Uwar Gafalallu Book By Oum Yasmeen

Author :  Oum Yasmeen Category :  Read Hausa Novels

Chapter   6 / 7

15K to 18K   out of 20.3K words

na rawa kamar mazari...

TUDUN YOLA

A gajeye ta tayi parking daidai fitowar ASH da file a hannunsa yace '' Hajiya ba dai fita kikai ba
ba driver...,

fitowa ta ƙara sa yi tace '' wallahi kuwa yau training nayi na shiga kasuwa na danyi siyayya
wallahi naji dadin jikina..,

haba hajiya me isaka kikai haka bayan kinsan ciwon ki nan da anjima zaki zo kina cewa bayan
ki kafar ki na ciwo

kar ka damu insha Allahu hakan ma baza ta faru ba wallahi yau na haɗu da wata yarinya yar
albarka ba ruwanta jakata ta waɗi ta dauko min ta bani ita bata dubi yawan kuɗin da suke cikin
ta ba lokaci ɗaya naji ina son yarinyar

kai ya gyaɗa yace '' Allah ya kiyaye gaba ya buɗe motar sa ya shiga domin be ga abin da ya
hada shi da zancan yarinyar ba kai Hajiya ta girgiza tace '' Allah ya shirye ka ASH duk maganar
da ya shafi mace baka so...,

buɗe motar ta tayi ta dauko kayan da tayi siyayya ta shiga main Parlour Hajiya yanzu nake
shirin kiran ki sannu da zuwa

ajiye kayan hannun ta tayi tace '' yauwa jidda ya kike..?,

Alhamdulalilah komai lafiya

zama Hajiya tayi tace '' ina su ikram..,

suna makaranta nan da anjima za su tawo nan na shiga wajen inteesar na tarar tana bacci

ajiyar zuciya ta sauke tace '' maganin da ake bata ke sakata bacci har uku za ta kai tana
bacci...,

Allah dai ya bata lafiya

amin ya Allah baba lantana da sauri ta fito daga kitchen tace '' Hajiya sannu da zuwa..,


yauwa sannun ki ya aiki

Alhmdllh ta faɗa tana tsugunawa a ƙasa cikin sauri Hajiya tace '' baba dawo nan ki zauna dan

Allah ki dinga sakin jikin ki ai an zama ɗaya ni wallahi bana son wannan fadancin ki dena yi min
shi..,

zama ta gyara tana cewa nan ma ya isa

baba lantana Dan Allah Dan kawo min ruwa wallahi kinga duk da ba wata rana bace tayi na fita
amma maƙoshina duk a bushe

tashi tayi tana cewa sannu Allah ya baki lafiya

amin ya Allah ta faɗa tana mai da kallon ta kan tv tace '' wallahi wallahi wata na gani nayi wa
ash sha'awar ta..,

da sauri aunty jidda ta kalle ta tace

'' Hajiya ba ga ni'imatullah ba yarinyat na da kirki wallahi ni wallahi nayi mai sha'awar auren ta
ga yadda take nunawa inteesar soyayya...,

jidda duk na karya ne wallahi kalli sam yarinyar ba tayi min ba idanuwanta a buɗe yake gwara
na sama mai karamar yarinya wacce zata so shi ɗan Allah bata san waye shi ba ta zauna da shi
tsakani da Allah amma kinga masu cewa suna son sa wallahi akwai abin da suka gani jidda

Gaskiya bana tunanin haka tun da kince haka ga sakina nan itama yar manyan mutane ce idan
ya aure ta zai ji daɗin zama da ita

jidda abin da nake hangowa sam bashi kike hangowa ba shi ya saka zakiya ta fiki sanin ya
kamata

ɗaukan wayar ta tayi tana cewa hajiya kenan yanzu gaskiya fa nake faɗa badai wacce zata kula
da inteesar ake nema ba

a'a ba ita ake nema ba zai yi aure ne domin ra'aya sunan manzon Allah idan Allah ya temake
mu ta kula da inteesar tamkar ita ta haife ta amma ni ba dan ita zai yi aure ba


Allah ya kyauta

Amin ya Allah ruwa baba lantana ta kawo mata amsa tayi ta fara sha sannan ta ajiye tace ''
Nagode..,

juyawa baba lantana tayi saukowa tayi tace '' baba lantana ga kayan nan kai su kitchen..,

