Author : Maman Afrah Category : Tknovels
wasu zauna tana ta addu,ar Allah ya sa aljanin nan ya yi wa Haule da Hadiza abin da ya mata don a dawo ɗaya!. Haka ta kwanra cike da takaici haushin Malam Nura take ji can zuwa jimawa ta ɗauro ɗankwali ta fito ta sake alwala ta yi ta yi sallolin ta ta kwanta, don ko sha,awar zuwa turakar Malam ɗin ba ta yi tun da aka mata aski, haka ta ringa murƙususun ciwon marar magungunan da ta sha!.
Malam Nura bayan ya gama komai ya dawo gida, yana ɗan duƙawa, saboda mararsa da take riƙewa cike yake da buƙata amma babu hali tun da amarya tana gidansu, shi kuma don ita ya yi gyara don haka ba zai je wajen sauran matan ba. Haka ya ringa safa da marwa yana neman ɗauki amma daga karshe ya jiƙa jar kanwa ya sha ya samu dama-dama ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi cike da mafaekin tarewar Hadiza.
Washe gari da fara,a ya tashi kasancewar yau ce ranar da yake mafarkin zuwanta, sannan ya fara lissafin zuwa amarya ya samu yake ɓanɓarar kuɗi ko ya maida gurbin da ta masa na kuɗaɗen da ya kashe. Da ya yi wanla ma tazugen ya saka a wandon shaddar ya saka ta don ita ce rufin asirin sa a kaf kayansa, wajen sha ɗaya ya je gidan su amarya bayan sun yi waya, sun yi magana cewar da yamma masu jera kaya za su zo. Daɗi kamar ya kar Malam Nura tana tambayarsa mai ya sa ya saka kayan jiya ya ce ai saboda tare suka ɗinka shaddar shi ya sa yake son saka kayan, ba ta san cewar kayan ne babu na kirki ba wannan ne ɗaya-ɗaya.
Sun yi sallama ya kamo hanya yana ta fainciki, don da zai tafi har da ba Zainaba da Shafi,i ɗari biyar ya ce su raba, har yana kama hannun Shafi,i yana faɗin su yi sallama, har da cewa Zainaba sai watarana, ita kuwa Hadiza da bata ma gane mai yake nufi ba ba ta kawo komai ba.
Kuluwa haka ta tashi da baƙinciki da takaici musamman da ta ga gashin kanta a shara da Haule ta zuba, ta so ake mata kitso ɗan gaban goshi tana yarfo gashin domin ta nunaw amarya cewar ba fa dangin buzaye ne kawai masu gashi ba, duk da ta san ba za ta taɓa kamo ta a gashi ba amma dai ta kwatanta sai kuma gashi aljani ya yi mata tsiya.
Da yamma ƴan jere suka zo, Haule ta musu abinci da Malam Nura ya bayar a dafa musu da kuma cingam da kuɗin tukuici na jere dubu biyu. Ƴan jere suna jeru suna waƙa suna shewa, duk Kuluwa tana jin su, tana tsegumin abin da aka kawo na jeren daga windon ɗakin ta. Suka gama jera kaya tsaf suka yi wa Haule da take musu faram,-faram magana, Kuluwa kuwa yadda ba ta musu magana ba haka babu wanda ya kula ta bare ma ita da ta so shuka musu tsiya da ture ka ga tsiya za ta yi ɗaurin ɗankwali amma kuma ganin babu komai kan a saisaye sai ta ɗauri tamtam kar ma ɗankwalin ya je ya faɗi ya kunyatata a gaban dangin kishiya. Tun da dai ba ta ɗauki Haule a matsayin kishiya ba yanxu hankalin ta yana kan Hadiza.
Hadiza da za a kai kaya ta haɗa kayan sawarta karkaf da na Zainaba da jakar Shafi,i shi ma da aka kwashe masa kayansa duka, yaro yana ta murna za su koma wani gidan a inda Zainaba take ta ƙiyasta irin ɗaukan maganar da za ta yi da irin kunna wuyar da za ta yi a gidan sabon mijin innarta.
Malam Nura bai sna wainar da ake toyawa ba ta tarewa da agololi har guda biyu, shi ya sa ma ya basu ɗari biyar don ya san shi da su sai dai idan sun je ganin mahaifiyarsu shi ma idan bai basu fuska ba daga zuwa ɗaya ba za su sake marmarin zuwa ba. Yana ta washe baki, kasancewar ranar da aka ɗaura auren ce ranar da mai gasa kaju yake gasa kaji da yawa to ranar kuma amarya bata tare ba, ranar lahdin kuma duk babu kaji a wajensa, hakan ya sa Malam Nura ya je kasuwa ya siyo danƙareriyar kaza, ta kai wa mai gashin ya ce ya masa gashi mai shegen daɗi!.
