ICEN DAMUNA HAUSA NOVELS PDF BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Tknovels

Chapter   36 / 40

105K to 108K   out of 117.2K words

ta ni kuma na mata banza naƙi tankamata.

Kuka kawai nasaka mata ganin taƙi dena tsokana ta, dole ya haleepha ya mata magana Sannan ta ƙyaleni.

Muna zuwa gida muka tarar da yan ɗaukar amarya sunzo.

Hannuna a cikin nata har gaban mamah.

“Mah a saka mana albarka a cikin rayuwar auren da zamu fara” ta faɗa muna tsugunnawa a gaban ta.

Dafa kaina tayi sannan ta fara jeromin addu’o’ har bansan sanda na fashe da kuka ba.

Wajen baffa ta raka ni shima sosai yamin addu’a ya kuma yimin nasiha me ratsa zuciya.

Shida mahmah har suna haɗa baki wajen faɗin mun yafe miki duk wani abu da kikamana sumayya! Wanda muka sani dama wanda bamu sani ba, Allah yasa ki fara sabuwar rayuwa a Sa’a.

Fatan Alkhairi kala-kala nasha shi a wajen iyayena se fatan Allah ya amsa addu’o’insu gare ni..

Da ƙyar aka ɓanɓare ni daga jikin mamah, aka fitar dani daga gidan mu.



********** ********** *********

Daga gidan mu gidan iyayen ya Ahmad aka tafi dani, har muka je kuma kuka nake.

Bamu tsaya ko ina ba se a ɗakin mamyn sa.

A gaban ta ammie ta ajiye ni.

Bayan sun gama gaishe gaishe tace nidai ga yar nan na kawo miki dan bazan ce sirika ba, tunda mudai Ahmad ɗan mu.

Gata nan a saka mata albarka.

Murmushi tayi sannan ta kalli ammie tace!

“Daman tuntuni sumayya ai yatace albarka kullum cikin saka mata nake”

“Dan haka idan ma amana ce aka bani na karba hannu bibbiyu”

Sosai abun nasu ya burge mutane.

Bayan sun gama mamy da kanta ta kaini har cikin mota sannan ta koma cikin gida.

Daganan kuma muka nufi gida na dake rijiyar zaki ring road.

Ganinan dai yau an kawo ni gidan ya Ahmad, kowa ya tafi anbarni daga ni se hali na.

Ina zaune ina tunanin ko wace kalan rayuwa kuma zanyi a gidan ya Ahmad ? Ko wane irin zama zamuyi da shi ??

Jin hayaniya na fara yi na abokan ango sun shigo cikin gidan, gabana ne ya fara faɗuwa, sai naji abun wani iri, cuz auren baba Abbas da auren ya Khalil duk ba’ayi min wa’yannan abubuwan ba, sallamar da ake yi ne a falon ya katse minhttps://chat.whatsapp.com/KwLWS5ecBTt446RcWPdOF3?mode=wwt tunanina...........https://chat.whatsapp.com/KwLWS5ecBTt446RcWPdOF3?mode=wwt

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 33

Ji nayi ya Ahmad yana dakatar da abokan nasa a falo, yace ku jira anan ban yarda ku kallar min mata ba, yana fadar haka ya nufo cikin ɗakin ya barsu a falo suna masa tsiya, harda masu gori, bai kulasu ba ya shigo dakin da nake.

Jin motsin shigowarsa dakin yasa gabana ya tsananta faɗuwa, duk wata addu’a da tazo baki na karanta ta nake, idan har nace ba’a tsorace nake ba wallahi nayi ƙatuwar ƙarya.

Sai yanzu naji haushin tafiyarsu best, ni da kaina na amince ta tafi bayan ta lallabani yanzu kuma shigowarsa na fara jin tsoro tare da fatan dama ace tana kusa to tsorona zai zama da sauki.

Mayafi na sake ja na rufe kaina sosai, gabana yanata faduwa kamar ace ƙyatt! Na fita da gudu.

Ledojin hannunsa ya ajiye akan mirror sannan ya hawo gadon, ya kama mayafina yana kokarin budewa, na saka hannu na riƙe mayafin cike da tsoro.

Buzuwa! Bazaki taɓa canzawa ba, Allah ya shirya min ke ya faɗa yana shanye murmushin sa.

Toilet ya tashi ya shiga, ya jima a ciki sannan ya fito da lema a jikin sa, alamun alwala yayi.

“Tashi kiyi alwala zamuyi sallah”

A zuciya ta nake raya kawai ince masa periode nake, na buɗe baki da niyar faɗa masa, naga yana min kallon da yasa naji shakkar sa sosai a lokacin.

Mikewa nayi kawai na nufi toilet din, ina alwala ina kuka a haka na fito.

