Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
na je na tarar da wani mutum ya yi gini har ginin ya kusa linta."
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Wallahi ban san yadda abin ya kasance ba..."
"Ai kuwa za ka sani, don wallahi naira biyar tawa ba za ta yi ciwon kai ba." Alhajin Ya katse Abba, nan take suka shiga musayar kalamai. Shi Abba yana ƙoƙarin kare kansa, shi ma Alhaji yana nuna dagiya a kan haƙƙinsa. Har wayarsa Abba ya ciro yana neman layin Gambo dillali amma ta ƙi tafiya. Ganin hayaniya ta yi yawa ya sa ɗansandan cewa.
"Yanzu ba abin tashin hankali ba ne, za mu yi duk cike-ciken da ya dace mu miƙa ku kotu. Idan ya so sai a yi bincike a tabbatar wa da mai gaskiya gaskiyarsa, wanda ba shi da gaskiya sai a hukunta shi."
Da wannan suka tashi, a kan Abba ya saurari sammaci daga kotu. Koda Abba ya fita daga zonal kai tsaye wurin filin da ya sayarwa Alhajin ya nufa, sai dai yana zuwa ya yi turus ganin leburawa rututu suna ta aiki. Wasu suna kwaɓa ƙasa, wasu suna ɗiban bulo suna jerawa, yayin da wasu suke hawa tsani suna miƙa suminti. Ruwan mamaki ne ya wanke shi, don ya gasgata abin da ya gani ba gizo idonsa ke yi ba sai da ya tambayi ɗaya daga cikin leburorin.
"Assalamu alaikum! Don Allah tambaya nake yi."
Abba Ya furta yana mintsinin hannunsa don ya tabbatar da ba mafarki yake yi ba.
"Wa alaikassakam, Allah Ya sa mun sani."
Suka amsa masa suna zuba masa ido, sai da ya sake leƙen yadda ginin ya yi tsawo ya ce.
"Don Allah waye mai wurin nan ina nufin wanda ya ba ku aikin ginin nan."
"Amma bawan Allah ina ruwanka da mai ginin nan? Ko kai ma aikin kake son ka samu? To idan ma haka ne ya gama ɗiban ma'aikata"
Abba ya girgiza masa kai, sai ɗaya daga ciki ya ce.
"Mai wannan wurin ai ba bahaushe ba ne, kai ba ma ɗan ƙasar nan ba ne. Na wani ɗan china ne, idan kana jin kamfanin shinkafa na Girma rice to nasa ne." Abba yana jin haka jikinsa ya sake yin sanyi, don haka ya yi musu sallama ya wuce gida kansa yana masifar ciwo.
Yana zuwa gida Tani ta shiga ɗakin ta ga lokaci ɗaya duk ya firgice ya fita hayyacinsa, zama ya yi ya zuba tagumi da hannuwa biyu. Ba ta yi tsammani ba ta ga hawaye bibbiyu suna fita daga idonsa.
'Hmmm wallahi tallahi hawaye ma yanzu ka fara shi.'
Tani ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Alhaji wai me yaka faruwa ne, tun fa da ka fita na kasa zaune da tsaye."
"Mene ne ma bai faru ba Tani? Komai ya rikice mini, masifa ta kowacce hanya sai faɗo mini take yi. Ya zan yi Tani? Mene ne mafita?"
Nan take ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da ita, sai da ya goge hawayen idonsa sannan ya ɗora da cewa.
"Na nemi layin Gambo dillali sama da ƙasa ba ya shiga, har wurin dillancinsu na je ko za a ba ni layin da zan same shi amma sun ce mini babu, yanzu haka sun ce matuƙar ban kawo Gambo dillali ba ni ne zan ɗauki asara tun da shi ya sayar mini. Kuma har abokinsa da suka zo tare na neme shi ban samu ba, ina cikin tashin hankali Tani."
"Har yanzu ba ka shiga ba."
Tani ta yi suɓutar baki ba tare da ta san zancan zai fita ba, da wani irin kallo ya dube ta. Cikin wayancewa ta ce.