Ya hana kansa sakar yana ta ɗokin zuwan amarya, Hudu ya tsokane shi ya fi cikin carbi ya ce
"Gaskia abokina Hadiza ta ciri tuta har da wannan zabgegiyar kaza haka?" Malam Nura ya yi dariyar mugunta ya daɗe yana dariyar sannan ya ce
"Ka saka a ranka Hudu wannan kaza a jakar Hadiza za a fanshe ta, don ba zan sarawa jaki ciyawa ba, dole duk zan fanshi kuɗina a hankali"
Hudu ya ce
"Ni kuma gani nake Hadizar nan ta sha bamban da sauran matan da kake aura fa, anya za ta yarda a ci tuwo a kanta da alama za ta kwatawa kanta ƴanci ba, kuma ta wani ɓangaren sai in ga kamar ta fi Kuluwa masifa, kar fa su mayar da kai ƙwallon ƙafa,, waccen ta garo nan waccan ta garo can" Tsaki ya yi yana jaddada ƙaryarsu dubu!.
Suna can da shi da Hudu har aka yi isha,i sannan ya je ya karɓo kazarsa da take ta ƙamshi, Hadiza sau uku ta kira shi tana jaddada ya sayi kazar amarci, yana tabbatar mata da cewar danƙareriya ma kuwa, tana ta masa rantsuwar cewar matuƙar babu kaza wallahi ba zai kwana a ɗakin ta ba, ganin yana maƙale da kazarsa ya tabbatar masa cewar ga kaza nan ma a haƙarƙarinsa, sanin ta yi tanadin gyaransu na mata tun da ya san duk amare suna gyara na musamman idan xa a yi aure ya shanye sauran magungunan sa yana ta tanadin yau!.
Ko da motoci biyu da aka aika ɗakko amarya suka tafi sho yana can yana ta zuba surutu shi da su Hudu a majalissa.
Kuluwa wacce ta sheƙa wanka ta sha turare ta sake shan kayan mata don ta tabbatarwa kanta ko za a mutu yau ita ce amarya ba Hadiza ba wato ita ce da miji. Haule tana lura da ita amma bata ce mata komai ba. Ta gama shiryawa tsaf ta kame a kan gadon ta tana jiran a yi wacce za a yi.
Tana na zaune ta ji dirar motoci ana ta zabga guɗa ta yi gajeran tsaki ta gyara zaman ta, tana ayyanawa a ranta rigima uban wa ta kashe!.
An shigo da amarya Haule tana musu marhaba, aka tafi da ita ɗakin ta, bayan jimawa can ƴan kawo amarya suka farawa amarya sallama suka fito suka yi wa Haule sallama suka tafi. Hadiza ta ajiye mayafi ta turo ɗaurin ɗankwalin sabuwar atamfarta da ta saka, ta ɗakko jakar Zainaba da ta Shafi,i ta ajiye a gefe ta fito daga ɗakin tana ƙarewa tsakar gidan kallo tana taɓe baki. Gaban Haule ta je ta tsaya ta ce
"Barkan ki da gidaa" Haule ta amsa tana mata barka da zuwa don ta gane ita ce dai Hadizar Malam Nura, Kuluwa da take zaune ta kasa kunne jin wata baƙuwar murya ta yi saurin leƙowa ta windon Hadiza ta bata baya don haka a kan gashin da Hadiza ta yarfo kitson har gadon bayan ta ta yi wa idanun ta masauki, gaban Kuluwa ne ya bada dididiffff ta zaro ido, da sauri ta janye ɗankwalin ta daga saman kanta ta shafo kan jin ƙwal uwar kwabon da wanzam ya mata ta ce
"Allah tsinewa Usaini wanzam, yanzu daga gashi ma za a fara ci na wasa" Ta faɗa tana komawa ta zaune ta ɗaura ɗankwalin tana tunanin mafita.
Hadiza ta gyara tsayuwa ta ce
"Ina ne ɗakin da su Zainaba za su zauna" Cike da rashin fahimta Haule ta ce
"Su wace Zainabar?" Hadiza ta yatsina fuska tana mata nuni da Zainaba da Shafi,i da suke tsaye ta ce
"Ƴaƴan Malam Nura mana "Haule ta ɗan yi jimmm a ranta tana danne dariyar ta a zuciyarta ta ce
"Bantan uban can kayyasa!!! Yau ake yin ta anya Malam ya san da yara nan za a tare kuwa? Taɓ akwai daru" A fili ta ce
"Ni dai ban sani ba sai dai ki jira dawowar mai gidan" Ko amsawa ba ta yi ba ta juya tana wata tafiya, Haule ta shige ɗakin ta tana jijjiga kai alamar Malam ya ɗakko ruwan dafa kansa garin aure-aure.
