Uwar Gafalallu Book By Oum Yasmeen

Author :  Oum Yasmeen Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 7

3K to 6K   out of 20.3K words

ka-na-ji-na ta fada a rarrabe ajiye wayar tayi Gaddafi ne yace

''tab yau kinsha wacc tafi ƙarfin kanki...,

wara hannu wanta tayi ta yi a lamar uku da yatsun hannunta dakyar ta iya cewa

kwalba uku nasha nayi tatul

naja ce ta fito tace

'' badai kamru uwar laifi kika sha ba...?,

ita na sha wani abu ne

tab tsoho ya haifi wacce tafi ƙarfin sa dan Allah lokacin ku momcy tsoho yasha giya...?,

tab ai besha ba iya kacin sa taba daga baya ma tun kafin muyi aure ya dena

to yau gashi ya haifi wacce ta fi karfinsa wai dan Allah momcy a haka kika yadda kika aure
tsoho

dariya tayi tana gyara zaman rigarta tace

'' ke nima gagara nayi mahaifina ya bashi ni na san kuma ɗan dabane mene abin gudu a dan
daba wallahi ina sane na aure shi...kuma ina son kayana

wani ihu su Gaddafi suka saki suna mata kirarin da suka saba yi mata cau cau cau uwar
gafalallu dan iska naki ban da dan banza dan kirki me tsinuwar iyaye shi ne babban shedani na
hannun daman ki an buga dake an barki maƙiyan ki fadawanki dubu jiran dubu bilahillazi ba me
taddo ki cau cau ki yi taki kinyi ta wasu bata kare miki ba
Sai ma gaba da kikai ke ce uwar da zamu ɗauko magana ki shige mana gaba a fito damu

ya isa haka yanzu haka sumy salon ki saka a dinga zagina a unguwar nan shi ne kika tawo a
haka haba sumayya so kuke baƙin mutane ya durarmin

dakyar ta iya tashi tana haɗa hanya komai da ta shigo dashi anan ta bar shi tana zuwa daki ta
kwanta a ƙasa matsawa mufeeda tayi ta fito tana cewa wallahi momcy idan har ba zaki gyara
halinki ba mu tare da dana sani

kai ka kai turƙashi mufeeda ashe bayan tafiya ta niger rashin kunyar ki ta kara gaba to yanzu ni
ko mahaifiyar ki , kike faɗawa haka...,

baba lami ta faɗa tana kama haɓa

baba gaskiya ce dole a faɗa wallahi bana jin dadin rayuwar nan da muke Please mu canza mu
koma irin ko wanne gida mana jin sallamar mahaifinta ta ɗago amsawa tayi ai kafin kace me
kowa ya tashi ya fita ƙarasa shigowa yayi cikin sanyin murya kamar ko da yaushe tace baba
sannu da dawowa

yauwa yar kirki Allah yayi miki albarka

sauran kuma Allah ya kwashe musu wallahi idirisa ka dena raba kan ya'yan ka

girgiza kai yayi a ko wacce rana yakan yi dana sani mara adadi na zaɓowa ya'yansa uwa bata
gari ba shima rashin dacen uwa bata gari ba shi ya jefa shi halin da ya shiga a baya kallon
mahaifiyar sa yayi yace

''baba kin dawo lafiya..,
kallon ledar hannunsa take yi tana sakace hakoranta tace

''lafiya qalou me ka shigo da shi ne...,

tabbas hausawa sunce me hali baya fasa halinsa ƙasa yayi da kansa yace

'' taliya ce na samo dakyar bayan nayi faskare a gonar Alhaji mansur gwarzo shi ya saka kuka
ga ban dawo da wuri ba ga manja nan ku dafa kowa yaci...,

baba wazai ci wannan abar saidai ban ƙi ba kai da mufeeda kwaci

jalila ta faɗa tana gyara zaman riga a jikinta duk tabi ta dameta...

banza yayi mata yana yi mata fatan shiriya ko sau daya be Allah wadai da halin ya'yansa ba ko
yayi mu su baki addu'a ce yana tafi ko yana zaune yi musu yake ungo lami baya yaran nan su
dafa mana

Wani kallon hadarin kaji tayi masa sannan ta ɗauke kanta mikawa mufeeda yayi ta amsa tana
godiya ƙara cewa yayi Allah yayi miki albarka ya kai ki inda zaki huta

a zuciya ya amsa da amin murhunsu ta nufa tana kokarin saka icce da sauri asabe ta kwace
tace

