Author : Oum Yasmeen Category : Read Hausa Novels
'' insha Allah zan É—auki nasihar ku bawai na kasa cire nusaiba a raina bane yanzu wannan
lalurar da inteesar take ciki ita take ƙara jefa ni cikin rudani...,
damuwar ka ba zata saka ta samu lafiya ba sai ma ayi biyu da kwance uwa kwance kaga ba
amfani ke na ko Hajiya ta fada tana goge bakinta da tissue
Kai ya jinjina sannan ya ci gaba da cin abincin sa dan ƙadan ya ci daman shi dabi'arsa ce baya
cin abinci da yawa tashi yayi yana cewa Hajiya Alhaji sai da safe insha Allahu nan da wani satin
zan kaiwa junaid ziyara Cyprus daga nan zan biya nayi umara
to masha Allah Allah Ya kai mu lokacin
Alhaji ya faÉ—a cikin kulawa
Hajiya tace
'' insha Allahu lokacin da matar ka zaka tafi..,
ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya fara tafiya hajiya ta kasa fahimtar sa shi ba wai zama da
macen ne bazai iya ba a'a gani yake ba matar da zata iya kula da inteesar gwara su zauna su
biyu har ta girma yayi mata aure ba zai juri ganin ana wulakanta mai yarinya ba
musamman ma , matan yanzu da kansu kaÉ—ai suka sani babban burin su idan sun shigo ba
wanda zai raɓi mijin su sai su kaɗai da yan uwansu wata ma kuwa duk wani naka saita rabaka
dashi sun matana da ita rayuwa shiga da fice ce wanda beba ma akai mai balle kinyi wata da
addabawa uwar miji ta manta da wannan karatun cewa
itama uwar miji ce wata rana yana wannan tunani har ya kasara shashinsa chak ya tsaya ganin
kamar tana yi mai murmushi ta wara hannu wanta biyu da sauri zai kamota sai ta ɓace runtsai
ido yayi jijiyoyin kansa sun fito rada rada tabbas shi da kansa yasan ba lafiya yake ba anya
kuwa be zama dis order ba ta ko ina ya kasa haÉ—a son da yake wa nusaiba ta ko ina tayiwa
mata fintinkau adai zamanin nan ba lallai a samu kamar ta ba
í ¾í´”
dakyar ya ja ƙafafuwansa ya dauko mukulli ya buɗe shiga yayi tsayawa yayi yana kallon ko ina
na gurin kamar yau fa aka kawo masa ita a matsayin mata duniyar tunani ya lula
wai waye adon tafiya
wallahi nusaiba ji nake kamar na janyo ranar nan ta dawo yau
Ashraf ya faÉ—a yana kafeta da idanuwansa
kau da kai nusaiba tayi tana wasa da hijabinta tace
'' da yau da ranar juma'a duk É—aya ce a gurin Allah, Allah dai ya kai mu da rai da lafiya...,
Anya kuwa ban fiki son mu kasance tare ba
rufe fuskarta tayi da tafukan hannayen ta tace
'' bansan da wanne baki zan kwatanta maka irin adadin son da nake maka ba..,
ni wallahi sweet anya kuwa wannan kunyar take zata bari ki nunamin son da kike min
jin gina tayi a jikin kujera tace
'' kaidai Allah ya nuna mana lokacin lafiya..,
sarkin wayo maganar ce bakya so ko
har abada bazan gaji da sauraron daddaÉ—ar muryar ka ba ina rokar Ubangiji idan zaka mutu mu
mutu tare bazan iya rayuwa idan bakai son ka shine jini na jikina kaga kuwa mutum zai iya
rayuwa ba idan babu jini
lumshe idanuwa yayi sai kuma ya buÉ—e su yawa me jin bacci yace
'' nima bazan iya rayuwa babu ke ba Allah ya raya mu tare ya kashe mu tare..,
amin ya Allah
tashi yayi yace
'' zan shiga daga ciki lokacin da Hajiya ta diba mana ya cika tsoro take kar nayi aika aika..,
murmushi tayi batare da tace mai komai ba wallahi maganganun sa kunya suke bata ashe
shima ba kanwar lasa bane a satin nan fa lamarinsa har mamaki yake bata kamar ba yayan da
tasani bane me muzurai da tsare gida amma a yanzu kam ita sheda ce ko kallon da yake mata
na zallar so ne magana fanake miki kinyi shiru ko na zo na raka ki dakin ki Ashraf ya faɗa yana ƙara kafeta da idanuwansa