"Ƙwarai kuwa Alhaji, tun da ai za a iya samun abokinsa. Da ace babu abokin Gambon shi ne ka shiga tashin hankali." Tsaki ya saki bai tanka mata ba, suka yi shiru gabaɗaya kowannensu da abin da yake saƙa wa a cikin ransa.
Daga wannan ranar Abba ya firgice ya lalace ya fita hayyacinsa don ko abincin kirki da bacci mai daɗi ba ya yi, duk inda zai buga neman Gambo dillali ya yi amma sama da ƙasa bai same shi ba. Yana cikin wannan gaɓar Alhaji Isah ya aika masa sammaci a kotu, kuma a wannan gaɓar ce Alhaji Dikko ya taso shi a gaba da zancan kuɗinsa don ya kwashe sama da sati biyu bai waiwayo shi ba. Saboda haka abin duniya goma da ashirin ya haɗe masa, ta ko ina fuskantar matsin lamba yake don ko kuɗin da zai ɗauki lauya ba shi da su. Sun fara zaman shari'arsa da Alhaji Isa ko wata guda ba a rufa ba, Alhaji Dikko ya aiko masa da na shi sammacin daga kotu. Cikin abin da bai wuce wata ɗaya ba Abba duk ya tsururuce, ƙanwarsa Goggo da ke ba ƙarfi gare ta ba kullum cikin yi masa addu'ar samun mafita take. Abu ɗaya ne ma ya ɓata mata rai da farko har ta ɗauki fushi da shi, maganar kai Fauwaz almajiranci da ba ta ji labari ba sai bayan da ya riga ya kai shi. Saboda da ta ji da wuri ita za ta ɗauke shi ya koma wurinta da zama, duk da har lokacin ba ta gane ainahin kalar Tani ba. Sai da ta ji jarrabawar da Abba ya shiga sannan ta sauke fushinta, har take zuwa wurinsa tana sake kwantar masa da hankali.
A ranar da za su fara zaman shari'arsa da Alhaji Dikko, har ya shirya zai fita Tani ta biyo shi ta ce.
"Ji mama Alhaji ina magana."
"Tani sauri nake kada na makara."
Abba ya ba ta amsa a gaggauce, da sauri ita ma ta sha gabansa tana cewa.
"Ba daɗewa zan yi ba, da ka aiwatar ne za ka yi gaba malam."
Jin yadda take yi masa magana cike da isa-isa ya sa shi kallonta, Tani ta turo ɗankwalinta gaba ta ce, "Takardar sakina za ka ba ni, don ni ba matar shan wahala ba ce."
MALAM HASAN
Ganin ta cigaba da tafiya sai ya sha gabanta da sauri ya ce.
"Ba magana nake yi miki ba Rakiya, ki tsaya ki saurare ni."
"Ba zan tsaya ba! Ka ƙyale ni na tafi tun da ba ni da sauran amfani a rayuwarka. Dama an faɗa mini tamkar baiwa haka nake, tun da babu wata mamora a gare ni saboda ni juya ce."
Rakiya ta furta masa a fusace cikin ɗaga murya, waigawa ya yi ya ga babu mutane a ƙofar gidan nasu sai wani matashi guda ɗaya da ya zo wucewa. Malam Hasan ya sauke ajiyar zuciya, ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Don Allah ki daina ɗaga murya kada mutane su ji, ki zo ki wuce gidan Kawu yanzu a daren nan ina za ki je."
"Zan tafi duk inda ya yi daidai da rayuwata, ka rabu da ni Hasan babu inda zan je." Rakiya tana gama maganar ta cigaba da tafiya, duk yadda Malam Hasan ya so ya dakatar da ita fir ta ƙi amincewa. Don haka ya riƙo hannunta da niyyar su koma, a haukace ta fizge hannunta cikin ƙaraji ta ce.
"Ka rabu da ni, ba na son ganinka ba na ƙaunarka..."
Tass! Ya tsinke ta da mari, cike da ƙunan zuciya ta riƙe kuncinta tana kallonsa hawaye yana zuba, ta ɗauki lokaci a haka cikin sassanyar murya ta ce.