ɗauka tayi ta kai su kitchen sannan ta ci gaba da aikin da take Hajiya tace '' wallahi dabi'un

yarinyar ya burgeni jaka ta na yar a kan hanya ban sani ba amma yarinyar nan yar mutunci ta
ɗauka ta dinga bina har sai da ta kawo min ita naji dadi sosai wallahi...,

yanzu Hajiya domin tayi miki wannan aikin shine ta sace zuciyar ki..? abu nawa su ni'imatullah
suke miki..?,
jidda kenan ke yarinya ce ba zaki taɓa gane ina na dosa ba wasu mutanen suna tare da kai dan
wata ni'ima da Allah yayi maka randa ba ni'imar nan kai da banza duk daya dan haka ki kula ki
gane ni kwata kwata bata yi min ba yarinyar budaddan ido gare ta kar wata ran muyi dana sanin
hada zuri'a da ita
ita wannan yar wacce gida ce kafin kiyi wani abu kiyi bincike

insha Allahu zan yi sosai sannan sai muje gurin maga batan ta ayi magana

Allah isaka yar mutanen kirkice ba kara da kiyashi bace

idan har ta gari ce ba ruwana da halin iyayenta rayayye yana fitowa a cikin matacce haka
matacce yana fitowa a jikin rayayye be kamata muna yiwa mutane kuɗin goro da wanda ya
dace a faɗawa da wanda be dace a faɗawa

anya kuwa yarinyar nan ba asiri tayi miki ba ita ni'ima kin ga tayi wani abu da be dace ba

dariya hajiya tayi tace

'' jidda kenan yau na taɓa ganin ta ita kanta bata san wace ce ni ba...,

Allah ya saka haka amma yanzu dan adam abin tsoro ne wallahi irin wannan yabo haka yau ki
hadu da ita ki dinga yaban ta

Hmmm Allah ya kyauta

Amin ya Allah ta faɗa tana tashi daga zaman da tayi tace '' zan leƙa gidan su zainab naga
kwana biyu bana ganin ta ko a charting ba magana muke ba...,

sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya

amin ya Allah ta faɗa tana fita

dauko waya tayi tana karanta Alkur'ani mai girma ko zata samu sauki a zuciyar duk lokacin da
ta tuno da yar uwarta ta kanshi ga wani hali tana fatan Allah ya kai rahama kabarinta

Wannan kenan

kora ce ta lafa kowa ya fito daga inda ya ɓoya yar kwalas yace

'' wallahi Allah yau naga tashin hankali duk wacce take so tayi magana dani idan ba zata zo
gidan mu ba kirani a waya a she haka gidan ku ya koma sansanin huƙuba tun da nazo ake
ruɗamin jiki...da duka..,

yar kwalas wallahi Allah ban ga laifin ki ba mu ma da da inda zamu da tuni mun tafi wallahi
haba wannan wahalar haka kaga hakarkarina yarda yake min ciwo yadda kuka san daddatsa
min shi akai cewar asabe ta faɗa cikin tashin hankalin halin da take ciki

Mufeeda tace '' momcy ko zaki gurin me gyaran targaɗe...?,

kai rufan asiri su daɗa karya ni saya aike ni

ta fada tana ƙoƙarin zama shigowa yayi yana saɓa babbar rigar sa kafa me naci ban baki ba
asabe cewa take dan girman Allah kuyi min rai ku kai ni daki wallahi bani da kafar guduwa
ganin yana ƙoƙarin cin mata ta kama katanga ta shiga gidan hajara gwuicho kut melesi yan
sace sace da yaran ki ke min shine ba i she ki ba kika tawo da kan ki , ki daukar min kayana to
Allah ya kama ki asabe yau sai naci bura'uban ki wallahi daman nace miki zamu haɗu

cikin tashin hankali take kallon hajara gwuicho kiɓane da ita sosai duwawunta yayi kujera two
seater ga uban tunbu kallon hannun ta tayi yawa shebur ja da baya tayi tace

'' tsaki ji hajara gwuicho kinga wallahi Allah shazali ne ya kore ni tun safe muke abu ɗaya kwata
kwata yau bamu da kwanciyar hankali abin yaci tura yau kusan sauke min kafaɗa...,


kinga yimin shiru ɓarauniya ke kanki kin sani wallahi nafi ƙarfin ki dan habaicin da kike min ina
jiyoki dan haka yau dole na turbuɗa kanki cikin ruwan dafaduka

kallon katuwar tukunyar dake kan wuta ruwa sai tafasa yake da yake haraja gwuicho saida
abinci take.....

sauran fa page biyar na gama free page wannan tafiyar yanzu muka fara ta ko book one bamu
gama ba

Domin payment zaku turo ta wannan account din ₦500

Opay

Amina alhasan Muhammad

ku turo da she da ta nan

UWAR GAFALALLU

daga 25 free page ya tsaya ku hanzarta payment din ko domin jin yadda zata kaya

EPISODE 14-15

Dan Allah hajara gwuicho kiyi hakuri karma ta sake ta haƙura daman ke nake nema wallahi yau
sai na saita miki zama bake tara karuwai ba shazali ya faɗa yana ƙoƙarin cire malin malin dinsa

kallon kallo aka shiga tsakanin asabe da hajara gwuicho hadeyar yawu me kauri hajara gwuicho
tayi tace

