Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Usman Sufi.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Hausa Read

Chapter   8 / 12

21K to 24K   out of 34.1K words

dako wawan tsalle daga inda yake tsaye ya daki ƙirjin
jarumin dake samun nasarar da dukkan ƙarfin shi. Saboda ƙarfin dukan sai da jarumin ya yi sama yana mai tsandara ihu sannan ya faɗo
ƙasa a matuƙar galabai ce, hannayen biyu suka karye ji kake ruƙus! Ƙas.
Cikin matuƙar al'ajabi jama'a suka duba domin su ga ko wane ne, ai kuwa koda suka yi arba da
sarki lazwayr sai suka cika da matuƙar mamaki, domin sun san cewa tabbas koma wane ne shi
baƙo ne kuma ya jifa kanshi a cikin bala'i, domin ba ka yi laifin komai ba ma sarkin yaƙi Darusu
ya zalunce ma ballantana ka shiga gonar shi. Sarki Lazwar ya matsa izuwa inda ɗayan jarumin ke kwance ya tashe shi zaune ya karkaɗe
mashi ƙurar dake jikin shi.
Al'amarin da ya yi matuƙar fusata sarkin yaƙi Darusu kenan zuciyarshi ta kama tafarfasa
tamkar zata kone, kawai sai ya dakawa dakarun shi tsawa suka zare makaman su suka yi ɗauki
kan Lazwar.
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi
nan fa artabun ya zamto abin tsoro da kuma ban al'ajabi, domin ga shi dai sarki Lazwar ba ya
riƙe da makami amma sai ya zamtowa dakarun alaƙaƙai kuma GUGUWAR AJALI suka rasa
yadda zasu yi da shi.
Duk wanda ya gabzawa naushi a wata gaɓa a jikin shi sai ka ji ta ƙarye ta yi ƙara ruƙus!
Ƙas.
Kuma ya wanzu yana zillewa hare-haren dakarun cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA
BAJINTA irin ta ZARATAN MAYAKA,
Nan fa ihu da kururuwar dakarun gami da ƙarar karafniyar karafa ta cika dodon kunne, nan fa
ya zamana cewa waɗansu dakarun na daban ya rugawa izuwa kan sarki Lazwar cikin matuƙar
fushi, bisa ganin yadda yake ragargazar 'yan uwan su.
Kafin cikar daƙiƙa arba'in sarki Lazwar ya bazar da dakaru fiye da saba'in, dukkanin su sun
zube a ƙasa magashiyan suna nishin wahala.
Nan fa zuciyar sarkin yaƙi Darusu dake tsaye a gefe guda ta kama tafarfasa tamkar zata
fasa ƙirjinshi ta fito waje, amma kuma wani abu da ya faɗo mashi arai shi ne.
Tabbas wannan baƙon jarumi ya cika GWARZON DUNIYA yadda ake bukata, kuma tabbas idan
na kai shi ga mai girma Ladiyas zan samu ƙarin daraja da girmama wa, shin me zai hana ka
kama shi a matsayin bawa ga tafi da shi ga mai girma Ladiyas?
Koda gama yanke wannan shawara sai sarkin yaƙi Darusu ya shammaci sarki Lazwar ya
lallaɓo ta bayan shi ya dunƙule hannunshi ɗaya ya kirɓa mashi wawan naushi a fuska a gadon
bayan shi. Saboda ƙarfin dukan sai da ƙashin bayan Lazwar ya yi ƙara ya faɗi ƙasa sumamme.
Cikin matuƙar farin ciki sarkin yaƙi ya yi umarci waɗansu dakaru suka ɗaure hannayen
Lazwar da wata sarƙa suka ɗora shi a kan doki.
Nan take Darusu ya kama dokinshi ya haye ya sakar mashi linzami ya durfafi hanyar da zata
sada shi da gidan sarauta dakarunshi suka rufa mashi baya
Waɗansu kuma suka shiga ɗaukar dakarun suka samu raunuka domin ba su taimakon
gaggawa.

Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a lokacin da ya shiga cikin gari domin
saduwa da baiwa Sharifa.
Al'amarin yaro Imran kuwa, lokacin da fice daga masaukin su bayan ya kammala kalaci sai
ya wanzu yana ratsa saƙo da lungu na birnin Istanbul. Domin cigiyar 'yar uwarshi, hakan ya
sanya duk wajen da hango taron jama'a sai ya je ya tsaya, domin ya ga me ake gudanar wa.
Yana cikin hakan ne ya iso wani waje mai cike da tarin al'umma, wani dattijo yana tsaye yana yi
masu wani jawabi, kallo ɗaya za ka yiwa mutumin ka fahimci cewa ya kasance jagoran wani
addini.
Kawai sai yaro Imran ya ja ya tsaya yana sauraren jawabin sa.
Malamin na cikin jawabin shi sai yaro Imran ya ɗaga hannunshi ya ce "ya shugabana ina da
wata tambaya idan ba za ka damu ba. Koda jin wannan tambaya daga bakin Imran sai gaba
ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matuƙar mamaki.
Domin ba a taɓa jin wanda ya yiwa matsafi Shamrul wata tambaya ba akan abin da yake bayani
game da bautar gunki.
Cike da matuƙar mamaki matsafi Shamrul ya dubi yaro Imran da fuskarshi ke rufe da
rawani idanuwan kaɗai ake gani ya ce da shi ''ya kai wannan yaro faɗi tambayar ka ina
sauraren ka".
Yaro Imran ya yi gyaran murya sannan ya ce "ya kai wannan malami tambaya ta a gare ka
ita ce, shin waɗanne mutane ne suka fara bautar gumaka a duniya kuma mene dalilin su na yin
hakan?
Tambaya ta biyu mene ne ya sanya gaba ɗaya gumakan da ake bauta mu ne muke sassaƙa su
da hannayen mu, to ya ya abin da mune muka samar da su daga babu a ce kuma su ne allolin
mu?
Koda jin waɗannan tambayoyi daga bakin yaro Imran sai fuskar matsafi Shamrul sai ta
sauya daga walwala izuwa fushi, kuma ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi ainun.
Amma saboda kar jama'ar dake wajen su fahimci hakan sai kya basar.
Abin da matsafi Shamrul bai sani ba shi ne haƙiƙa maganganu Imran sun yi tasiri a
zukatansu baki ɗaya al'ummar dake wajen.
Tabbas waɗannan tambayoyi da wannan yaro mai hikima ya yi sune abubuwan da ya kamata
kowannen su ya sani kafin ya kasance cikin wannan addini na bautar gumaka,
Nanfa mutanen dake wajen suka dunga cewa a amsa masu waɗannan tambayoyi haƙiƙa
muna so mu ji ya tabban malami.
Sautin muryoyin jama'ar ya sake ruɗa matsafi Shamrul, kuma suna amsa kuwwa izuwa cikin
birnin, tare janyo hankulan sauran mutanen gari suka dunga tuttɗowa izuwa wajen, sa'adda da
matsafi Shamrul ya ga cewa adadin mutanen da ke wajen yana cigaba da hauhawa, kuma ya
tabbatar da cewa idan ya amsa tambayoyin abin kunya zai faru. Sai kawai ya yi wuf! Ya shafi wani gurun tsafi a damtsenshi na hagu, nan take cikin daƙiƙa biyu
kacal hadari ya taso gadan-gadan sama ta yi duhu, a ka fara tsawa, walƙiya gami da iska mai
ƙarfi, nan fa waje ya hargitse jama'a suka fara darewa suna rugawa izuwa unguwannin su domi
kar ruwa ya yi masu ɓarna. A bangaren yaro Imran kuwa yana ɗaga kanshi sama ya kalli hadarin sai ya fahimci
cewa, an samar da shi ne ta sihirin tsafi domin matsafi Shamrul ya kawar da hankulan al'umma
daga amsar tambayoyin da ya yi nashi. Kawai sai ya yi dariya ya juya ya nufi hanyar koma gida,
domin ya tabbatar da cewa idan har matsafi Shamrul ya kasa amsa wa mutane tambayoyin za