"Na gode da wannan tukwicin da ka yi mini, amma ka sani ko kashe ni za ka yi ba zan koma cikin ahalinka ba."
Ta yi yunƙurin ƙwacewa ya janyo ta, ya saka hannuwa biyu ya matse ta a jikinsa. Sunkuyar da kai ya yi har sai da suka fara jin numfashin junansu, cikin muryar nadama ya ce.
"Don Allah ki yi haƙuri, a tsakanina da ke ba na son na ji kalman ƙiyayya da kike furta mini. Yanzu ki zo mu je ki gidan Kawu."
Furzar da iska mai zafi ta yi ta girgiza masa kai ta ce.
"Ba za ni ba, ka ƙyale ni babu inda zan je."
Sai da Malam Hasan ya kai ruwa rana sannan ta amince ta bi shi suka wuce gidan Kawu Sani. Lokacin da suka ƙarasa Kawu Sani yana shirin rufe gida, yana ganinsu ya ce.
"Hasan lafiya na ganku a daren nan? Hala Kulu ce ta sake yin wani rashin mutumcin?"
Malam Hasan ya ɗan sosa kai ya ce, "Kawu maganar tana da ɗan tsayi, yanzu dai Rakiya za ta kwana a nan idan Allah Ya kaimu safiya zan dawo sai mu tattauna." Jinjina kai Kawu Sani ya yi ya ce, "Ikon Allah, Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan masifar." Suka amsa da Amin, Har Malam Hasan ya juya zai tafi Kawu ya ce. "Hasan idan ka san matsalar nan ta haɗa da su Kulu, to kana komawa ka ce gobe da sassafe ina son ganinsu ku dawo tare." Hasan ya amsa masa sannan ya tafi, bayan tafiyarsa Kawu da matarsa sun jima suna tausar Rakiya da ba ta baki, sannan suka bata makwamci ta kwanta.
Malam Hasan yana komawa gida a inda ya bar su Inna a nan ya koma ya same su, Inna tana ganinsa ta taɓe baki ta ce.
"To gantalalle, bayan ka sake ta uban me ka bi ta ka faɗa mata."
Shiru Malam Hasan ya yi yana jin zuciyarsa babu daɗi, Inna ta ɗora da cewa.
"Ai wallahi tun da har muka rabu da jaraba kun rabu kenan, na san halinka da nacin tsiya kana iya dawo da ita..."
"Inna Kawu yana son ganinku gobe idan Allah Ya kaimu."
Malam Hasan ya furta yana katse ta, riƙe baki Inna ta yi ta ce.
"Ai ƙara ta kuka kai kenan ko? To Allah Ya kaimu ai duk wacca za a yi sai dai ayi ta ta ƙare. " Malam Hasan bai tanka mata ba ya miƙe ya shiga ɗaki, da yake Zuwaira ta san ba ta shuka abin arziki ba ko magana ba ta yi masa ba, saboda yadda ya hautsine musu tsoron tanka masa take ji.
Washegari da sassafe su Inna suka dira a gidan Kawu, bayan an gaisa a nan ne ya nemi jin ba'asin abin da ya faru. Nan take Rakiya ta zayyane duk abin da ya faru, cike da jin haushi Kawu ya ɗauki hularsa ya jefa wa Zuwaira ya ce. "Yanzu Zuwaira rashin mutumcin naki har ya kai haka? Rakiyan ce za ta yi miki wanki har kike zaginta?"
Inna da ta gama cika fam ta ce, "To amma ai ka ji ɗayan ɓangaren indai ba son kai za ka yi..."
"Ke dallah rufe mini baki, kin girma ga yawan shekarun amma babu hankali." Kawu ya katse Inna, Rakiya ta saki murmushin takaici ta ce.
"Kawu ni dai a wurina komai ya wuce, dama fata na ya ba ni takarda ta kuma AlhamduLillah ya sake ni jiya."
