Author : Maman Afrah Category : Tknovels
ya ɗago da faskaran icce mai wuta a jiki shi ya sa jikin taƙaura ya yi la,asar wato bakin Kuluwa ne ya rufu ruffff
Malam Nura ya ce
"Yadda kika datse ƙafafun wandon shaddar ɗaurin auren Hadiza, haka zan datse ƙafafunki da wannan addar ki koma gurguwa, sannan na saka bakin wutar nan a dungulumin ƙafar taki yadda za ki ji a jikin ki, kin maida min wando gajere na maida ki gurguwa, ramuwar gayya ai ta fi ta gayya !" Haule sai yanzu gabaɗaya ta gane inda aka saka gaba da gudu ta tsallake wayarsa da take ƙara ta yi hanyar ƙofar gidan don a kawo ɗauki.
Kuluwa ido ya raina fata a yadda yake magana rai ɓace ta san zai iya aikata komai ma, tun da ransa a ɓace yake ƙololuwa iya zamanta da shi bata taɓa ganin wannan ɓacin ran ba, kuma ta san duk a kan Hadiza ne yake wannan shi ya sa ita kuma ta riƙe ta abokiyar adawa ta har abada ba za ta daina kishi da ita ba.
Hannu biyu ta ɗora a ka tana tunanin kar fa ya ɓalle ƙofar ya aiwatar da ƙudurinsa, kafin a zo a kawo ɗauki cike da magiya ta ce
"Gida zan tafi"
Yana mata kallon tsana ya ce
"Sai dai a kai ki gida a baro, don sai na mayar da ke gurguwa!."
Ƴar uwa ban hankalinki minti biyu,,, kina son sayen kayan kicin? Ko zannuwan gado kike so? Leshi,,, shadda atamfa kayan yara,,, takalmi da jaka,,, ko kina son siyan abaya,,, mayafai huluna da sauransu ki tuntuɓeni 09025576222
MAMAN AFRAH
09025576222
[4/11, 5:14 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t
*UWAR AGOLA*
🅿️6️⃣
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*
*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿️6️⃣
Kuluwa jin furucinsa na cewa sai dai a kai ta gida a baro domin zai gurgunta ta ne, sai ta ji gabaɗaya hankalin ta ya tashi musamman da ta san daga ita sai shi ne yanzu a cikin gidan Kuluwa ta fita samo masu kawo ɗauki.
Cike da yaudara ce
"Na ji zan biya ka shaddar gabaɗaya... Ai furucin ta ƙara hasala shi ya yi hakan ya sa ya ajiye addar da faskaren iccen, saboda ya ga ita Kuluwa kamar ta ɗauki abin da wasa bata san irin baƙinciki da ƙunci haɗe da takaicin da ta ƙunsa masa ba, yana ajiyewa ya shiga buga ƙofar amma ta ƙi buɗuwa Kuluwa gabanta sai dukan tara tara yake tana jin tsantsar tashin hankali da fargaba domin da alama ƙaramar hauka ta samu Malam Nura. Jin ƙofar ba za ta buɗu ba ya yanke hukuncin ɓalle ƙofa, waige ya fara ya tafi a guje ya ɗakko taɓarya duk ya haɗa gumi wuyan rigarsa ya jiƙe. Yana ta saƙa da warwara a zuciyarsa domin yana tunanin idan ya gama nakasta Kuluwa wato ta mayar da ita marar ƙafa to zai haɗa mata da takardar saki, don ya hango wannan ce kawai mafita in ba haka ba idan amaryar ma ta zo babu alamar kwanciyar hankali.
Yana fara buga ƙofar da ƙarfi Kuluwa ta shiga zabga ihu tana neman ɗauki. Haule tana fita ta ga mutane a tsaitsaye da yara a can ma ta ga yaran ta su Alawiyya suna tsaye suna kallon kiɗa. Kalle-kalle ta fara Hudu da ya hango fitowar ta ya taho da sassarfa ganin babu alamar nutsuwa a tare da shi, cike da damuwa da tashin hankali ta ce
"Hudu akwai matsala fa a gidan" Ta faɗa tana nuna gidan da hannu. Hudu hankali tashe ya ce
"Mene ne?"
Haule ta ce
"Kuluwa"
Cike da fargaba ya ce
"Allah sa ba wankan manja ta masa ba, hana shi fitowa ta yi?"
