Author : Maman Afrah Category : Tknovels
ya salwanta" Kallon -kallo aka shiga yi tsakanin Kuluwa da Haule Haule tana ƴar dariya ta ce
"Toh Malam ai abin wannan ba komai ba ne, idan ka ce a baka wata biyu ma sai mu baka ka gama cin amarcin...
Kuluwa ta bugi ƙirji ta ce
",Sannu Haule dami sarkin haƙuri, wallahi ba zan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine mini, wato ke saboda baki san ƴancin ki na mace ba za ki bar kwananki tun amarya bata tare ba namiji yake mata tanadin jikinsa, to ni dai ba zan yarda ba, tun da yau ma baki kwanana ne kuma bani da wani wajen kwana da ya wuce turakar Malam a yau, haka idan kwanan ya zagayo ma sai na je... Wani haushi da tsanar Kuluwa ce ya cika Malam daman ita take kawo masa cikas a kowane abu shi ya rasa wannan jaraba da ya je ya kwasowa kansa biyan bashin auren ta gashi ta addabe shi.
Ganin tana masifa shi ma ya ce
"Haule Allah miki albarka ai shi ya sa kika daɗe a gidan nan kika yi ƙarko"
Kuluwa ta yi karaf ta ce
"Ai ciwon kanta ne bata sani ba shi ya s... Haule ta haɗe rai ta ce
"Kuluwa ki taka a sannu fa, shiru -shiru ba yana nufin gudun magana ba, kawai kyalewa ce da son zaman lafiya, kuma na san ciwon kaina kawai biyayyar aure ce da bin maganar miji, ni nan da kika ganni ina iya sadaukar da duk wani abu don farincikin mijina, ina iya haƙura da jin daɗina don in faranta masa" Baki sake Kuluwa take kallonta ba tare da ta ce komai ba ta ɗauke idanunta daga kallon ta ta mayar kan Malam, don ita idan ta tsaya maimaita magana da Haule hawan ruwa ne zai kamata.
Tana kallon Malam ta ce
"Na faɗa maka ba zan yarda ba, kuma da ka saka mata albarka nima ai ba tsine mini aka yi ba"
Da yatsa ya nuna ta ya ce
"Ai duk ƙwawarki kwanan turakar miji ya barki Kuluwa ki ɗauki na annabawa... Tana tafa hannuwa ta ce
"Wallahi yau ma kwanana ne a ɗakinka zan kwan...
Ya katse ta da faɗin
"Ga fili ga mai doki, in dai za ki je ɗakin ki kwanta ga wurin nan, ni dai sunna ce ba zan aikata ba tun da na faɗa miki tanadin amarya Hadiza ne, ban da neman jaraba ma ke da kika kwana jiya a ɗakin ki amma yau shi ne don na nemi ku bani lokaci shi ne kika hau dokin zuciya kike sukuwa" Banza ta masa ta juya ta ci gaba da aikin ta.
Hannu ya saka a aljihu ya ciro naira ɗari ya miƙawa Haule ya ce
"Ungo nan Haule, ai ke kam kina cin ribar zaman aure daman mai haƙuri shi yake cin ribar zaman duniya, kin ga jiya ga ɗari biyar ɗinki ta faɗar kishiya, yanzu ga naira ɗari ta haƙurin bin maganar miji ɗari shida me kika manta" Tana dariya ta ce
"Allah amfana, Allah barka da Hadiza amarya"
Ya washe baki kamar gonar auduga ya ce
"Amiiiiiin Haulen arziƙi"
Kuluwa ta ɗago daga sharar da take ta ce
"Ina tsiya ina wata ɗari shida, kamar wata matar kyankyaso zan ke karɓar wannan kuɗin ai wallahi sa,a ka yi da sai na ɓare maka kai a biyu"
Tsaki ya yi ya ce
"Ai duk namijin da ya auri mace mai baƙin kishi bai yi dace ba, gashi nan bakya cin ribar zaman auren kina zaune miji yana yi wa kishiya kyautar kuɗi"
Ta ce
"Ai ko ni zan iya kyautar sama da naira dubu ba wai naira ɗari ba" Ita dai Haule bata tanka musu ba, haka ya shige ɗaki ya bar ta tana ta kumfar baki, sai ta yi shiru kamar an tsikare ta sai ta ci gaba da masifa ita kaɗai.
Da yamma Kuluwa ta shirya ta nufi gidan Baba Ramma mahaifiyar Malam Nura da sallama ta shiga bayan an amsa ta same ta tana tuƙa tuwo, tabarma ta shimfiɗa mata suka gaisa Baba Ramma ganin ran Kuluwa a ɓace ta ce
"Kuluwa ina fatan dai kuna lafiya kuma kuna zaune lafiya" Kamar mai jira ta ce
"Ina fa zaman lafiya gidan kamar filin yaƙi"
Baba Ramma ta ce
"Ya subhanallahi mai ya yi zafi shi ba wuta ba?"
