da ƙauna. Nan take jama'ar fadar suka yi mubaya'a a gare shi, daga bisani kuma sai aka shiga
shagalin ɗaurin aure mutum shida sarki Imran da yarinya Shuraiba baiwa Sharifa da bawa
Shamsal, sarki Lazwar da gimbiya Mashlira.
A wannan rana anyi gagarumin shagalin da ba'a taɓa yin kamar shi ba tsawon kafuwar birnin
Istanbul.
Bayan an kammala ciye-ciye da tanɗe-tande, kowa ya cika cikinshi sai sarakunan da
suka halararci bikin naɗin sarautar suka dunga zuwa, gaban sarki Imran suna karɓar KALMAR
SHAHADA tare da jama'arsu, haƙiƙa farin ciki ya cika zuciyar kowa.
Bayan tarewar angwaye uku sarki Imran, shamsal da sarki Lazwar.
Sai sarki Imran ya umarci aljani Hadimul-kahiri ya ɗauki sarki Lazwar da amaryarshi gimbiya
Mashlira da sarkin yaƙi haɗe da aljani Za'aratul-layal domin ya kai su izuwa birnin
ZAWATUL-IFDAR, amma sai da aka fara zuwa ta birnin su gimbiya Mashlira aka musuluntar da
sarkin maridai da mutanenshi kuma aka karya sihirin tsafin da aka yi masu suka dawo ainahin
siffar su irin ta bil'adama suka daina cin naman bil'adama bisa taimakon Ubangijin halitta.
An yi shagalin farin cikin dawowar yar sarkin muridai gimbiya mashlira. Sai da aka shafe
mako ɗaya sannan aka sake ɗungumawa aka durfafi birnin Zawatul-ifdal, amma sai aka bar
sarkin yaƙi imhal domin ya cigaba da bayar da ilimin addini ga jama'ar birnin, kuma sarkin
maridai ya naɗashi wazirinshi. Lokacin da aka isa birnin Zawatul-ifdal sai sarki lazwar ya cika da matuƙar farin ciki, bisa jin
labarin abin da ya faru tsakanin magajin gari Yasiran da amarya Munirat wacce a halin yanzu ita
ce ke riƙe da karagar mulkin birnin.
Jama'a sunyi farin cikin dawowar sarki Lazwar, ba tare da ɓata lokaci ba aka sake ɗaura
auren amarya Nunirat da sarki Lazwar, sakamakon mutuwar angonta, amma da ƙyar da siɗin
goshi sarki Lazwar ya shawo kan gimbiya Mashlira ta amince aka ɗaura auren. Sai aljani
Za'aratul-layal da Hadimul-kahiri suka koma izuwa birnin Istanbul. Sannu-sannu bayan mako ashirin sai aka wayi gari matayen sarki Lazwar Munirat da
Mashlira suna ɗauke da juna biyu.
Farin ciki a wajen sarki Lazwar kuwa kamar ya zautu, ya dinga rabon dukiya da suturu na
alfarma.
Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI ya mamaye duniya baki ɗaya zaman
lafiya ya wanzu, zalunci da bautar gumaka suka rushe baki ɗaya.

Ƙarshe

Alhamdulillah

Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.

MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071



FATAUCIN BAYI
Rubuta labari
MANSUR USMAN SUFI

Lokacin da su jaruma Nabihat suka iso izuwa bakin tanatin, sai Nabihat ta ɗauko hodar
banju a cikin aljihun rigarta ta busa ta izuwa cikin tantin, jim! Kaɗan sai suka kunna kai ciki suna
shiga suka tarar dakaru masu dafa abinci sun kama barci mai nauyi.
kawai sai suka cire tufafin dakarun suka maye da na sannan suka rufe fusakunsu da hulunan
ƙarfe.
Kawai sai suka matsa izuwa inda dakarun suka ɗora sanwa akan wuta suka buɗe
murafun tukunyoyin suka zazzaga wannan hodar banju a cikin, sannan suka mayar suka rufe
ruf.
Bayan shuɗewar daƙiƙa goma sai suka zuzzuba abincin a cikin waɗansu ƙananan
akushi, suka ɗora akan farantai na azurfa, sannan juya suka fice daga tantunan suka shiga
rarrabawa dakarun dake cikin jirgin ruwan abincin mai dauke da hodar banjun har suka iso
izuwa inda wani sadauki yake. Nabihat ta ɗauki akushi ɗaya ta miƙa mashi ya karɓa ya bude ya sanya hannunshi ya yi
loma ɗaya, kawai sai ya dubi Nabihat ya ce "ya kai Himairu ya aka yi abincin nan ya yi ɗan
karen daɗi haka?
Koda jin wannan tambaya sai Nabihat ta yi murmushi gami da gyaɗa kai, kawai sai ta huce
gaba ba tare da bawa sadaukin amsar tambayar shi ba.
Haka dai suka cigaba da rabawa dakarun abincin, har suka iso inda suka bar saduki Hushaibu.
Nabihat ta ɗauki akushin ta miƙa mashi ya karɓa.
Har Hushaibu ya buɗe da nufin cin abincin kwai ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi, kawai sai ya yi
jifa da akushin ya durfafi madafa cikin hanzari.
A dai-dai lokacinne su jaruma Nabihat suka kammala raba abincin suka samu wata
maɓuya a cikin jirgin suka laɓe.
A fusace Hushaibu ya kunna kai izuwa cikin tantin, ai kuwa sai ya yi arba da masu dafa
abincin kwance suna sharar barci babu tufafi a tare da su.