Haule cike da ƙosawa da maganganub nashi duk da ya matso kusa da ita kuma ba kowa ne ya lura ba don kowa sabgar gabansa yake. Tana kallonsa ta ce
"Idan manja ne ra watsa masa da sauƙi, wallahi wandon ɗaurin auren ta ƙone" Idanu ya zaro tamkar za su faɗo ya dafe ƙirji ya ce
"Amma wannan mata an yi masifaffiya, ta san shaddar nawa ce wannan...Haule ta katse masa magana da faɗin
"Wallahi yana can ya ɗakko adda zai sare mata ƙafafu" Da sauri Hudu ya shige gaba ta mara masa baua, don ya san a yadda abokib nasa yake da son samu son kuɗi kamar tsohon da ya shekara casa,in, ga uban buri da ya ɗora a kan shaddar har cigiyar dillalai ya bashi bayan auren ya samo masa masu saye amma ta aikata wannan ƙanƙancin.
Da gudu gudu suka nufo cikin gidan gudun kar a yi aika-aika.
A can cikin gidan kuwa Malam Nura ganin aikain ɓalle ƙofar babba ne sai ya cire rigar ya rataye, kasancewar lokacin da ya saka rigar yana sauri daman ko singlet bai saka ba, don kiran da Hadiza ta masa ta ce za a ɗaura auren da wani in bai zo a kan lokaci ba shi ya dagula masa gabaɗaya lissafin da bai shirya a tsanake ba, ko mai bai shafa ba haka ya fito jiki fari tas, taimakon da Allah ya masa guda ɗaya wannan man da ya lakuta a saman hanci ba tare da sanin ya lakuta ba, shi ne Haule da ta saka ya murje fuskar ta yi dama dama duk da man ya yi yawan da ban da sheƙi da gumi babu abin da yake kamar ba sabon ango mai shirin angwancewa ba.
Ko da ya cire rigar ya rataye a kan igiya, ya ɗauki taɓarya ya shiga bugawa a jikin ƙofar tana ƙara duk ya loɓa ta, kasancewar akwai langa-langa a jikin ƙofar daga waje..
Hudu yana shigowa da ɗan gudu a kan hular Malam ta ɗaurin auren ya yi wa ƙafarsa masauƙi ba tare da ya sani ba, hular ta lotse, bai ƙaramin kai zuciya nesa ya yi ba da ya hangi Malam Nura ba sanye da wando gajere na shadda iya cinya duk ƙafar a ƙone baƙiƙƙirin tamkar wanda aka fito da wandon daga gidan da gobara ta kama. Ya daddage sai bugun ƙofar yake.
Yana zuwa ya kama shi yana riƙe shi yana bashi baki, Malam Nura rai a ɓace ya ce
"Hudu, Hudu, Hudu, sau nawa na kira ka?" Ya faɗa yana fisge riƙon da ya masa, Hudu ya ce
"Sau uku"
Malam Nura ya ce
"To babu ruwanka a cikin wannan magana, abu ɗaya za ka mini shi ne, ka tafi wajen Hadiza kake ta bata haƙuri ta yi wa iyayenta ta jira in zo a ɗaura auren nan da ni, wallahi aka ɗaura da wani na shiga uku na kaɗe har ganyena" Dariyarsa ya danne ganin duk abokin nasa ya susuce a kan mace, duk ya karaya ya rasa wane irin tafiya da zuciyarsa Hadiza ta yi.
Hudu ya ce
"Ka kwantar da hankalin ka abokina, ai Hadiza bata da wani miji sai kai"
Malam yana riƙe da taɓarya ya ce
"Kai dai ka je ka yi abin da na ce maka Hudu, baka san wace ce Hadiza ba, ita ta kirani a waya ta ce in zo kafin wasu daƙiƙu duk da bata faɗi daƙiƙa nawa ba ne, amma ta ce idan na haura daƙiƙu ban je ba da wani za a ɗaura mata aure" Kuluwa wacce take cikin ɗaki kunnuwanta a buɗe tamkar kunnuwan maciji jin wannan batu ranta fari ƙal, tana fatan Allah kai damo ga harawa, don za ta fi kowa farinciki wataƙila har ruwa sai ta zuba a ƙasa ta sha idan aka fasa ɗaura auren nan da Malam Nura ta ga ƙarshen tsiya da kuma tijara.
Hudu bai amsa masa waccan maganar ba ya ce
"Yanzu dai garin neman gira za ka rasa idanu gabaɗaya, domin kana nan kana ɓata lokacin ka za ta samu wani bazawarin a yi wufff da lokacin ɗaurin auren ka a ɗaura, yanzu abu ɗaya ya dace ka yi mu tafi a ɗaura auren idan ya so muna dawowa ka yi wa Kuluwa huluncin ƙona wandon nan" Kamar zai yi kuka ya ɗaga ido ya sake kallon windon ɗakin inda yake iya hango Kuluwa tare sa tsantsar ƙarfin hali a tare da ita domin babu da na sani a fuskarta, don ta ji an zo ceton ta gabaɗaya sai ma ya ga rawar kanta ya dawo.
