GAMMON RAMA BOOK COMPELET AMEERA ADAM

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 33.6K words

ya gama karantawa tsufa. Yana buɗe ta bayan ya ƙura mata ido ya ji gabansa ya yi mummunan bugawa, zanen rubutun da aka yi da baƙin biron da ke jikin takardar ya tuna masa da tarun al'amauran da suka faru a shekaru goma sha bakwai da suka wuce. Da sauri ya wurgar da takardar, sai ya ji tamkar ya riƙe ruwan dalma a hannunsa. Ya kifa kansa a sama cinyarsa yana faɗin.

"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!"

Shiru ya yi yana jin zuciyarsa tana yi masa raɗaɗi, raɗaɗin da ya gagara tantance a mahallin da zai ajiye shi. Musammam da ya tuna shukar tsiyar da noma wa Tani a shekarun baya.


Gobe za mu gama free pages ɗinmu🥳 jama'a yanzu ne za a fara naɗa GAMMON RAMA, kowa yasan za a sha tsami a cikinsa. Akwai tarin ƙalubale da darussan hannunka mai sanda, kada ku yi sanya domin yanzu ne za a fara wasan.👌🏻

500 ne ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan ya kammala zuwa document 800 ne.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[20/05, 16:30] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA GOMA

Abba ya jima a zaune cikin rashin daɗin yanayi, jikinsa a sanyaye ya miƙe ya shiga ɗakin su Fauwaz. Tsaye ya yi yana ƙarewa ɗakin kallo, abubuwa da dama suka shiga dawowa cikin kwanyarsa ciki har da mutuwar Abida. Sai a lokacin yake tuna irin kalaman da Tani take yi masa a kan 'ya'yansa, da irin shakulatan ɓangaro da ya yi a game da amanar da mahaifiyarsu ta ba shi kafin ta bar duniya.

"Kaico Abidata, Allah Ya sabunta rahama a gare ki da mahaifiyarki."

Ya furta a sanyaye, sai kuma Fauwaz ya faɗo masa, cikin nadama da danasani ya ce.
"Yanzu ɗan cikina ne a almajiranci? Shin me ya faru da ni a wancan lokacin da na gagara gane gaskiyar da yaron nan yake son nusar da ni?"
Amsar da ya gagara ba wa kansa kenan, shi kaɗai ya shiga surutan nadama a kan cuzgunawa su Fauwaz da suka dinga yi a baya shi da Tani.

"Ya zama wajibi na je na dawo da shi gabana."

Ya furta a sanyaye, sai kuma wani tunani ya faɗo masa don haka y furzar da iska mai zafi ya ce.
"A ina zan samu kuɗin mota?"

Saboda a wannan a gaɓar da yake hatta naira ɗari ta kansa wuya take yi masa, ganin rubuta wasiƙar jakin da yake yi ba za ta kai shi ba. Sai ya miƙe ya fito, ya shiga ɗakin kwanansu. A nan ma ɗakin ya shiga bi da kallo ganin Tani ta yashe komai nata, hularsa da ke yashe a ƙasa ya ɗauka ya saka. Tunanin zuwa gidan kawun Tani ne ya faɗo masa, don haka cike da ƙwarin gwiwa ya rufe gidan ya nufi shagon Nalami da ke bayan gidansa.

Nalami yana ganinsa ya haɗe rai, Abba ya saki murmushi don ya san dalilinsa na sauya fuska.
'Tabbas rayuwa darasi ce, sautari idan kana da shi mutane kowa ƙaunarka yake. Amma da zarar wata jarrabawa ta afka maka a nan ne za ka fahimci wanda zai mu'amalance ka tsakani da Allah.'
Abba ya raya a ransa, sannan ya yi sallama a shagon. A ɗan daƙile Nalami ya ce.
"Wa alaikassalam."
Abba ya ɗan yi jim sannan ya ce. "Don Allah Nalami kada a gaji da ni, yanzu ma aron ɗari biyu za ka ba ni, idan aka haɗa da waɗancan sun kama dubu ɗaya." Kamar Nalami yana jira ya yi zaraf ya ce, "A gaskiya Alhaji ba za ta samu ba, waɗancan ma yanzu nake shirin aika maka kuma sai ga ka."
Nalami ya ƙarasa kalamansa yana ƙara tsuke fuska.

