Author : Oum Yasmeen Category : Read Hausa Novels
tare da sunce mata komai ba kunce mayafinta tayi ta daura a kafaɗa ta ci
gaba da tafiya tana yar waƙa bakin titi ta fita batare da ta tsayar da me napep ba ta fara tafiya
har ta isa police station
tana shaga tace '' dan bala ina DPO yake..,
banza yayi mata ya ci gaba da rubutun sa doka kantar da yake rubutu tayi tace
'' kai dan bala ba da kai nake ba amma ka ci gaba da rubutun ka bawa banza ajiyata to wallahi
zanyi maganin ka har ni zaka kalla ka watsar yawa sa'ar wasan ka...?,
daga littafin sa yayi yana dubawa tamkar da dutsai take magana a fusace ta warce littafin tace
'' tambayar ka nake ina DPO yake...?,
ya tafi koyo sallama ya bata amsa kamar ba shi yayi magana ba
kama kugu tayi ta ajiye littafin tace
'' to yanzu na fahimci inda ka dosa kuma zanyi maganin ka ...,
kofur inusa ne ya shigo yana cewa tab yau manyan ƙasa ne a gidan namu
gyatsuna fuska tayi tace
'' kai ni ajie wannan wasan a gefe tawa ce ta kawo ni shi wannan cutar kurumta ce ta kama shi
na tambaye shi yayi shiru yana yi min kallon hadarin kaji..,
kofur inusa yace
'' hajjaju me ya faru duk wata hanya ta kurɗa kurɗa kinsan na kware a gurin nan ba inda bana
shiga na fito indai da hatumin na sara kina mannamin zaki ji information..,
zama tayi a kan benchi tace
''hmmm kufa tsiyata da ku kenan komai kuɗi wallahi ku guje ranar da Ubangiji zai damƙe ku ina
ji ye muku wannan rana amma ku bakwaji haram kuka saka a gaba duk inda cin hanci yake
kuna nan ku dashi kamar dan jumane da dan jummai..,
kinga faɗamin me ya kawo ki na lura yau ba arziki kika zo gurin nan cewar kofur inusa
kamar kuwa ka sani dan wallahi kalma kaɗan za ayi min na zubar da haƙoran mutum wallahi
har ni za a nunawa rashin mutunci
cikin daga murya kofur yace
'' asabe reza tamayar ki nayi me ya kawo ki...?, amma kin tsaya kina tayi min wasu zantuttuka
ga abin da na tambaye ki amsar da kike bani dabam to bani da lokacin fast fast maza ki
faɗamin ina da abin yi...,
to sai ka nuna wanda bashi da abin yi ta faɗa tana harararsa
ke ki fita idan sa'insa kika zo yi gurin nan dan bala ya faɗa yana haɗe rai domin sam ba shiri
suke da ita ba
tofa yau nake ganin kudirar Allah yanzu fa tsab zai iya dagani ya fitar dani to wallahi ba ka san
wace mace ba za ka haɗu da dana sani mara a dad'i ta faɗa tana wura hanci
a'a abin duk be kai haka ba mu nan gurin wajen sasanci ne ba gurin tada tarzoma ba ke asabe
me ya kawo ki gwara kiyi kiyi ki bar gurin nan domin na lura yau transformer kika haɗiyo
Alkur'an baza ki amayar mana da ita a nan ba yanzu jikin ki sai yayi tsami hukuma gaba take da
kowa cewar kofur inusa
tamkar me shirin dauko duniya haka ta zura hannu a zaninta tana lalube tsayawa sukai suna
kallon kudirar Allah sai can ta fito da kudi washe baki tayi tace
'' kofur ina DPO..?,
kauda fuska yayi yana gyara zaman hularsa kallon sajan dan bala yake domin shine gaba dashi
yanzu yana ba dai-dai ba DPO zai ta magana yawa yayi me wanna hali nasa shi yake gudu
UWAR GAFALALLU
Episode 6-7
tofa kai ma nayi maka magana kayi shiru me hakan ke nufi wallahi ni karamin aikina ne na
shiga har office dinsa to wajen nan baƙona ne bani da wani lokaci wani satin nijar zani naje na
nemo sa'ar da yaran nan zasu dinga samin dan na ɓatarwa komai ya tsaya chak dan kuɗin da
suke tarawa shima yanzu ba wani bane da yake yanzu ba lokacin siyasa bane, ba dan siyasan
da nake gani dan haka raina duk a bace yake kuyiwa kanku kiyamal laili ku fadamin inda yake,
bayan kuma shi ya ce na zo ya kama sunusi
kallon kallo suka shiga tsakanin su ba me magana sajan dan bala ne yace
'' yana ganawa da baki ne ...,
ai be rufi bakin saba sai gashi ya fito yana washe baki yawa gonar audiga shi da wata yar
