Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
lura ba har ta fita tsakar gida.
Littafin 500 ne ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta nan lambar 07062062624 idan littafin ya kammala zuwa doc 800 ne.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[19/05, 17:24] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA TARA
Zuwaira tana zuwa ba ta yi wata-wata ba, ta hankaɗa Rakiya da ke duƙe za ta ɗauki ledar da a Malam Hasan ya ajiye mata. Kasancewar Rakiya ba ta san da Zuwaira ba hakan ya sa da ta faɗi ta bugu a hannu sosai, daga ita har Malam Hasan sakin baki suka yi suna bin ta da kallon mamaki. Cike da masifa Zuwaira ta ce.
"Saboda rashin adalci, ranar girkin nawa ka kawo nama za ka ce ta fito ta gyara. Dama ai ka sha cewa ta fi ni iya girki, wato shi ne za a nuna mini rashin adalci. To wallahi uban kuturu ma ya yi kaɗan ballantana na makaho." A wannan karon ma mamakin kalaman Zuwaira ne ya mamaye su, tana sunkuyawa za ta ɗauki leda ta ci karo da waken ƙosa da geron wainar Rakiya. Sororo ta yi jiki a saɓule ta ajiye, tana ɗagowa za ta juya ta tafi da sauri Malam Hasan ya fisgo ta ya ce.
"Wai ke wacce irin jahilar mace ce? Me ya sa ko kaɗan ba ki san ciwon kanki ba? Yanzu me kika aikata haka? Ko kin ɗauka yadda kike abu da jahilci haka kowa ma yake yi?"
Da farko shiru Zuwaira ta yi duk kunya ta kama ta, amma ganin Malam Hasan ya cigaba da yi mata faɗa ya sa ta fara borin kunya wai don kada Rakiya ta raina ta.
"Eh na ji ɗin, duk abin da za ka ce sai dai ka faɗa. Ai da ba a yi mini rashin adalci ba zan magana ba, wa ya sani ma waken ko da kuɗinka ka sayo mata." Zuwaira ta furta tana wurga musu harara, don Malam Hasan ya ƙara tunzura ta sai ya ce.
"To ai daɗin zama ne yake sa wa mace ta ce da miji baba, idan na sayo mata ai matata na ƙara wa jari ba wata ba."
Zuwaira ta sake hassala, suna jin ta fara hargagi Malam Hasan ya miƙa wa Rakiya hannu ta riƙe ya ɗago ta. Don ya sake dagula wa Zuwaira lissafi ya rungume ta yana kaɗe mata ƙasar jikinta haɗe da yi mata sannu. Waken ya ɗauka da kansa ya kai mata har ƙofar ɗaki, sannan ya shimfiɗa tabarma a tsakar gidan ya ɗauko ƙaton kwandon turarensa don Allah Ya saka masa albarka jarinsa ya ninku. Dogon tsaki Zuwaira ta saki ta koma ɗakinta cike da takaici, sai da ta zauna idonta ya sauka a kan ƙafarta da take jin maiƙo. Ƙirjinta ne ya yi mummunan bugawa, har sai da ta dafe shi da hannunta tana jin tamkar zuciyarta za ta finciko ta fito sarari. Laluben ledar maganin ta fara yi ta hango ta a bakin ƙofa ledarsa ta fashe wanda ya tabbatar mata da take shi ta yi da ƙafarta.
"Wayyo Allahna, na shiga ukuna."
Zuwaira ta ƙwalla ihu tana ɗora hannu a ka, saboda zallar tashin hankali. A hargitse Malam Hasan ya shiga ɗakin da gudu, cikin damuwa ya shiga jera mata tambaya.
"Lafiya me ya faru?"
Rasa bakin magana ta yi, don ba ta san me za ta ce masa ba, cikin inda-inda ta ce. "Dama zame wa na yi na faɗi, sai nake jin ƙafata kamar ta gurɗe."
Kallon tsaf ya yi mata, don duk wanda ya ƙare mata kallo zai ga ba ta yi irin zaman da za a ce mutum ya faɗi ba. Guntun tsaki Malam Hasan ya saki ya ce.