Kuluwa ta ce
"A kan wannan neman auren da yake yj ne sai tauro da abubuwa yake yana kafa mana dokoki a gidan duk sai kambama amarya yake yana nuna ta fimu matsayi"
Baki sake Baba Ramma take kallon Kuluwa cike da kasa ɓoye mamakin ta ta ce
"Ke yanzu Kuluwa a kan ƙarin auren ne kika kawo ƙaran mijinki?In ce dai ba ke kaɗai ba ce ita Haulen fa?"
Kuluwa ta ce
"Ita bata san inda yake mata ciwo ba"
Baba Ramma ta ce
"Ni dai tun da Nura yake aure-aurensa Haule bata taɓa kawo ƙaransa ba amma ke kin zo kina ba kanki wahala, shin baki san cewa shi namiji idan zai ƙara aure sai mace ta kawar da kai ba, sannan duk wani rawar kai da wulaƙancinsa sai a lokacin yake tsurowa, duk da ba kowane namiji bane yake haka amma yawanci mazan duk haka suke"
Kuluwa takaici ne ya cika ta hakan ya sa ta ce
"Ni dai Baba dan Allah ki bashi umarni ya fasa auren nan ji nake kamar zuciyata ,a ta buga... Baba Ramma ta ce
"Inyeee lallai fa, sannu Kuluwa, wato in hana shi rawar gaban hantsi bayan da ransa da lafiyarsa da ƙarfinsa a jikinsa ai daga nan in aure hamsin zai ƙara ba zan hana shi ba, komai lokaci ne wataran ko an ce ya yi ma ba zai yi ba"
Kuluwa ji ta yi tamkar ta shaƙe Baba Ramma har sai ta bar numfashi, duk da ba wannan ne auren ta na fari ba amma bata san mai ya sa ko mijinta na fari bata son sa kamar yadda take son Malam Nura ga wani kishi da ta ɗorawa ka ta yake ɗawainiya da ita. Tana so ta faɗa mata har ƙairace musu ya ce zai yi wai tanadin amarya zai yj amma kunya ta hana ta magana haka ta taso ta baro gidan tana da na sanin zuwa tun da babu biyan buƙata!.
Yau wani yadinsa da yake ganin ya fi kowane yadi kyan gani a cikin kayansa duk da shekara ta uku kenan da ɗinkawa ya gyara tass ya saka saboda ya gaji ya biyan kuɗin aro kaya.
Hadiza ko da ya zo yau ta ga hannunsa babu komai hakan ya sa ta ƙi sakin jiki take wani kumbure-kumbure shi ma yana ganin yanayin ta ya san dalilin fushin amma haka ya basar don shi a nashi ganin ya gaji da nomawa jaki ciyawa yana kawo kayan daɗi don su ji daɗin hirar soyayya amma tana ba ƴaƴanta ita cw kaza uwar son ƴaƴa a zuciyarsa ya ce
'Idan aka ɗaura auren ai na huta sai su koma gidan ubansu, ko ki bar su a gidan kakannin nasu ina dalili'
Hira yake jan ta da ita tana basarwa ya gaji ya ce
"Hadiza yau ko bakya jin daɗi ne?"
Ta yatsina fuska ta ce
"Ƙalau" Fitowar Zainaba daga gidan tana riƙe da hannun Shafi,i shi ya katse musu maganar. Zainaba ce ta tsaya shi ma ya tsaya kasancewar hannunsa cikin nata, ta sunkuyo ta masa raɗa a kunne. Kai ya gyaɗa ta saki hannunsa ya taho da gudu yana cewa
"Oyoyo baba" Yana zuwa ya haye cinyar Malam Nura ya ƙanƙame shi, kasancewar yana cin tuwo Zainaba ta je ta kamo shi suka fito. Dariyarta ta shiga dannewa ganin haƙarta ta cim ma ruwa, daman tun da ta ga Innarsu ta fito, ta saka a ranta yau ma sai ta masa abun da zai masa ciwo, hakan ya sa ta saka luda ta kwalfo miyar kuka ta ƙara a kwanon da Shafi,i yake in tuwo da yake miyar ta huce, ta ringa ɗaukan miyar da ludan ta zuba masa a jikin kayansa da duka hannuwansa har bayan hannun. Shi ne da suka fito ta raɗa masa cewar ya je ya haye cinyar Malam Nura duk ya ƙanƙame shi.
Malam Nura gabaɗaya ya rasa ma ya zai yi, jikinsa jaga-jaga da miya gashi kuma miyar manja ce yadda fari yadin ya sha miyar tamkar ya saki kuka.