su juya mashi baya su daina karɓar fatawar addini daga gare shi, sai da yaro Imran ya bar
wajen, sannan matsafi Shamrul ya daina waigen shi ya na satar kallon shi
Wannan shi ne abin da ya faru da yaro Imran


BABI NA SHA ƊAYA


Al'amarin Gimbiya Mashlira kuwa dukkan abin da wakana da masoyin ta sarki Lazwar a
kasuwa tun daga lokacin da ya fafata artabu da waɗannan dakaru har izuwa lokacin da sarkin
yaƙi ya yi umarni aka ɗauke shi aka nufi gidan sarautar, tana tsaye a gefe guda tana kallo.
Koda ganin hakan sai hankalin ta ya dugunzuma ainun, bisa ganin cewa babu tabbacin
za su bar shi a raye, bisa mummunan laifin da ya aikata. To kenan idan har hakan ta faru za bai
samu damar cika burin shi na saduwa da baiwa Sharifa ba, harya bayyana mata bukatar shi,
wai shin ma ta ya ya zan iya barci a daren yau matsawar ba na jin motsin masoyina Lazwar a
kusa da ni, bayan cewa zuciyata ta kamu da matuƙar kaunar shi.
Tabbas zan kasance a tare dashi duk TSANANI DA UKUBA koda kuwa bazai taɓa gane
cewa ni ba ce
Sa'adda gimbiya Mashlira tazo dai-dai nan a tunaninta, sai kawai ta dunga bin sahun su
sarkin yaƙi Darusu a baya ba tare da wani ya gan ta ba , lokacin da ta ga cewa an kusa isa
gidan sarauta sai kawai tayi ruf ta rafke ɗaya daga cikin dakarun, a cikin wani lungu ta maye
gurbin tufafin dake jikinta da na shi, sannan ta kama dokinshi ta haye ta shiga cikin dakarun ta
saje da su ba tare da wani ya gane ta ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da gimbiya Mashlira 'yar sarkin maridai Zammar, bayan ta
fice daga masaukin su dake tsakiyar birnin Istanbul.

BABI NA SHA BIYU

Al amarin yarinya shuraiba kuwa lokacin da ta gabza wa ɗaya cikin dakarun dake karɓar
haraji naushi a magoranshi ya faɗi ƙasa matacce, sai sauran suka zare kulaken su cikin
matuƙar fushi suka yi ɗauki kan ta.
Ko da ganin hakan sai almijiran dake wajen suka ruga suka bar wajen domin su tsira da
rayukansu.
Ita kuwa Shuraiba sai ta gyara tsayuwar ta tana jiran isowar dakarun a lokacin da jama'a
suka buɗe masu fili mai faɗi sosai.
Lokacin da suka iso sai aka yi KARON MAZA suka afkawa Shuraiba da azababban yaƙi, suka
wanzu suna kai mata duka da kulaken cikin zafin nama domin su yi mata kisan farat ɗaya.
Ana fara wannan artabu ne wani abin mamaki ya fara gudana, domin kuwa Shuraiba ta
zamo tamkar shaidaniya a tsakanin dakarun, ta wanzu tana zillewa tare da hare-haren dakarun
cikin matuƙar zafin nama.
Nan fa ta dunga haɗa karo tsakanin dakarun, suna zubewa kasa magashiyan.
Amma sai su yunƙurawa su sake afka mata da yaƙi.
Lokacin da aka shafe tsawon rabin sa'a ana wannan karon batta sai ya zamana cewa
Shuraiba da dakarun sun fara galabaitar da juna