"Amma kamar ba musulma ba Zuwaira, ai sunan Allah ya kamata ki kira ba ihu ba."
Ita dai Zuwaira shiru ta yi tana kukan zuci, don hatta jikibta rawa yake saboda tashin hankali.
"Ina ne wurin na yi miki addu'a."
Malam Hasan ya tambaye ta yana zama a gefenta, ƙafar da ta taka maganin bokan ta nuna masa ta ce.
"Duk ƙafar take yi mini ciwo, ka tofe mini ita."
Gyaɗa kai Malam Hasan ya yi, sannan ya shiga karanta mata addu'o'in yana tofa mata.
"Allah Ya sawaƙe, ki dinga kula."
Ya furta mata cikin tattausan lafazi ganin duk ta yi laushi ta fita hayyacinta, wani tunani Zuwaira ta yi. Har ya je bakin ƙofa ta ce, "Ko na zo na je gidan Malam Bala mai kamu."
Malam Hasan ya juyo ya ce, "Ke da kike fama ina za ki iya fita, ba gara na kira miki shi ba ya zo har gida. Amma ƙafar taki ta yi tsamari haka ne?"
Zuwaira dama ta tambaye shi ne don ta samu ta fita daga gidan, ko ta je gidan bokan da ke can gaba da ƙauyensu ta sanar da shi ɗanyan aikin da ta aikata. Amma jin amsar Malam Hasan ya sa ta ce.
"Ƙyale dai mu gani zuwa gobe, idan ban ji daɗin jikina ba ka kira shi."
Malam Hasan bai kawo komai a ransa ba, ya sake yi mata sannu sannan ya fita. Bayan fitarsa wani sabon kukan ta dasa marar sauti, abin duniya ya haɗe mata don har ji take kamar rayuwarta ta zo ƙarshe.
Tun da ta ga an yi sallar magriba zuciyarta ta cika da tsoro, da yake Malam Hasan bai sake fita ba har sai da ya lura da firgicin da take ciki.
"Zuwaira wai akwai abin da yake damunki ne?"
A firgice ta ɗago ta girgiza masa kai, ana kiran sallar isha'i Malam Hasan ya miƙe zai tafi masallaci da sauri ta riƙo shi ta ce.
"Don Allah ka yi a gida."
Da mamaki ya dube ta ya ce, "Sallar zan yi a gida Zuwaira? Wai ko wani abu ne yake faruwa ban sani ba na ga duk kin firgice."
A wannan karon gyaɗa masa kai ta yi ta ce, "Eh wallahi tsoro nake ji, don Allah kada ka fita."
Komawa ya yi ya zauna a gefen gado ya ce, "Ikon Allah, to shi kenan bari na ɗauro alwala sai mu yi jam'in tare." Da wannan maganar Zuwaira ta gamsu, Malam Hasan ya ajiye hularsa a kan gadon ya fita ɗauro alwala. Malam Hasan yana fita kamar wacce aka dasa wa allurar da ke saka bacci, lokaci ɗaya Zuwaira ta ji idanunta suna lumshewa. Duk yadda ta so dakatar da baccin ya gagare ta, nan take ta ɓingire nannuyan bacci ya yi awon gaba da ita. Koda Malam Hasan ya shigo murmushi ya yi ya matsa gabanta, ganin bacci take hankali kwance har da munshari sai ya ƙi tashinta. Ya ce zuwa jimawa kaɗan ya tashe ta, don tun da ta samu ciki idan ta fara bacci da an tashe ta da ciwon kai take tashi. Da yake shi ma ya gaji, kwanciya ya yi da niyyar kishingiɗa sai baccin ya yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai da asuba da ya ji motsin Zuwaira ta tashi.
