Author : Saadatu bint Abdullah Category : Read Hausa Novels
an tabbatarmin da malamaine na Allah
da Annabi Muhammadu SAW, bawai bokaye ba…wasu kuma masu bada maganin gargajiya
ne…” JAROOD ya amshe da “Amma kuma shine ka kaini gün wanda yasani na Auri Hajiya
Aisha dasunan za asamu waraka inna Aureta? Kaga watoma yasan gaibu kenan, Gashi kuma
ba nasara, ubangiji na kuma nuna mana bawanda yasan gaibu seshi, kuma ba wanda ya isa ya
bani lafiya Se ubangijin daya jarabceni da wannan ciwon, dan Allah mu hakura mu Fawwalawa
Ubangiji komi wlhi dogaro ga Allah ya isar min komi kawai na hakura…” JAROOD ya karashe
mgnr yana kwantar da seat din dayake ya d’anyi baya kadan, se sauke ajiyar zuciya yakeyi
yayinda yakeji kmr zuciyarsa zata kone saboda zafi da tukikin da take masa, maganganun
hajiya Zulaikha kawai ke yawo a kogon zuciyar tasa. Cikin tattausar lafazi malam wanzan yace
“Ranka ya dade dan Allah kabari muci gaba da gwadawa inaji ajikina wata rana za a dace,
kuma ubangiji yaga zuciyarmu muna rokon lafiyarka agaresa kuma muna neman magani, shi
dakansa yace katashi in taimakeka, Allah yafimu sanin kanmu, ba haka Aka haifekaba yi maka
Abunnan Akayi, marasa imanine suka maka wannan mugun sihirin, ka kwantar da hankalinka
ranka ya dade mun tsaida Allah daya munsan ze temakemu insha Allahu wannan problem din
ze zama labari, amma fa semun dage da Adduah kuma da neman maganin , kafin ubangiji ya
sauke cuta saboda san da yake mana seda ya sauke mana maganinta,, insha Allahu Aski yazo
gaban goshi dan Allah ranka yadade karka Sare karfin guiwarka nima kasaremin tawa…”
JAROOD daketa sauraransa kuma yana tunano maganganun hajiya Zulaikha. Yanaso yasamu
lafiya saboda bejin dadin abinda hajiya Zulaikha ke masa Gashi ba halin yasaketa, sbda
mahaifinta yace duk randa tarabu da JAROOD toh tsinuwarsa ta tabbata agareta kuma karta
sake ta Tunkaro masa gida. “Shikenan Baba Allah ya tabbatarmin da Alkhairi…” Cewar
JAROOD. Malam wanzan yaji dadin abinda yace ya amshe da “Yawwa kokaifa yallabai, Amin
ya Rabbih… wallahi nasan me kakeji ranka ya dade ga mata har mata ka tara Amma baka
basu wutaaaa..” JAROOD yayi dariya yace “Babana kuma Aminina…” malam wanzan ma
dariyar yayi yana Cewa “Eh mana ai gaskiya nafadi ka tara kaya ba injin, amma insha Allahu
kwanan nan Injin ze fara aiki…” JAROOD ya amshe da “Amin ya Rabbih Allah ya amince…nida
Kaifa baba marabar kadan ce…” JAROOD ya karashe maganarsa yana kwashewa da dariya
çıkın zolaya , inde suna tare da Malam wanzan se yaji Rabin damuwarsa ta gudu. Malam
wanzan ya bushe da dariyar shima yana fadin . “Gyan-gyan nake jina ai yanzu gashima harna
