UWAR AGOLA COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AFRAH.txt

Author :  Maman Afrah Category :  Tknovels

Chapter   9 / 15

24K to 27K   out of 44.2K words

ce

"Ai ba zan jure ba, tahowa zan yi in tsaya ta windown gidanmu in hango ka, ka ga na yi kwalli kenan" Malam Nura wata wahalalliyar ajiyar zuciya ya sauke, jin wata lukutar masifar.

Bai gama tunani ba da ya ji ta sake cewa

"Dan Allah idan kun zo wucewa ka ɗago min hannu" Cike da ƙoƙarin danne damuwarsa ya amsa mata, amma a ransa yana raya cewa ba zai taɓa yin abin da ta ce ɗin ba saboda kar ta je ta ganshi komai ya caɓe.

Yana shirin datse kiran ta ce

"Ni yau duk kishin ka ma nake ba na so ake gani min kai, domin ko matanja ba don matanka ba ne da basu fara gane min kwalliyar ɗaurin aurena da kai ba" Dariya ya yi amma a zahiri ta ji sautin a baɗini kuwa dariyar yaƙe ce ya ce

"Daman na yaga buhu na rufa a kaina yadda babu kowacce mace za ta gane miki ni, ko wajen ɗaurin auren sai na je da buhun rufe a kina" Dariya take sosai ta katse wayar bayan ta faɗa masa tana jiran wulgawarsa.


Tana katse wayar ya kalli Hudu bayan ya sanya hannu ya goge gumi, ya ciro hularsa ya shiga fifitawa a kansa da shi ma tuni ya jiƙe da gumin yana ƙasa da murya ya ce


"Hudu ina cikin talatainin masifa, Kuluwa ta cuceni, yanzu ga Hadiza can a windon gidansu in za mu wuce in ɗago mata hannu ta ga kwalliyata" Hudu ya bushe da dariya ganin gabaɗaya jama,ar fa suka taho tare kowa sabgar gabansa yake ya ce

"To mene ne abin tashin hankalin sai ka ɗaga mata hannun ai" Harara ya aikawa Hudu bai sake cewa komai ba, har suka kusa shiga layin gidan su Hadiza gaban Malam Nura yana dakan lugude.

Tun da aka shiga layin ya kutsa tsakiyar mutanen da suke tafiya, ya dunƙufar da kansa yake kallon ƙasa, Hudu ne yake faɗa masa cewar ya hango ta tana leƙowa daga windown, suna zuwa Malam Nura ya nannaɗe hannun rigar jikinsa sai da ya kai wajen kafaɗa yadda ba za a hango kalar yadin jikinsa ba, yana ɗan sunkuyawa kamar mai ƙusumbi ya shiga ɗaga hannu saitin ƙofar gidan nasu, don shi dai kawai ɗaga hannu yake yana bye-bye yi yake babu ƙaƙƙautawa.

Hadiza wacce ta kira ƙawayenta guda biyu take shirga musu ƙaryar kuɗin shaddar da Malam Nura ya ɗinka musu ita da shi da yaranta, don dai da ta linka kuɗin ta faɗa musu, su kuma suka yarda suna fasa mata kai a kan cewar lallai ta tsinci dami a kala tun da dai gashi har ƴaƴanta ya yi ws kayan fitar biki ba su san cewar dai da aka kai ruwa rana ba ya ɗinka.

Tsaye suke sun zubawa hanyar ido har dai suka fara jiyo tashin kiɗa, Hadiza ta ji kanta ya fashe, ƙawayenta suka ci gaba da wasa ta, musamman da suka ga mutane sun shawo kwanar sai kiɗa ake ana wasa ango, kowa ya gyara tsayuwa don ganin angon Hadiza don ta ce musu ya fi tsohon mijinta komai, gashi da kuɗi kuma ba ya jin ciwon fitar da kuɗi, hakan ya sa suka sake ganin girmanta.

Tun da suka hango mazan suka zuba na mujiya, kasancewar ma su mazan da suka taho tawagar angon daga can tsallaken hanyar suke ba daga saitin inda gidan su Hadizar yake ba, wato daga tsallen dama suke tafiya, gidan su Hadiza daga ɓangaren hagun.