'' Kaga shazali zo ka ɗauke ta ku tafi.. wallahi ba zaku zo gurin sana'ta ba ku daga min hankali..,

ke da gurin sana'ar taki kunci kundun uban ku shegiya me kama da tifar yashi yan zunan sai na
dilmiya kanki cikin wutar nan wani...ja da baya tayi gashi babu kowa a cikin gidan balle ta samu
a ɗauke shi tace

'' wallahi asabe kin cuce ni wannan tashin hankali dame yayi kama kiri kiri ina ji ina gani ki
hanani kwanciyar hankali a cikin gidana ban da zagin da kike aika min ta katan ga ta faɗa tana
goge hawayenta da suke zo bo mata a kurmin idanuwan ta


da hallacan rufe min baki nima haka naso ba gurin tsira nake nema ba ta fada tana ƙoƙarin zare
hannun ta daga riƙon da jahara gwuicho tayi mata amma ina hakan ya fassaka hajara tace

" Wallahi ba inda zaki ki kawo min masifa gidana sannan ki gudu gawara ya jibge mu tare
wallahi kamar yadda bazan iya guduwa ba kema dole ki tsaya..ba inda zaki..,

gumi ne ya ƙara karyo mata tace '' dan sabbatin Ubangiji ki cika ni...,

wallahi Allah ba inda zaki kafin ta ƙarasa shazali ya kara so da gudu suka shiga da cikin daki
hajara gwuicho ta zauna akan kafar asabe wani wahalallan ihu ta saki da sauri Hajara ta rufe
mata baki tace

'' baki da hankali zaki kuka sai kin saka ya shigo mana wallahi zan cillaki waje duk abin da ya ga
dama yayi miki...,

bata da bakin magana haka tayi shiru tana zare ido hawaye nabin kuncinta wani irin zogi kafar
ta ke mata ta tabbata ta karye wannan shegen duwawu na hajara yawa siddin shegu

Shazali kuwa sai wuru wuru yake ko zai ga inda suka shiga idonsa faɗawa yayi kan kazar

hajara ɗaukan ta yayi, yayi wulli da ita tare da murɗe mata kai yana cewa shegiya tun dazu take
ta ihu ai yanzu kyeje can kiyi musu kuka

ganin be gan su ba ya fita yana ta masifa da sauri hajara ta fito tana cewa Wallahi bazan yarda
ba dole asabe ki ɗauki wannan kaza ki biyani kuɗin ta

Asabe da ciwo yaci karfin ta tace '' haba Hajara ina ne ina cin mataccan abu ni da ba arniya ba
ki dai bawa ƙaren Haruna yaci...,

ke bana son iya shege wallahi dole ki ɗauki wannan kaza duk abin da zaki da ita kiyi da ita
amma wallahi dole ki siya ban da ma zuciyar musulunci ba sai na karya miki kashin kafaɗa ba
har ni zaki dinga bi da sharri to wallahi tun muna shedar juna ni dake kiyi gaggawar biyana
kudin wannan kazar dubu bakwai na siye taci abincin dubu biyu dubu goma sha ɗaya kenan

nida bani nayi abin nan ba dan Allah kiyi hakuri ta faɗa tana ƙoƙarin tashi da kyar take jan kafar
ta fusgota hajara tayi ta ɗauki kazar da shazali ya murɗe wa wuya tace '' maza biyani sannan
kibar gidan nan ....,

zama tayi domin abin yayi mata dai-dai tace '' wallahi daman ba son fita nake ba..,

au haka kika ce to wallahi yau na lahira sai yafi ki jin dadi asabe

kan bala me yashi tab jajar ubancan ke kar kiga ina yi miki lumbu lumbu yan zunan zan choge
kafata naci uban ki kowa ya sani fankan fankan bata kilishi

kai lallai matar nan kin raina min wayo yau zanyi maganin futsarar ki wallahi

mudai yi maganin juna nan fa fada ya kaure a tsakanin su haruna ne ya shigo yana tsalle hadi
da rausaya yana cewa ku tasu babba ku tasu ku taso ba me raba ku haka ya dinga mai maita
wa
ganin faɗan ya ƙara kamari ya canza salon waƙa wanda yafi wani ƙarfi ya cuci Dan uwansa
wallahi ba wanda zan kira ya raba ku taya dan akuya zai yi fada da giwa yace zai ci riba

baƙaramin wuya suka bawa juna ba ba zato ba tsammani Hajara taji asabe ta gartsa mata cizo
abin ka da ta samu tsoka ba ƙaramin shigarta cizon yayi ba ta kwalla kara ta sakita ba shiru
tana sakin ta ta fara cewa

