ICEN DAMUNA HAUSA NOVELS PDF BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Tknovels

Chapter   31 / 40

90K to 93K   out of 117.2K words

/>
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 29

Doctor ta taɓa cewa bata sonka ne ?

Kana da tabbacin shi wanda zaka aura matan ze rike ta amana ?

Karki damu insha Allah.

Bazan juri rasa girman da ta bani ba a barshi a haka kawai, ngd sosai da kulawa.

Gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi, ta rasa ta ya zata bullowa lamarin!! Dole ba dan ta so ba ajiye wayar.

********* ********** **********

Nikam ina nan hankali na kwance ganin baffa be ƙara min magana ba.

Shikam ya doctor nasan daman wasa yake min, wane mara tunanin ne ma ze aure ni ? Ai babu shi a wannan duniyar dai.



“ Bansan wace wainar ake toyawa ba, har seda baffa yazo ya kirani.

Ahmad yazo min da wanda kika tsayar sumayya!

Dum dum dum dum haka zuciya ta take bugawa.

Kaina yana ƙasa nakasa ɗagowa.

Yace min a cikin sati biyu yake so ayi komai, kuma nima na amince, ina fatan hakan yayi miki?

Da kyar na saita murya ta, duk yanda kayi ai daidai ne baffa.

Allah yayi miki albarka tashi kije.

Wallahi seda nayi da kyar na mike.

Ina tafiya ina haɗa hanya.

Best na kira na sakar mata kukan dana rikewa.

Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un!!

Menene kuma ?

Wai aure baffa da ya Ahmad zasu min nan da sati biyu!

Mtssss shine me toh, ba daman kun gama magana ba ?

Na ɗauka da wasa yake ai.

Toh yanzu ma fito na fito zaki dasu kenan ?

Ko a mafarki bana tunanin haka best, kawai dai inajin tsoron kar abinda ya faru dani ya kara maimaita kansa.

Ki kwantar da hankalin ki khairan insha Allah kinji sashina.

A sanya ba amsa mata da “to Shikenan!

********* ********** *********

A daren sega kiran ya Ahmad kaman bazan ɗaga ba se kuma nayi picking.

Murya a can ciki nace “Hello!

Shiru yamin bece komai ba.

Jin shirun yayi yawa yasa na sake cewa “Barka da dare ya doctor!

Kina lafiya? Ya amsa min a kasan makoshi.

Alhamdullah.

Saida yayi jimm sannan yace, kunyi magana da bappa ?

Eh!

Yawwa zezo gobe ku gaisa.

Da kyar nace Tom.

Allah ya sanya Alkhairi.

Tsawon lokaci babu wanda ya ƙara magana a cikin mu.

Ya Ahmad!

Uhm... meyafaru?

Babu komai.

Shikenan seda safe.

Washe gari sukuku na tashi dani, kaman bani da lafiya.

Kusa da mama naje na zauna.

Meyafaru sumayya ?

Babu komai mah.

Jiya baffan ku yamin bayani.

Ina fatan bazaki bawa Ahmad kunya ba, ta haka ne kawai zaki biya sa tarin alkhairan sa gare ki.

Insha Allah mamah.

Kisaki ranki kinji, kici gaba da addu’a.

Toh mah!

Daddare na shirya karbar bakona.

Wani iri nake jina, yau shine rana ta farko da zanyi zance da saurayi a kofar gidan mu.

Khaleel bai taba zuwa gidanmu ba, sedai ni na bishi.

Tuna hakan kawai yasa na nemi ɗan farin ciki dana fara samu na rasa.

A haka na fita jikina duk a sanyaye.

Bayan mun gaisa, nayi ƙasa da kaina.

Sosai yake kallo na, bashi da wani muni amman ko kaɗan be burgeni ba.

Gaskiya duk yanda doctor ya bayyana min ke, kinfi kyau a fili.

Yanzu sauran sati biyu biki, nidai ɗaurin aure kawai zanyi amman bansan koke kina da wani shiri ba?

Nima bani da wani shiri hakan yayi.

Masha Allah.

Na matsu na tafi gida, amman shi kuma se zuba yake kaman kanya.

Daze tafi ya ɗakko kuɗi ya bani, juyin duniya naƙi karɓa haka ya hakura ya kyale ni.