Ɗaya daga cikinsu har ɗaɗɗage take tana son hango angon, Hadiza tana hararta tana cewa za ta gane mata ango. Amma maimakon ango ya fito fili a ganshi tamkar wata ɗan daren goma sha huɗu, sai ya ɓace a cikin mutane tamkar kifin da ya nutse a ruwa, hannunsa kawai ake hangowa, a haka yake tafiya a dudduƙe tsoronsa ɗaya ma kar ya yi tuntuɓe ya je ya faɗi a shiga uku don idan ya faɗi ya san dole Hadiza ta ganshi don daga ya faɗi za a fara cewa ango ya faɗi dole a ganshi kuwa. Hudu ztsabar dariya har da hawaye, mutane kuwa babu wanda ya lura da abin da yake faruwa.


Ƙawayen Hadiza ne suka ce


"Kin ce mu zo mu ga ango zai ɗago hannu, amma mu babu wani ango da muka gani bare mu ga kwalliyarsa, kawai iya wancan hannun da ake ɗago daga cikin jama,a tamkar shamuwa tana ɗaga fiffike shi kaɗai muke gani"

Ɗayar ta ce


"Ni hannun ma kamar wanda ya ji uwar wuya, duk kawai kamar dai ana rauda hannun ne ba wai ana ɗagoshi ba"


Ɗayar ta ce

"Ni fa yadda ta ce ya saka shadda irin tata kawai zatona zan hango haɗaɗɗan hannu ake hango shadda a jikin hannun, amma wannan babu abin da ake gani na shaddar fa, kawai sangalalin hannun ne ake gani tamkar wanda singileti ce sanye a jikin mai ɗago hannnun babu kaya" Ran Hadiza ne ya ɓaci da tsiyar da suke mata ta fara tunanin ko dai sun ɗauka ma ƙarya take bai ɗinka musu tare da ganin hakan ya sa a zuciye ta ce


"Wallahi duk cikin ku kun san na fi ƙarfin in muku ƙarya, idan har ba shi ya saya mana ba babu dalilin da zan sa in ce shi ya saya, kuma har shi ya siyo ya ɗinka, amma tun da har kuka musa bari na kira shi ya fito gefe guda daga cikin ayar mutanen, ku hango shi" Ta faɗa tana doka masa waya.

Malam Nura da ya kusa tsallake rijiya da baya wato gani yake an kusa wuce saitin gidan su Hadiza ya huta da wannan jarabar ta ɗaga hannu, ya san dai idan an je an ɗaura aure in ta ganshi kowacce jaraba za ta yi sai dai ta yi tun da an ɗaura. Amma me yana cikin wannan halin wayarsa ta fara neman ɗauki, saboda tsoron abin da zia biyo baya ƙin ɗagawa ya yi da ya ga sunan Hadiza hannunsa ne kawai yake karkarwa domin hatta hularsa da ya cire yakw riƙe da ita a ɗaya hannun neman suɓucewa take amma har lokacin bai daina ɗaga hannun ba.

Hudu ne ya kalle shi ya ce

"Dan Allah ka daina ɗaga hannun nan, kamar wani mai ɗaga tutar nigeri,a"


Malam Nura ya ce

"Wallahi wanda yake ɗaga tutar ma ya fini ƴanci nidai wanna aure na Hadiza ya wahalar da ni" Hudu ko tausaya masa bai yi ba ya shiga masa dariya don shi kaɗai ya san waye abokinsa da irin tsiyar da ya shuka, ya san yanzu kawai abin da ya shuka ne bai ma fara girba ba.


Ran Hadiza ne ya ɓaci ganin ɗaga daga cikin ƙawayen nata ta yi tsaki ta ce


"Ƙaryar banza" Tana faɗar hakan ta tafi, ɗagar ta tsaya tana mata dariya, Hadiza tana kallon aminiyar tata ta ce

"Kema Bintu baki yarda da ni ba?" Bintu tana dariya ta ce.