"Alhaji kana da canjin ɗari takwas fa."

"Alhaji ka biyo ni ɗari biyar jiya."

"Kullum dai Alhaji ba ka gajiya, to an gode Allah amfana."

"Gaskiya ne Alhaji, ni fa duk unguwar nan na fi jin daɗin cinikinka, saboda ko babu komai mutum zai ƙaru da 'yan canji."

Abba ya tuna ire-iren kalaman Nalami a baya, a lokacin da kuɗi yake gara masa idan ya zo sayayya wurinsa. Don a wancan lokacin canji indai ba mai yawa sosai ba ne bar wa masu shago yake, musamman Nalami da ya fi kusa da gidansa. Amma shi ne a kan dubu ɗaya Nalami yake ɗaure wa fuska har yana nuna masa iyakarsa.

'Marar shi ba ya zuciya.'

Abba ya sake raya wa a ransa, don haka ya ce.
"Don Allah ka taimaka mini Nalami, zan yi ƙoƙari na haɗa maka kuɗin cikin ƙanƙanin lokaci."

"A gaskiya wannan ne na ƙarshe indai ba ka kawo wani abin ba na gama ba ka rancen kuɗi."
Nalami ya furta sannan ya zaro ɗari biyu ya miƙa masa a wulaƙance, idanun Abba ne suka ciko da ƙwalla. Ganin a kan ɗari biyu ana ƙoƙarin cin zarafinsa, ɗari biyun da yake ganin ba komai ba ce a wurinsa. Karɓa ya yi ya masa godiya ya tafi, a wancan lokacin da yake kuɗi suna da daraja. Ɗan achaɓa ya tara ya nufi unguwar Sheka gidan Kawun Tani.

A lokacin da ya ƙarasa Dattijon yana zaune a kan bencinsa ƙofar gida, cikin girmamawa Abba ya russuna ya ce.
"Barka da yamma Baba."
Faɗaɗa fara'arsa Dattijon ya yi ya ce, "Barka dai, au Lawan ne da yammacin nan?"
Abba ya ɗan sosa kai ya ce, "Eh ni ne Baba, ya mutanen gidan?"
Baba ya nuna masa tabarmar da ke gefen bencin ya ce, "Ga wuri ka zauna mana, ya su Tani?"

Abba har ya miƙe domin ya je ya zauna, sai ya ji gwiwarsa ta yi sanyi da tambayar da Baba ya yi masa. A saɓule ya zauna ya yi shiru ya faɗa tunanin wurin da Tani ta tafi, har sau biyu Baba ya yi masa magana bai ji ba. Sai da ya taɓa shi bayan Abba ya amsa Baba ya ce, "Lawan ko wani abu ne ya haɗa ka da Tani? Ina fatan dai lafiya ko?"

Abba ya shafo gemunsa ya ce, "Eh to gaskiya ba lafiya ba Baba..." Duk abin da ya faru Abba ya kwashe ya ba wa Baba labari, sannan ya ɗora da cewa.
"Shi ya sa na ce bari na zo nan, don na san duk garin nan babu wanda take da shi sama da kai. Da har zan je gidan abokin mahaifinta, sai na ga nan ne ya dace na zo tun da ka fi kusanci da ita." Gyaran murya Baba ya yi ya ce.

"Eh kam tabbas haka ne, ni na fi kusanci da ita a kan Alhaji Harisu, tun da a lokacin da muka yi zaman Shagamu da mahaifinta Alhaji Harisu bai zo garin ba sai dab da mahaifinta zai rasu. Ni da shi bacci ne yake raba mu amininsa ne ƙud da ƙud."
Da ɗam rashin fahimta Abba ya ce, "Baba kana nufin kai ba yayan mahaifinta ba ne?"

"Yayan mahaifinta? Ita Tanin ce ta ce ni ne yayan mahaifinta?"
Baba ya furta da sauri, Abba ya gyaɗa kai ya ce.
"Eh haka ta ce mini bayan haɗuwarmu, shi kuma Alhaji Harisu abokin mahaifinta."