Be tankamin ba ya shinfida dadduma, bayansa na tsaya ya jamu sallah raka’a biyu, bayan munyi sallama, tambayoyi yamin sosai, kuma alhamdullah duk na bashi amsa, addu’o’ i yayi mana sosai sannan ya mike ya fita.

Wata wawuyar ajiyar zuciya ce ta kubcemin, dan jinake kaman akan ƙaya nake zaman mu waje ɗaya wallahi.

So nake na cire kayana, amman tsoro nake ji.

A hankali na tuno ranar da aka kaini gidan baba Abbas, kafin yazo har nasaka kayan bacci abuna, bayan rashin mutunci da na kafta masa.

Haka gidan khaleel tun a wajen da mukayi celebration, nayi watsi da kayan jiki na.

Astagfirullah na furta da sauri tuna cewar yanzu akwai igiyar wani a kaina.

Toh amman meyasa nake jin fargaba akan ya doctor ? Bansaniba nabawa kaina amsa.

Kwanciya nayi a haka da kayan a jiki na, amman alamun bacci babu su a idanuna.

Jin karar buɗe kofa na tashi zaune da sauri.

Ganin sa da kayan bacci, sosai na tsoro ta.

Yazo zama a gefen gadon kawai na sakar masa kuka.

“Jeki dakko plet muci abinci.”

Kaina na girgiza masa alamar ni na koshi.

Ƙasa na sauka na zauna a kasa ina rera kuka kaman wadda aka ce mata mamah ta mutu ko baffah.

Bansan ya zagayo inda nake ba seda naji ya rike min hannu.

Ƙarawa kukan nawa sauti nayi kawai.

Sosai yake kokarin rike ɓacin ran sa amman yaga alamun indai yarinyar nan ce seta kaishi bango.

“Na miki wani abu ne kike wannan kukan?”

Kaina na girgiza masa.

“Cire kayan ki ki kwanta”

Tabbas da yana kusa dani sosai da yaji yanda zuciya ta take bugawa da sauri.

Kuka nane ya karu har shiɗewa nake a yanzu, ajiyar zuciya kawai nake ja.

Tsamm ya mike ya nufi kofa ko juyowa beyi ba har ya fita ya bar ɗakin.

Memakon nadena kukan sena cigaba da abuna.

Kuka nake sosai bawai na kiyayyar sa bane a’a, ni nasan bandace da shi ba.

Bawai ina tsoron sa bane, amman ina tunanin tayaya yana saurayi ze aure ni, nida nayi aure har biyu, kafin nan wace kalar rayuwa ce banyi ba, gani nake auren shi danayi kawai na cutar da shi.

Baya na matsa na jingina a jikin gadon, har lokacin kuma hawaye nake gogewa wani nabin wani.

Bansan sanda bacci ya ɗauke ni a haka a zaune ba.

Kiran sallar farko ya tashi, alwala yayi, ze tafi masallaci, har ze wuce ɗakin yayi tunanin ya tashe ta tayi sallah.

Mamaki da takaici duk su suka rufe shi a lokaci ɗaya.

Wannan kwanciyar datayi dole ne ma ta tashi da ciwon wuya da jiki, tsabar taurin kai yabar mata dakin base ta kwanta ba, amman shine zata yi bacci a zaune.

Gefen gadon ya bubbuga.

Idona na fara buɗewa a hankali, yana tsugunne a gaba na da jallabiya.

Zan ɗago kaina naji wuya na ya rike yar siririyar ƙara nasaki ina ɗora hannuna a wuyan.

“Tashi kiyi sallah”

“Toh na faɗa ƙasa_ƙasa.”

Miƙewa yayi ya fita daga ɗakin.

Seda naga fitar sa sannan natashi da ƙyar ina jin jikina yana min ciwo, na nufi toilet.

Ruwan zafi na haɗa me zafi sosai nayi wanka, sannan nayi alwala na fito.

Wardrobe na buɗe ina kallon jerin kayan da akayi, doguwar riga na janyo nasaka, sannan nayi sallah.

Koda na idar rasa me ya kamata nayi a gidan nayi.

Ina zaune ya shigo ɗakin hannun sa da man zafi.

Miƙomin yayi na shafa. Marairaice fuska nayi ina kallon sa.

“Da zafi fa” na faɗa kaman zanyi kuka.

“Koki shafa kona shafa miki”

Da sauri na miƙa masa hannuna ya bani, ina shafa ina hararar gefe.

Kallon ta kawai yake yana ayyana wa a cikin ransa, indai baki ba ai ba buzuwa bace.

Ganin yanda yake kallona sena ji kunya, ƙasa nayi da kaina.

“Ina kwana katashi lafiya”?

“Bangansu ba ya faɗa yana nufar kofa.