'' Hajara daman na fada muku faɗa dani babu riba wallahi amma kika toshe kunnuwanki ai gashi
nan yanzu kinga uwar bari kin sakeni kaza kuma wallahi ko kobo bazan biya ba kije kine mi
wanda ya kashe miki abar ki ya biya ki kiga idan be sace ki ba kin koma samfurin mucija da
zani...,

Haruna kamo min ita wallahi ba zan yadda ba kaga fa a kirjina ta cije ni shegiya yar iska wallahi
sai nayi maganin ki

kin dade baki ba Hajara, nace kin dade baki ba kana sakewa ka karaso nan wallahi sai na ɗauki
iccen nan na saka maka a fuska shege da fuskar ka yawa kayi sujja a buhun gawayi...

kut ashe daman ina kallon ki kamar mutuniyar kirki ke ba ta kirki bace hmmm zan karaso ni
kuma tafasasshen ruwan nan zan diba nayi miki wanka da shi..

fakar idanuwansa tayi, tayi wuf ta fita maza maza haruna ka bita kar ka barta ko bayan layin
nan tayi bin ta yayi kafin ya cimmata har ta shiga gida dafa gwuiwowinta tayi tana haki tace

'' kuna ina dan Allah ku kawo min ruwa wannan bala'i har ina daga wannan sai wannan...,

a hankali baba da ba ta dade da dawowa ba ta dan leƙo da kanta dariya ce ta kubbuce mata
ganin yadda asabe ta koma yawa wata rubabbiyar gwanda fuskar nan taci bleaching duk tayi ja
sai zare ido take..

bayan ki asabe ga shazali nan zan sara miki gadon baya da gudu ta shiga dakin
ta dariya lami ta fara yi harda fati tace

'' gaskiya kin bani kunya asabe ina daban cin ki yake da sai ki tsaya ku dambatu ku buga yar
kashi ke da shi...,

takaici ne ya kama ta tace '' yanzu baba dariya kike dan bake yakewa abin da yake min ba haba
baba gaskiya haka be kamata ba..,


tura dauri gaban goshi tayi tana cewa dole fa shazali ya raina ki duk abinda da yake faɗa
gaskiya ne bakya tara karuwai ko dazu ba dan daudu bane ya bar gidan nan?

shiru tayi duk ranta ba dadi ta gyara zama tana miƙe kafarta tace '' mufeeda mufeeda..,

ta tafi makaranta

makaranta kuma ban hanata bin duk hanyar da shegen yaron nan yabi ba kai wannan jaraba
har ina anya kuwa ba asiri yayi mata ba tabi ta nane mai ala dole sai shi yasa ubanta ko da
yake mahaifinta ke daure mata kinsan ranar nan da naje mahaifiyar cewa tayi ai itama ba ba
son wannan alaƙa take ba ke kinga irin mutuncin da taci min kai gaskiya matar nan kwata kwata
bata da mutunci wallahi inda yaje bata je shi ba

Shiru baba tayi mata tamkar da dutsai take magana

Wannan kenan


ASH gaskiya Hajiya ke faɗa maka ta kamata ka dawo kamar da ka gina sabuwar rayuwa
mahaifina ya mutu na dena farin ciki ne

jingina yayi da kujera ya lumshe idanuwansa yace

'' har abada farin ciki na ya tafi Yasir..,

tab abin naka azeemun ne anya kuwa fatalwar nusaiba ba ita takama ruhinka ba

dariya yayi yace '' kome zaka faɗa saidai ka faɗa wallahi ko da yake ba kai kaɗai ba hatta
Hajiya kallon da take min kenan..,



wallahi dole tayi maka nifa ban taba cin karo da labari irin naka na kabi Ka kwallafa mace ɗaya
a ranka

file ya ɗago fara dubawa yace '' mubar maganar haka zanyi aiki...,

korata kake yi ko to bara na tafi gurin madam ta ɗebe min kewa cewar Yasir da yake danne
dariyar da ta taso mai ganin yadda fuskar ASH ta canza

ajiye file din yayi yace '' ni ba korarka nake ba kawai dai nace maka zanyi aiki..,

okay ai kai daman duk maganar da za a taɓa marigayya ba sonta kake ba idan ka ƙara aure
bawai yana nufin ka manta da rayuwar ta bane

dafe kansa ASH yayi yace '' ya Allah nifa bana son wannan zancen amma na lura ku kamar
dadinsa kuke ji...,

sosai ma kuwa wallahi domin bamu da buri da ya wuce mu ganka yau kayi aure har da ya'ya
buɗe baki yayi zai magana sai aka turo kofar da sauri dukkan su suka kalli kofar wani irin riga
da wando ne a jikinta yawa fata ta saka kimono amma ita da babu

6 / 7