Ajiye y’a, nayima Giwar sarki takwara…” JAROOD yayi dariya yace “Au namanta fa, amma yar
taka nawa take koni da haihuwa nakeyi ai da yanzu nahaifi wadda tafita wallahi…” cikin
barkwanci suke maganar. Malam wanzan daketa dariya har yanzu yace “Tinima kuwa ranka ya
dade, da kyar nasamu Nima wallahi, in baka mantaba kusan mata goma sha biyu na Aura muka
rabu duk basu haihuba sbda matsalar daga gareni ne, se yanzu ubangiji yasa dana Auri
wannan matar tawa ta karshe Nasamu na haifa y’a daya shekararta goma sha hudu yanzu,
kaga komi ai hikimar ubangiji ne akaina ma yakamata kaga ishara, duk gun me maganin da
mukaje cewa akeyi bazan taba haihuwa ba, asibitocin daka kaini da kanka har kasar waje sunfi
akirga,,, Kagani se yanzu ubangiji yabani haihuwar, kaima inaji ajikina zan dauki d’anka a
hannuna insha Allahu…” JAROOD ya jinjina kai yayinda yakejin dadin hirar tasu yace “Allah ya
nunamin randa zan hau duri inyi sukuwa…” JAROOD ya fadi ko kunyar malam wanzan beji ba
sbda Amininsa ne sun Saba irin wannan maganar. Malam wanzan ya kuma kwashewa da
dariya kana ya amsa da “Amin ai kai daga ganinka bazaka ragama duri ba… Yanda kake
labcecennan ai nasan itama Gimbiyar labceciya ce…” JAROOD da nishadi ke kwance Akan
fuskarsa yace “Ai nida Kaina innaje wanka Abarnan nabani tsoro innaga girmanta, kai kaga
Abaaa lafceciya…Kai Allah ya ragema Aya zakiii…” malam wanzan yasake dariya yace
“Wannan Ayar kam da zakinta…wannan inta mike yaya kenan, Inka shiga gunnan Yanda
yakeda mugun dadih da ruwa-ruwa kamar fadama ai inaga seka kusa kashe yar mutane..”
JAROOD ya tashi zaune yana dariya yana fadin “Sekace de wani Mugu…Amma nide inaso ka
fassaramin yadda gun yake da dadinnan da kullum in muna magana seka fadi gun nada dadih
nifa ko shaawah baya bani…” malam wanzan yace “Ai duk yadda zan gaya maka dadinsa baza
gane ba nan gaba da kanka zaka gayamin yadda kaji dadin nasa, Kaiii inka fara sukuwa
agunnan zakaji kamar karka fito sbda dadinsa…Kabari kawai lokaci na nan zuwa…” JAROOD
daketa murmushi yace “Allah ya tabbatar,” malam wanzan ya amsa da “Amin….” Suna tafe
suna hirarsu ta nishadi har suka iso Anguwar sarki inda gidan Sarki yake sauka inyazo Nigeria
a kaduna. Babban gida ne wanda ya amsa sunansa tako ina an kewaye gidan da zanen
sarauta da adon sarauta yan sanda zagaye da gidan suna tsaron gidan, wannan sarkin ba
karabutin sarki bane, sarkine ga Kudi ga Mulki, kuma Gadon sarautar yayi bawai asama
yasameta ba, masu abune da Abunsu. Packing motar malam wanzan yayi a babban packing
space din gidan. A tare suka fito da JAROOD daga motar, nanfa mutanen dake zagaye da
gidan suka fara zubewa suna miko masa gaisuwa yanata binsu yana amsawa cikin safin fuska.