Yana can yana washe baki lokacin da direbobin kai amarya suka kira shi suka ce sun cika aiki. Waya ya ɗaga yana washe baki ana ta masa kirarin ango Hadiza ya kira lokacin ta fito daga ɗakin ta tana duba randunan ruwan da aka kawo mata ko an zuba ruwa, ɗagawa ta yi yake tambayar ta ta zo lafiya ta faɗa masa, na ya shiga tambayar ta tana ina ta faɗa masa tana ɗakin ta, ya ce ta koma ɗakinsa, Kuluwa da take tsaye ta kasa kunne tana jin wayar da suke ta ji tana cewa
"Ai ni ban san turakar taka ba" Daga ɗaya ɓangaren ya faɗa mata inda ɗakin yake, ya ce mata ba a kulle yake ba a buɗe yake sannan ya ce gashi na zuwa ta jira shi. Kuluwa tana jin ta tana cewa to shikenan bari ta je turakar. Amma tana gama wayar a fili ta furta
"Ai wallahi babu turakar da zan je sai dai idan ka zo ka nunawa ƴaƴana ɗaki sun kwanta " Ta faɗa tana ci gaba da abin da take, tasowa ya yi ya kamo hanya ya zo ƙofar gida kenan ta kira shi twke tambayarsa ya siyo ruwan roba mai sanyi tana jin ƙishirwa?Wannan karon ma a kan Kunne Kuluwa amsa mata ya yi da cewar ya manta lemo ya siyo, sai ta ce to ya taho da shi, har ya kashe wayar ya sake kira yake tamabayar ta tana turaka, a kan kunnen Kuluwa ta amsa masa tana turaka!.
Tana gama wayar ta koma ɗakinta, Malam Nura gudun kar ya tafi da kaza na da lemo ganin taro ɗan maƙotansu ya ce
"Hashimu ungo ledar nan ka je ɗakina amarya tana ciki ka bata!" Hashimu ya karɓa cike da ladabi.
Kuluwa wacce tarar aradu da ka ta sanya ta fitowa ta lallaɓa ta tafi turaka ta zauna, don ta rantse yau ita za ta kwana da miji, duk bala,in da za a yi kuwa. Tana shiga ta zauna, Hashimu da ya shigo da sallama amma babu wanda ya amsa kasancewar Haule har ta kwanta bacci, Hadiza kuma tana ji amsawa ne ba za su yi ba ita da yaran ta, ganin hakan ya tafi ɗakin Malam Nura ya tsaya ya yi sallama, Kuluwa ta maƙe murya ta amsa yadda ba zai gane ta ba don ya san muryarta yana miƙa ledar ya ce
"Amarya wai gashi in ji Malam" Hannu ta miƙo ta karɓa tana amsa masa yana bata ya juya ya fita daga gidan. Rashe-rashe ta zauna a tsakar ɗakin, ta buɗe lafiyayyar gasasshiyar kazar nan ta buɗe robar lemo ɗaya, ta shiga yi wa kazar cin ƙasƙanci tana korawa da lemo.
Malam yana zuwa shagon ya siyo ruwan ya taho amma wasu abokansa da suka tare shi, su suka sanya ya ɗan jinkirta duk da hankalinsa yana gun amarya, har hannunsa yake shinshinawa a hanya yadda hannun ya riƙe ƙamshin kazar nan saboda tsabar riƙon da ya mata ta daɗe a wajensa.
Yana shigowa zaure ya tsaya ya rufe ƙofar ya saka sakata sama da ƙasa, ledar ya ajiye a ƙasa ya ɗaga hannuwansa sama ya yi wata uwar miƙa ya ɗauki ledar yana murmusawa a zuciyarsa yana faɗin
'Hadiza ta yau ta dawo mallakina za ta kwana a gidana, an bar wannan shegun yaran fitsararriyar Zainabar wannan ai zan nuna musu yanzu uwar tasu a ƙarƙashin take fuskar zuwa gidan nan ma ba za su samu ba!"
Wasa farin girki ya zaman zai kasance, Kuluwa ta tari aradu da ka ta cinye kazar amaryar da malam ya sha wahala ya siyo ta ɗanya ya bayar aka gasa ya biya kuɗi duk don a mori amarci, kar fa kuluwa ta sake laifi a karo na biyu, ga kuma agololi har biyu sun tarw a gidan malam nura da sai yanzu zai yi arangama da su, ga Hadiza ta shigo da zafin ta, shin tsakanin Malam da Hadiza waye zai ci moriyae auren da ya yi shin ita ce za ta samu kuɗin daga wajensa ko kuwa shi da ya ɗora rai, anya zaman zai je ko ina, ya batun zaman kuluwa a gidan, shin zai samu damar ci gaba da aure-auren sa?
Amsar tana cikin ci gaban labarin domin mu yi tafiyar da ke ki tura 700 ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay don ki shiga grp mu gama har ƙarshe idan na kammala cmplt docment 1k ne.
Mutanena na niger za ku tura 700 ta 88630104 issaka issofou nita ko amana shaidar biya ta 09025576222
MAMAN AFRAH