duniya sai gyara mayafinta take yana ganin ta yace
'' sweet sai mun ƙara haduwa nagode da kawo miin ziyara da kikai...,
wani far tayi da idonta tace
'' sweet kar ka damu insha'Allah zaka dinga ganina akai akai..,
wata dariya DPO yayi yana shafa ƙaton cikin sa yace
'' aikuwa sweet nagode sosai...,
hannu ya daga mata har ta kulewa ganinsa sannan ya juyi kan asabe yace
'' asabe yar tasha ke da nace miki karki zo shi ne kika zo me zan miki belin katotan dan ta'adda
zan bayar a dubu biyar yawa belin ƙaramin ɓarawo me satar kaji to ko masu satar waya idan
sun kawo min ziyara haka kurum batare da wani abu ba dubu hamsin suke bani shi yasa ka
zaki ga bana kama su na barsu suna yadda suka ga dama a garin nan balle belin dan daba
makashi mutum nawa ya naƙasta a ƙa'ida ma wallahi gidan gyaran hali za a kai shi ai mai
daurin rai da rai amma saboda kin daure mai ai gashi nan yana yawo a gari...,
kwantar da murya tayi tace
'' DPO ka temaka wallahi dubu biyar ɗin nan ce dani kuma kaga ...,
kinga bana son dogon bayani shigo daga ciki tashi tayi ta bi bayan sa zama tayi a kan kujera
shima ya zauna a tasa yace
'' ci gaba ina jin ki...,
yauwa temakawa za kai ka sakar min shi a haka yanzu harkar damfara nake so su fara wallahi
gari fa yaci wuta ji kake ɗib ba wani bayani yan siyasa ma yanzu ba lokacin zaɓe bane kasan ita
wannan gwamnatin bawan Allah nan baya yawo da yan daba sai ma ya nema musu abin yi
dan shiru yayi sannan yace
'' to bani amma wallahi dan kece da ace wata ce wallahi bazan karɓa haka ba ko kuɗin da na
kashe mai ban mayar ba ga zagina da yadin Ka yi kullum sai ya saka na a siyo mai tabar wiwi
da maganin sauro saboda tsabar samun waje har da a siyo mai turaren wuta nace wallahi baka
isaba nan dakin uwar'ka bane ko gidan uwar gafalallu ne...,
rausayar da kai tayi tana cewa nagode DPO Allah ya barmu tare Allah ya saka wata ran a baka
IG
wai za aga iya shege ai harka zan fara da yan fashi kinsab fa sun fi kawo kudi me tsoka wallahi
wata miliyan ashirin a sati sai na jita a account dina wallahi
Kai DPO wai ina zaka kai kuɗi haka
hmm nima bani kaɗai nake cinyewa ba ni da abokanan hurɗata muke cinyewa sun fini ma ci
wallahi sai da kuɗi suke zama idan ba kuɗi wallahi kashi ya fika mutunci a idon su shi yasa ka
nake neman kuɗi hurjajhan domin a samu a faranta musu rai
cewar DPO yana amsar kuɗin da ta bashi
tashi tayi tana cewa to zo muje ka sako shi mu tafi tare domin wallahi bazan yadda ba na tafi na
barsa ka sake saben lale
tashi yayi yana cewa ke ko irin kewarnan tawa baki ba
haɗe rai tayi tace '' wallahi tun da nayi aure na bar wannan sabgar ko sha'awa bata bani wallahi
daidai har a kwanar dan gora na zauna zaman kaina kai duniya haka ma fa tayi mana da kyau
wasu su nan sun haukace...,
amma kika saka ya'yan ki a wannan hanya kinsan da haka ya faɗa yana kafeta da ido domin
har yanzu da kyen jikinta komai yana nan kamar ba ita ta haifi zaratan yan matan nan ba har
guda hudu rigis lashe baki yayi ya ci gaba da cewa
Please ko sau ɗaya a bani na taɓa
sai kuma fa kayi wallahi haka kurum da aurena
to biyo ni ki amshe shi wallahi ya bari muka ƙara kama shi hmmm sai ya gammace kiɗa da
karatu dan wallahi sai na goge mai duk wata hadda dake kansa ban da rashin mutunci ace duk
wani fadan daba kai ne a sauhun gaba kwanaki fa gwamna ya kirawo shi akai sulhu amma
shine ya ƙara jan wata tawagar
kaga bana son dogon jawabi muje ta faɗa tana gyara zaman mayafin ta a jikinta domin idan ba
wuta wuta tayi mai ba sai dare yayi mata anan kuma kyalli baya son ta kai dare duk inda taje
magariba tayi mata a gida dan ma dai ba wai tsoransa take ji ba be isa ya saka mata doka tabi
ba ....