Cikin yaƙe don kar ta ga kamar ba ya son ɗanta ya ce
"Oyoyo Shafi,i ɗana na kaina" Ya faɗa yana ƙoƙarin ɓanɓare yaron don ya maƙalƙale shi, hannuwansa suna maƙale a wuyansa hatta wuyansa da gefen fuskarsa sun san Shafi,i ya ci tuwo. Dakyae ya ciro shi yana faɗin
"Duk ka ɓata ni da miya" Ya faɗa yana kallon jikinsa. Hadiza ta haɗe rai ta ce
"Haba Malam Nura to mene ne don ya goga maka miya kai baka san yaro ba" Gudun ɓacin ranta ya sa ya washe baki ya ce
"Haba Hadiza amaryata ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, ina ni ina masa faɗa ai ba miya ba ko kashi ne ya goga mini ba zan ji komai ba ai ɗana ne" Dariya ta yi tana faɗin
"Shafi,i jeka gida ka wanke hannunka" Don ita ba ta san duk shirin Zainaba ba ne, Zainaba kuma ta ce
"Kake kamshin miya a maimakon ƙamshin turare " Ta faɗa tana dariya, don ita Hadiza ba ta son a kwaɓi ƴaƴanta bata ganin laifinsu. Ta kalle su ta ce
"Innata yau ba a kawo nama ba?"
Malam Nura a fili ya ce
"Yau ba a kawo ba a yj haƙuri ƴar baba"
A zuciyarsa ya ce
'Aikin banza shafa lalle a mazaunai kamar ubanki ne yake nema mini kuɗin'
Idanun uwar ta faka ta galla masa harara tare da yatsina fuska ta juya ta nufi cikon gidan Shafi,i kuwa ya ja tunga ya tsaya ya ce
"Alewa" Babu yadda Malam Nura ya iya haka ya ciro 200 ya bashi ya ce ya saya. Bai wani jima ba ya bata dubu biyun ta ta karyawa a zuciyarsa yana faɗin
'An kusa ɗaura aure ki tare in huta da wannan jigilar bada dubu biyu ki je can ki haɗu da su Kuluwa, ba kina kyashin cin tuwo a gidanku ba, idan kika je gidana tuwon ma gaya za ki samu sai kin nemawa kanki miya, kafin na gama cin moriyar ganga na hankaɗa ƙeyarki'
Sun yi sallama ya kamo hanya ya tafi gida yana ta jera tsakin wankan miyar da Shafi,i ya masa.
A can gida kuwa Kuluwa ta samu maganin matan ta bita zai-zai ta sha don ita tun da ya ce su bar kwanan turaka ta saka a ranta yanzu ta fara kwanan turaka. Ko da ya zo wanka ya yi ya cire wannan kayan. Tana sane da shi, don biredi da lemo ya siyo ya ci iyalinsa kuwa ko oho. Sai da ta daidaici ya gama komai ta nufi ɗakin tana zuwa ta ji ƙofa a rufe ta tura amma ƙofa bata buɗu ba. Daga waje ta bubbuga tana faɗin
"Ka buɗe mini in shigo" Haule tana jinta a zuciyarta ta ce
'Kin haɗu da wahala'
Daga cikin ɗaki ya ce
"Wallahi sai dai ki kwana a waje amma na haramtw muku kwanan turaka" Tun tana magiya har ta lura abin ba na wasa ba ne. Haka ta raba dare tana zaune a ƙofar ɗakin da ta gaji ta ringa masifa ta koma ɗakinta. Washe gari ta yi ta masifa amma ko kallo bata ishe shi ba.
Zaune suke a kan benci shi da abokinsa Malam Hudu, Malam Nura ya ce
"Wannan dubu ashirin ɗon ka siyo mini shadda yadi huɗu yar dubu biyar biyar, wannan dubu biyar ɗin ka haɗo mini magani"
Ya kalle shi da mamaki ya ce
"Maganin mai?"
Yana masa hararar wasa ya ce
"Haba kai ma, maganin maza mana, gyara zan yi fa, ai shi ya sa ma na dakatar da su Haule daga zuwa turaka, saboda gyaran tarɓar amarya zan yi, ka ga kuwa tun da ba su na yi wa gyaran ba babu dalilin da zai sa suke zuwa mini turaka,sai dai wacce aka yi gyaran dan ita idan ta zo ta mora" Da dariya ya fashe ya ce
"Wallahi kaima abokina da wani abu to ina kai ina wani gyara" Yana masa wani kallo ya ce
",Naka wasa ne, ka san dai mata suna gyara to mu maza mai yasa ba za mu yi gyara ba? Gwara ka siyo mini ka ga ai ba raini" Karɓa ya yi yana faɗin
"Gaskiya na yarda amaryar nan ta musamman ce kana son ta, wato shadda ma sabuwa gal aleda mai kyau za ka yi ga magani," ,Shi ma dariya ya yi yana tuna irin son kuɗinsa sai dai ya samu yadika masu araha amma wannan karon dai ya yi ƙuri zai yi mai tsada.
