ICEN DAMUNA HAUSA NOVELS PDF BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Tknovels

Chapter   25 / 40

72K to 75K   out of 117.2K words

komawa bacci ba bayan tayi sallah dan lokacin baifi karfe shida ba, ya haneep kuwa yana masallaci ma bai dawo ba.

Tsaki tayi ta jawo wayar ta ɗora a kunne batare da ta duba waye me kiran ba, cikin magagin bacci tace “Hello!

Shiru taji anyi, sai kuma take jin kamar kuka daga ɗaya bangaren, bude ido tayi tana fatan Allah yasa ba wani ne ya mutu ba, tunanin duba wayar taga me kiranta ma batayi ba!.

“Hello waye yake magana!

“Best!!!!!!

Ko daga baccin mutuwa taji wannan sunan da kuma Muryar bazata manta me ita ba, da sauri ta duba fuskar wayar taga waye me kiranta! SASHENA ta gani sunan radau a fuskar wayar, marin kanta tayi dan ta tabbatar da ba mafarkin da ta saba bane.

“Tabbas ba mafarki bane! Ta fada a bayyane.

Ba mafarki bane best sashenki ce take kiranki, Sumayya ta fada tana me rushewa da kuka.

Wani irin kuka best ta fashe dashi “ina kika shiga ? Ina kika saka wayarki ? Meyesa ba’a samunki ? Meyesa zakiyi mana haka ? Ko zakiyi fushi da kowa ai bazakiyi damu ba! Kina ina yanzu ? Haka ta dinga jero tambayoyi batare da ta jira an bata amsa ba.

Ina Lagos yanzu, ki tura min kuɗin dawowa yanzu da kuma wasu rarar kuɗin.

“Nooo ki fada min inda kike zamu zo nida ya haneep mu taho dake.

Saida na tambayi address a wajen wata nurse sannan na fada mata.

To dan Allah ki bar wayarki a kunne zan hadaki da mama yanzu zani gidanta.

Ina ajiye waya ta kira haneep tace yayi sauri yazo gida.

Ba shiri ya baro masallaci, yana zuwa ta bashi labari da jallabiya a jikinsa ya dauketa suka tafi gidan mama lokacin.

Ko kofa ba’a bude ba suka kwankwasa, mama Saida gabanta ya fadi tace to wannan lafiya ? Lokacin tana ƙoƙarin haɗa wuta “waye ? Ta tambaya tana kokarin tasowa, a lokacin ma bappa ya fito daga daki jin kwankwasa kofa.

Mama nice! Best ta fada.

Da sauri mama ta bude kofa tana tambayar lafiya kuwa ?

Haki best take yi kamar wata wacce tayi gudu.

Kamata tayi suka karasa cikin gidan, haneep ya biyosu, sai a lokacin mama ta ganshi, tambaya mama take lafiya, amma best ta kasa magana.

“Sumayya ce ta kirata a waya da safennan yanzu tana so zata dawo gida a tura mata kudin mota, da alama addu’arki ta karbu mama, shine ita kuma halima take ta wannan hakin saboda farin ciki, yanzu ma haka ta kwatanta inda za’a sameta, to in Sha Allah nida best zamu bi Flight din yamma zamu je mu taho da ita!! Ya haneep ne yake wannan dogon bayanin.

Zubewa mama tayi a kasa tana hawayen farin ciki, sai kuma tayi sujjada ga Allah, yanzu Sumayyata ce ta kiraku ? Kai alhamdulillah!!

Kiran Sumayya best ta sake yi, ringing biyu ta daga, tana ɗagawa ta mikawa mama, Muryar Sumayya ce tayi mata tsinke a kunne ta hanyar yi mata sallama.

Kuka mama take tace sumayya!!!

Nan kuma sai kuka, sumayya na kuka itama na kuka.

Ki gafarceni mamah! Bazan sake bijirewa umarninki ba in Sha Allah. Kiyi hakuri ki bawa bappa hakuri shima.

Shhhh!!! Bakiyi komai ba, mun gafarta miki har bappan naki ko bappan yara ? Mama ta fada tana kallon bappa da tun dazu yake tsaye bai ce komai ba.

Ƙwalla ce a Idonsa kai kawai ya gyadawa mama.

Nan fa hira ta barke gida ya ɗauki hira har bappa aka bawa waya yayi magana da sumayya, humairah da angel duk sun tashi dan a lokacin da best tazo suna bacci.

Likita ne yazo zagaye dole SUMAYYA tayi sallama ta ajiye wayar, su best kuma suka tafi gida shiri.

Suna fita mama ta mikawa humairah waya akan ta kirawo mata ya Ahmad, ba shiri ta labarta masa komai, yayi farin ciki matuka.