"Ina fa zan yarda sai na ganshi ido da ido, wannan mazan na yanzu masu shegen son kuɗin tsiya har zai tsaya kashe miki kuɗi a kayan fitar biki ke da shi da ƴaƴan da ba ma nashi ba, bayan kuɗin da kika ce ya baki" Ƙwafa Hadiza ta yi ta bar wajen cike da haushin Malam Nura da bai ɗauki waya ba, tana saƙawa a ranta cewar zai zo ya same ta.

Sai da ya ga sun gota wajen yadda ba za a iya gane shi ba tun da sun ɗan yi nisa ya ɗago yana sauke nannauyar ajiyar zuciya ya ce

."Haba ina dalili gabaɗaya wuyana ya ƙage a sunkuyon nan, hannuna ma da nake ɗagawa haka" Ya faɗa yana mayar da hularsa ya ɗora a kansa ya danna ta sai kuwa ya zama kamar wani maroƙi!.


A haka suka ƙarasa wajen da aka tanada don ɗaura auren, Malam Nura yana ta sauke ajiyar zuciya, ana ta kaɗe-kaɗe har dai aka saurara aka yi abin da aka taru dominsa, wato aka ƙulla aure tsakanin Hadiza da Malam Nura!. Maroƙa suna ta cewa
...."Aure ya ɗauru, Allah bada zaman lafiya"


Malam Nura ya ce


"Hudu babu pure water a nan wajen ne?" Ya faɗa yana waige-waige.

Hudu ya ce


"Mai za ka yi da pure water?"


Malam ya ce


"A ƙasa zan zuba in tsotse, wallahi ƙirjina tun da na fito daga gida kamar ana bubbuga kalangu, har sai yanzu da auren nan ya ɗauru duk da har yanzu ina jin tamkar mafarki ne" Tsaki Hudu ya yi ya shiga gaisawa da jama,ar da suke musu Allah sanya alkairi, bakin Malam Nura har kunne yana ta washe bakin murna.

Ana ta raba alewa da goro, sai hotuna ake ɗauka tsakanin abokan ango da ango, Malam Nura duk lokacin da aka ƙyalla hoton sai yake tuno haɗuwarsa da Hadiza maganar hoton nan amma idan ya tuna cewa an ɗaura auren sai ya ji da dama-dama wai kibiya a ido!.


Wani saurayi da yake maƙotan su Hadiza wanda ya ji Hadiza tana faɗawa mai hoton da ta kirawo cewar zai musu hoto na kata,i, wanda zai ɗauki hankali a wanko musu na bango za ta liƙa a ɗaki, shi ma angon hakan, har rana cewa ita da shi tamkar an biyun sarari suke kayan nasu iri ɗaya ne, ana ta fasa mata kai, ganin Malam Nura da wani shegen yadi wanda yake tsohon yayi ne an jima da gama yayinsa, ga wata uwar hula da ya kifa sai wani uban maiƙon mai yake ga wani gumi yana kwaranyo masa, da sauri ya saita wayarsa ya ƙyalla hoto guda biyu, wato ya ɗauki Malam Nura gabaɗaya biyun kuwa yana dariya haƙoran nan a waje tamkar an bashi kyautar kujerar makka, duk da shi a wajensa Hadiza babbar kyauta ce .


Yana gama hoton ya saka wayar a aljihunsa ya hau mashin ɗinsa ya bar wajen taron ya nufi gidan su Hadiza. Yana zuwa ya faka mashin ɗina a waje har neman tuntuɓe yake saboda tsabar gulma.


Yana shiga da ƙaran guɗar mata kunnuwansa suka fara cin karo, ana ta murnar an ɗaura aure. Kiran Hadiza ya yi gefe tana ta washe baki tana wani farfari da iyayi tana zuwa ya ce


"Wai Hadiza ba Malam Nura ne kika aura ba, mijin Haule da Kuluwa?" Harara ta dalla masa ta ɓata rai ta ce

"Ba na son gulma da rainin wayo, ni ina ruwana da matansa da zan ɓatawa kaina lokacin wajen sanin sunansa, na san dai Malam Nura sunansa, kuma mijin Hadiza don ni yanzu kaina kawai na sani, ba ruwana da kowacce shegiya ta yi ta kanta su shiryawa zuwana gidan!"