Ana cikin wannan yaƙi Shuraiba tayi wuf ta ƙwaci wani kulki a hannun ɗaya daga cikin dakarun,
ta shiga gabza masu duka a ƙafafuwansu, kafin lokacin mai tsawo, ƙafafuwan dakarun sun
sage, sun yi tsami gaba ɗayansu su sun zube a ƙasa suna nishin wahala
Nan fa jama'a suka dunga shewa suna yiwa Shuraiba jinjina gami da kirari cikin matuƙar
farin ciki bisa ganin cewa ta karya alƙadarin dakarun
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai akaga jiyo haniniyar dawakai gami da bugun tambura
daga can nesa kaɗan, alamun dake nuni da cewa wani ma'abocin sarauta yana gab da
bayyana.
Koda jama'a suka waiga baya sai suka hango ashe tawagar gimbiya Lamrat ce.
Cikin matuƙar firgici suka sunƙuiya ƙasa bisa gwiwoyin su, domin girmamawa a gare ta, sannu a
hankali har suka iso izuwa wajen.
Kawai sai aka ga keken dokin dake ɗauke da gimbiya Lamrat ya tsaya dai-dai inda yarinya
shuraiba take tsaye
Take Waɗansu dakaru mutum biyar suka ruga izuwa inda Kofar keken take suna masu
durƙusawa ƙasa bisa gwiwoyin tare shimfiɗa gadon bayansu, sannu a hankali ƙofar keken
dokin ta buɗe, sai ga gimbiya Lamrat ta fito ta taka gadon bayan dakarun ta sauko ƙasa.
Sanye take cikin kariyar alƙyabba da aka yi mata cin baki da zaren lu'u lu'u da zubar
daju, sanye a kanta akwai wani kambu na sarauta na zinare fuskarta rufe take da wani mayafi
idanuwanta ma'abota kwarjini kaɗai ake gani.
Kai tsaye gimbiya Lamrat ta taka da ƙafafuwanta ta durfafi inda yarinya Shuraiba ke tsaye
wacce ita ce kaɗai bata faɗi ƙasa domin girmama a gare ta ba.
Lokacin da ya rage saura taku uku a tsakanin su sai gimbiya ta ja ta tsay, ta kai duba izuwa kan
dakarun da Shuraiba ta a raunata, sannan ta dubi Shuraiba tana mai ƙura mata idanu ko
kiftawa ba ta yi.
Nan take su duka biyun suka ji zukatansu na buga wa da ƙarfi wani abu ya ɗar su a cikin ta.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa gimbiya Lamrat mamaki kenan, ta tambayi kanta a cikin
ranta tana mai cewa. Shin mene ne ya sanya zuciyata ta buga lokacin da na yi arba da wannan
yarinya? Shin ko kuwa hakan na nufin har yanzu 'yata ƙwaya ɗaya tilo tana raye?
Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, kawai sai ta cigaba da ƙurawa mata idanu.
Daga can sai ta buɗi baki cikin zazzakar murya mai ɗaɗin sauraro ta ce "ya ke wannan
yarinya shin wace ce ke kuma mene ne dalilin da ya sanya kika zaɓi ki yi bara ki ƙyale sana'a,
wacce za ta ba ki damar ci da sha.
Ko da jin wannan tambaya sai yarinya Shuraiba ta dubi gimbiya cikin ladabi da girmama wa ta
ce "ya shugabata ki yi sani cewa ni baƙuwa ce a wannan birni, bani da kowa na shigo wannan
birni domin neman mahaifiyata da aka rabu Ni da ita tun ina yarinya ƙarama".
Da jin amsar wannan tambaya sai gimbiya ta sake jin zuciyarta ta buga da ƙarfi a karo na biyu
Koda ta sake ƙurawa Shuraiba idanu sai ta taga tana ɗauke da kamanni iri ɗaya sak da na
masoyin ta kuma uban 'ya'yanta sadauki Murrasu.
Nan take abubuwan da suka faru da masoyinta da sarki Ladiyas ya fara dawo mata a cikin
ƙwaƙwalwarta, cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta shiga tafarfasa tamkar zata ƙone.
Tsananin ƙiyayyar sarki Ladiyas ta ci gaba da ruruwa a cikin ranta.
Haƙiƙa babu makawa wannan yarinya ba wata bace face 'yata Shuraiba, wata zuciyar kuma ta
ce da ita, amma a halin yanzu bai dace ki wani yasan da hakan ba, dole ki yi jinkiri ki sake
nazari akai sosai.