Da wani irin ciwon jiki Zuwaira ta wayi gari wanda ko kaɗan ba ta san dalilinsa ba, sai abin ya sake haɗe mata ga damuwar asirin boka Lado da ya faɗa kanta ga kuma ciwon jikin da ya addabe ta. Kuma ta gagara sanar da Inna domin ta san daga lokacin da Inna ta san ta fara zuwa gidan boka daga nan sun rana hanya. Saboda duk miyagun halin Inna ba ta yarda da bin malamai ko 'yan tsubbu ba. Hasali ma ko lura ta yi kana biye-biyen bokaye, daga lokacin ta kafa maka ƙahon tsana kenan duk ƙarfin alaƙar da ke tsakaninku. Ga shi Malam Hasan ya ƙi barin ta fita ko nan da can, don har ƙaryar ciwon ciki ta yi masa ya ce zai raka ta asibiti saboda faɗuwar da ta yi. Da ta ji haka har tsoro ta ji, a ranta ta raya ko dai ya fahimci halin da take ciki.
Zuwaira haka ta shafe sama da kwana goma cikin wannan yanayin, duk bayan isha'i haka nannauyan bacci yake ɗaukarta. Malam Hasan ko kaɗan bai kawo komai a ransa ba, domin a tsammaninsa ciki ne yake saka ta yawan baccin da take yi. Musammam da ya tuna marigayya mahaifiyar Fatihu a lokacin da ta yi goyon cikinsa, da yake lafiya ƙalau suka zauna da Rakiya hatta girki wani lokacin ita take yi mata ranar girkinta, musamman idan ta ga tana bacci lokacin ɗora abinci ya wuce. A kwana na sha ɗaya ne Zuwaira ta tambaye shi zuwa kitso, bai hana ta ba don haka ta ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda farinciki. Ko wanka ba ta yi ba ta zura hijabi ta fita, kai tsaye ƙauyen Marke ta nufa, gudu-gudu sauri-sauri har ta ƙarasa bukkar boka Lado. A wannan ranar mata uku ta samu ita ce cikon ta huɗu, saboda yadda ta ƙagu har ji ta yi kamar ta shiga ba tare da an zo kanta ba. Da layi ya zo kanta tana shiga ko kyakkyawar gaisuwa ba ta yi masa ba, har ta buɗe baki za ta yi magana ya ɗaga mata hannu.
"Ƙaiƙayi ya koma kan mashekiya ko?"
Tun bai gama magana ba Tani ta hau gyaɗa kai, boka Lado ya cigaba da cewa.
"Ki gode mini, ki kuma yi imani ni ne mai taimakon lamuranki da ba ki yi sati biyu cikin wannan yanayin ba." Jin ta yi shiru sai ya wara mata daƙwa-daƙwan idanunsa da suke jajir ya ce. "Ko ba ki yi imani da ni ba?"
"Na yi imani da kai boka Lado, shi ya sa ma na dawo wurinka."
Zuwaira ta furta murya tana rawa, boka Lado ya saki wata shashashar dariya wacce ta sake munana faffaɗar fuskarsa ya ce.
"Tun da kika yi imani da ni kin gama taɓewa duniya da lahira, ni kuma dama da taɓaɓɓu nake mu'amala. Tashi ki saka ƙafarki a cikin ruwan can, idan kika yi haka komai ya warware daga jikinki. Da ace kin wuce makonni biyu, da za ki dawamma ne a haka."
Da sauri Zuwaira ta miƙe ta isa gaban wani sihirtaccan ruwansa da ke cikin wata ƙatuwar jar ƙwarya. Ƙafar hagu ya ce ta fara sakawa, sai da ta tsame ta ta saka ta dama sannan ta koma ta zauna.
"Me kike so a yi wa kishiyarki? Ko kin janye buƙatarki?"
Ya wurga mata tambaya yana tsare ta da ido, furzar da iska mai zafi ta yi ta ce.
"Boka ina son a hana ta nutsuwa, a raba ta da mijinmu. Sannan hatta sana'ar da take yi a dakusar da ita, sai dai kuma don Allah..."
"Nan ya yi miki kama da wurin ambaton Allah?" Boka Lado ya katse ta a tsawace, sannan ya ɗora da cewa.