Yafi karfin 30mnt a waje yanata amsa gaisuwar ma’aikatan wadanda ke sanye da irin kayan da
ma’aikatan gidan sarauta kesawa. Da kyar JAROOD yasamu ya nufa part din mahaifiyarsa,
gidan babba ne sosai girmansa ya wuce lissafina. Allah-Allah JAROOD yakeyi ya isa falon nata
domin yayi ido biyu da mahaifiyar tasa. Nanma yanata cin karo da maaikata abunka da gidan
sarauta. Afalon mahaifiyarsa yahadu da Jakadiyar mahaifiyarsa hajiya sabuwa tsohuwa ce
amma ba sosai ba sbda tana cikin hutu. Suka gaisa da JAROOD ya tambayeta “Awani Falo
Giwar sarki take?” Jakadiya ta amsa masa da “Tana falon sama, tinda ta tashi daga bacci da
asubahi tayı sallah yau bata koma bacci ba sbda tanaso taganka…” murmushi JAROOD yayi
hadi dacewa “Okay…” ya nufa Saman ita kuma jakadiya ta nufa hanyar fita daga falon. Ko ina
ya tsaru da kayan alatu ado iri daban-daban na gidan sarauta, se kamshi kawai ke tashi tako
ina domin itama Hajiya Fatima batason kazanta tanasan kamshi agunta JAROOD yagaji san
kamshi. Da sallama yashiga falon nata wanda ya tsaru yaji luntsuma-luntsuma din kujeru na
alfarma kalar Ligt brown,. Wata farar mace na hango gishingide akasan carpet ta tada
hannunta da tin-tin irin na sarauta, sauratarma ta mutanen Agadez. kyakyawa ce sosai dukda ta
manyanta amma hakan be hana bayyanar tsananin kyaunta ba, kai dagani kasan itadin
cikakkiyar buzuwa ce wadda ta amsa sunanta na buzaye, Sak ita JAROOD ya biyo amma
gaskiya yafita kyau, ko alaunin fata ze tabbatar maka dasu ba yan nigeria bane. Tanajin
sallamarsa ta amsa ta tashi zaune tasha doguwar rigar Abaya wacce tasha ado tako ina ta
daura dankwalin Abayar akanta, wuyanta sanye da sarkar danyen gold da hannayenta.
bakaramin amsarta Abayar tayi ba, hancinta zir har baka ga karamin baki, sak de kamarta da
JAROOD tanada karamar fuska wato baby face, hutu ya ratsata tako ina, jikinnan kamar ataba
jini ya bulbulo, se glowing takeyi Tana shekin kyau da fitar da wani shu’umin siririn kyau, ita
bame qiba bace kuma ba siririya bace, babbar macece amma sam bata tsufa ba sbda Akwai
gyara irin na yan Niger uwa uba kuma ga Hutu. “Vie moi…(rayuwata)” hajiya Fatima ta fadi da
siririyar muryarta cikin harshen French, se murmushi takeyi wushiryarta tasama da kasa ta
bayyana yar siririya, Abinda ya rabasu da JAROOD kenan shi beda wushirya amma yafita kyau
da farar fata ma duka. Wani irin murmushi JAROOD ya saki na zallar murnar ganinta dajin
dadin sunan data kirasa dashi, tin yana karami daman haka takece masa RAYUWATA. ya
karaso ya kamo hannayenta yayi kissing kana ya tsugunna ya gaidata da harshen French
“Bonjour mon premier amour,(good morning first love)” hajiya fatima tayi murmushi zatayi
magana JAROOD yace “Kiyi hausa Amour (Love)…” murmushi hajiya fatima tayi cikin hausarta
da bata kware ba, saboda ita cikakkiyar buzuwa ce, tace “Kasan hausar nan da wahala…”
JAROOD yace “Da haka zaki Iya Ai Amour..” ta jinjina kai tace “Haka ne…Yana sameku ya