Koda gama tunanin hakan sai ta dubi Shuraiba ta ce "ya ke wannan yarinya idan ba za ki
damu ba ina so ki zauna tare da ni, har izuwa lokacin da zan sa a nemo maki mahaifiyarki".
Da jin wannan batu sai farin ciki ya kama yarinya Shuraiba ta ce a cikin ranta, tabbas wannan
wata dama ce da zan ɗauki fansa a kan sarki Ladiyas da kuma gano inda mahaifiya ta ke.
Shuraiba ta ce "na amince da wannan alfarma da kika yi min, amma nima ina roƙon
alfarma a wajen ki da a daina karɓar haraji a wajen waɗannan almajirai har abada".
Koda jin wannan batu daga bakin Shuraiba sai gimbiya Lamrat ta cika da matuƙar farin ciki ta
dubi wani badakare a dake tsaye a gefenta ta ce da shi ''daga yau na haramta karɓar haraji a
hannun dukkan wani almajiri dake wannan waje.
Badakaren ya risina ya ce ''an gama ranki shi daɗe''.
kawai sai ta kama hannun Shuraiba ta durfafi inda keken dokinta yake suka shiga izuwa
ciki suka zauna a tare, sannan badakaren dake kula da keken ya zaburi dawakan kenan ya ci
gaba da tafiya.
Nan fa jama'a suka cika da matuƙar mamaki, almajiran dake wajen kuma sai sai farin ciki ya
turnuƙe zukatansu, suka shiga yin shewa, kiɗa da rawa bisa ginin cewa Shuraiba ta ƙwato
masu 'yanci a hannun miyagun dakarun.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya shuraiba.


BABI NA SHA UKU


Al'amrin matsafi Shamrul kuwa lokacin da ya rabu da yaro Imran bayan ya kunyata ta shi a
gaban mabiya addininshi.
kai tsaye sai ya nufi hanyar da za ta sada shi da ɗakin abin bauta gunki Zallas.
Da shigar shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa yana mai yi mashi sujjada, a karo na farko sai
matsafi Shamrul ya ji wata irin kakkausar murya ya mamaye ɗakin baki ɗaya
"ya kai Shamrul ma'abocin biyayya a gare mu dago kanka sama domin ka ji abin da zamu sanar
da kai.
Cikin matuƙar al'ajabi matsafi shamrul ya dago daga sujjadar, domin tsawon shekaru
saba'in yana bauta ga gunki Zallas amma bai taɓa jin ya yi mashi magana ba sai a yau.
Kakkausar muryar ma'abociyar tsoro da firgitarwa taci gaba da cewa "haƙiƙa mun san kana
cikin matuƙar fushi da damuwa akan abin da ya faru tsakanin ka da hatsabibin yaro Imran, na
kunya taka a barnar jama'a, haƙiƙa yaro Imran ya taɓo tsuliyar dodo, domin ba zai taɓa samun
nasarar yaɗa addinin musulunci a wannan birni namu ba. Kuma lokaci ya yi da zamu kawar da dukkan wani musulmi a doron ƙasa.
Abin da muke so da kai shine ka kwantar da hankalinka tamkar tsumma a randa, a ranar da

8 / 12