Yana mata hararar wasa ya ce


"Bakya cin ribar zance, ni fa kawai so nake na tabbatar don ni dai na ga shi ake ta tayawa murna a wajen ɗaurin auren, kuma na san shi kika ce za ki aura"


Tana zare ido ta ce.

",To uban mai kake son sani, eyeh masu zuwa lahira da ƙoƙon masaki, ku fa ko kashi mutum yake idan ya ganku ya tashi"


Ganin tana neman ja masa lokaci ya ciro wayarsa daga aljihu ya kamo hoton Malam Nura ya miƙa mata wayar, tana karɓa ta sauke idanunta a kan Malam Nura da ya hangame baki yana dariya, hular nan tasa da ta masa wani iri tamkar tashi da ƙwawa ta mayar da shi kamar wani tsoho, yadin jikinsa ta kalla gaba ɗaya a ɗaya hoton ma mazan da aka ɗauke su tare ne suka cinye hoton shi yadda idanunta suka nuna mata ma duk a firgice yake, can ta sauke idanunta a inda ya tattare hannunsa lokacin da zai ɗaga mata hannu, kasancewar a firgice take da ya gyara hannun ma bai gama gyaruwa ba ya bar shi a hakan, shi kuma Hudu bai lura ba bare ya sanar da shi.


Wani uban ashar ta ɗura ta ce

"Sallamanu kuma an ɗaura auren? Ka tabbatar an ɗaura mana auren da shi????"



*A page 10 zan gama free pages, wanda yake so zai iya saya mu ƙarasa har ƙarshe, wanda bashi da ra,ayi babu dole kar ma ki zo ki min ƙananun maganganu ba ɗauka zan yi ba a toh*


MAMAN AFRAH
09025576222
[4/13, 6:37 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t



*UWAR AGOLA*

🅿️8️⃣

KINA BUKATAR INGANTATTUN SKIN CARE PRODUCTS TO KIZO SH SKIN COLLECTION DOMIN TA SHIRYA TSAF DAN MAGANCE MK MATSALAR FATARKI YAR UWA
KURAJENE DAKE A A GLASS NE Y BATA MK FUSKA KIKA RASA YADDA ZAKIYI KO KUMA DAI TABO NE YAYI MK DANBARE DANBARE A FUSKA TO ZO NA BAKI SIRRIN MATSALARKI
WANI ABUN SHA AWA MA ITA FA SH SKIN COLLECTION BATA DAUKAR MAI TA BAKI KAI TSAYE BA TARE D TAGA KALAR FATARKI BA SBD SANIN MAKAMAR AIKI

ZAKU IYA TUNTUBAR CEO SH :08029156203 what up only 👆🏻


*UWAR AGOLA*


NA

MAMAN AFRAH

*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222


🅿️8️⃣


Salmanu yana kallon ta ya ce

"Ƙwarai kuwa an ɗaura aure" Tamkar ta rusa ihu haka ta ji, a take zuciyarta ta shiga mata zafi tana tuna irin kyau da iya gayu na tsohon mijin ta, duk da dai shi ma Malam Nura yana gayun idan zai zo zance, amma dai bai kyautu a ce yau ranar farinciki, ranar da dangi da abokai da ƙawaye za su yi tozali da shi a matsayin mijinta a ce ya saka wannan yadin tsoho hakan kamar rainin wayo ne.