Malam Hasan yana jin haka ya yi zaraf ya ce, "Ban saki matata ba Kawu, takardar da na ba ta jiya ba ta saki ba ce ta ban haƙuri ce."
"Ni kuma gaskiya na gaji da zaman gidanka, domin mahaifiyarka da matarka sun mayar da ni baiwa ni ma kuma 'ya ce kamar kowa." Inna ta yi mamakin jin furucin Rakiya, nan Kawu da malam Hasan suka shiga ba ta haƙuri. Kafin Rakiya ta haƙura sai da ya tabbatar musu da cewar daga wannan ranar babu aikin Zuwaira da za ta sake ɗauka. Hatta wankn Inna ta daina idan ba ita ta yi niyya ba, yadda su Inna suka ga Rakiya ta fitsare idonta tana faɗar maganganu ya sa har suka ji shakkunta. Sai da Kawu ya yi musu faɗa da nasiha sannan suka wuce gida Rakiya sai harare-harare take tana shan kunu.
Tun bayan da wannan al'amarin ya faru Rakiya ta samu 'yancin kai a cikin gidan, daga Inna har Zuwaira babu mai shiga sabgarta. Ita ma harkokinta take yi cikin kwanciyar hankali, kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci ta samu nutsuwa don har kiɓa ta yi. Ita kuma Zuwaira ta cigaba da feleƙe tana laulayin cikinta, yau ta tsiro da wannan gobe ta tsiro da wannan. Da gayya take kiran Malam Hasan idan yana ɗakin Rakiya ta ce masa wani abin take son ci, ko ta fito tsakar gida ta yi ta amaye-amayen ƙarya har sai Inna ta ƙwala masa kira ya fito. Daga ƙarshe ma sai ta tsiri cewa tana gane-gane a ɗakinta, don kada Malam Hasan ya zargi ƙarya take har da rana ko safiya haka take ihu ta ce ta ga giftawar mutum ko ta ce ta ji magana ko motsi a ɗakinta. Hakan bai taɓa damun Rakiya ba, don wani lokacin da kanta take saka shi ya tafi wurin Zuwairat ya kwana da ita idan makircin nata ya motsa.
Da yake Inna tana sana'ar sayar da koko da kunu da safe, sai Rakiya ta fara sana'ar ƙosai da wainar gero kuma cikin hukuncin Ubangiji tas suke ƙarewa. Zuwaira tana ƙyalla ido da ta ga haka, sai ta tsiri aman ƙarya da safe ta ce warin suyar ƙosai da waina ne ba ta so. Shi kuma Malam Hasan ya ce ba zai dakatar da Rakiya ba, kuma da ta yi wa Inna ƙorafi sai ta ga ba ta ɗauki wani hukunci ba. Da ta ga makirci ba zai kai ta ba, sai ta zari bin gidajen malamai da bokaye.
"Malam na yi yawo gidan malamai da dama, amma kusan duka kuɗina suke ci babu wata biyan buƙata a kan kishiyata. Don haka aka kwatanto mini wurinka, na ce zan gwada nan na gani."
Zuwaira ta furta wa mutumin, wanda ya fi kama da riƙaƙƙen ɗan bori. Daga shi sai wani ganye a ƙugunsa, wuyansa, hannuwansa da tsintsiyar ƙafarsa duka sanye yake da wuri. Kansa cike yake da wani irin ƙazamin gashi marar tsafta, kallo ɗaya mai ƙyanƙyami zai yi masa ya ji zuciyarsa tana tashi musamman idan warin jikinsa ya daki hancin mutum.
"Ni ba irin jabun malaman da kike zuwa wurinsu ba ne, kuma zan ci ki gyara ni ba malami ba ne. Ni boka ne taɓaɓɓe, ke ma kuma taɓaɓɓiya ce. Ki sa a ranki buƙatarki ta gama biya, saboda kin zo ne a kan kishiyarki. Me kike son ki yi mata, nakasa ta kike so ayi ko kuwa kashe ta zan yi. Domin ni ina kashewa, haukatawa kuma ina nakasawa amma da ikon Allah."