Baki ya damƙe ya ce
"Ka san dai babu wanda zai ɗauki maƙudan kuɗi ya sayi rigar shadda kaɗai ko? Ta cuceni ta taƙaitani ai dai ba zan je wajen ɗaurin aure da gajeran wandon ba, wallahi babu mai cewa ma gajeran wando ne tun da ba a iya hango wandon sai zallar ƙwanrin ƙafata, kalli yadda ta mayar da wandon nan iya cinyata dab da tsantsa ta fa yake, banbancinsa da ɗan kamfai(Pant) Kaɗan ne"Ya faɗa yana saka hannu ya kama wandon yana nunawa Hudu. Hudu ya danne dariyarsa saboda arziƙin da Malam Nuran yake da shi ya wuce ya yi wannan abun a kan shaddar da bata kai dubu talatin ba har kuɗin ɗinkin, amma duk ya saka damuwa a ransa.
Hudu ya ce
"Ka bar batun wanna shaddar tata ta ƙare, don ko a Kano shagon da na siyo ita kaɗai ta rage a bandir ɗin ni na saye gabaɗaya, ka ga kuwa ko da an sake kawowa ba lallai a samu mai zanenta sak ba da sai a yanko a yi wandon ka siyar da ita tun da asarar kake hangowa" Kasa magana ya yi harara kawai yake aikawa Kuluwa ji yake tamkar ya zama ƙuda ya shiga ɗakin ta windown ya aiwatar da nufinsa ko ya samu sauƙi.
Maimakon ya yi wa Hudu magana sai ya juya wajen Kuluwa ya ce
"Kuluwa baki da zanen shadda kalar wannan?" ,Da mamaki take kallonsa har dariya ta so kuɓuce mata amma gudun masifarsa ta danne, saboda ta san tana darawa zai ce bata damu da halin da yake ciki ba, muryarta da alamar dariya domin sai da ta danne, yau ne ta tabbatar da cewar idan mutum yana neman mafita komai ma gani yake zai dace tana karkata kai cike da nuna damuwar da yake ciki ta ce
"Haba Malam ina ni ina shadda irin wannan mai tsada, kai ma ina jin a kaf rayuwarka wannan ne karon farko da ka ɗinka kuma kananganin siyar da ita za ka yi ba za ka ci gaba da sakawa ba bare ni... Kamar zai kai mata duka ya ce
"To na ji abun da na tambaye ki da ban amsar da kike bani da ban... Hudu ya ce
"Ba fa ita ta kai zomon ba rataya aka bata, ga wacce ta yi abun can tana ɗaki baka da damar hukuntata kawai don ita ce kuka mai daɗin hawa... Malam yana masifa ya ce
"Ya isheka matarka ce ko tawa?" ,Hudu ya ce
"Allah ya baka haƙuri, wai kana nufin zanin shaddar za ka ɗaura idan tana da akwai?" Ya faɗa yana haɗiye dariyarsa don har ya hango gogan nasa ɗauri da zani.
Malam Nura ya yi shiru yana tuno da yanzu fa yana can a cikin jama,a ana masa Allah sanya alkairi, ana ta musu hoto shi da Hadiza wataƙila ma har hannunsa dai ta kama, tana masa murmushi, da yanzu ta zama mallakinsa amma Kuluwar nan ta kawo masa tsaiko a lamarin auren nan.
Kamar ya kai wa Hudu duka ya ce
",Kamar wani bayerabe zan ɗaura zani, ka san dai na ɗaura zani na je wajen nan wallahi kwanan ɗaurin aurena da Hadiza ya ƙarw don ba za ta aureni ba, daman nufina a je a samu wani tela mai saurin ɗinki ya ɗinka mini wandon, ko zanin ba zai isa ba sai ya mini ƙafafun in ya so daga saman ko atamfa ce ya saka a mini kwanbileshin (Combination) ka ga idan na saka babu mai cewa zanin atamfa ne daga sama tun da rigar shaddar za ta rufe wajen.
Idanun Hudu gabaɗaya sun kawo kwalla, amma ba ta kuka ba sai ta tsabar dariyar da take cinsa yake dannewa, ba komai yake bashi dariya ba illa idan ya kalli Malam Nura da wannan ƙonannan wandon, abu na biyu idan ya tuna yadda ido ya juye da mujiya, wato Malam Nura ya je wajen Hadiza ne da soyayyar ƙarya saboda an ce mijin ta da suka rabu mai kuɗi ne, kuma ita ma tana da kuɗi shi ne ya je da nufin ya aure ta ya wanki banza, ya tatiƙe kuɗaɗen ya sake ta, ya tsakuri wani abu daga abin da ya mora daga gare ta ya auro wata, amma da yake Allah ya ga mugun ƙudirinsa aai ya jarabce shi da son ta na gaskiya, sannan sai gashi shi take wanka a maimakon ya wanke ta, ita take cin kuɗinsa har yanzu yana ganin idan ya aure ta, zai ci kuɗin ta ne. Abu na uku yana mamakin yadda Kuluwa ta shammace shi ta ƙona wandon shaddar, ya san ba komai ba ne yake faruwa da abokinsa sai irin tijarar da yake yi wa mata, da ɗaukan haƙƙinsu ya aure ki ya wulakanta ki ya sake ki, shi a lamarinsa ma bai san mene ne so ba, don kowacce ba yana auren ta don so ba ne, kawai son zuciya ne.