''wallahi baku isa ba tab ni zaku dura da ka...,

Momcy girki zanyi fa

dawanau zaki dafa

dan ubanki shi da ya baki ai sai ya kawo miki iccen da zaki kona

mufeeda ajiye jike ki waje akwai ledoji ki zo ki dafa mana wallahi bani da kuɗin icce

kai ta gyaɗa mai ta fita ta jima kafin ta dawo ajiye wa tayi ta soma haɗa huta kuttumar uba nan
kusa da kajina kike wannan aiki salon ki babbaka min su


shiru tayi jikinta duk yayi sanyi bayadda ta iya da mahaifiyar ta amma sam halinta ba me kyau
bane matsa gefe tayi da kyar taliyar ta dawo saboda rashin makamashi

Bayan ta gama ta soya manja tace


'' momcy a zobo muku...,

girgiza kai tayi tana cewa Allah ya sawwaƙe ni dacin fara damai ko magi babu yawa a gidan jero
(prison)

Baba lami na zobo miki
aa barshi kina jin abin da asabe ta faɗa ita da take da sauran kwarinta balle ni a'a kuci kayar ku

daga haka ba wanda ta ƙara yiwa tayi zobo musu tayi wadali ishi suka ci har da ragowa tashi
sumy tayi tana zuba wata uwar miƙa da hamma zuwa yanzu ta dawo dai-dai amma ba sosai ba
tashi tayi ta shiga toilet wanka tayi a lokacin ana kiraye kirayen la'asar aunty sumy baki ji ana
kiran salla ba zaki koma
makka naji ana kira ta faɗa tana zabga mata uwar harara shiga daki tayi

ci gaba da alwalarta tayi bayan ta idar ta tashi ta shiga daki shinfiɗa daduma tayi ta ɗauki
hijabin da ya rage musu ta saka ta tada sallah


TUDUN YOLA

cikin sauri yake toki babban burinsa ya isa gida so yake ya ga gaskiya saboda gudun da yake
zabgawa ai kuwa ya isa a yan mintoci ƙalilan tun daga nan babbar ma'aikatar wutar lantarki
horn yayi me gadi ya buɗe mai parking yayi ya fito cikin sauri stairs case bibbiyu yake haɗawa
na barandar inda zata sada shi da main parlour
Cikin sauri yake komai Hajiya ya tarar tana zagaye yawa me ɗawafi tana ganinsa tace

'' doctor ya zo yanzu haka yana ciki asharaf anya kuwa ba ƙasar waje zamu ƙara fita ba ko zasu
gano abin da ke damun inteesar...,

ƙasa yayi da idanuwansa duk irin dauriya tasa nema yake ya zubar da kwalla a hankali ya buɗa
baƙin sa yace

'' Hajiya kawai mu haƙura mu barwa Allah sau biyar ana fita da ita ba canji kullum abin kara
gaba yake wancan satin likita ce min yayi a ƙara taka tsantsan da ita saboda lakarta tana gab
da ƙarasa zubewa...,

yanzun nan nake ce mata na fito da ita ta sha iska kai ta gyaɗa min shine na dorata a kan
wheelchair na fito da ita wallahi bansan yadda akai ta zabe ba wai photo ka zata gani

runtsai idanuwansa yayi yana roƙon Allah ya bashi ikon cinye jarabawar nan yana cikin
mahuyacin hali ya rasa matar sa sakamakon haɗari
inteesar ce ka dai ta rage masa sai yayyunsa biyun da kanin sa junaid

duk wanda ya kalli haɗarin sai ya shiga roɗani motar lotsaiwa tayi jini sai mulala yake ba wanda
yayi zaton za a samu mutum ɗaya ya tsira a cikin motar sai gashi inteesar ta tsira lokacin da
motar take murginowa nusaiba ta cillota banda kujewa da tayi ba abin da ya sameta sai daga
baya an kaita asibiti aka ga lakarta ta sami matsala haɗa gawar ta aka kai ta gidan gaskiya ba
irin kuɗin da inteesar bata lashe ba amma ji kake shiru ba wani ci gaba maganar ta ma ba fita
take sosai ba...

Fitowar likita ita ta katsai mai tunanin sa da sauri ya karasa gurin doctor Imam yace

'' doctor me yake damunta..?,

calm down ansh komai ya zo da sauki yanzu haka ma tana bacci nayi mata allura kamar yadda
na faɗa maka zan kara maimaita maka inteesar tana buƙatar me kulawa da ita har tayi bacci
Ummina take faɗi dole idan muna so tunaninta ya dawo normal irin nada


UWAR GAFALALLU

OUMYASMEEN


3-5


sai an nemo wacce zata zame mata copy din mahaifiyar ta cemin tayi zan nemo mata umminta
nace mata eh yarinyar abar tausayi ce kamar ta ta haɗu da wannan lalurar

gumine ya wanke mai fuska handkerchief ya zaro a aljihunsa ya goge zufar dake tsassafomasa
yace