Tunani ta fara a ranta shin ina kayan da yake sakowa masu kyau idan zai zo hira? Mai ya sa duk bai saka su ba sai wannan tsohom yadin? Wata zuciyar ta shiga faɗa mata cewar ya yi hakan ne don ya tozata ta, in ba haka ba ya za a yi ya mata haka, cike da takaici ta ce

"Salmanu mutumin nan fa cewa ya yi ya mini kwalliya ta ban mamaki, cewa ya yi ya yi matuƙar yin kyau, haka na shiga faɗawa ƙawaye in ta zuzuta shi, daga an ce in zo a yi hoto sai na hau faɗa musu cewar sai ya zo saboda mu yi hoton tare domin shaddar mu iri ɗaya ce, kenan yanzu ya mayar da ni maƙaryaciya a idon duniya ko mai yake nufi, yanzu kamar ni Hadiza gayu a ce mijin da zan aura ya je wajen ɗaurin aure da wannan matsiyacin yadin? Kamar ni a ce angona ya je wajen ɗaurin aure duk a firgice kamar wanda ƴan bindiga suka biyo ya tsere" Salmanu ya taɓe baki ya ce

"Ai ko ni na yi mamaki, shi ya sa ban yi ƙasa a gwiwa ba na ce bari na ɗakko miki hotonsa ki ganshi muraran, wani dagaje-dagaje da shi wuyan riga duk gumi, ji wani hannun riga a tattare wallahi ko nutsuwa bashi da ita"

Hadiza ji ta yi kamar ta rusa inu, a take ta fara saƙa da warwarar cewar wannan dalilin ne ya sa da ta ce tana window tana jiran wucewarsa ta ganshi, shi ya sa ya ɓoye kansa. Cike da baƙinciki ta ce


"Ashe shi ya sa da za su wuce ban ganshi ba sai hannunsa da yake ɗagowa yana reto kamar kututturen icce, ni dai wallahi Malam Nura ya cuceni kuma a yau ba sai gobe ba zai warware auren da aka ɗaura" Baki Salmanu ya kama ya ce


"To ke kuma haka ake, wannan ai sai ki sa mutane su ce na kashe miki aure, kawai na annabawa za ki ɗauka" Idanunta ne suka kaɗa suka yi jawur tana fata da addu,ar Allah dai ya sa wannan batun a mafarki ne, wayar ta sake ƙurawa ido tana kallon hoton sosai, zooming ɗinsa ta shiga yi tana jin kamar ta shaƙo Malam Nura daga wayar ta masa rashin arziƙi zuwan Bintu ƙawarta wajen ne ya dakatar da ita daga abin da take, ta yi saurin wayincewa tana miƙawa Salmanu wayarsa haɗe da sakin dariyar yaƙe ta ce

"To shikenan Salmanu na gode ga wayar taka" Karɓa ya yi ya juya, Bintu ta ce

"Ango da abokan nasa basu ƙaraso ba ne?" Wani farrr ta yi da ido don ta kawar da ƴar sauran ƙwallar takaicin da ta taru a cikin idanunta ta ce


"Eh basu ƙaraso ba" Ta faɗa a fili a zuciyarta kuma ta ce

'Aikin banza shafa lalle a mazaunai, ai idan kin ga ango a wajen nan to sai dai in gawarsa ce za a kawo, domin ba karen mahaukata ne ya cije ni ba da zan bari ya zo wajen nan da wannan koɗaɗɗan yadin, haka kawai ya kunyata ni, a ɗaukeni maƙaryaciya'


Gaba ta yi Bintu ta take mata baya, tana zuwa ta shiga ɗakin da take, waya ta shiga dokawa Malam Nura domin ta kora masa kashedin kar ya kuskura ya zo musu gida, sannan ta ƙara da faɗin ya kawo mata takardar sakin ta. Tana jin wayar tana shiga amma har ta tsinke ba a ɗaga ba, babu ƙaƙƙautawa ta ci gaba da kiran amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa domin ba a ɗaga ba.

A ɓangaren Malam kuwa ana tsaka da ɗaukan wannan hoto wanda ya yi wa laƙabi da hoton masifa, ya ji wayarsa tana ƙara, yana dubawa ya ga sunan Hadiza ya shiga faɗawa Hudua bayan sun ware gefe guda Hudu ya ce


"Malam Nura ka daina tsoron matar nan fa, kawai ka ɗaga wayar, daga nan mu wuce gidan nasu kamar yadda ta buƙata"

9 / 15