Malam Hudu yana irga kuɗin ya ce
",Gobe ai da sassafe zan tafi kanon saboda na kammala abun da zan yi in gama, ni anya wannan Hadizar za ka iya sakin ta kuwa kamar yadda kake sakin sauran matan? Na ga fa ka kamu da sonta"
Ya yi tsaki ya ce
",Ita wa ta fi, ka san ai mace kamar riga na ɗauke ta in saka wannan in cire wannan"
Haka suka yi ta tattaunawa abin su suna tsara yadda abubuwa za su kasance, daman ita Hadiza ya sallame ta kuɗin da ta yanka masa yanzu kawai ɗaurin aure ne za a yi da tarewa
Mu je zuwa ba a fara wasan ba akwai ƙura mai tsakuwa ma kuwa🤔😹
MAMAN AFRAH
09025576222
[4/7, 5:00 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Bu295Z6iGnL3SoKYtgqnbZ?mode=gi_t
*UWAR AGOLA*
🅿️3️⃣
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*
*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
Labarin mai cike da abin dariya
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿️3️⃣
Tun da ya kama hanyar zuwa gidansa yake jin farinciki don yana son ba marar ɗa kunya a wannan ƙarin auren da zai yi, musamman da Kuluwa take son hana shi rawar gaban hantsi tana son shige masa hanci da ƙudundune. Shi kuma bata san hakan ƙara rura masa wuta take ba tana ƙara zuga shi domin ya saka a ransa cewar zai yi abin da zai shallake mata tunani abib da bata zata ba, sai ya cusa mata takaici tun da shi bai saba idan zai yi ƙarin aure mace ta takura masa ba ko ta nuna rashin amincewar ko ta ɗaga masa hankali sai a kanta, don ita Haule in don ta ita ne duniya ta zauna lafiya.
Ko da ya ƙarasa gidan tsaye ya tarar da ita tamkar tana jiran dawowarsa. Yana sallama amma bata amsa ba sai Haule ce ta amsa masa daga cikin ɗaki. Zai wuce ta sha gabansa ya ƙara ratsewa ta sake shan gabansa a ƙufule ya ce
"Mene ne kuma?" Tana masa kallon raini ta ce
"Duk abin da ka zata shi ne, ko in ce duk abin da kake ji da shi ni ɗin ma shi nake ji" Kallon ta ya yi ya a ransa ya fara tunanin anya wannan za ta bari ya ci amarcin nan a kwanciyar hankali kuwa? Zuciyarsa ta fara raya masa cewa ko dai ya aikata gidansu amma ba da zummar saki ba, tun da ya saka a ransa ba zai sake ta ba sai ya gama amfanar kuɗinsa amma dai yanzu tun da tana son kawo masa cikas gwara ya ce ta tafi gidan, sai dai ya ƙudiri cewa ba zai dawo da ita ba sai bayan wata biyu wataƙila ma lokacin ya saki Hadiza ya fara neman wani auren.
Gyaran murya ya yi ya ce
"Kuluwa abin naki ya fara yawa, ke baki san mace mai kishi fita take daga zuciyar miji ba?" Ta kama ƙugu da hannu ɗaya tana jijjiga jiki ta ce
"To na nawa kuma? Ai na san wannan bazawarar da kake kira mai jiran gado ta daɗe da yin fatali da ƙaunata daga zuciyarka, shi ya sa baka ganin kaina da gashi"
Haule da ta fito daga ɗaki ta mata kallon ɗaya saura kwata ta ce
"Kuluwa ya kamata ki wa kanki faɗa, ki yi karatun ta nutsu, shi mijin da ya damu da kai shi kake kishi a kanka, kuma wa ya ce miki akwai ɓurɓushin ƙaunarki a zuciyar Malam da har kike ikirarin wata ta tunkuɗe son naki, idan baki sani ba in faɗaa miki, daga lokacin da mace ta sako ƙafarta a cikin gidan Malam Nura daga ranar duk wata ƙaunarta take bankwana daga zuciyarsa shi ya sa zaman ba ya iya zuwa ko ina ake rabuwa domin daga ya hango wata zancen ta cikin gida ya ƙare amma kin ɗauki kishi kin hana rai da zuciyarki sakat ki kafa faɗin wai mai jiran gado shin ke idan ta jira gadon sai me? Kafin ta jira gadon mata nawa ne suka jira dan Allah ki sauƙaƙawa kan ki amma shawara....
Cike da masifa da kallon raini ta ce
"Haule ki