Kaina na langwabar ina kallon sa har ya fita.

Tashi nayi na fito parlor seda naji idona ya ciko da kwalla, kofofin dana gani na tsaya kalla ina tunanin wacce ce ta kitchen, kofar datake kallon ɗakina na kalla, a jiki na naji yana cikin ɗakin.

Wacce take ɗayan barin, na murɗa handle na shiga, idona da hanci da baki duk nasaki ina kallon kayan, yanzu duk kayan kitchen ɗin nan ni kaɗai, fitowa nayi ina ƙara kallon parlon da ɗakina.

Gaskiya iyayena sunyi kokari sosai, ga aminiyar arziki, ga kuma yar ƙanwata humaira, ga iyayen ƙwarai, ammie da daddy, sannan ga ya haleepha.

Hakika bansan dame zan biya waɗan nan mutanen ba tarin alkhairan su gare Ni, sedai zan kasance meyi musu addu’a a duk inda na kasance.

Kitchen ɗin na dawo na dafa ruwan tea, ganin leda akan saman cabinet na ɗakko, kazar jiya ce danace banaci, waming ɗin ta nayi na juye a flask, akan dining naje na ɗora.

Sannan naje nayi wanka, tunanin nake tayi akan kayan daya kamata nasaka, tagumi na buga da hannu bibbiyu.

Best ce ta faɗomin a rai dan haka kawai na kirata.

“Hello sashi na! Wannan kira haka da asabar fari in tawo gashi ne?”

“Gashin me ?”

“Aikin da doctor yayi mana”

Tsaki kawai nayi, ban bata amsa ba.

“Kinga waɗan na kaya zan saka?”

“Kisaka leshi kaman zefi tun da bamusan ko zakiyi baƙi ba”

“Ke bazaki zo bane?”

“Gaskiya ba yanzu ba sashi na”

“Ina kika baro doctor ɗin?”

“Yana ɗakin daya kwana nima ina nawa”

“Sumayya!”

Kashe wayar nayi banjira cewar ta ba.

Yanda tace nayi haka nayi, sedai narasa ta yanda zan ɗaura dan kwalin danni ko a gida ba ɗaurawa nake ba.

Waya ta na ɗakko ina game, naji ya ya buɗe ƙofar dakin shi, nayi tunanin ɗakin ze shigo se kuma naji shiru.

Tashi nayi jin shiru yayi yawa na fito.

Yana dianing a zaune yana haɗa tea, jin fitowa ta yasaka shi ɗagowa yana kallo na.

Betaɓa ganinta babu dan kwali ba, yasan bata ɗaurawa daman, iya kacin ganin daya kewa gashinta gaba ne kawai amman beta ganin shi gaba ɗaya a waje ba se yanzu, tayi masa kyau sosai a hakan.

“Zonan yar buzuwa ta”

Bance masa komai ba na matso kusa da shi na tsaya.

“Zauna muyi breakfast”

“Na koshi ya doctor”.

“Me kika ci?”

Kaina na girgiza masa.

“Zauna toh”

Ban kara jan maganar ba, na zauna a kujerar kusa da shi.

Tea ɗin daya ya haɗa ya miƙo min, karɓa nayi ina sha a hankali, muna chartting da best duk da faɗa muke murmushi nake har bansan sanda ya gama ba.

Ban ma kula ya matso kusa dani ba, seda naji hannun sa akan gashi na.

Da sauri na ɗago ina kallon sa.

Ignoring ɗin kallon yayi, yaci gaba da shafa gashin.

Kasa daurewa nayi, na ɗora hannuna akan nasa zan cire.

Haɗawa yayi har hannun nawa ya rike yana shafa.

Ƙasa;ƙasa yace “ina son gashin nan buzuwa”

Miƙewa kawai nayi zan bar wajen, ya janyoni ya rungume.

Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, nidai sumayya nice a kwance a ƙirjin ya doctor.

Kokawar ƙwatar kaina na fara amman na kasa, rungumar daya min bata wasa bace, dazan iya kwace wa.

Wuyana yake shinshinawa da gashi na yana dauke min numfashi.

“Ya doctor dan Allah ka bari! Ya Ahmad dan Allah!!” Na faɗa murya ta na rawa sosai, alamun kuka ze iya kwace min a kowa ne lokaci.

Ganin yanda yake neman haɗe baki na dana shi, kawai na haɗe kaina da kirjin shi, na zagaye sa da hannaye na, da ƙarfi sosai, dan bani da wani zaɓi daya wuce nayi hakan.

Beyi tunanin hakan ba shiyasa abu yazo masa a bazata.

Jin ya sassauta riƙon daya min, na kwace kaina da sauri na nufi ɗaki cikin sauri har ina haɗawa da gudu.