rufe baki tayi tana zaro Ido
UWAR GAFALALLU
EPISODE 8-9
PERFECTLY PEN'S
rufe bakin ta tayi tana zaro Ido tace
Please yaya ka rufan asiri ka tafi kar Hajiya ta biyo sahun mu wallahi Allah jiya faÉ—a tayo min
sosai tace sai ta hana ni fita idan an kai ni gidan mayi kome za mu yi
dariya yayi ya nuna mata hanya yace
'' Hajiya kenan ta gama isarta ƙarshe dai dole ta kawo miki bissalam Allah ya tashe mu lafiya..,
nusaiba tace '' amin ya Allah tana fara tafiya sai da yaga tayi nisa sannan ya juya ya tafi part
dinsa yana shiga junaid ya shigo da yake dakin su yana kallon na juna kallon a gogon parlour
ASHRAF yayi yace
''9:30 kai kuwa ina kaje haka kasan fa Alhaji baya son yawa Junaid a dinga kiyaye wa kar kuma
ya saka maka dokar fita..,
kallon a gogon dake manne a bango Junaid yayi yace
'' wallahi naje gidan su Abubakar ban san lokaci ya ja haka ba amma insha Allahu zan dinga
kiyaye wa hakan ba zata sake faruwa ba ...,
Kai ASHRAF ya jinjina yace
'' Allah ya saka yana shiga dakinsa shirin bacci yayi sannan ya kwanta..,
Washegari
cikin sauri take haÉ—a musu breakfast Hajiya ce ta fito tace
'' a'a nusaiba har kin tashi kin fara aiki...?,
Eh wallahi Hajiya bana so na ɓatawa yaya lokaci ransa ya ɓaci yayta jira shi ya saka na ɗora da
wuri cewar nusaiba kanta tsaye domin ta manta da halin hajiya na zolaya yanzu zata tusata a
gaba
dafa table din kitchen Hajiya tayi tace
'' kaga me miji wato kar ki ɓara mai rai daman haka ake so matar kware ta dinga yi..,
murmushi tayi batar da tace komai ba
fita Hajiya tayi bayan ta gama ta kwashi komai ta kai dining jin sallamar su ta É—ago amsa wa
tayi tana gaishe da Alhaji har ƙasa
Cikin kulawa ya amsa jawa kowa kujera tayi sannan ta zauna zuwa kowa tayi junaid na
tsokanarta Alhaji na tare mata shi kuwa ASHRAF kamar baya gurin cin abincin sa yake cikin
kwanciyar hankali bayan ya gama ya saka tissue ya goge bakinsa ta tashi zai bar gurin yana
cewa
Zan tafi gun aiki
kallon sa alhaji yayi yana cewa gaskiya bana son zuwan ka wajen wutar nan ga kasuwanci nan
idan ma baka san zama a ƙasar nan ga shaguna na Dubai kaje kayi kasuwancin sai da gold
ana samu sosai
ƙasa yayi da kansa baya so ya tashi a jingina da ƙarfin mahaifin sa yafi so ya nemi nasa yasan
zafin nema dariya Hajiya tayi tana cewa ASH ba magana naga kayi shiru
sosa ƙeyarsa yayi yana cewa sai na dawo na tafi
Alhaji ne yace
'' Allah ya kiyaye hanya ya bada nasara da sa'a tun da kafi son nan sai mu bika da addu'a...,
wallahi kuwa Hajiya ta faÉ—a tana kallon nusaiba ta ci gaba da cewa nucy ba rakiya...?,
kai ta gyaÉ—a mata a hankali tace
'' Hajiya ba sai na raka shi ba..,
kwaji da shi zama ku dawo dai-dai ne ta faÉ—a tana tashi daga gurin shiga bedroom dinta tayi
bayan kowa ya gama ta kwashe kayan ta kai su kitchen
akwana a tashi ba wuya yau ta kama juma'a za ayi daurin aure sosai manyan ƙasar nan suka
halarci daurin auren NUSAIBA ABDUL HADE da ASHRAF MANSUR GWARZO amma ban da
dangin mahaifin nusaiba kalilan ne suka zo domin ba son auren suke ba akan wani ban zan
dalilinsu mara makama da abin yi gani suke Hajiya ta nuna musu kuÉ—i taya yaya yarinya ta taso
a gunta kumu ta aurer da ita ba tare da ta Da musu da ita ba dan tana taƙama da kuɗi...
bayan an gama daurin aure da yamma akai lecture daga nan a ka wuce da ita dakin ta ba abin
da Hajiya da Alhaji suka rage ta dashi komai sun mata haka kowa ya watsai ya bar ta ita kaÉ—ai
bata da tarin ƙawaye bayan isha na shigo gidan....