"Idan kika sake ambaton sunan Allah sai na hallaka ki."
Jiki yana rawa Zuwaira ta shiga gyaɗa kai ta ce, "Tuba nake, dama cewa zan yi kada ayi mata wanda za a ba ni ace na saka mata. Ina tsoron kada na sake samun matsala."
Boka Lado bai tanka mata ba, ya ɗauko wani ruwa mai zarni a cikin wani ƙoƙon kai. Sai ya ɗauko wata yar tsana mai ɗan girma, wacce aka rubuce jikinta da jini. Ta ƙasan 'yar tsanar ya ɗauko ƙusa ya ɓula, sannan ya ɗura fitsarin a cikin 'yar tsanar. Abin da ya fi ba wa Zuwaira mamaki, yadda duk yawan fitsarin aka ɗurewa 'yar tsanar ba tare da ko kaɗan ya zubo ƙasa ba. Miƙa mata 'yar tsanar ya yi ya ce ta duba, duk iya dube-duben da ta yi ba ta ga fitsarin ba. Tana shirin yin magana ya katse ta.
"Wannan da kike gani, tsafataccan fitsarin alade ne. Wannan 'yar tsanar da kika gani tana mazaunin kishiyarki ne, fitsarin da na ɗura mata yoyonsa za ta fara. Amma ina son ki sani, kishiyarki tana da ƙoƙarin riƙo da addini, sai dai kin san inda ta ba mu damar da za mu aiwatar da aikinmu a ƙwanciyar hankali?"
Da sauri Zuwaira ta girgiza masa kai, Boka Lado ya cigaba da cewa.
"Tana da ɗabi'ar zama kai babu ɗankwali, ba iya da rana ba har da daddare tana iya zama babu ɗankwali a kanta. Kuma idan ta zo kwanciya bacci ba ta damu da addu'a ba, mu kuma duk wani asiri mun fi gudanar da shi da dare. Ta wannan hanyar za mu yi amfani mu cimma manufarmu."
Cike da ƙeta Zuwaira ta saki dariyar mugunta tana yi masa jinjina da hannu ta ce, "Aikinka yana kyau boka Lado." Wata matacciyar jaɓa ya ɗauko a cikin leda har ta fara wari, ya ɗauko 'yar tsanar ya saka wani zaren guru ya ɗaure sannan ya miƙa wa Zuwaira. A ɗan tsorace ta ja da baya, kallon da ya yi mata ya sa ta yi saurin miƙa hannu ta karɓa. Ya nuna wata tasa da ke kan wuta tana zaɓalɓala da jini a ciki ya ce ta saka tana ambatar sunan Rakiya. Haka Zuwaira ta matsa gaban wutar ta jefa su tana ambatar sunan kamar yadda ya ce ta yi, tana jefawa ya ya saki dariya ya ce.
"Kin gama da wannan babin."
Cike da farinciki Zuwaira ta kawo kuɗi ta ba shi, sannan ta yi masa godiya. Har ta miƙe za ta tafi ya ce.
"A yau da daddare za mu gudanar da ƙarashen aikin a kanta, zuwa wayewar gari za ki ga abin da zai faru."
"Godiya nake Boka Lado, haƙiƙa na yarda da hatsabibancinka."
Daga haka Zuwaira ta fita zuciyarta fes ta wuce gida, kamar kuwa yadda Boka Lado ya ankarar da ita tana shiga ta samu Rakiya a zaune tana tsintar wake kanta babu ɗankwali. Zuwaira ta saki murmushin mugunta mai sauti har sai da Rakiya ta ɗago ta kalle ta.
ABBAN FAUWAZ
Mamaki kwance a saman fuskar Abba ya ce, "Tani kin san me kike faɗa kuwa?" Tani ta dube shi ido cikin ido ta ce.
"Ƙwarai kuwa na sani, takardar saki na ce ka rubuta mini don ba zan iya cigaba da zama da matsiyaci ba."
Matsawa gabanta ya yi, ya kamo hannunta ya shafa ya ce.
"Tani kina ji na?"
