Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Usman Sufi.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Hausa Read

Chapter   5 / 12

12K to 15K   out of 34.1K words

kallon abinda ke faruwa, dola ne ya yi wa
Allah godiya bisa ganin cewa mushriki maƙiyin Allah zai yi mutuwar wulakanci.
Koda kyakyawan yaron ya fahimci cewa wutar zata iya kona su sarki Lazwar da har yanzu
su ke cikin halin barci.

Sai kawai ya ya yiwa hadimin shi umarni da ya kai masu ɗauki.
Cikin zafin nama aljani ya miƙa hannayenshi biyu ya ɗauko sarki Lazwar, Mashlira, shuraiba,
aljani Za'aratun-layal, sarkin yaƙi da bawa Shamsal, ya ajiye su bisa gadon bayanshi, sannan
ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luu!. Ya sauka a turba a dai-dai lokacin da aljani
Durusul-fannar ya ƙone kurmus tokar gawarshi ta sheƙe cikin iska. Ya yin da ya sauka a turba sai ya sauke su sarki Lazwar a ƙasa.
Yaron ya koma gefe guda ya share ƙasa yana mai fuskantar alƙibila ya fara gudanar da
ibadar shi irin ta ma'abota addinin Musulunci, kawai sai aljanin ya tsaya a gefen shi a yana mai
koyi da shi, Sarki Lazwar ne ya fara farkawa daga barcin, sannan gimbiya Mashlira, bawa
Shamsal, sarkin yaƙi, yarinya Shuraiba aljani Za'aratun-layal a ƙarshe. Lokacin da kowa ya wartsake ya dawo cikin hayyacin shi, suka arba da wannan kyakkyawan
yaro da hadimin shi suna gudanar da Sallah,
sai kowa ya yi turus! Cike da matuƙar mamaki gami da al'ajabi.
Abu na farko daya bawa ko mamaki shi ne yadda yaron ke gudanar da ibadar cikin tsafta da
tsari mai ban sha'awa, sannan ya aka yi su ka tsira da rayuwar su? Kuma ina aljani
Durusul-fannar ya ke?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kan su kenen, kawai sai suka zuba idanu suna
kallo, har ya kammala ibadar sannan ya juya ya fuskanci su sarki Lazwar ya ce "ya ku
waɗannan mutane ku yi sani cewa ban ceto rayuwar ku domin ku saka min da wani abuba, face
kawai saboda Ubangiji na ya bayyana mini ku a cikin mafarki na. Kuma ta silar ku ne zan samu
nasarar gano 'yar uwata da ta ɓace, kimanin shekaru bakwai.
Bisa wannan dalili ne ya sanya na ce ci rayuwar ku bisa taimakon Ubangijina, duk da cewa
ta mai bautar Allah maɗaukakin sarki, ku kuma kun kasance kuna bauta wa gumaka".
Sa'adda su ka ji wannan batu daga bakin yaron sai kowa ya sake cika da matuƙar
mamaki da al'ajabi.
Ita kuwa yarinya Shuraiba sai ta ƙura wa yaron idanu, gami da yi mashi wani irin kallo da ita
kan ta bata san dalilin yin shi ba, tana mai cewa a ranta.
Shin wai dama akwai wani Ubangiji da ya halicci mutane bayan allolin mu?
Amma addinin wannan yaro yana tattare da tsafta da kayatarwa,
Nan take ta ji tana matuƙar ƙaunar yaron a cikin ranta tamkar ta daɗe da shaƙuwa da shi.
Sarki Lazwar ya buɗi baki ya ce ''ya kai wannan yaro mai ban al'ajabi shin mene ne sunan ka da
labarin ka?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai yaron ya yi murmushi da ya ƙara wa fuskarshi kyawu
ya ce "Ni suna na Imran ibn Nadir na fito daga ƙasar Yemen ne neman 'yar uwata wacce na
rasa ta sakamakon farmakin bazato da aka kawo birninmu, ita ce kaɗai ta rage mini a cikin
jinina, sannan babban burina shine kuma na yaɗa addini na gaskiya a doran ƙasa, game da
tambayar ka kuwa mene ne labari na wannan hikaya ce mai tsawo yanzu babu lokacin yin shi
sai dai a nan gaba".
Ko da jin amsar wannan tambaya sai sarki Lazwar ya juya ya dubi sarkin yaƙin shi yana
mai yi mashi raɗa a kunne ya ce "ya dirkar birnina shin yanzu kana ganin zamu amince da yaro
Imran mu yi wannan tafiya tare da shi alhalin ya kasance mabiyin addinin Musulunci, kuma
sanin kanka ne cewa iyayenmu da kakanninmu mun mutu ne bisa ƙiyayyar wannan addini. Sannan ka san babu yadda za'a yi sirrikan tsafi na su yi tasiri a wannan tafiya matsawar
yaro Imran zai karanta abin da ya shafi addinin su,