'' insha Allahu zan yi maganin matsalar...,

wani kallo Hajiya tayi mai ta maida hankalin ta gun doctor tace

'' dr na gode sosai...,

bakomai Hajiya ki huta lafiya sai anjima

to mu jima da yawa

fita yayi shiga dakin sukai tana kwance kalbar da Hajiya tayi mata ta kara yi mata kyau an mata
ado da beat pink da blue colour adon rigar ta zama yayi a bakin dan gadon ta yana shafa
fuskarta

Allah ya baki lafiya takwarata

a hankali ya motsa lalɓansa yace

'' amin...,
wacce shawara ka yanke akan batun doctor

ba ƙaramin saka shi rudani maganar Hajiya tayi ba sarai yasan halinta kamar yunwar cikin sa
gashi doctor ya ƙara saka ta a hanya daman kullum maganar ta nusaiba ta tafi baza ta dawo ba
kayi kokarin fitar da ita a ranka tsakanin ka da ita addu'a

ganin kamar baya sauraronta tace ...kai da kai fa nake

Hajiya wallahi ban san abin yi ba

ban gane ba lafiyar ka ƙalau kuwa asharaf

ta gumi yayi yana fargabar a bin da Hajiya zata ce ba zai iya zama da ko wacce mace ba tun da
nusaiba ta tafi ta barmai duniyar zai ci gaba da zama har shima randa kwanansa zai ƙare yana
fatan Allah ya haɗa su a aljanna

wallahi asharaf buɗe kunnen ka da kyau ka jini idan har baka nemi mafita ba to wallahi ni da
kaina zan ne mi wacce naga ta dace na aura baka shima mahaifinka ya zuba maka ido yanzu
Junaid yau sauran wata biyar a yi bikinsa amma kai ko a jikin ka rayuwar ka kake ba abin da ya
dame ka
ina ji ina gani ba zan rasa inteesar ba bayan kana da maganin matsalar ta na rasa yar uwata na
zo na ƙara rasa nusaiba ita nake gani nake jin sanyi a raina ita kaɗai ce ajiyar da nake gani
kamar yar uwata hamdiya to itama Ubangiji ya dauke ta

shiru yayi ya kasa kwakkwaran motsi har ta gama ya tashi yace

'' zan shiga daga ciki bazan koma gun aiki ba .....,

okay haka kurum tace masa ganin kamar ranta a ɓace yake ya ɗurƙusa yace

'' Hajiya kiyi hakuri insha Allahu komai zai zo ƙarshe..,

murmushi tayi ta dafa kansa tace

'' da yardar Allah , Allah zai zaɓa a maka matar da zaka ji daɗin zama da ita zata kula da
maraicin inteesar nasan abin da kake hange kenan shi ya saka ka kasa aure insha Allahu zaka
sami farin ciki Allah ba zai taɓar da kai ba...,

tasho yayi yana murmushi fakar idonsa tayi ta goge kwalla hakika suna cikin jarabawa Sai dai
Allah ya basu ikon cinye ta

fita yayi kai tsaye shashinsa ya shiga ciro wayar sa yayi ya ajie sannan ya kwanta a kan kujera
yana kallon P.O.P ya lura duniyar tunani


UNGUWAR YAN BITA,KOFAR NASARA

tun daga nesa kake hango yan ca'ca damƙam sai bugata suke asabe ce ta fito tana gyara
daurin zanin ta da taba a faranti irin na silver din nan da goro har da letar ta ajiye wa tayi tana
cewa

yauwa jagwa gashi nan ta dubu biyar ce cib wallahi naga ba haka ba billahillazi sai ka biyani
ficikata ba za tayi ciwo ba

asabe idan zaki dinga zargina to wallahi zan dena amsar kayan ki ke kenan kullum zuciyar ki da
tsatsa

kut langa langa ce ba tsatsa ba sau nawa kake min runto

shafa gemunsa yayi yace sau uban talle

ehyi mee kace

yar dariyar shaƙiyanci yayi yana cewa a'a ba magana kika ji nayi

sarai ta gane sunan babanta ya kirawo ya ce sau uban talle tashi tayi tace

'' na tafi police station..belin sunusi...,

to sai kin dawo

gyautai ne ya ɗago da sauro yace '' Asabe ina zuwa haka da yammacin nan..kike sauri kamar
zaki tashi sama ko wani abin ne ya faru ki dan tsakura min...,

wani kallon banza tayi mai tace '' Gyautai inda ka aike ni...,

to abin kuma har da faɗar magana cewar gyautai yana har haɗa katin karta

gyara matafinta tayi tace

'' ajiye ni kayi da zakai min wannan maganar wallahi gyautai ka kiyayeni ke kenan jiya a yau ko
ca'car nan ba wani min sa'a kake ba...,