********** ********** *********

Bayan na ajiye waya kuka nayi ta yi, lallashin duniya naki shiru, nadama ce nake yi me tarin yawa, tare da jin kunyar family Dina da kowa ma, saboda yanda suka dage akan kar naje Lagos gashi gashi, amma nayi kunnen uwar shegu.

Yanzu gashi duniya da kuma soyayyar da na zaba sun koya min darasi mai wuyar koya.

Bacci ne ya daukeni ban sani ba, ashe a allurar da likita yayi min akwai ta bacci.

A daren ranar su best suka ƙaraso, lokacin ina bacci still, best zama tayi tana ta kallona kamar tayi kuka saboda yanda na rame na ɗashe, gaba daya kamar ba Sumayya ba.

Sai Wajen sha biyu na dare na farka, lokacin ya haneep ya tafi masauki, ita kuma best tana zaune tare dani, kafin ya wuce saida ya fara nemo mn abunda zanci idan na farka.

Ina farkawa naga best a kusa dani, rufe idon na sake yi na sake budewa, saidai still itace a zaune a gabana tana kallona ta toshe bakinta tana son hana sautin kukanta fitowa.

Tashi nayi zaune na rungumeta sai sabon kuka, kuka kawai muke muna rike da juna, saidai muka sha kuka muka koshi sannan na lura da baby a kwance a gefena tana bacci! Kallon best nayi mai nuna alamun tambaya, gyaɗa min kai kawai take ba magana.

Ɗaukar babyn nayi na rungume, sai hawaye, a lokacin kewar Marigayin babyna ya fado min, kuka biyu nake, na kewar rashinsa da kuma na farin cikin ganin dan best.

Wata sabuwar hirar ce ta balle, nan ne best ta bani labarin cewa babyn ai sunana aka saka mata, farin ciki kamar nayiwa best sujjada, Nima haka na kwashe labarin duk abinda ya faru tun zuwana Lagos har zuwa yanzu, ba abinda na boye mata, ya Khalil yasha zagi, tsinuwa, jafa’i, bala’i, da komai ma ya shasu, ban tanka mata ba duk abinda take cewa, dan Ni kadai nasan me nake ji akan khalil.

********** ********* **********

Da safe ya haneep ya kara siyo mana kayan kari muka karya, Maman Uche ce tazo dubani kamar yanda ta saba, saidai ganina da baki yas tayi turus.

Gabatar mata dasu nayi suma n gabatar mata da su, mun jima anata hira mukayi sallama da maman Uche saboda da yamma zamu wuce gaba daya, kudi na karba a hannun best mai yawa na bata tare da yi mata godiya, sannan na karbi lambarta wacce zan iya samunta.

******** ******** ********** Karfe biyar jirginmu ya tashi sai Kano, zo kaga farin ciki, zo kaga kuka a wajen mama dani da sauran yan gidan, ya Ahmad ma yazo saidai ba magana sai kallon juna, sai hawaye, yau har bappa Saida yayi hawaye, fadar irin farin cikin da ake yi yau a gidanmu kai kasan fada bata baki ne.

Tun ina ɗari-ɗari har Saida na dan saki jikina, ganin ba wanda ya tayar min da magana, a daren yau na bawa gidan labarin zaman aurena komai da komai ban ɓoye ba, nan ma dai kukan akayi, sannan Khalil ya sake shan tsinuwa, a gidanmu yau best ta kwana, kwanan hira muka yi yau, hira ba kama kafar yaro.

“Daddare ina kwance mama ta kawo min abinci, sedai duk yanda naso naci abincin na kasa ci.

Damuwa dan kare a cikin raina, nakasa yarda da abun da khaleel yamin, har yanzu ina mamaki.

Kalaman sa, suna min ciwo a duk lokacin dana tunasu, gashi duk daren duniya se sunzo kaina.

A yanzu idan akwai wata kalma da natsana a duniya ita ce kalmar soyayya.

Soyayya gaba daya karya ce, tunda har masoyi ze iya cutar masoyin sa, tabbas soyayya karya ce.

Bana bukatar namiji a tare dani a yanzu.

Rayuwa ta kawai zan gyara da gobe na.

Amman yanzu babu lissafin namiji a tare dani.

********* ********* **********

Wata kalan rayuwa nake tamkar dai bani ba, na koyi miskilanci ta karfi da yaji.

Ko da yaushe ina zaune shiru dani, bani da aiki se tunani.

A duk lokacin da zan tuno irin rayuwar da nayi kuwa sedai kawai naita zubar da hawaye.

Tabbas khaleel ya cutar dani cutar mafi muni a duniya.