Hudu ya ce
"Kawai ka haƙura da shaddar nan ka samu wani kayan ka saka" Yana masa kallon ka janyo ruwa ya ce
"Haba Hudu ka hana ni sakat da maganganun da ka san amsar su, yanzu a kaf suturuna ina na ga wanda zan shiga taron jama,a, babu wani kayan kirki fa ka sani, a ce kamar aurena da Hadiza amma ban saka kaya na kirki ba, ni wallahi damuwata ma idan har ba da shaddar nan na je wajen Hadiza ba wallahi ba za ta ɗauki hoto da ni ba, har fa cewa ta yi za ta kafe hotonmu a ɗakin ta, wallahi Kuluwa idan muka yi gaba da gaba ni da ke ina ga ba wai ƙafafu kawai zan datse miki ba, gunduwa-gunduwa kawai zan yi da ke" ,Ya faɗa kamar an caka masa wani abu ya zabura ya koma ya buga taɓaryar hannunsa da ƙarfi a jikin ƙofar ɗakin nata, da yake ta san ƙofar tana da ƙwari ta ce
"Lokacin da zan fito ma baka gidan nan, kuma dole ka aika mini takardar sakina... A masifance ya ce
"Ƙarya kike mai mugun hali, ai wallahi ba zan yi asarar kuɗina ba da aka ɗaura mini aure da ke, ba yanzu zan sake ki, bare ma ke da kika mini aika-aika ai ko a gurguce kike sai na ci gaba da gana miki azaba a gidan nan, ke Hadiza ma a kan bayanji za take zaunawa tana tuƙa tuwo, kuma dole ki sunkuya ai sai kin karɓi ukuba...
Saboda ta sake cusa masa haushi ta ce
"Haule miƙe mini wannan rigar shaddar da ya cire, miƙo min ita ta window in ƙarasa babbake ta, in ya so sai ki ara masa riga da zani na atamfa tun da neman aron zani yake" Da sauri ya kalli igiya ya ga rigar tana nan a rataye. Bai ce komai ba domin shi kaɗai ya san irin haushin da yake ji a kan Kuluwa baki ba zai misalta ba.
Wayarsa da take ta neman ɗauki Haule ta tafi ta ɗakko tare da hularsa da Hudu ya take ta lotse, ta haɗo kan takalmansa, wayar ta miƙo masa ya karɓa ya kalli sunan Hadiza ne ɓaro -ɓaro a jiki ya rasa ma ya zai yi Hudu ya ce
"Ka ɗaga wayar mana, wai ni yaushe ka zama matsoraci ne wai? A ce kana tsoron mace haba abokina" Malam Nura kamar zai yi kuka ya ce
"Baka san so ba ne Hudu, so ne ya mini raga-raga da zuciya ni ban san ma akwai so ba sai wannan karon, ni dai na san masoyina kuɗi amma ban san ana son ɗan adam ba... Hudu ya ce
"Taɓɗi ai daman idan mutum ya ƙi sharar masallaci ta kasuwa yake yi, yanzu ai ga ta inda jarabawarka ta fito, idan ka saki mata ba har kuka suke ba ka mayar da su saboda suna sonka amma ka ce musu son banza... Kiran da ya shigo ne ya datse maganar haka ya yi ta maza ya ɗaga yana ɗauka ta balbale shi da masifa kamar uwarsa ta ce
"Nura ni za ka wulaƙanta a idon duniya? Tun ɗazu lokacin ɗaura aurenmu ya cika, amma dai baka duba lokaci ko? Tun daɗewa sha ɗayan ta wuce yanzu Babana ne ya ƙara awa ɗaya ɗaya, idan har awa ɗaya ta cika akwai mazan da zan sa su hau layi duk wanda na ga wankansa ya mini shi zan zaɓa...
Sai da ya gyara muryarsa ya ce
"Haba masoyiyata gani nan fa ai kaf garin nan babu wanda zai kai ni ɗaukan wanka, in kin ga yadda shaddar nan ta karɓe ni zaki yi mamaki su Hudu ma sai yabawa suke, abin da ya