batare da yace mata komai ba ya fita binsa tayi har baƙin cell ya bude sunusi fitowa yayi daman
yana baƙin kofa wata uwar miƙa yayi yace
'' hajiya asabe reza...sai yan zu kika ga damar zuwa..,
kaga nususi idan baka godemin ba ai baka tsinemin ba dududu kuɗin da kuke tarawa nawa
yake ....?
yanzu ma sai da na saka jagwa ya ɗan har hadomin sannan na samu damar tawowa wallahi
rashin hakurinka yayi yawa yasin
to ai shikkenan hakan ma na gode a gidan mu wane yazo sai ke da bakya gajiya damu
au ashe ka gane gaskiya wuce mu tafi
cewar asabe tana dafa kafaɗar sa
kai kuma zamu haɗu a way ne wallahi sunusi ya faɗa yana mai da idanuwansa ciki
dariya DPO yayi yace '' wa kake faɗawa haka lallai yaron nan wallahi idan bakai wasa ba sai na
mayar da kai inda ka fito wallahi..,
wani kallo sunusi yayi mai yana nuna mai ya tsunsa biyu tankaɗa ƙeyar'sa tayi tana cewa maza
maza mu tafi shige mu tafi shigewa yayi yana faɗi yaci uban malin malin da takalmi combos da
hula
irin ta kaurayen nan kai bani wayata tunda bata tsoho bace
kofur inusa ya miƙo mai warta yayi yana cewa wallahi da kudina a ciki naga babu sai na dawo
anyi ta wallahi domin bazan yadda ba haka kurum ku cinye min kudina
da sauri asabe tace '' kai wanne kuɗi kake magana...?,
to uwar son kuɗi katina ne na saka na dari biyu sunusi ya faɗa yana bincika wayar sa
to bana son neman magana shige mu tafi bana son bar baɗa haka kurum ka ƙara ballo min
ruwa har nawa kuka tara da zan ƙara zuwa belin ka wallahi sai dai akai ka gidan yari idan na
samu na fito daga kai
cewar asabe tana tankaɗa keyar sa sukai waje ci gaba tayi da magana tana cewa yauwa nifa a
kafa na tawo dan haka idan zaka iya to sai ka tawo mu daɓa dan wallahi bani da kuɗin mota
ƙaramar wayarsa ya fito da ita yana lallatsawa dakyar take dannuwa sunƙuyawa yayi yana
neman tsinke yace
'' Bara na kirawo honourable ya turo min da kuɗi domin wallahi ba zan iya tafiya a ƙafa ba yawa
wani doki ai sai maƙiya ma su yi dariya ana nunani da baki ana cewa ga sunusi ta ƙare mai idan
ke zaki iya tafiya to ga hanya nan mu haɗu a gida kawai...idan ma ban same shi ba zan kirawo
bazzawara ta turomin kuɗi...,
asabe dundu tayi mai tace
'' a'a kirawo shi idan naji zai bayar sai ka bani kudina ni zan tafi a ƙafa..tafiyar nawa take..,
kai ka kai ni kika daka me nayi miki wannan wanne irin cin zaline sunusi ya faɗa yana ɗagowa
ganin bata kula shi ba ya ci gaba da kiran amma ba a ɗauka ba duk wanda ya kira ba a picking
kamar haɗin baki suka juyo a tare suka kalli juna wata dariya asabe tayi har da buga cinya tace
'' me kake jira naga jikin ka yayi la'asar kaga tun kafin dare yayi mana a nan gurin kazo mu tafi..,
Ba tare da yace mata komai ba ya fara tafiya binsa tayi har suka isa gida ba me ce wa dan
uwansa kala al'adar gidan ce bayan sallar magariba wa'yannan masu ca'car zasu kasa gurmi ai
ta kiɗa mahauta nata sudda baru dan haka kafin isha tayi har sun hallara,
wani maroƙine ya taso yana cewa cau cau cau sarkin daba ko wa yaƙi bin umarninka yanzu
lahira za tayi baƙo huƙa ya ƙarba a hannun wani yana wulwulawa
sosai maroƙin nan ke wasa shi kuɗi yan gurin suka fara zuba mai ana liƙi shiga gida tayi ta bar
su da sauri tace
'' innalillahi me zan gani jalila daman ban gama kashe wutar nan ba shi ne kuka ƙara wurata har
ta kai ku da gwada yar ƙashi ..,
Cikin haƙi jalila tace '' wallahi momcy idan ban karya yarinyar nan ba wallahi Allah ba zata