Da zafin nama ta fisge hannunta, cike da rashin mutumci ta ce.
"Malam ka kama kanka! Ko kuma takaucin ya fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ne?" A fusace Abba ya ce, "Wai Tani kin san me kike faɗa? Ni mijinki kike faɗa wa haka?"
"Wane ne mijin? Mijin irinka mijin banza da wofi, ƙasƙantacce matsiyaci..."
Tass! Abba ya sakar mata mari a fuska, da sauri Tani ta riƙe kumatunta tana bin sa da kallo. A madadin ta ji zafin abin da ya yi mata sai ta saki murmushi ta ce.
"Tun kafin yau na shirya jin marinka a fuskata, don kaine a makare. Abin da ba ka sani ba, tun ranar da na shigo gidanka nake shiri da tanadin abubuwa a kanka. Ruwanka ne ka nemi mafita, ruwanka ne ka tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi maka ƙafa." Daga haka Tani ta koma cikin ɗaki ta haye gado cike da rashin mutumci. Saboda mamakin kalaman Tani da ƙyar Abba ya iya jan ƙafarsa ya fita daga gidan, sai dai har ya isa kotun jikinsa a mace yake ga tarun damuwa da tashin hankali da suka zame masa abokan shawara.
A wannan ranar da suka fara zaman shari'a aka gabatarwa da Abba tuhumar da ake ƙararsa a kanta, nan take ya amince da ƙunshin tuhumar. Bayan tattaunawa alƙalin ya cewa Abba da ya yi ƙoƙarin nema wa Alhah Dikko haƙƙinsa kafin wani zaman. Da haka zaman kotun ya watse, daga kotun Abba ya wuce gidan 'yar uwarsa Goggo. Kallo ɗaya ta yi masa ta ga duk ya sake fita hayyacinsa, sai da suka gaisa sannan ya sanar mata da abin da ya faru tsakaninsa da Tani. Murmushin takaici ta saki ta ce.
"Yanzu ka ga maganar yaron nan tana hanya? Ka ga abin da Fauwaz yake son ankarar da kai, ka rufe ido kake ƙyamarsa."
Shiru Abba ya yi, sai zuwa can ya ɗago cikin damuwa ya ce.
"Wallahi tallahi ban taɓa tsammanin Tani za ta yi mini haka ba, Tani ta shammace ni ta ci amanata."
Ya ƙarasa maganar kamar zai zubar da ƙwalla, Goggo ta jima tana ba shi baki sannan ya yi mata sallama. Da ɗan canjin da Goggo ta ba shi, ya tsaya ya sayi naman miya da zummar idan ya kai gida ko zai shawo kan Tani. Sai dai yana zuwa ya buɗe ƙofar ya ga gidan wayam, a haukace ya dinga duba ɗakunan yana kiran sunan Tani sai dai gabaɗaya kayan sawarta ya ga babu ta kwashe su. Daga kan Tv ya hangi wata farar takarda guda biyu, jikinsa yana rawa ya saka hannu ya ɗauka ya fara karantawa.
_Har yanzu na san zuciyarka tana cike da wasu-wasi a kan kalaman da na furta maka, ina son ka sani. Ni Tani dama ina tare da kai ne domin biyan buƙatar kaina, a yanzu kuma na cimma manufa ta dole na wurgar da ƙwallon mangoro na huta da ƙuda. Ina tunasar da kai da ka sani, Tanin da ka sani a shekarun baya, ita ce dai wacce ka yi rayuwar aure da ita a yanzu. Girma da shekaru ba su isa su sauya Tani ba, idan Tani ta ce sai ta yi duk daren daɗewa sai ta zartar da shi. Zan sake sanar da kai, wallahi tallahi ko kana so ko ba ka so dole ka sake ni. Ka saurari haɗuwar da za mu yi a gaba._
Abba yana gama maganar ya ji gumi ya shiga keto masa, ɗayar takardar da ke gefe ya ɗauka sai dai tun kafin ya buɗe ta ya ga a ido ta fi wacce