JAROOD dina yake da iyalinsa?” Murmushi JAROOD yayi daya ganta dukse taji damuwarsa ta
gushe. “Alhamdulillahi Amour, ya gajiyar hanya ya kuka baro Mon Pere?(My father)” hajiya
fatima ta amsa da “Lafiya lau yaso mu taho tare amma hakan be samu ba, ayyuka sun masa
yawa, baka tambayi su Mardiya da sajeeda ba seka fara da tambayar babanka…” duk cikin
rashin kwarewa ahausa take maganar. Mardiya da sajida kannen JAROOD ne su uku kawai
mahaifiyarsu da mahaifinsu suka haifa duk suna gidan Aurensu. “Ai daman yanzu zan
tambayesu Amour, yasu Mardiya da sajida ya kuma mamana?” Cewar JAROOD da yayi mgnr
yana murmushi. Hajiya fatima tadan hade rai sbda mgnrsa ta karshe. “Lafiya lau..” tabashi
amsa agajarce. Murmushi JAROOD yayi yafi kowa sanin duk duniya ba wacce mamanshi ta
tsana kamar Abokiyar zamanta, wato Amaryarta Hajiya Sadiya. “Yaya jikin naka? Har yanzu
Anata Fama ko? Gashi shekaru nata tafiya kwance tashi asarar me rai…” JAROOD ya sadda
kansa kasa yace “Ehe wallahi Amour har yanzu anata fama, insha Allahu, Allah ze kawo
sauki…” jinjina kai kawai tayi nan da nan yanayinta ya sake sauyawa tace “Wallahi Sadiya
tacuceni , ni nasan ita tamaka wannan mugun asirin, duk inda mukaje cewa akeyi itace tayi
wannan kullin saboda taga ita bata taba haihuwa ba, seni nahaihu kuma nahaifa d’ana miji, da
mata biyu, shine ta kashemin namijin yadda bazaka moruwa, Allah ya isa tsakanina da Hajiya
Sadiya, wata shara’ar nida ita se munje lahira…” hajiya fatima ta karashe tana sharar kwallah.
Cikin muryar kwantar da hankali JAROOD yace “Ki kwantar da hankalinki Amour, kinga fa
ba’atabbatar ita tamin asirinba, ni nadauka jarrabawar ubangiji ne kawai, insha Allah seya
yayemin Amour bawanda yasan gaibu se Allah, duk lalube ake Cikin duhu…” humming kawai
hajiya fatima tayi tace “kai yarone JAROOD nafika sanin wacece hajiya sadiya ta azabtar dani
tin kana ciki ubangijine ya rubuta sena haifeka JAROOD …” JAROOD yace “Haka ne Amour toh
Abar masa komi shi yasan yadda zeyi dani…” ya karashe yana kokarin danne damuwarsa
saboda yadda yaga mahaifiyarsa nacikin damuwa. “shikenan Allah ya kawo mafita…” hajiya
fatima ta fadi, daman ita macece me hakuri da saukin kai. JAROOD ya amsa da Amin. “Wanzan
yacemin ansamu wani me maganin kou ?” Hajiya fatima ta jefo masa tambayar. JAROOD ya
amsa da “Ehe Amour, amma nagaji da ziryar neman maganinnan…” “Me nema ai baya
gajiyawa JAROOD, ka jure insha Allahu wata rana za adace, inata maka adduah bana bacci
sbda kai wallahi…yanzu tinda nazo ma tare zamuje gun masu maganin…” Cewar Hajiya fatima.
JAROOD yace “Toh shikenan Amour…” sukaci gaba da hira irin ta d’a da uwa çıkın So da
kauna.
Anan gidan yayi azahar tare da mahaifiyarsa sukaci abincin rana, se hira sukeyi taso da kauna,
sukayi video call shida mahaifinsa ta wayar mahaifiyarsa. Se wuraren 3;pm suka bar gidan
shida Malam Abdullahi wanzan , hajiya fatima taso sutafi tare gun maganin amma JAROOD
yaki da kyar yasamu ta hakura bata biyosunba sun rabu Akan ze dawo zuwa dare.