fahimci ni da ita da babbanci takwalas ne ya turo da kuɗi yace gashi nan mayi kunshin bikin ajo
shine wai dubu daya zata bamu ta riƙe dubu shidda..,
taɓarya ta dauko a kusa da bayi tace
'' ku cika juna ki na sauke muku allon kafaɗa wannan wanne irin iskanci ne ku bani kuɗin kowa
ya rasa da man ke jalila baki kawo min balance ba maza maza ke sumy zo ki ciro min kuɗin nan
wallahi kun rasa saboda da tsabar mammaƙo wanda kika je gurin sa ko kobo bani da tabbacin
ya baki...,
rabuwa sukai har rigar naja ta yage bako kunya ta bata rufe jikin ta ba duk kirjinta a buɗe
maza ku miƙo min tun kafin na ci mutuncin ku asabe ta faɗa tana kafe su da idanuwanta
miko ATM din tayi amsa tayi tana cewa mene pin din
Kau da kai naja tayi ita bawai faɗar ne ba za tayi ba yanzu momcy zata samu damar ɗaukar
mata kuɗi tana yi mata bincike tace
'' kawo naje na curo har yanzu sumy bata cikin hayyacinta...,
miƙa mata tayi ta amsa shiga daki tayi ta canza kaya ta fita neman guri jalila tayi ta zauna akan
tabarmar da mufeeda ta shinfiɗa
Lami yar gumama tace
'' sai yanzu kika dawo..,
wallahi baba sai yanzu dakyar ya bani shi kinsan fa yanzu komai ya tsaya asabe ta faɗa tana
zama ɗaukan kayan da ke gaban baba tayi tana cewa kai wannan riga tayi kyau
Ajiye ninƙin da take tayi tace
'' nima wallahi naga kyawunta yan zun nan challi ta kawo min su gobe insha Allahu yarinyar nan
zata dauka mi tafi kasuwa..,
ni wallahi Allah bana son zuwa gurin yan gumamar nan yan iska ne wallahi mufeeda ta faɗa
tana turo baki
wani kallo baba lami tayi mata sannan tace
'' dan kan uwar ki sai kin je su wa'yannan manyan mata ne ke ce ƙarama duk da dai kina nema
ki kere'su ga kirga dangi nan duk ya cika miki kirji yawa za su faso kirjin ki su fito amma ba fuss
tsuliyar me duki...,
turo baki tayi tana kunƙini ta tashi jin an kira sallar magariba tashi tayi ta dauro alwala bayan ta
idar ta kalle su tace
'' baba an kira sallar magariba fa..,
ba wanda ya tanka ta balle baba da ta cika tayi fam ninke kayanta ta ci gaba dayi tana rera
wakarta da tashi tayi ta shiga daki ta tada salla
zama tayi har aka kira sallar isha'i lokacin kuma har gidan su ya fara dinkewa da jama'a na
kallon gurmi bata fita ba ta kwanta a ɗaya tana jan carbi domin hana zuciyar ta tunanin komai
ke miko min mayafina kinga naja shiru yawa an aiki bawa garin su kar dai yau ba a nan zata
kwana ba
tashi nayi zuciyata na ƙuna na miko mata mayafin ta sannan na koma na zauna fita tayi tana
sababi
TUDUN YOLA
ƘARFE 8:45
baka jin karar komai sai ta chokali da AC kowa ya mai da hankali kan abincin da suke ci ido
Hajiya ta karawa Ashraf tace
'' Ash kamar akwai abin da ke damunka tun dazu sai juya chocali kake ka kasa ci idan har ba
zaka hana kanka tunani ba wallahi zakai mutuwar tsaye ka takurawa zuciyar ka sai tunani kake
mara makama da abin yi to wallahi ka rufawa kanka asiri ni wallahi abin ka har tsoro yake bani
ai wannan rashin tawakkali ne yanzu ina iyayena ba hakura nayi ba na ci gaba da rayuwa bawai
tana yi min dadi ba a'a kawai dai na ɗauki hakuri amma kai ke nan ai ta abu ɗaya..,
ƙasa yayi da kansa kallon sa mahaifinsa yayi yana cewa haba Ashraf yan zu kai takure kanka
da kayi shine jin dadin ka kome Ubangiji yana jaraba mune yaga iya kacin imanin mu mutane
nawa suke naman damar da Allah ya baka mutane nawa suke cikin wani mawuyacin hali amma
sun saka hakuri da dangana Ubangiji fa yana jarabtar bayin sa na kware ne
Ashraf sunkuyar da kai yayi yace