********** ********** *********

Anata shirin biki dan ma ba taro za’ayi ba, atoh auren bazawara wane shiri za’ayi.

Best tazo ta lallaɓa mama zamu tafi gidan ta har zuwa lokacin biki.

Da muka fito nayi tunanin gidan ta zamu wuce amman naga mun nufi kasuwa.

Sosai tayi siyayya sannan muka wuce gidan ta.



Ina shirin bacci ta shigo, tashi sashi na.

Meye kuma Malama ?

Gyaran jiki zamu fara ai.

Kallon mahaukaciya kawai na tsaya ina mata, toh mahaukaciya mana, idan ba bata da hankali ba Ni za’ayi wa gyaran jiki.

Tsaki nayi kawai na juya mata baya.

Wallahi sekin tashi, ta faɗa tana shirin miƙar dani.

Kinsan Allah kika dame ni gida zan tafiyata da safe.

Wallahi sashi na, kome zakiyi se anyi gyaran nan, shiyasa ma na dakko ki dan ni zan miki ciki da waje ma.

Toh sannu uwa ta!

Faɗa sosai muke nace bana so, ita kuma ta dage lallai setayi min.

A hankali rayuwarmu ta fara dawo min, ni taurin kai, ita kuma kafiya.

Bansan sanda na fara dariya ba, dariya nake sosai wadda rabon da nayi irin ta har na manta.

Dan Allah best kiyi hakuri na faɗa ina dariya.

Allah bazan kyale ki ba sashina!

Shikenan naji mayya, na faɗa ina hararar ta, amman har lokacin da dariya a muryata.

A hake ake gyaran jikin kullum se munyi faɗa, ga wasu magunguna data ke ɗura min, nida kaina naga sauyi a jiki na, gaba ɗaya jiki na ya ciko sosai, fata tayi shar abunta.

Sosai gyaran jikin yake karɓar fata ta da jiki na.

Kodan wannan karon babu damuwar komai a raina, nayi shar dani, kaman dai ba wannan sumayyar ba.

Ana sauran kwana uku ɗaurin aure na koma gida.

Sosai mama yaji dadin yanda taga na koma.

Ni kaina burgeni abun yake sosai.

Gida ya fara karɓar baƙi, duk da ba wani taro za’ayi ba.

Ana gobe ɗaurin aure, ango yazo waje na.

Bansan meyasa ba haka naji gabana yana faɗuwa.

Wannan shine zuwan sa na 5 ina ga waje na, amman banta ba jin hakan ba se yau.

Koda na gaishesa be amsa min ba se tambayar daya jefo min.

Dagaske ne kin kai saurayinki gidan tsohon mijinki?

Da bala’in sauri na ɗago kaina ina kallon sa.

Tambayar ki nake ?

Eh! Nabasa amsa jikina yana rawa.

Kuma kin bi maza kafin kiyi aure ?

Eh! Shima na basa amsa ina ƙoƙarin ɓoye tashin hankali na.

Meya rabo ki toh daga gidan saurayin naki ?

Wannan tambaya ce da bazan iya basa amsar taba shiyasa bance masa komai.

Ganin naki yin magana kawai ya juya ya tafi.

Idona na lumshe ina karanta duk addu’ar data zo baki na.

Wannan shine abinda nake gudu, wannan shine abinda nake jin tsoro tun asali.

Ninasan yanzu babu wani namiji daze aure Ni.

Kobe cemin komai Ni ai ba mahaukaciya nace tambayar sa tabani amsa.

Yaya su mama zasuji.

Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un!!!

Allah na tuba Allah, Allah ka sassauta min.

Da ƙyar na kai kaina cikin gida, ɗakin mu na shige na kwanta, gaba ɗaya jikina na rufe har kaina ina wani irin kuka, kuka nake da dukkanin zuciya ta, tabbas khaleel yamin illa sosai a cikin rayuwa ta, amman ba komai a kwai Allah, har akayi kiran sallar farko idona biyu, ban rintsa ba.

Da ƙyar na tashi nayi sallah na koma na kwanta.

Ina jin yanda su mamah suke ta gaganiyar ɗora abincin ɗaurin aure.

Sashina! Ke na ganki a kwance lafiya kuwa ?

