Author : Rabiat Fulani Category : Tknovels
tsawon lokacin dana ɗauka kafin nasamu na dinga bacci ba.”
“A lokacin da auren ki ya mutu, abu biyu ne yasameni, na farko ina tunanin zan same ki a wannan lokacin, na biyu kuma banji daɗin faruwar hakan ba”.
“ Lokacin da mukaje office kike faɗa min abinda ya kashe miki aure, Allah ne kaɗai yasan irin abinda naji, amman haka na danne, saboda har lokacin kina tare da soyayyar saurayin ki, karshe ma kika aure shi kika bar kowa kika bishi.
“Bazan iya faɗa miki irin tashin hankalin dana shiga ba, a wannan lokacin.
“Naji a raina kawai na rasaki har abada.”
“Na koma gefe ina ta miki addu’a, lokaci ɗaya best ta dawo dake gida.
“A lokacin nan, naji har a raina bazan bari na kara rasaki ba, amman se kikace min ko zakiyi aure, auren kaddara ne”
“Fadamin taya zan auri gangar jikin ki buzuwa ?”
Hakan yasa nace miki ga abokina.
“Kinsan lokacin dana tabbatar kin zama mallakina, a wani irin farin ciki na kasance ?
“Duk wannan wahalar dana sha akan soyayyar ki, ban cancanci ki soni ba? Ban cancanci samun soyayyar ki ba buzuwa ???
“Fadamin mezanyi ki soni!!!!
Kuka nake da ƙarfi muryata har ta dishe, gaba ɗaya na rasa a ina ya kamata na ajiye tunani na.
Ganin irin kukan da nake ne yasa ya miƙe ze fita.
“Zan baki lokaci, idan kuma hakan be yuyu ba zanyi miki abinda kike so !!!!!!!!!!!!
https://whatsapp.com/channel/0029VaCfzOMHVvTWSDWuVr41
A gafarceni yau page din yau bashi da tsawo, mu hadu a page 33 domin jin irin rayuwar da SUMAYYA zatayi a gidan likita.
Taku har kullum Rabi’atu Fulani.
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 35
*WANNAN PAGE ƊIN NAKI NE AN KARIME KARIME NA KIYI YANDA KIKE SO DA SHI MALLAKIN KI NE*
Juyawa yayi ze fita daga ɗakin, ban bari ya fita ba na tashi da gudu na rungume sa ta baya.
Kuka nake sosai a bayan sa.
Juyo dani yayi ta gaban sa, ya riƙe fuskata, zame fuskar na ƙarayi na rungume sa, ina ci gaba da kuka na.
Be hanani kukan ba, dan shi ma da dama kukan zeyi.
Seda nagaji dan kaina da kukan, sannan na zame jiki na daga na shi na zauna.
Becemin komai ya juya ya fita daga ɗakin.
Sonake na dakatar da shi amman nakasa tayaya zan ma ce masa kar ya fita ai da kunya.
Kaina na haɗe da gwiwa ta ina tunanin dama zan samu wanda zemin irin wannan soyayyar ? Toh meyasa ya doctor ya ɓoye min cewar yana sona ? Anya ma nayi mishi adalci ? Shi be gujeni ba amman ace nice nake gudunsa ? Ya rabb!!!.
Ya zanyi yanzu?
Waya ta na janyo ban damu da daren da yayi ba, na bugawa best waya.
“Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un gaskiya sashi na kidena shiga hakkin musulmi, kinji yanda na firgita ganin kiran ki a daren nan”
Jin yanda nake sheshshekar kuka ne, yasa kuma ta dawo tambayar meyafaru.
“Duk abinda ya faɗa min, seda na faɗa mata, yanzu sashi na daman akwai wanda ze soni domin Allah bansaniba, meyasa be faɗa min ba tun lokacin toh.”
“Bayan son ya rasaki sashi na shiyasa yaƙi faɗa miki, dan a wannan lokacin soyayyar mutum ɗaya kike ganewa da fahimta, a lokacin da ya kamata ya faɗa miki kuma, soyayyar gaba ɗaya ta fita daga ranki, wannan shine dalilin shi”.
“ Idan har zan baki shawara kiji ki ajiye komai a gefe, ki rungumi mijin ki da auren ki, don yana sonki”
“Insha Allah best”.
Ajiye wayar mukayi, daren gaba ɗaya ban rintsa ba ina ta saka da warwara.
********* ********** **********
Da asuba bashi ya tashe ni ba, da kaina na tashi.