Cikin matuƙar fushi gami da tashin hankali ya zare takobinshi ya ruga izuwa waje yana
mai ƙwallawa sauran dakarun kira.
Al'amarin da ya janyo hankalin sadauki Sharkar kenan ya zare takobinshi da nufin
dakawa dakarun tsawa.
A dai-dai wannan lokaci ne hodar banjun da su Nabihat suka zuba a cikin abincin ta fara
bugar da dakarun suna ɓingirewa kasa suna sharar barci.
Kafin Sharkar da Hushaibu su farga fiye da rabin dakarun dake cikin jirgin ruwan sun kamu da
barci mai nauyin gaske, cikin matuƙar kaɗuwa gami da tashin hankali sadauki Sharkar ya
cigaba da falfala azababban gudu, yana mai kurma wawan ihu
Nan fa sauran dakarun da ba su kai ga cin abincin ba suka firgice suka ɗauko
makaman yaƙin suka dinga fitowa daga kowace kusurwa a jirgin.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga su jaruma Nabihat da sauran 'yan matan
fursunonin sun yo fitar burgu daga maɓuyar su suna, suka yi ɗauki izuwa kan dakarun suna ihu
da kururuwa mai firgitarwa.
Koda ganin hakan sai dakarun suka yi ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgita
DANDAZON MAYAƘA a filin daga.
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan zaratan 'yan mata su ashirin
kacal! Suka tunkari ɗaruruwan dakarun dole ne ya cika da mamaki kuma ya jinjina masu ya
tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA, mata masu kamar maza.
Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro daban
al'ajabi.
Nan fa gaba ɗaya jirgin ruwan ya yamutse da ƙarar haɗuwar makaman yaƙi, gami da ihu da
kururuwar mazaje.
Nanfa Nabihat da 'yan matan fursunonin suka wanzu suna kaiwa dakarun sara da suka
cikin matuƙar zafin nama tamkar jikkunan ba su kasance na jini da tsoka ba.
Cikin abin da bai gaza daƙiƙa arba'in ya zamana cewa sun samu nasarar hallaka fiye da mutum
hamsin na dakarun sun rauna ta fiye da ɗari biyu.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin dakarun kenan kuma ya fusata su ainun, bisa
ganin cewa a matsayin su na GWARAZAN MAYAƘA, amma a ce 'yan mata sun zame masu
alaƙaƙai kuma GOBARAR ANNOBA.
Nan fa dakarun suka ZAGE DAMTSE wajen kaiwa su Nabihat miyagun hare-hare.
Ana cikin wannan artabu ne wani garjejen sadauki, ya kaiwa wata daga cikin 'yan
matan wani wawan sara, da nufin tsinke mata wuya amma budurwa ta sunkuiya cikin zafin
nama, takobin sadauki ta sari iska. Kafin ya sake mayar da martani, budurwar ta cire wata
siriyar wuƙa a damtsenta s caka mashi a maƙogaranshi, sannan ta sanya ƙafarta ɗaya ta daki
ƙirjin shi da dukkan ƙarfin ta.
Saboda da matuƙar ƙarfin dukan sai da ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya
faɗa cikin tekun yana mai tsandara ihu.
Kawai sai budurwar ta sake afkawa cikin dakarun ta ci-gaba da saran su.
Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne SADAUKi Sharkar ya samu nasarar make Nabihat ta faɗi
ƙasa, magashiyan nunfashin ta na fita daƙyar, kawai sai ya sanya hannunshi ya damƙo wuyanta
ya tattare dukkanin karfinshi da nufin karya wuyan Nabihat.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Nabihat ta dunƙule hannayen ta biyu ta
girɓawa sharkar naushi a fuska.

Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa a sama sau uku, sannan ya kife a ƙasa,
yana mai tsandara ihu sakamakon zafi da zugin da ya ji, haƙorinshi guda ɗaya ya yi fitar burgu
daga cikin bakinshi

11 / 12