Bokan ya furta mata yana zuba mitsitsin idanunsa a kanta, tsuru Zuwaira ta yi ta shiga zare ido jin bokan ya ninka ta rashin imani. Jiki yana rawa ta ce.
"Ni kawai so nake.a datse alaƙarta da mijinmu, wallahi ba na son wani abu ya cigaba da shiga tsakaninsu. Amma ina son a ɓullo ta sigar da wani ba zai zarge ni ba, idan na ga wannan ya ci zan dawo ayi mini wani daban."
"Idan na lura ke ƙaramar sheɗaniya ce, har yanzu da sauran imani a zuciyarki. Amma tun da kika zo wurina dole mu halaka gabaɗaya, zan yi miki yadda kike so kuma babu wanda zai zarge ki. Ungo riƙe wannan."
Ya ƙarasa furucin yana miƙa mata wani garin magani da aka dama shi da ruwan sihiri a cikin farar leda.
"Ki tabbatar wannan maganin ya taɓa jikinta, amfaninsa a kan mutum ɗaya ne. Indai ya taɓa mutum ɗaya kowaye, to ko ya sake taɓa wani ya riga da ya tashi daga aiki. Ki yaye don kada a samu matsala, idan kika shafa mata shi duk bayan magriba Aljani Furzum zai dinga saka ta nannauyan bacci, ba shi zai ƙyale ta ba sai gari ya waye. Kuma duk tashin da za a yi mata ba za ta tashi ba, garin maganin mun haɗa shi ne da ruwan wankan gawa da kuma iccan kabari." Hannun Zuwaira yana rawa ta miƙa hannu ta karɓa sannan ta ce.
"Godiya nake boka Lado. Nawa ne abin da zan biya?"
"Ba kuɗi za ki biya mu ba a zuwanki na farko, za ki kwanta tsirara akwai abin da baƙaƙen Aljanu za su ɗiba a jikinki. Amma kada ki ɗaga hankalinki, babu wanda zai cutar da ke." Ya furta mata yana ɗauko wani ja da baƙin ƙyalle, Zuwaira tana son musa masa tana jin tsoro. Don haka a ɗarare ta tuɓe kayan jikinta, cikin jikinta da ya fara fitowa bokon ya ƙura wa ido. Bayan ta kwanta ya rufa masa ƙyallayen hannunsa, sannan ya rufe idonsa yana kiran aljanu. Sun ɗan jima a haka sannan ya ce ta miƙe ta saka kayanta, daga wannan ranar kuma idan za ta zo kuɗi kawai za ta kawo masa su ma ba masu yawa ba.
Zuciyar Zuwaira cike da farinciki ta nufi gida, sai bayan da ta shiga ɗakinta ta sake ciro ledar magani ta ƙare mata kallo ta tuntsire da dariyar ƙeta. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ajiye ta a gefe, ta shiga nazarin yadda za a yi ta kai maganin jikin Rakiya. Tun da na farko ita ba zama inuwa ɗaya suke yi ba, na biyu ba wata doguwar hira suke yi ba. Da ta yi tunanin ko ta takale ta da faɗa don ta shafa mata sai kuma ta tuna da boka ya ce maganin a jikin mutum ɗaya yake aiki. Kenan babu damar ta lakata ta shafa mata a jikinta.
"Ko na bari idan dare ya yi sai na shiga ɗakinta na shammace ta?"
Ta tambayi kanta, da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta. Tana nan zaune ta ji sallamar Malam Hasan, da yake ita ce da girki sai ba ta fita ba don ta san ɗakinta zai shigo.
"Rakiya zo ki gyara wannan."
Malam Hasan ya furta daga waje.
Jin haka ya sa Zuwaira ta ce, "Bantan uba, ni da girkina amma a ba wa wata shegiya gyaran nama."
Da sauri Zuwaira ta tashi, don duk a tsammaninta nama ne Malam Hasan ya kawo, bisa rashin sani ta take ledar maganin ta fasa ta. Maganin ya wanke yatsun ƙafarta, da yake a yunwace ta miƙe da masifa sam ba ta