Bayan nayi sallah direct kitchen na nufa, girki nayi mana, sannan na gyara gidan.
Wanka nayi na shirya, tunda nazo gidan ban taɓa saka kananun kaya ba, haka kawai nake jin yau ya kamata nasaka.
Riga da wando nasaka, jar riga da baƙin wando, nayi parking ɗin gashi na da jan ribon a tsakiya.
Sosai kayan suka haska ni.
Kallon kaina nake a mudubi anya zan iya fita a haka.
Dake wa nayi kawai na fito.
Har zan wuce na tsaya ina kallon Kofar ɗakin shi dan ban taba shiga ba.
Jikin kofar na matsa, ina son jin koya dawo daga training, jin shiru ne yasa na tura kofar na shiga.
Ɗakin tsaff da shi se kamshin freshner yake.
Banga abinda zan gyara ba, shiyasa na juya zan fita.
Zan murɗa handle ɗin ya riga ni.
Shanye duk wata fargaba ta, nayi nace masa “ Barka da safiya yayana! Katashi lafiya”
“Alhamdullah” yace yana zagaye ni ya wuce.
Tsai kawai nayi jin yanda ya amsa min, jiki babu ƙwari haka na nufi dining na zauna ina jiran shi.
Yakai 30 minutes kafin ya fito da shirin tafiya wajen aiki.
Ganin ze fita be karyaba yasa nayi masa magana.
“Ya doctor abinci fa ?”
“Alhamdullah” kawai yace yana ficewa daga gidan.
Shiru kawai nayi ina maida hawayena.
Ganin nima ba iya cin abincin zanyi ba, na koma ɗaki na kwanta.
Haka da yamma nayi girki sosai, na gyara gidan, nayi turaren wuta har a ɗakin shi, ban taɓa haɗa masa ruwan wanka ba, haka na haɗa masa da turaren wankana.
Sosai na zauna nayi kwalliya rabon danayi kwalliya ina ga tun lokacin biki.
Sosai nayi kyau se kamshi nake.
Parlor na dawo na zauna dan nasan, yana hanya, ban daɗe da zama ba naji shigowar motar sa.
Fuskar waya ta na duba naga fuskata daidai, ajiyar zuciya kawai na sauke, ina kallon Kofar shigowa parlor.
Be tunanin ganina a parlor ba.
Kallo ɗaya yamin ya ɗauke kanshi ya wuce.
“Sannu da zuwa ya doctor”
“Sannun ki”
Meyake shirin faruwa dani ne haka ? Bansaniba nabawa kaina amsa.
Kasa tashi nayi, naci gaba da zama a wajen, ina kallon ƙofar ɗakin shi.
Ina zaune ya fito da kananun kaya alamun yayi wanka.
Kitchen ya shiga ya fito da flet a hannun sa, ɗakin shi ya shiga be jima ba ya fito da leda a hannun sa, a ƙasa ya zauna ya juye abinci a take away.
Kasa jurewa nayi seda nayi masa magana.
Muryata na rawa sosai nace “ya doctor nayi maka abinci fa”
“Na riga na siyo ko baki gani ba ?”
Yanda yamin magana a dake ne yasa hawayen dana ke riƙewa suka zubo, ƙasa nayi da kaina ina kuka a hankali.
Be bi ta kaina ba, yaci abincin sa hankali kwance.
Tashi nayi na nufi ɗaki ina kuka.
Akwai ciwo sosai, kaga mutumin dabe taɓa shareka ba ya canza maka, gwanda yamin faɗa zan ɗauka amman bana juran shariya ko kaɗan raina baya so, shiyasa naji na ma sare tun yanzu.
Har dare ban fito ba ina ɗaki, kofa nake ta kallo ina jiran ya shigo, amman ko motsinshi ban ƙara ji ba.
********** ********* *********
Tun daga ranar ya doctor ya canza min, yanda nasan shi da fara’a banyi tunanin ya iya fushi haka ba, koda yake bazan ce fushi ba, idan na gaishe shi ze amsa min sama sama, daga haka baze ƙara cemin komai ba.
Duk kwalliyar da zanyi baze kalle ni ba, haka duk wahalar da zanyi wajen haɗa masa abinci baze ciba, babban abinda yake ƙona min rai a gabana ze juye abinsa a takeaway yaci, bayan nadafa masa.
Ɗakina kuwa tun ranar be ƙara shigarshi ba.
Tsawon sati biyu muna wannan zaman gaba ɗaya nagaji da zaman gidan, kukan ma nagaji da yin shi, gashi na kasa faɗa wa best.