Numfashi kawai nake maida wa kaman wadda tayi tsere, gaba ɗaya na haɗa gumi kaman wadda tayiwa sarki ƙarya.

Anya zan iya hada ido da shi, ko ada chan ina mugun jin kunyar shi bare yanzu.

Innallilahi kawai nace ina kwanciya.

Kuka nake a kwance da tunanin narasa ta yanda zan karbe sa a matsayin miji na, kowa yana cewa yana sona, amman ni har yanzu banganiba.

Bansan sanda bacci ya ɗauke ni ba.

Se wajen daya na tashi daga baccin, wanka nayi da alwala, nasaka doguwar riga mara nauyi, sallah nayi, na nufi kitchen dan yunwa nake ji.

Simple girki nayi, kaɗan naci, na ajiye masa nashi a dining, na shige daki.

Gaba ɗaya zaman ya ishe ni, yanzun ba’a zuwan gidan amarya washe garin kaita, sedai kaita zama daga kai se mijin a gida.



******** *********** **********

Da Daddare nayi wanka, nasaka kayan bacci na kwanta, bacci nake ji sosai saboda haka ina kwanciya bacci ya ɗaukeni na manta batare da na rufe dakin ba.

Ina bacci naji kamar a mafarki mutum ya hawo gadon, ina bude na ganshi a gefena, miƙewa nayi zaune ina kallon sa, sauka nayi daga kan gadon ta ɗaya bangaren.

Tsamm yayi yana kallona, sai kuma ya tashi ya fice daga dakin bai ce komai ba.

Washe gari ma haka mukayi da shi, tsawon sati biyu indai ze shigo ɗakina, duk sena birkice.

Zan masa girki na ajiye masa, amman indai ze matso kusa dani, yanzu zan nemi na birkice masa, dole shima ya haƙura ya ƙyale ni.

Har ya koma wajen aiki wasan ɓuya muke da shi a cikin gidan.

Duk yanda nake son na cire komai a raina na kasa, har yanzu ina ganin banyi masa adalci ba, dana aureshi, domin be dace dani ba.

********** ********** *********

Kaman a cikin bacci naji ana shafa fuska ta, a firgice na bude idona na tashi zaune.

Janyoni yayi ya rungumeni, duk yanda naso ƙwacewa na kasa.

Yaune rana ta farko daya nunamin shiɗin namiji ne, wannan kokawar danake da shi bazata hanasa abinda yayi niyya ba.

Jin abinda yake min ne yasa na fashe da kuka sosai.

Be fasa ba ya cigaba, kuka nake sosai har shiɗewa nake, baƙin ciki na yanda nakasa kwatar kaina, jin yanda nake jan ajiyar zuciya ne yasakashi dakatawa.

Idanun sa da sukayi jajir ya zubamin yana kallo na, kasa kallon sa nayi, nayi ƙasa da kaina, ina goge hawaye na.

Ni kikewa wanna kukan dan na taɓaki buzuwa ? Duk ƙiyayyar da kike min ne yasa kike wannan kukan har kina neman shiɗewa?

So nake na buɗe baki na, nace masa Ni ban tsaneshi ba amman na kasa.

Sautin kukan kawai na ƙara.

Kinsan wani abu ? Bejira amsata ba ya ɗora.



“Daga ranar dana ganki na fara son ki! Tunda nake ban taɓa son kowa ce mace ba se akan ki! Kinsan yanda na dinga azabtuwa da soyayyarki kuwa ? Kina da imani kuwa ? Baki da tausayi ko kaɗan buzuwa!!!!

Ɗagowa nayi da sauri ina kallon sa.

Ban taɓa saka idona a cikin nashi ba se a lokacin.

Gaskiyar abinda ya faɗa nake son tabbatarwa.

“ Nashiga jikinki, duk dan nasamu soyayyarki”

“Nayi ta bibiyar ki har zuwa lokacin dakika fara sakewa dani, a lokacin ji nake nafi kowa farin ciki, kullum naje gida sena bawa mamyna labarin ki”

“ Lokaci ɗaya naji bana bukatar ganin ki, a damuwa nafara tunanin tayaya zan san matsalanki, har na magance miki ita, kwatsam kika bani labarin ki.

“Babban tashin hankali na, a lokacin dana san cewa matar aure nake so”

“Labarin ki, da duk wani abu da kika aikata be bani damar tsanar ki ba, sema tausayin ki da soyayyar ki data ƙaru a raina.”

“Babban tashin hankali na ganin ki, kina kuka akan wannan gayen, zuciya ta sosai take min zafi da raɗaɗi, amman hakan nake shanyewa.”

“A lokacin da kika tare a gidan Alhaji Abbas, bansan

36 / 40