“Wai har Ina ne gun me maganin?” JAROOD ya tambaya malam wanzan dake driving tin Dazu
sunata tafiya har sunyi tafiyar 1H amma basu isa ba. Malam wanzan yana driving yace “Mun
kusa isa, ,,” JAROOD yace “Wani irin gurine wannan amma dagani dajine kou ?” Malam
Abdullahi yace “Ehe amma ba daji sosai ba, karka damu ranka ya dade mun kusa isa…” cikin
gajiyawa JAROOD yace “Wallahi nagaji da zakan motarnan..gaba daya ma nagaji da yawon
neman maganinnan…” ya karashe kmr ze fashe da kuka. “Insha Allahu wata rana se labari,
kwanan nan zaka hau Aiki kama hajiya babba ciki ka dawo kama hajiya karama ciki…” Cikin
kwarin guiwa malam wanzan ya fadi hakan. JAROOD yayi murmushi kawai. Yace “Allah amince
…” “Amin..” Cewar malam wanzan. “Inka samu masallaci mu tsaya muyi sallah…” Cewar
JAROOD malam wanzan Yace “Toh ranka ya dade…” tafiyar 2H sukayi suka isa wani masallaci
acikin gari, sukayi packing da motar securities dinsa. sukayi sallar la’asar suka idar sukaci gaba
da tafiya acikin wani kasurgumin kauye dake Cikin zariya. “Tafiya kamar ta barin kasa..” Cewar
JAROOD daya gaji da tafiyar, seya kwantar da kujera ya tasar ya rasa ma yazeyi dukya gaji
saboda be saba tafiya me nisa ba a mota sede ajirgi. “Mun kusa insha Allahu…” Cewar malam
wanzan. Jarood yaci gaba da mita “Ai da kawai jirgi muka hau dakasan da nisa har haka…”
Malam wanzan de yayi shiru se basa hakuri yakeyi danya kula yagajine. Seda suka kara tafiyar
20mnt kana suka isa wani d’an karamin gida Awani daji gabaki daya dajin gidanne kawai gida
adajin, gabas da yamma bawani gida se wannan gidan, mutanen dake zaune awajen gidan
sunyi layi sunfi mutane dari uku, kama daga kan jinsin maza da mata, amma gaskiya mata sunfi
yawa sun baibaye ko ina ga manyan mutane tako Ina, anyi packing motoci sunfi motoci dari
biyu ata farfajiyar bukkar gidan. “Wani irin gida ne wannan kamar gidan matsafa? Dan duk
mutumin dake shuka alkhairi baze baro çıkın gari ba yadawo daji…” Cewar JAROOD daya fadi
mgnr yana kallon gidan yana kallon malam wanzan. Malam wanzan ya bude baki zeyi mgna
JAROOD yaga wani mutum ya fito daga gidan hannunsa rike da wani jan kyalle irin na tsafi.
Haka kawai JAROOD yaji sam hankalinsa be kwanta ba gaskiya. “Gidan bada maganine ranka
ya dade bakaga mutane tankanba…” JAROOD ya girgiza Kai yace “Gaskiya wallahi ban yadda
da gidannan ba, nan gidan matsafa ne, dagani ba Aikin ubangiji ake shukawa ba a
gidannan…ajuya mota kawai ka mayar dani Gidan Amour maza cikin hanzari kafin gari ya fara
duhu kasarnan ba lafiya bace da ita…” malam wanzan ya kalli JAROOD yace “Haba ranka ya
dade musha wannan doguwar tafiyar kuma kace mu juya? Dan Allah ka fita muje kashiga
kagani bawai gidan tsafi bane gidan maganin gargajiya ne, shiga kawai zamuyi nariga naje jiya
nakama mana layi yanzu shiga kawai zamuyi…” “wallahi bazan shiga ba… dan Allah mu juya
kawai wallahi nagaji , bazan kara dawowa ba gun wani neman magani daga yau wallahi, nariga
na hakura…@ JAROOD ya fadi. Malam wanzan yashiga lallaminsa da lallabasa kan yashiga
amma JAROOD yayi fır yaki, wanzan yayi-yayi JAROOD ya tubure. Dole suka juyo da motar
suka dawo kaduna ran Wanzan adagule, sam ba haka yasoba, yaso ace su shiga su amshi
maganin yanaji ajikinsa za adace. Amma JAROOD yaki, hakan ba karamin batama wanzan rai
yayi ba. A anguwar sarki sukayi sallar Magriba, awajen gidan kana suka nufa falon Hajiya
Fatima atare shida JAROOD, daman Hajiya fatima tanata kiran malam wanzan saboda tasan
inta kira JAROOD bezama lallai yana kusa da wayarsa ba, sbda shi ba ma’abocin waya bane,
amma yana kiran mahaifiyarsa sede itadin tafiso takira malam wanzan, tafi sabuwa da hakan.