girgiza kai yayi yace ''Allah ya baki hakuri amma wallahi zaki zo ki same ni saina karta miki
rashin mutunci.., yana gama faɗar haka ya juya ya ci gaba da ca'car sa.,

wata dariya ta sheƙe da ita tace

'' mudai kartawa juna har ni zaka faɗawa tashanci ka manta wacece ni..,

ina fa namanta wane besan halin uwantale ba kudai ga kunan duk ba na Allah gwara mu gidan
mu gidan malamai ne

wata uwar dariya tayi tana buga cinya tare da rausaya irin na tsofaffin yan bariki sannan ta
juyawa tayi ta fara tafiya wayar ta ce ta fara ringing a ciki ta soke ta da sauri ta fito da ita ganin
sunan D.P.O wata uwar dariya tayi tana cewa shegen kaya yaga har yanzu be ji wani motsina
ba shine yanzu ya biyo sawu na to gari yaci wuta aljihu ba ko sisi
ɗagawa tayi ta kara a kunne tace '' to uban son kuɗi daman tun da naga ka kama yarona kuɗi
kake nema..,

D.P.O yace '' ki zo da wuri wallahi dan gobe zan tattara su na kai kotu babban laifi ya aikata
kuma har ke ta shafa domin cewa yayi ke ce dilar sai da kayan maye duk wani kayan maye kina
siyar wa har hodar ibilis dan haka idan baki zo ba har ke ta shafa ato...,

a fusace tace '' kai anya kuwa kanka ɗaya na zama dilar kayan maye na zauna a haka kai
kasan wallahi nafi karfin gidan da nake zaune sai dai zama a j.r.a kuma wallahi karya kake kace
ya faɗa maka haka , haka kurum sai ka bushi iska ka dinga kama mini yara to wallahi
hawainiyar ka ta kiyaye ramata gani nan zuwa dubi biyar zan baka daga ita ko kobo bayan ƙara
ba domin wallahi a haka ma da nawa na ƙara kasan an kama ANAI to na batar da kuɗi wallahi

kafi a sako shi hukuncin shekara biyar fa aka yanka mai to ko wata bakwai beba suka sako shi
yanzu a kudin da suke tarawa sauran dubu uku yar satar nan ba samu suke sunayi ba yanzu
kowa taka tsantsan yake da abin sa rayuwa tayi tsada.. yanzu so nake na tafi nijar na nema
musu sa'ar rufe ido damfara za su fara wallahi ina dalili bani da komai ya ƙare...,
cikin ɗaga murya D.P.O yace

'' to wallahi kar ma ki sake ki zo, me kika mai dani ban san me nake ba kome belin kwatan dan
ta'adda shi ne za kiyi a 5k yawa belin ƙaramin ɓarawo tab gyara kalaman baƙin ki kema kinsan
bazai saɓo ba bindiga a ruwa...,

da sauri ta tari numfashin sa tace '' to ka ci gaba da riƙe shi......yawa da chainanci nake maka
bayani ka kasa fahimta kana ga jibi ajon dan bashir ya kake so nayi da raina sarai kasan yadda
ajo yake ba sai na tsaya ina yi maka dogon bayani ba dole rance zanci nima na fito na watsa
yan dubu dubu...,
ke wai da ruwa muke magana...kin tsaya kina yi min sokiburutsu kema baki wuce na jefa ki a
cell ba

hhhhhhh anayi muna jin dadi ni asabe reza zaka jefa a cell tab to wallahi ka iya baƙin ka ni abin
kunya baya na bashi sai na tona asirinko ko banza zan samu sassauci a gurin hukuma amma
kai fa ba hukuncin da baka sani ba ka take kana karbar haram

ta faɗa tana girgiza yawa a gabasa take jin wayar ta tace kitt da sauri ta duba dariya tayi ta soke
ta a inda ta fito da ita

kamar saukar a rado taji durowar mutum yace '' ke kawo wayar hannun ki..,

da sauri ta ɗago tana hura hanci tace

'' ban gane ba...,

zaki fito da ita ko sai nayi gunduwa gunduwa da naman ki

Cikin sauri asabe tace '' a'a sala sala za kai da nama na dan kuka ashe haka ka zama.,

da sauri wanda yake laɓe ya fito shine wanda idan ya kwata zai cilla mai ya gudu yana shan
sholisho yace

'' baba ankar mana uwar gafalallu ce..da hallacan zo mu ware..,

a'a hafizu da ka barsa na ci kuttumar ubansa wallahi har yanzu nima ina ji da dabanci banda
haihuwa da ta gama buɗa kashina ai wallahi da tuni wani zancen ake yi ba wannan ba

cewar asabe tana kulle mayafinta a ƙugu

wucewa sukai ba

2 / 7