Abu ɗaya ma da nake tsoro ya kasance shi ne a koda yaushe zan iya rasa sirrikan tsafi na.
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai sarkin yaƙi kara bakinshi dai-dai kunnen
sarki cikin ladabi ya ce "ya shugabana tabbatas zancen ka dutse ne, sai dai wani hanzari ba
gudu ba, baka ganin cewa dukkanin abokan tafiyar mu sun faɗa tarko da yawa amma sirrikan
tsafin ka ba su tseratar damu ba. Yanzu da wannan yaro bai ceci rayuwar mu ba da yanzu
kuma wani labarin ake yi daban ba wannan ba.
Ni dai shawara ta shine ka ga dai Imran yaro ne ƙarami babu ta yadda za ayi ya canja
tunanin ɗayan mu mu shiga addinin shi, kawai zamu yi amfani da shi ne, domin cimma buƙatar
mu daga baya sai mu yi watsi da shi".
Da jin wannan shawara ta sarkin yaƙi sai sarki Lazwar ya bushe da 'yar karamar dariyar
mugunta ya dafa kafaɗunshi ya ce "an gaishe ka namijin duniya shi yasa dai-dai da sa'a ɗaya
bana son a ce na rabu da kai saboda irin wannan al'amari,
Ko da gama wannan shawara sai sarki Lazwar ya dubi yaro Imran ya ce "ya kai wannan Imran
ma'abocin taimako haƙiƙa mun amince mu yi wannan tafiya tare, sai dai bisa sharaɗi guda,
sharaɗin kuwa shi ne iya tsawon wannan tafiya da zamu yi har ka sadu da 'yar uwarka, ba za ka
tilasta ɗayan mu cewa sai ya yi imani da Ubangijin ka ba"; Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yaro Imran ya yi lallausar murmushi a
gare su ya ce "ka kwantar da hankalin ka ya kai wannan sarki mai daraja ai addini ba a tilasta
mutum ya shige shi face idan ya yi niyya da kan shi,
Da jin wannan batu daga bakin Imran sai kowa ya gyɗa kai alamar gamsuwa, yaro Imran ya
mayar da duban shi zuwa ga aljanin shi ya ce "ya kai Hadimul-khair ina mai umartar ka ka shiga
izuwa cikin wannan daji ka samo mana abin da zamu yi kalaci gami da ruwan sha.
Aljani Hadimul-khair ya risina ga yaro Imran ya ce "an gama ya shugaba na. Yana gama
faɗin hakan ya kaɗa fuka-fukanshi ya nausa izuwa cikin dajin,
Jim kaɗan bayan shuɗewar waɗansu 'yan daƙiƙu sai Hadimul-khair ya dawo ɗauke da waɗansu
nunannnun kayan marmari da suka haɗar da tuffa, gwanda, ayaba, lemu gami da ibini.
Ya ajiye a gaban Imran,shi kuma Imran ya yi umari kowa ya ɗebi wanda zai ishe shi, sannan
kowa ya shiga kimtsa cikinshi, ita kuwa damisar yarinya Shuraiba sai ta kama kiwon a wajen
tana kama kwari da kananan dabba tana lamushe su.
Bayan an kammala ne
an samu nutsuwa sai aka
ɗunguma a ka ci-gaba da tafiya, inda aljani Za'aratun-layal ya ɗauki sarki Lazwar, sarkin yaƙi,
bawa Shamsal da gimbiya Mashlira, amma sai yarinya Shuraiba ta ki yarda ta hau kan shi, inda
ta nemi alfarma a wajen naaro Imran da ya amince mata ta hau bisa kan aljanin sa tare damisa
Faizur. Al'amarin da ya yi matuƙar fusata sarki Lazwar kenan ya buɗe baki da nufin ya hana
yarinya Shuraiba hawa kan aljani Hadimul-khair, amma sai sarkin yaƙi ya dakatar da shi yana
mai yi masa raɗa a kunne ya ce "haba ya shugabana kar ka manta cewa Shuraiba tana da
matuƙar muhimmanci a wannan tafiya tamu, domin ita ce ta san sirrin birnin Istanbul dama shi
kanshi sarkin birnin, kar tun yanzu ka ɓata kiɗan da rawa, har Shuraiba ta fahimci cewa kana
ɓoye mata wani abu game da yaro Imran har ta yi ƙoƙarin shaƙuwa da shi ta fahimci addinin
shi.
Idan kuwa har hakan ta faru to kuwa zamu rasa su baki ɗaya wato Imran da Shuraiba.

Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai jikin sarki Lazwar ya yi sanyi ya koma
ya zauna aka cigaba da tafiya.

BABI NA BAKWAI

A can birnin Zawatul-ifdar kuwa, jama'a kuwa sun fara yabawa aya zaƙin ta, domin magajin
gari Yasiran yana yi masu MULKIN ZALUNCI da ya zarce na sarki lazwar.
Domin ɗan ƙankanin laifi mutum zai aikata sai a yanke mashi hukuncin kisa ko zaman gidan
kaso, yiwa 'ya'ya mata fyaɗe, ƙwace gami da fashi da makami ya yawaita a birnin Zawatul-ifdar.
Duk wanda ya yi sabon aure to ba zai tare da matarshi face an kai ta ga magajin gari
Yasiran ya tara da ita sannan zai karɓi amaryar shi kashe gari.
Yan kasuwa aka matsa masu da karɓar haraji, nan fa ya zamana cewa hatta 'yan majalisar
birnin sun fara ƙosawa da mulkin zaluncin Yasiran, suka shiga tunanin hanyar da za su kawar
da shi daga kan karagar mulki, duk da cewar a halin yanzu sun fi matuƙar tsoron shi fiye da
sarki Lazwar. Wata rana da hantsi lokacin zaman fada an cika maƙil da jama'a babu masaka tsinke, duk inda
mutum ya duba kawunan bil'adama ne rututu tamakar dandazon kiyasai, ana jiran fitowar
magajin gari Yasiran.
Ana cikin wannan hali kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji fadar ta kaure da wata irin
mahaukaciyar dariya mai ban tsoro, daga can sai aka ga Yasiran ya bayyana tsulum! A fadar
tamkar an jefo shi daga sama, hannunshi na dama riƙe da wata sharɓeɓiyar takobi, na hagun
kuwa riƙe da wani mashi an tsire kan wani mutum a jikin shi jini na zuba. Sa'adda jama'a su kayi arba da kan, sai suka ɗimauce 'yan majalisa kuwa sai jikkunansu suka
kama ƙyarma saboda matuƙar tsoro, ba komai ne sanya su ƙyarma face bisa arna da kan
sarkin fada, wato ɗaya daga cikin yan majalisar magajin gari Yasiran ya ɗaga hannunshi sama
fadar tayi tsit! Tamkar mutuwa ta kawo ziyara. Fuskarshi a murtke ya ce "ya ku al'ummar wannan fada mai albarka ku yi sani cewa,
wannan shi ne darasi ga duk wanda baya goyan bayan mulki na a wannan birnin".
Yana gama faɗin hakan sai ya yi jifa da kan sarkin fada a kas, cikin hanzari wani badakare ya
shigo fadar janye da hannun wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa, tana ta rusa kuka sai ya iso
da ita daf da ida karagar mulki take sannan ya risina ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa.
Sannan ya buɗi baki cikin ladabi ya ce "ga ta nan na zo da ita ya shugabana";
Yasiran ya dube shi ya ce "sai ayi hanzari akai min ita turakata".
Badakaren ya miƙe tsaye ya fice da budurwar wacce ke rusa kuka tana magiyar a rabu da ita,
komai rashin imanin mutum idan ya ga halin da budurwar ke ciki, dole ne ya zubar mata da
hawaye saboda matuƙar tausayi, da yawa daga mutanen fadar sai da su ka zubar da ƙwalla
sabo da matuƙar tausayin budurwar. Wannan shi ne abin da ya faru a can birnin Zawatul-ifdar bayan sarki Lazwar ya ɗora
magajin gari Yasiran a bisa sarautar shi ya shiga izuwa duniya.
Haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce, sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a
daɗe ba'a je ba, sai ga shi an shafe tsawon kwanaki arba'in da huɗu ana tafiya tsakanin sarki
Lazwar, gimbiya Mashlira, yarinya Shuraiba, sarkin yaƙi ,bawa Shamsal aljani Za'aratun-layal
tare da yaro Imran.