Duk yanda nake tunanin dame na karu a rayuwa da khaleel ban samu komai, se tarin baƙin ciki.

Ya cimin mutunci yaciwa iyaye na, kuma na kasa komai a kai.

“Duk yanda mama take jana ajiki na kasa sakewa da ita.

Saboda gani nake gaba daya ban cancanci wannan kulawar datake bani ba.

Tsakani na da baffa kuwa, kadaran kadaham.

Yau a kalla nayi wata biyu a gida, a madadin na fara maida jiki na, sema wata sabuwar ramar da nakeyi.

Mama tayi rarrashin har ta gaji.

Da zan iya nima da na cire komai a raina kodan kwanciyar hankalin mama.

Amman ina nakasa, kullum ji nake tamkar a lokacin komai yake faruwa dani.



********** ********** *********

Tun da na tashi ina kwance, abin duniya duk ya dameni.

Ko shayin da mama ta kawo min na kasa sha.

Har wajen 12 ina kwance.

Sallamar sace tasa na tashi zaune amman ban fito ba, ina jin sa suna gaisawa da mama.

Sosai mama tayi masa godiya kuma tasaka masa albarka.

Bakomai fa mama ita ɗin ai kanwata ce.

Idona kawai na lumshe ina jin yanda ya kara samun matsayi a cikin zuciya ta.

Sumayya!

MaMah!

Bakiji yayan ki bane?

Gani nan ai.

Ina zuwa wajen mama ta tashi.

Zama kawai nayi nakasa ce masa komai kaina a kasa.

Buzuwa!!!

Uhm ya doctor.

Meyake damun ki? Wani waje na miki ciwo ne.

Kirjina na nuna masa, zafi yake min ya doctor! Ciwo yake min sosai! Bana iya bacci ya Ahmad! Inajin tamkar na mutu nabar wannan duniyar, nagaji da rayuwar gaba daya.

Rayuwa ta bata da amfani.

Kuka nake tamkar raina ze fita ina dafe da kirjina..

Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un!!! Kawai yake maimaita wa.

Shikenan ya isa haka dan Allah kiyi shiru.

Kaman yace na kara sautin kuka na, kawai na kara fashewa da kuka.

Ɗagowa yayi zemin magana yaga mama a tsaye tana hawaye.

Mama zamu je asibiti na dubata.

Se kun dawo!

Tashi muje.

Tashi kawai nayi nabi bayan sa, muka nufi motar sa.

Har mukaje asibitin kuka nake.

Ya isa haka mana, kiyi shiru dan Allah.

Nakasa tsaida kukan.

Gaba ɗaya na birkita mishi tinani har besan sanda ya daka min tsawa ba.

Malama nace kiyi min shiru, ya kike so nayi ne a’a! Wani ya aike ki ne? Sanda ake hana ki maganar wa kikaji?

Wallahi kar na kara jin kukan ki a wajen nan!!

Tsitt na shanye kukan se ajiyar zuciya da nake ta saukewa, gaba daya ya bani tsoro, bansan ya iya faɗa har haka ba.

Kan kujera kawai ya zauna ya lumshe idon sa.

Munfi minti 30 a haka.

Sumayya!! Ya kira sunana a hankali.

Kumburarrun idanuwana kawai na ɗago na zuba masa.

Zonan! Ya nuna min kusa da shi.

Ban zauna anan ba, sena zauna a kasa wajen kafar sa.

Fadamin meyafaru.

Ganin bani da niyar magana.

Shima se ya sakko Kasan ya zauna.

Fushi kikayi saboda na miki faɗa?

Kaina na girgiza masa.

Kiyi hakuri banasan kukan kine ɗagamin hankali yake shiyasa.

Nan na kaina na gyada masa.

Fadamin toh meyafaru.

“A hankali na bude bakina na fara bashi labarn rayuwar aurena gaba daya.

Ya Ahmad idan na tuna kalaman sa a kaina zuciya ta bugawa take da karfi fiye da tunanin ka.

Jinake tamkar zuciya ta zata fashe!

Ke har kina da bakin kiran wata mara tarbiyya?

Ai duk wani mara tarbiyya a bayan ki yake sumayya! Ba gwanda ita tana jin maganar iyayen taba, kome suka hanata tana ji.

Kefa.? Baki dauki iyayen ki a bakin komai ba! Tunda gashi kin zabi namiji akan su! I

Haka kuma kin zaɓi namiji akan aminiyar ki!!!

Kuka ne ya sarke ni nakasa ci gaba da magana.

Ya Ahmad duk abinda ya fadamin gaskiya ne dan aikata hakan.

Amman ai nayi komai ne saboda shi, saboda ina sonsa, amman ya min gori da kansa ya Ahmad.