"Tirƙashi! Lallai yarinyar nan makira ce, ashe haka ta iya yaudara? To wallahi yaro babu abin da na haɗa na jini da Tani, ni ban san ma yadda aka yi ta lalubo gidana ba. Ta zo da kukanta wai aurenta ya mutu ba ta da wurin zama, ganin irin zaman mutumcin da muka yi da mahaifinta ya sa na ba ta ɗaki. A lokacin har zance ta tafi dangin mahaifinta ko mahaifiyarta, to sai na ga kamar ba za ta ji daɗi ba tun da ta san da can ɗin ta taho wurina." Baba ya ƙarasa maganar yana sakin ƙwafa, sannan ya ɗora da cewa.

"Ni ban san lokacin da Tani ta lalace haka ba, kodayake tun haɗuwarta da wani ɗan iskan yaro a shekarun baya duk ya lalatata. Allah dai ya kwashe masa albarka, duk ya gurɓata tunanin yarinyar nan."

Shi dai Abba zuru ya yi kamar an jiƙa ɓera a buta, haka kawai jikinsa yake ba shi kamar shi ake kwashe wa albarka yana zaune.
"To yanzu Baba a ina kake ganin zan iya ganinta?"
Abba ya tambaye shi cike da damuwa, cikin sauri Baba ya wara hannuwa ya ce. "Allah masani Lawan, don wallahi ba na ce ba. Ka leƙa gidan Alhaji Harisu ƙila ko can ta nufa, ni kuwa dama ta gama zaman gidana don ba za ta haɗa mini masifa da kafirar ƙaryarta ina zaune ƙalau ba." A sanyaye Abba ya miƙe har zai saka takalminsa ya ɗan sunkuyo ya ce.
"Amma Baba ya sunan yaron da ka ce ya cuce ta ya gurɓata mata tunani..."

"Kai da ka zo neman matarka ina ruwanka da wani ƙato?"

Baba ya katse shi a fusace sannan ya ɗora da cewa, "Wai me ya sa wasu mazan sun cika kishin masifa ne? Idan na faɗa maka sunan me za ka yi da shi bayan wannan zancan da nake yi maka ya doshi shekara goma sha biyar zuwa sama." Da sauri Abba ya zura takalminsa ya yi wa Baba sallama, don ya lura tun da ya faɗi ƙaryar da Tani ta yi masa ya hassala.

Kai tsaye gidan Alhaji Harisu ya nufa, a lokacin har an fara kiran sallar Magriba. Sai da ya yi sallah sannan ya same shi ya sanar da shi abin da yake tafe da shi, sai dai shi kansa a nan ya tabbatar masa da Tani ba ta gidansa. Kuma ya ɗauki lokaci mai tsayi bai saka ta a idonsa ba. A saluɓe Abba ya baro gidan, ya shiga tunanin inda zai ga Tani saboda akwai muhimmiyar tattaunawar da yake son su yi.
Lokacin da ya ƙarasa gida gani ya yi gidan ya zame masa kamar kango, saboda yadda damuwa ta cunkushe shi ko abincin da ya sayo ya kasa ci. Daga kan gado ya hango wata farar takardar, nan take gabansa ya faɗi. Domin a yanzu farar takarda ta fi komai ɗaga masa hankali, kamar wanda za a kama haka Abba ya miƙa hannu a hankali ya ɗauko takardar. Sai ya ga wani rubutun Tani ta ajiye masa.

_Daga lokacin da ka karanta waccan wasiƙar, na tabbata zuciyarka a ɗokance take da san sanin wurin da nake rayuwa. Sai dai ka sani, za ka yi ta bulayi bara a kufai ne har zuwa lokacin da zan bayyana maka kaina. Kada ka ɗauka wannan takardar a tare da waccan na ajiye maka, a'a, na ajiye maka ita ne ɗazu bayan ka tafi gidan Baba nemana. Na barka lafiya._

Abba ya karanta wasiƙar babu adadi tamkar yana son gano wurin da Tani take a cikin takardar, a nan ya cigaba da zama har bacci ya yi awon gaba da shi.