A iya tsawon wannan tafiya shaƙuwa mai karfi ta ƙullu tsakanin yarinya Shuraiba da yaro Imran,
kuma Imran ya bayyana abubuwan mamaki gami da ƙarfin ikon Ubangiji.
Domin sau talatin da bakwai yana ceto rayuwar su sarki Lazwar bisa taimakon Ubangijin
musulunci.
Bisa wannan dalili ne ya sanya Mashlira da Shuraiba suka fara kwaɗayin shiga addinin.
A ranar da kwana hamsin suka cika ne aljani Za'aratun-layal ya sauka a bisa wani daji dake
kusa da birnin Istanbul, nan fa farin ciki ya kama kowa shima aljani Hadimul-khair ya sauke
Imran da yarinya Shuraiba
Bayan kowa ya sauko sai aka shiga tattaunawa akan hanyar da kowa zai bi wajen shiga birnin
Istanbul, inda Shuraiba ta dubi kowa sannan ta yi gyaran murya ta ce
"akwai shawarwari da zan bamu waɗanda matsawar muka kiyaye su zamu shiga cikin birnin
Istanbul lafiya kuma mu fito lafiya sumul.
Da farko dole ne kowannen mu ya ƙaurace sanya tufafi masu tsadar gaske, ko wada ke nuna
wata alama ta mulki .
Na biyu gujewa ƙarya da ha'inci, sannan yin biyayya ga dukkan abin da ya shafi
masarauta.
Waɗannan sune shawararin da idan muka kiyaye su zamu cimma nasara.
Koda Shuraiba ta zo dai-dai nan azancen ta sai ta juya da dubi Gimbiya Mashlira ta ce "ya ke
Mashlira ya zama wajibi idan zaki shiga cikin wannan birni na Istanbul ke rufe fuskarki da
rawani, har zuwa lokacin da zamu kammala samun abin da muka shiga nema, domin tsananin
kyawun surarki zai jawo miki matsala. Koda yarinya Shuraiba ta zo nan a jawabin ta sai tayi bankwana da damisarta suna masu
zubar da hawayen rabuwa da juna, har sai damisar ta ƙule izuwa cikin daji ta daina hangen ta.
Ko da jin wannan batu daga bakin Shuraiba sai kowa ya gyaɗa kai cikin farin ciki, kawai sai
sarki Lazwar ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya nuna aljani Za'aratun-layal da ɗan yatsan
shi na hagu, take Za'aratun-layal ya riƙiɗa izuwa wani garjejen sadauki mai kwarjini daban tsoro,
sannan ya sake karanto waɗansu dalasiman tsafin take tufafin dake jikin su ya canja launi zuwa
makasƙanta, babu wanda zai ga sarki Lazwar da gimbiya Mashlira a wannan hali face ya cika
da mamaki bisa ganin yadda suka koma tamkar almajirai saboda tufafin dake sanye a
jikkunansu.
kaico! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka biyan buƙata ya fi dogon buri. kuma
ranar biyan buƙata rai da dukiya ba a bakin komai suke ba.
Kawai sai aka ɗunguma aka durfafi ƙofar birnin Istanbul gadan-gadan, shi kuwa yaro Imran sai
ya matsa kusa Shuraiba ya yi mata raɗa a kunne, sannan ya dawo da duban shi ga hadimin shi
ya ce dash ''ya kai Hadimul-khair ina ganin ya kamata ka kasance a ɓoye, koda ka bayyana har
sai lokacin da na buƙaci hakan" koda jin hakan sai Hadimul-khair ya risina ya ce ''an gama
ya shugabana, kawai sai ya ambaci sunan Allah gami da yiwa Annabi salati take ya bace bat,
tamkar bai taba wanzu wa ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Lazwar lokacin da suka iso izuwa birnin
Istanbul.