Ganin ban motsa ba, da sauri ta matso ta yaye abun rufar tawa, jin yanda jikina take rawa ne ya fara ɗaga mata hankali, tana kawo hannunta jikina ta ɗauke baki da lafiya daman ?

A hankali na juyo na zuba mata idona da yake cike da zafin zazzaɓi.

Tun yaushe ne baki da lafiya ? Bara na kawo miki magani. Ta fada tana juyawa zata bar dakin.

Hannun ta na janyo.

Batayi musu ba ta zauna kusa dani, tashi nayi da sauran kwarin jikin daya rage min, kaina na ɗora akan kafadar ta kawai na fara hawaye.

Duk yanda taso na faɗa mata meyafaru na kasa, itama kukan ta fara ba tare da tasan meyasaka ni kukan ba.

A haka mama ta shigo ta same mu, lafiyar ki kuwa ? Akan me zaku zauna kuna mana kuka, ko gidan makoki ne nan ?

Mamah nima samunta nayi tana kuka, best ce ta bawa mamah amsa cikin kuka.

Kuma shine zaki biye mata.

Meyafaru sumayya? Kaina kawai na nuna mata.

Sannu ku tashi ku shirya, lokacin ɗaurin auren ya kusa, haleemah ki bata magani ta sha.

Toh mah!

So nake nawa best bayani amman bansan ya zata ɗauki zancen ba shiyasa na kasa.

A haka na lallaba nayi wanka na shirya, itama ta shirya.

Wajen sha ɗaya saura na fara jin hayani sama_sama a cikin gidan mu, can kuma na fara jin kuka.

A hankali na furta ta faru ta ƙare, na dafe kaina dayake jujjuya mini.

Da gudu ta shigo ɗakin.

Sashina! Ganin yanda na riƙe kaina da duka hannuwa na se hankalin ta ya ƙara tashi.

Kinji me wannan mutumin ya mana kenan ? Yarasa inda zece ya fasa aurenki se a wajen ɗaurin aure ?

Zata fara bala’i na riƙe hannun ta.

Ina murmushin da yafi kuka ciwo nace mata!

“Meye ne abin damuwa best? Abinda nayi ne yake bibiya ta, wannan shine dalilin da ya saka nace na haƙura da aure a rayuwata, ki sani babu wani namiji daze iya aure na a halin yanzu.

Da sauri ta rufe min baki, zaki auru sashi na, kuma zaki rayuwar farin ciki insha Allah.

Murmushi kawai na ƙara sakar mata, ina ɗago kaina muka haɗa ido da mama, idon ta yayi jajir.

Duk yanda naso miƙewa naje gare ta na kasa saboda jirin danake gani.

Humaira kuka, best kuka, mamah kuka.

Nama rasa me zanyi a lokacin, dan ni na nemi kukan na rasa a cikin idanuna.

Ga shi kowa ya baza ido da kunne yaga zamu kare.

Baffa ne ya shigo ɗakin, hakan yasa duk suka rage sautin kukan su.

Ni nasan yau idan baffa ya fara duka na babu ne ƙwatata a hannun sa.

Baya na fara ja a hankali jiki na, yana rawa, dan wallahi gaba ɗaya jiki na ya bani duka na zeyi.

Dena ja baya sumayya!

Kina a wannan halin mezan miki.

Kiyi hakuri kinji Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawar.

Allah ya musanya miki da wanda ya fishi.

Gaba ɗaya amin suka haɗa baki wajen amsawa.

Juyawa yayi ya kalli yan biki ya basu hakuri yace taro ya tashi, kowa yayi hakuri ya koma gida.

Kowa haka ɗibi gulmar sa ya kara gaba.

********** ********** *********

Tsoron Allah ya ƙara kamani a halin yanzu, meyayi min saura babu shi a halin yanzu, yan uwa da yan unguwa kowa yasan mena aikata, tayaya yanzu zan iya fita waje, Bama zan soma ba.

Gidan muma a halin yanzu alwala da wankane kawai yake fito dani.

Rabon danaci abinci har na manta.

Wata irin rayuwa nake nidai ganinan nan kawai.

Yaya doctor bansan adadin test nawa ya min na neman yafiya ta ba.

Haka bansan sau nawa yana zuwa bawa su mama haƙuri ba.

Nikam ban rike sa a raina ba, ko kaɗan.