Yau weekend baya fita aiki, kuma baya zuwa ko ina, ko ze fita se yamma, nagaji da wannan sharenin da yake dan haka na yankewa kaina hukunci wanda nake ganin shine daidai kawai.
Wanka nayi, nasaka doguwar riga, ko mai ban shafa ba, turare na fesa kawai, na fito dan tun ɗazu nake jin motsin sa a parlo.
Yana zaune yana danna waya yana shan fruit.
Kallo ɗaya yamin ya ɗauke kansa.
Bandamu ba na zuba a gaban sa kawai na fashe da kuka iya ƙarfina.
Ganin be tankamin ba, na ƙara karfin kukan.
Sosai mamaki ya bayyana a fuskarsa, hannun sa ya ɗora akan goshina.
“Baki da lafiya ne ?
Duk da halin danake ciki seda na zabga masa harara sannan naci gaba da kuka na.
Ɓoye fuskar sa yake dan baya son na gansa yana murmushi.
Ganin ze bar min parlon, na riƙe kafar sa naci gaba da kuka na.
“Ya rabb! Nayi miki wani abu ne sumayya ?”
Ai yanda kasan ya zage ni, wani sabon kukan na ƙara sakar masa.
Zama yayi sannan yaja hannuna nima muka zauna a kujera.
“Faɗamin meyafaru sumayya ?”
Idan yace min sumayyar nan ji nake kaman bakar magana yake faɗamin saboda, ba hakan yake kirana ba.
“ Dan Allah kayi hakuri!”
“ Kinyi min wani abu ne da kike bani haƙuri ?
Rasa mema zance masa nayi.
“Ayya yayana Allah bazan ƙara ba.
“Ah gaskiya baki da lafiya sumayya, yau kuma nine yayan ki ?
Ƙasa nayi da kaina wani hawayen nabin fuskata.
Nazo ina bashi hakuri amman se wulakanci yake min.
“ Dan Allah ya doctor!!!”
“Haƙurin me kike ta bani ?
“Komai ma Allah bazan kuma”
“Ni bansan hakurin me kike bani ba, amman na hakura dena wannan kukan”
Kallon sa nake ina marairaice fuska, dan gani nake kaman kawai faɗa yake.
“ Oh buzuwa wai ba kya gajiya da kuka ne?”
Ajiyar zuciya kawai na sauke na yadda ya haƙura koba duka ba.
“Zan fita amman bazan daɗe ba.”
“Dare yayi fa ya doctor”.
“Saƙo zan karbo ai.”
“Shikenan seka dawo Allah ya tsare”
Ameen
********* ********** *********
Jina nake sakayau koba komai mun shirya da ya doctor, amman zaman idan nace yana min daɗi nayi karya.
Wanka nayi na shirya cikin kayan bacci masu kyau, sosai nayi wa kaina ɓarin turare, parlo nadawo na zauna ina jiran shi.
Ina zaune ya shigo da leda a hannunsa, miƙa min yayi na karɓa batare dana san meye a ciki ba.
Ciki yayi ni kuma na buɗe ledar.
Ice cream nagani bansan sanda murmushi ya suɓcemin ba, “ngd sosai yayana” na faɗa da ƙarfi yanda ze jiyo ni.
Murmushi yayi kawai.
Sosai yayi mamakin chanzawar ta, beyi tunanin zata rusuna da wuri ba, amman shi ko ba komai hakan yayi masa.
Yafi ta jigata da nesanta kansa da yayi da ita, amman yana son dawo da ita hanya, kuma alhamdullah tunda hakan yayi aiki.
Sosai muka shirya da ya doctor, ze zauna muyi kallo, muci abinci tare amman baya shiga ɗaki na.
Hakan yana damuna amman narasa yazanyi in gyara kuskuren da nice na fara shi.
“Yar buzuwa zaki rakani unguwa?”
“Zani yayana” na faɗa cike da zumudi dan tunda akayi bikinmu ban fita ba.
“ Maza ki shirya toh”
Doguwar riga na saka nayi rolling.
“Mutafi ya doctor”
Ƙare min kallo yayi sama da ƙasa kaman baze yi magana ba se kuma yayi min.
“A haka zaki tafi ?
Kallon kaina nayi naga banga lefin shigata ba nace masa “eh”
“Idan har kina son fitar nan dole ki canza kayan nan.
Ina tura baki haka na koma na canza.
“Mutafi toh na canza”
“Da aure na akanki kike tunanin fita a haka wai ?”