Daga wannan ranar sai rayuwa ta sake juye masa, al'amuransa suka cigaba da dagulewa. Duk shagunan da yake karɓar bashin kaya sun daina ba shi. Abokan kasuwansa kuwa tuni suka janye jikinsu daga gare shi, idan ya ce su ba shi aron kaya ya kasa ko zai ɗora na shi fir suke hanawa. A haka suka cigaba da zaman shari'a wani lokacin ma sai dai ya tafi kotun a ƙafa, wani zubin kuma ya nemi alfarmar a rage masa hanya a wurin masu ababen hawa.
Sannu a hankali kwanaki suka cigaba da shuɗewa har aka kammala shari'ar su Abba, daga ƙarshe da ba a samu komai daga gare shi ba alƙali ya aika shi zaman gidan yari na shekara takwas babu zaɓin tara. Sakamakon an bi duk wasu ƙa'idojin da suka dace amma bai cika su ba, na farko an ce ya dinga biyan wani kaso lokaci-lokaci ya ce ba shi da hali. Alƙali ya ce ya sayar da wata kadararsa, ko a yi ƙiyasun kuɗinta ya mallaka wa mai fili ita. Amma gabaɗaya Abba ya nuna gazawarsa, Alhaji Dikko da Alhajin da ya sayi fili a wurin Abba suka lamunce da a tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari don ya yi musu zaman kuɗinsu. Don haka aka ingiza ƙeyar Abba da wasu tsirarun matasa, waɗanda su kuma aka same su da laifin fashi da makami.
Babban abin da ya fi tsaye wa a zuciyar Abba shi ne Fauwaz, saboda a cikin kwanakin ya sha yin mafarkinsa cikin mummunan yanayi. Don haka yake ta neman yadda za a yi ya samu kuɗin motar da zai je ya ɗauko shi, sai dai haƙarsa ba ta cimma ruwa ba har aka kai shi gidan yari. Don haka ya sa a zuciyarsa duk ranar da Goggo ta kawo masa ziyara, zai ba ta adireshin garin da Fauwaz yake da sunan makarantar allon da ya kai shi.

Ranar wata Alhamis ita ce ranar da aka kai Abba gidan yari, a ranar Asabar ɗin da ta zo yana zaune jigum cike da damuwa. Domin har da ya kwana biyu a gidan ya gagara sakin jikinsa yadda ya kamata, musamman da yake jin sa a takure da zaman wuri ɗaya. Mamaki abin yake ba shi da ya ga wasu sun sake kamar a gidajensu suke, ganin ana ta zuwa ziyarar mutane sai ya ji ina ma zai samu wannan gatan.

'Yanzu a duk duniya wa kake tsammanin zai kawo maka ziyara? Ko don wannan ai ka ga ranar Fauwaz.'
Zuciyar Abba ta raya masa, bai yi tsammani ba ya ji hawaye ya ziraro masa. Sai kuma ya tuna da Goggo, ya san duk duniya Goggo yake da ita shaƙiƙiyar 'yar'uwa, kuma a yadda take ji da shi ya san za ta samu lokaci ta shigo masa.
Yana cikin wannan yanayin wani ma'aikaci ya leƙo ɗakinsu ya ce, "Lawan Shu'aibu 2442."
Da sauri Abba ya ɗago ya ce, "Ga ni."

"Ka zo kana da baƙuwa."
Ganduriban ya furta, wani irin sanyin farinciki ne ya lulluɓe shi. Jikinsa yana rawa ya bi bayansa, suna zuwa Abba ya yi turus sakamakon ganin wacca ya yi tozali da ita. Saboda tsananin mamaki har sai da ya murza idanunsa don ya tabbatar ba mafarki yake yi ba.

GIDAN MALAM HASAN

Suna haɗa ido Zuwaira ta yi tafi cike da izgilanci ta fara waƙoƙin habaici, Rakiya ba ta kula ta ba ta cigaba da tsintar wakenta. Saboda yadda Zuwaira take jin ɗokin ganin abin da zai faru har alla-alla take dare ya yi, ita kuwa Rakiya da ba ta san wainar da ake toyawa ba ta cigaba da sabgoginta zuciyarta fes cikin kwanciyar hankali.