nima da yake bani da abokanai abokina É—aya salim shima a waje muka rabu shiga nayi tare da
addu'ar Allah ya kade mana fita Allah ya bamu zaman lafiya tura kofar nayi abin da na zata shi
ya faru a buÉ—e take na shiga bakina dauke da sallama bakowa a parlour direct bedroom na nufa
nayi sallama
É—agowa tayi ta amsa min sallama ta tsayawa nayi ina kallon ko ina tare da da yiwa Allah godiya
da ta cika mana burin mu mun mallaki juna
tun da mukai aure ba mu da taɓa samu. Saɓani ba nusaiba tana da haƙuri za kai mata ta dauke
kai ni ko da tasan Kai mata din har Allah ya azurta mu da yarinya,
ranar da zata tafi ganin dangin ta lokacin inteesar tana da two year hatsari ya faru me kama da
almara ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya gama tunaninsa tafiya ya fara har ya shiga palour
sa zama yayi akan two seater ya zuba ta gumi kallon agogo yayi karfe 12:00 gaskiya ya dade a
zaune a gurin nan haka ya kwashi lokaci..
Wannan kenan
baccin tane yayi nisa ta tamkar daga sama taji ana bugu tashi tayi tana kunna yar ƙaramar fitila
tana jan tsaki ashe naja bata dawo ba tun daga zuwa ciro kudi tashi tayi jin zata karya musu
kofar da suke ƙarawa da ita ta fita tayi ta isa soro ta buɗe kofa ta tsaya a baya tana liƙe bak'ar
motar da aka kawo naja a cikin ta har da tinted to munafuka uban me kika tsaya yi sauran
kuma kice mata na dawo
dan ubanki bani kuÉ—in da kika ciro da wanda kika samo ni wallahi bansan ke yar marasa bace
sai yau
wallahi momcy be bani wani kuɗi ba yau muka haɗu dashi ta faɗa tana turɓune fuska
uban be baki wani kuÉ—i ba bani ko ya zu wallahi na caje ki asabe ta faÉ—a tana zaro ido
ba yadda ta iya haka ta miƙa mata kudin murmushi tayi tana kirga su dubu arba'in cis tace
'' ina dubu biyar din ta kwalas...?wallahi naja ki kiyaye ni kuÉ—in nan zu zasu wanke ki daga laifin
da ki kaimin,
zun buro baki tayi ta miƙa mata amsa tayi tana washe baki Allah ya tsare ya kuma buɗa kofofin
hanyar samu...
saboda takaici kasa barin gurin nayi ƙafafuwana sun kasa ɗauka ta yan zu rufa'i ko kirana ba
yayi saboda taje har gidan su taja mai kunne tashi nayi na bar gurin ganin sun tafi sun barni
kulle kofar nayi na koma ciki shiga daki nayi runtsai ido nayi ganin tashin hankalin da na gani
jalila sumy suna ta aikata masha'a kamar ba yan uwa ba kamar addinin mu be yi hani da
wannan dabi'ar ba kasa shiga nayi na dauro alwala na daman da hijabi a jikina shiga dakin
baba lami nayi sai sharar bacci take har da mun shari shim fida daduma nayi na fara nafila
bayan na idar bacci ya É—auke ni can kuwa É—aki ai ko a jikin su ganin mufeeda ta gansu breast
din sumy da shi jalila tayi bacci basa tunanin Ubangiji zai iya É—aukan ransu a haka a kuma
tashe su a haka me za su ce mai jin kiran sallar asuba suka tashi ko wacce taje tayi wanka ta
dauro alwala kallon su mufeeda tayi tana cewa
kuji tsoron Allah abin da kuke aikatawa ba me kyau bane abu mafi muni
tun kafin ta ƙarasa sumy tace
'' kiyi mana shiru wallahi kema baki wuce na kwantar da ke ba na kwakuleki tas...,
kai ta girgiza ta bar gurin ƙasa sheƙewa sukai da dariya suka tafa
har sun tada kabbarar salla suka ji muryar takwalas da sauri suka sallame sallar suka fito yana
sanye da jallabiya yaci dauri ture kaga tsiya wata uwar buÉ—a ya saki yace
'' kut gaskiya mutane na kun yi kyau kunyi acan acan dan tafiya lagos da nayi shine kuka tara
wannan kayan aiki haka to gaskiya nima ba za a barni a baya ba ina momcy take ...?,
dariya sumy tayi tace
'' tana bacci kai ma wallahi Lagos ta amshe ka..,
kan bura ubancan kayyasa ai anan kano ba komai ake ba sai da naje Lagos sanna na ƙara