Meye amfanin rayuwa ta a yanzu? Rayuwata bata da amfani, na...

Waye yace miki rayuwar ki bata da amfani? Kuma waye yace miki lokaci ya kure miki? Karki kuma faɗar haka.

Insha Allah zaki rayuwar farin ciki sumayya!!

Yana gama faɗar haka ya shige toilet yabarni a zaune ina kallon sa.

“ Tabbas da za’a bashi dama ace ya kashe wani a duniya babu abinda ze hana shi kashe wannan banzan mutumin.

Amman bakomai, komai lokaci.

Yanzu lokaci yayi sumayya, lokaci yayi da zaki fuskan ci gaskiya, kukan ki yazo karshe insha Allah.

Wanke fuskar sa yayi sannan ya fito, ruwa ya dakko min na sanyi ya bani, har lokacin kuma kuka nake.

Ɗauki ki sha.

Ruwan na rike amman nakasa kai shi baki na.

Ji yake tamkar ya rungume ta ya rarrashe ta, amman baze iya ba.

Tashi mutafi gida.

Mikewa kawai nayi nabi bayan sa.

Mama yace yana son magana da ita dan haka, nabasu waje na tafi na kwanta.

******** ********* *********

Baffan su dan Allah ina son magana da kai idan babu damuwa.

Gaba daya hankalin sa ya bata, ina jinki yar buzuwa ta.

Murmushi tayi kawai.

Daman akan sumayya ne, ta faɗa kaman me ɗar ɗar.

Har lokacin da murmushi a fuskar shi, yace meyasa Meta?

Daman akan halin da take ciki ne, dazun Ahmad yazo, kuma yayi magana da ita.

Ya nuna yanada kyau Sumayya ta samu canjin waje yanda zata samu sakewa da farin ciki.

Babu damuwa gobe da kaina zan kaita gidan haleemahn, hakan yayi miki?

Godiya ta fara masa.

Akan ɗiyar mu kike min godiya kuma?

Makaranta kuma nama siya mata foam na islamiyya zata fara zuwa insha Allah.

Nima ina sane da ita ai, muci gaba da yi mata addu’a insha Allah komai se wuce tamkar be faru ba.

Wani irin farin ciki ne ya lullube mama jin furucin baffa hakan yana nufin baya fushi da sumayya yanzun.

Godiya ta masa sosai ta bayyana masa yanda tayi farin ciki da maganar sa.



******** ********* **********

Da safe ina kwance baffa ya shigo da sallama.

Tashi nayi ina gaishesa.

Ki shirya zamu unguwa.

Toh baffa.

Wanka kawai nayi na dakko kaya na saka, dan yanzu ni ba kwalliya nake ba.

Muna hanya yana ta min hira kaman dai, ba wannan baffan nawa, damuke kasance cikin faɗa ko yaushe ba.

Koda mukaje gidan best be shiga ba, yace naje na mata hutu.

Sosai naji daɗi da yace na mata hutu, kenan Bama yau zan koma gida ba.

Assalamu alaikum.

Parlow ba kowa, kawai nasamu waje na zauna.

Dan bansan ko mijin ta yana nan ba.

Kwanciya nayi akan kujera har bansan sanda bacci ya ɗauke niba.

Sakkowar ta kenan ta ga mace a kwance akan kujera taba bacci.

Hijab din jikina ne ya nuna mata tabbas nice, sannan kuma da yanayin kwanciyata da har yanzu ban canja ba.

Fuskata take leke ina bacci, murmushi tayi kawai tasata a gaba kaman tasamu tv.

Kwanciya ta na gyara, kawai naga yanda take kallo na, lafiya Madam?

Yaushe kika zo, ?

“kinacan kina bacci mana,

Ina little ?

Bata tashi ba.

Break fast ta haɗa, sedai duk yanda taso na shiga cikin su na kasa.

Gaba ɗaya jina nake a takure.

Gida zan tafi best! Wallahi baki isa ba, ai kin riga kince hutu baffa yace kiyi min.

Shiru kawai nayi mata.

Bayan ta sallami haneep ya fita, muka zauna dakin ta.

Hira muka dora kamar yau muka hadu da juna rabin hirar best tana tsinewa Khalil, yayinda Ni kuwa kuka da takaici yafi yawa a labarin nawa.

Can best tace yanzu me zamu fara ?

Zan koma makaranta.

Shine dai abun danake tunani kawai.

Hakan ma yayi Allah ya shiga cikin al’amurran ki.

Ameen.

Hira muka cigaba da yi.

Tayaya rayuwata zata dawo daidai ????? Shine tunanin da yafi tsaya min a rai

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata

25 / 40