amma JAROOD inyaga kiran mahaifiyarsa yana dauka. “Malam ina
zakaje? JAROOD ya juyo ya kalli malam wanzan ya jefo masa tambayar, ganin yanaya binsa
zuwa falon mahaifiyarsa.
This book is 1k 08101626484.
FIL’AZAL
(Romantic and love story)
https://chat.whatsapp.com/CyBhsjJtnx7C5FWgP88xX1
SAADATUBINTUABDULLAHI✍(Writer of Kyautar Allah)
This book is 1k 08101626484.
Free page3
Malam wanzan ya kalli JAROOD yasan dalilin dayasa ya masa wannan tambayar. “Zanje gun
uwata ne nima mu gaisa ,ko angaya maka kai kadai keda Giwar ne…” cewar malam wanzan.
JAROOD yayi murmushi yace “Ku tsaya a gaisuwar, wlhi karka sake ka gayama Amour naki
shiga gun me maganin…” “toh..” kawai malam wanzan yace da JAROOD, amma badan ya
dauka ba. Suka isa falon da sallahma Hajiya fatima na kasa tana zaune da charbi a hannunta
sanye da maroon hijjabi har kasa, dagani yanzu ta idar da sallah tana lazimi. wani sabon
kamshi ke tashi a Falon da Sassanyar sanyin AC. Tin shigowarsu ta washe baki hadi da Amsa
sallamar tasu tace tana kallon JAROOD. “Sannu Vie moi…” “Yawaah Amour…” JAROOD ya
fadi yana karasowa gareta ya tsugunna ya gaidata ta amsa kana ta dawo da dubanta ga malam
Abdullahi wanzan wanda shima ya zube se kwararo mata gaisuwa yakeyi. Ta amsa fuska sake
tace “Ga kauna, ga kaunah…” JAROOD yayi murmushi shima malam wanzan din murmushi
yayi, sun fahimci me take nufi, daman hakan takece Musu inta gansu tare. “Zauna mana malam
wanzan kabani bayanin yaya ake cikin Yanzu kuka dawo daga gun maganin? Ina fatan de a
dace?” Hajiya fatima ta fadi mgnr tana kallon malam Abdullahi dake tsugunne tinda ya gaisheta
be zaunaba. Zaunawa yayi Akan lallausar carpet din dake falon yana facing hajiya Fatima ya
kalli JAROOD yaga shima shi yake kallo ya wani hade rai. Amour ta kalli Wanzan ta kalli
JAROOD ta kula da irin kallon da yake ma wanzan. “Inajinka bani bayani nana, kasan wannan
Karan bazanbar kasar nan ba insha Allahu se naga ya Ake ciki?” Hajiya fatima ta kara fadin
hakan tana tsare malam wanzan da idanuwa. Yayi shiru ya kasa magana saboda ya rasa meze
ce. “Ya kayi shiru kuma inata magana ko kana tunanin wani abunne??” Hajiya fatima ta kara
jefo wa Malam wanzan tambayar ganin yayi shiru tanata mgna shiru. Malam wanzan ya dauke
idanuwansa Akan JAROOD ya dake ya fara magana cikin girmamawa kansa kasa yace “Ranki
ya dade Allah ya kara Miki lafiya, wallahi