fahimtar rayuwa wallahi idan har zata bar ku hmmm kudi ta riga da ta zama attajira sufa ba irin
biyan nan suke ba musanman ma ki haÉ—u da direba ko yare ba abin da basa kashewa mace
ya faÉ—a yana buga cinya hadi da fari
naja ce tace '' dan Allah ta kwalas ...?,
murguɗa baki yayi yana fari da idanuwansa yace '' zauna wasa har lokacin ki yayi ya ƙare ba
abin da kika tara can fa ba me damuwa da wani kowa harkar gaban sa yake...,
Ikon Allah yanzu kowa sai yayi sabgar gaban sa ba me damuwa da kowa anya kuwa jalila ba
nan za mu tafi ba cewar naja
gyara daurin kirjin ta tayi tana cewa nima fa abin da nake tunani kenan wallahi gwara mu shiga
sahun manyan mata
wata uwar shewa suka saki tare da cewa a hayye ras wannan shewa ita ta tasar da momcy ta
fito dai-dai shigowar baba cikin daure fuska yace
'' kai bana ce maka kar ka ƙara shigo min gida ba ..?,
gaskiya ba ruwan ka malam ya kake yawa ne nan ina gidan yake kwango dai amma wannan ba
gida bane ka bari sai arziki ya zo ya same ka kana kwanciyar asarar nan da kake kayi gida
wallahi ba ruwan ka da kawayena da suke zuwa guna da kuma na ya'yana naga ma gado aka
ci aka bar maka shine kake tun ƙawo da shi
Asabe ta faÉ—a tana yatsuna fuska da tabe baki
kasa magana yayi sai ma kasa da yayi da kansa ya wuce be ƙara ce mai komai ba bayan
kaddarar da Allah ya yi mai to Ubangiji sai ya ƙara jarabar sa da asabe bayan ya shiryu shiga
daki yayi yana jan carbi ko zai samu saukin zuciyar sa
kunga zo mu shiga daki takwalas sai ka sako da ga farko asabe ta faÉ—a tana nuna musu dakin
ta shiga sukai ya dinga basu labari momcy tace
'' bara mu gama bakin ajo ko bayan ka tafi ne sa tawo har waccen yarinyar sai an tafi da ita naji
dakai na wallahi...,
sai ma karshen watan nan zan tafi sai mu tafi tare
hakan ma yafi yi min gwara su sauka a hannun ki
ai momcy ina faÉ—a miki gida na gina kowa ya zo ya shiga ya bani yan kudina a agege
kai ka akai kace litkafa taci uwar ta da
Kware da gaske ai ina tare da addu'ar iyaye
ai kuwa Ubangiji bazai taɓar da ke fa ji sukai an ɗaga labulan dakin zaro ido sukai gaban su ya
yanke ya waɗi ɓare baki takwalas yayi yana cewa
Kai lafiya ka zo ka tsaya mana a ka da zabgegiyar huƙa
yimin shiru ko yanzu naci kuttumar..ubanka ba wajen ka na zo ba ya faÉ—a yana kallon asabe
tashi yar kwalas yayi yana girgiza kugu yace
'' ke idan kana ta ƙama da kai dan dabane ni naje inda baka je ba naje inda aka fika dabanci da
iskanci Dan haka maza wuce ka bani guri dan iskan ƙarya
ai be ƙarasa ba yaji saukar duba a bakin sa ihu ya saka yana cewa na shiga uku momcy ku
duba min ya cire min hanci ko
momcy da cikin ta ya É—uri uwa bama tasan me yake cewa ba kai a sabe da sauri ta É—ago jikin
ta yana rawa yaci gaba da cewa
daman na faɗa miki inhar kere na yawo zabo ma yana yawo rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak
ta me kaya kin saka an kai ni gidan yari to yau zan aika ki lahira dan uwar....ki ke shegiyar ƙarya
ce kuma wallahi sai nayi maganin wa'yannan ya'yan naki ba sune yan zuga ki ba to duk yanzu
zan yanke musu hukunci kai kuma dan daud ko to yau zan dawo da kai kalar ka ta ainiyi a
zaton ki zan dawwama a gidan yari ko
to yau zan ci ubanki ala'ada waje zan nuna miki jiya ba yau bace......
UWAR GAFALALLU
EPISODE 10-11
UWAR GAFALALLU
EPISODE 10-11
Gumi ne ya shiga wanke momcy tasan bata kyauta ba takurewa guri É—aya su sumy sukai jikin
su har rawa yake takwalas kuwa sai zare ido yake be taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba
wannan wacce irin rana ce
Wannan shi ake kira da ya taka sahun ɓarawo yace '' talge dan girman Allah kai min rai wallahi
Allah ban shirya mutuwa ba...,
wata dariya