“Allah ya doctor ni a haka zani, bazan canza kayan ba.”
Yanda ya nufo ni ranshi a ɓace ne ya bani tsoro naja baya.
“Kalli yanda rigar ta fitar da shatin jikinki fa”
Da idon sa ya nuna min kirjina.
Ya rabb wata iriyar kunya naji.
Igiyar dana ɗaure rigar ya saka hannu ya kuncen.
“ Toh mutafi”.
“Ayya ya doctor kalli fa nazama babba a rigar”
Beyi min magana ba yaja hannu na muka fita daga falon.
********* ********** **********
Wellcare mukaje yayi siyayya, komai guda biyu yake ɗiba yana rabawa a cikin basket, ganin ban ɗauki komai ba yamin magana.
“ Ki ɗauki duk abinda kike so.”
Kayan chocolate na ɗiba da biscuit bayan su ban ɗau komai ba se ice cream.
Bayan ya biya muka tafi gidan mamyn sa.
Hannu bibbiyu ta karɓe ni tamkar tasan da zuwa na.
Leda ɗaya ya ajiye mata acikin waɗan da ya siya.
Muna hira sama sama raihana ta dawo daga makaranta.
Ɗakin ta muka tafi muka ci gaba da hira.
Bamu daɗe mukayi mata sallama muka tafi.
Daganan gidan mamah muka nufa tun a hanya baki na yaƙi rufuwa.
Sosai yake kallo na yana tuƙi, gaba ɗaya ta canza kaman ba ita ba, yanzu murmushi baya mata wahala, kaman ba itace ta kasance cikin wani hali ba da duk wani me imani seya tausaya mata.
“Alhamdullah” ya furta a fili.
Kallon shi nayi yayi min murmushi.
Mayar masa nayi ina kallon hanya.
Banjira ya gama parking ba na buɗe motar na fice da sauri, ji nake kaman nayi gudu wallahi.
Ko sallama babu na faɗa gidan da gudu.
“Mamah! Mamah!! Mamah!!!
Gani kina ina?”
“ Wai ke bazaki yi hankali ba, yaushe zaki dena min kiran mafarauta ne ?
“Ayya mah farin ciki ganinki ne fa, amman kina min faɗa. Na fada ina tura baki.
“Ina angel ?
“Gata a baya na ta bani amsa tana hararata.”
Sallamar sa ce ta katse dramar mu da mah.
“Ahmad daman tare kuke ? Ke kam Allah ya nunamin ranar da zakiyi hankali.”
Murmushi nayi kawai.
Zama yayi suka gaisa kaman yanda suka saba.
Sannan suka ɗora da hira.
Jina nake kaman ina yawo a gajimare tsabar farin ciki.
Allah kabar min mamah, na faɗa a cikin raina.
Itama irin ledar da yabawa mamyn sa ya bata.
Sosai mama tayi farin ciki ganina musamman ganin yanda na canza, koba a faɗa ba duk wanda ya ganni yasan ina cikin koshin lafiya.
Da zamu tafi harda kukana, ni sena kwana, baran tafi ba.
Muna tafiya yana ta tsokanata.
Saida yaga dagaske ina masa kuka Sannan ya kyaleni.
Koda muka koma gida banyi mana girki ba dan bama tare da yunwa.
Wanka kawai nayi na dakko ice cream ɗina ina sha hankali kwance.
Armless ce a jikina da wando dukan sa gwiwa ta, ban damu ba na zauna a haka, ganin ko hannun sa ba kaishi jikina yake ba, koma duk kayan da zan saka ko a jikin sa.
Ina zaune ina shan ice cream ya fito daga ɗaki shima da pyjames a jikin sa.
Tunda ya zauna nake jin idanun sa a kaina, ƙin ɗagowa nayi, dan na manta rabon daya kalleni kaman haka.
Kusa dani ya dawo ya zauna.
Duk da gaba na ya faɗi ban nuna masa ba.
Gashina yake shafawa a hankali.
Kasa kasa yace “gashinan ba’a yi masa kitso ne buzuwa ta ?
“ Da zafi ya doctor nima na faɗa a hankali”
Robar ice cream ɗin ya ɗauke a hannuna ya juyo dani, banyi masa musu ba na juyo.
Kyakkyawar runguma yayi min, duk da ina jin wani iri banyi kokarin ƙwace wa ba, se hannaye na dana saka na zagaye shi, ina runtse idona.
Sosai yake sauke ajiyar zuciya..
Ɗago ni yayi daga jikin sa,