A daren ranar dama Malam Hasan a ɗakinta yake, tun bayan magriba ta yi kwalliyarta cikin riga da zani. Sai da aka yi sallar Isha'i sannan Malam Hasan ya shiga, da yake yawancin sai ya yi sallah yake shiga gida gabaɗaya. Sai da ya fara shiga ɗakin Zuwaira ya duba lafiyarta, da yake haka ƙa'idarsa take. Idan ba ya ɗakin mace to kafin ya shiga ɗakin mai kwana sai ya fara shiga ya duba lafiyarta sun ɗan taɓa hira ko ta minti biyar ce. Haka idan gari ya waye kafin ya fita sai ya leƙa ya ga yadda kika tashi.
Tun da ya shiga ya lura da annurin da ke saman fuskar Zuwaira, har sai da ya gagara haƙuri ya ce.

"Hala akwai wani albishir da kika ƙunshe mini a bakinki?"

Kamar Zuwaira tana jira ta yi zaraf ta ce, "Ni kuwa nake da albishir Yaya."
Murmushi ya saki ya ce, "Ina jin ki."

"A'a gaskiya, sai Allah Ya kaimu zan sanar da kai tun da na tabbata shi ne babban albishir ɗin da za ka fara cin karo da shi."
Zuwaira ta furta tana yin far da ido cike da kissa da jin daɗin ganin Malam Hasan ya sake mata yadda take so. Miƙewa ya yi ya ce, "To bari na wuce tun da ba za ki sanar da ni ba."
Wani abu Zuwaira ta tuna ta yi saurin cewa, "Mafarki na yi fa wai na haifi tagwaye duka maza."
Da sauri ta ga ya faɗaɗa fara'arsa ya ce.
"Allah Ya tabbatar mana da alheri, ko ɗaya Ubangiji Ya ba mu masu albarka muna so." Nan take ta haɗe fuska ta ce, "Sai ka ce Allah Ya tabbatar mana ai, ko tagwayen ne ba ka so? Ko kuma don ba matar so ce da cikin ba?"

"Zuwaira kina da matsala wallahi! Mene ne laifi a addu'ata? Ko kuwa kawai za mu ce Allah Ya tabbatar ko da ba mai albarka ba ne?"
Shiru ta yi ta zumɓuri baki gaba, sai ta ga ya miƙe zai fita. Tunowa da al'amarin da zai faru da Rakiya ya sa dariya ta suɓuce mata sannan ta ce. "To sai da safe mu kwana lafiya."
Mamaki ne ya kama Malam Hasan, don kusan tun da ya auro Zuwaira zai iya lissafa sau nawa ta yi masa sai da safe cikin tattausan lafazi, idan ba a ɗakinta yake da kwana ba. Amsa mata ya yi sannan ya fice ya nufi ɗakin Rakiya.

Da sallama ya shiga ɗakinta, ya hango ta zaune a kan tabarma ta sha kwaliyya sai ƙamshi take yi. Hannuwa ya buɗe mata, tana daga zaune ta ɗan tura baki gaba tana ɗauke kanta gefe. Ya lura neman kaɗan take yi 'yan kishin su motsa, don haka ya kama kunnuwansa da hannuwansa ya ce.
"Kaina bisa wuyana."

"Ka koma can na yafe kwanan."
Rakiya ta furta a shagwaɓe, waro ido waje ya yi cike da tsokana ya ce.
"Idan kika sallama ni ina zan saka kaina? Ki yi wa Allah ki taimaki marayan Allah."

Murmushi ta saki cikin zolaya ta ce, "Ai kana sani kake son yi wa marainiyar Allah riƙon sakainar kashi, kai da ga Inna nan a ina za ka kira kanka da maraya."
Ƙarasawa ya yi ya zauna a kusa da ita, ya janyo ta jikinsa ya zuba mata ido cike da so ya ce.
"Wai yaushe kika iya surutu haka?"

Ta saka hannu ta riƙo fuskarsa kusa da tashi, har

11 / 12