BABI NA TAKWAS

BIRNIN ZAWATUL-IFDAR

Al'amarin wannan budurwa da magajin gari yasiran ya yi umarni a kai mashi ita izuwa
turakar shi kuwa, ba wata ba ce face wata sabuwar amarya, kuma an ɗauko ta ne domin ya
keta mata haddi.
Lokacin da wannan badakaren ya isa da ita turakar sai ya tarar da kuyangi na ƙawata turakar
da kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, wani irin daddaɗan kamshi na tashi a ko ina.
A harabar turakar da bakin ƙofa kuwa dakaru ne birjik shirye cikin gagarumar shigar yaƙi
hannayensu ɗauke da miyagun makamai.
Ya yin da amaryar ta tsinci kanta a ciki turakar sai ta sake fashewa matsanancin kuka mai
tsuma zuciya, tsawon sa'o'i tana cikin fargaba da tsoron abin da zai faru gare ta, kuma tana
tuna halin da angon ta ya ke ciki.
Haka ta kasance a cikin wannan hali har duhun dare ya fara nisa, a cikin wannan hali ne
ta ji motsin shigowar magajin gari Yasiran ba, nan fa tsoro ya kara kamata ainu.
Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai kawai ta ga wani kyakkyawan
tsuntsu yana fitar da wani sautin kuka mai daɗin saurare, yana shawagi a harabar turakar.
Cike da matuƙar kwadaituwa da son ganin tsuntsun, ta matsa izuwa tagar dake turakar ta leƙa
ai kuwa sai ta ga anyi wani rubutu a jikin fuka-fukan tsuntsun da harshen Larabci
kawai sai ta furta a bakinta, faruwar hakan keda wuya, ai sai ta ji dukkan baƙin ciki gami da
tsoron dake zuciyarta ya tafi, tamkar babu wani mugun abu dake shirin faruwa a gare ta.
Cikin farin ciki mara musaltuwa ta cigaba da karanta kalmomin a cikin ranta
A dai-dai wannan lokacin ta ji an turo kofar shigowa turakar, tana buɗe wa sai ga Yasiran ya
bayyana, yana sanye da wani mayafi na alhariri da ya rufe daga cibiyarshi izuwa gwiwarshi.
Sa'adda amaryar ta yi arba da shi saboda matuƙar tsoro ba ta san sa'adda ta faɗi ƙasa
ba, jikinta na ƙyarma tamkar mazari, shi kuwa magajin gari sai ya nufi inda take yana mai
bushewa da dariyar mugunta har da ƙyaƙyatawa,
Lokacin da ya matso

5 / 12