Best kusan koda yaushe haneep seya kawo ta gidan mu.

Sedai har yanzu abinda ya maƙale min a wuya na ya kasa wuce wa.

Yau ki manin wata biyu da fasa biki na, kuma tsawon lokacin nan ko ƙofar gidan mu ban leƙa ba daga gida se gida.

Jin waya ta tun ɗazu tana ringing ne yasaka na ɗauka.

*YAYANA*

Hello ya doctor ina wuni na faɗa cikin sanyin muryar daya zamemin jiki.

Kina lafiya buzuwa ?

Idona na lumshe kawai a yanzu shi kaɗai ne me kira na da sunan nan, kuma indai ya faɗa sena tuna da abubuwa da yawa sosai a cikin a raina.

Uhmmmnm Alhamdullah!

Masha Allah.

Anjima zan zo muyi magana dan Allah?

Saida nayi jimm sannan nace “Tohm seka zo.



********** ********** *********

Daddare yazo.

Waya yamin yace na fito.

Da ‘toh na amsa sannan na kashe wayar.

Ina sako ƙafa ta waje na koma da sauri.

Tayaya ma zan iya fitowa bayan kowa a halin yanzu kallona yake, baze yuyu ba.

Tsawon wani lokaci zaki ɗauka kina ɓoye fuskar ki buzuwa ? Kifito waje muyi magana! Ya Ahmad ya fada yayin da yaga na fito na koma.

“Bazan iya ba ya doctor kunyar kowa nake ji.

In har kin ɗaukeni yaya dagaske ina son ki fito buzuwa!

Babu yanda na iya haka na fito ina ta ɓoye fuskata, a cikin hijabi.

Gaba ɗaya na kasa sakewa gani nake kaman kowa kallo na yake yana nunani.

Buzuwa! Buzuwa!!

Idona daya gama cika da hawaye na ɗago na zuba masa.

Ganin ta a haka baya masa daɗi, koda cewa be san ta a lokacin datake ainayin sumayya ba yasanta a cikin labarin ta.

Yana son dawo mata da farin cikin ta, tabbas taga rayuwa, taga darasi da jarabawa a cikin rayuwar ta.

Insha Allah shine ze zama sanadiyar tsayawar hawayen ta.

Ina so ki bani hankalin ki sumayya, kuma ina son kiyiwa magana ta kyakkyawar fahimta.

Bansan meyasa naji gaba na yana faɗuwa daga jin yanda yake min magana ba.

In har akan abinda ya faru ne ya huce ya doctor, wallahi ban riƙe ka a raina ba.

Bayan wannan kuma......

Da sauri na ƙara katse sa ya doctor komai ya wuce da gaske nake ma.

Bara naje gida mah na jira na.

Haka na wuce kaman wadda ake turawa.

Zama nayi kusa da mamah ina ta maida numfashi.

Ke kuma lafiya ?

Bance mata komai ba na tashi na shige ɗaki kawai.

Bansan me zece min ba amman haka kawai naji ina tsoron kalmar dazata fito daga bakin sa.



********* ********** *********

Idon sa kawai ya lumshe, ya gaji! Ya gaji da dakon soyayyar nan, ya gaji da ganinta cikin damuwa ya zama dole ya kawo karshen komai.

Be san tsawon lokacin daya dauka a wajen ba har baffa ya dawo daga unguwa.

Ahmad! Ahmad!! Seda baffa ya taɓa sa sannan ya ɗago kan sa ya kalle sa.

Ƙasa yayi da kansa yana gaishe sa, be amsa ba se tambayar daya jefa masa meyafaru Ahmad tunanin me kake haka ?

Babu komai baffa.

Hannun sa ya riƙe muje ka faɗa min damuwar ka kaji ahmadidi.

Duk da halin dayake ciki seda yayi murmushi.

Gidan suka shiga Ni kuwa ina cikin daki banji shigowarsu ba, daki ya jashi suka shiga suka zauna “Fadamin meyake damun ka kaji Ahmad.

Shawara yake tayi da zuciyar sa akan ya faɗa ko kada ya faɗa?

Toh amman a haka zeta zama ne?

Baffa dan Allah alfarma nake nema a wajen ka ina haɗa ka da girman Allah kada kace min a’a!!!

Faɗi kome kake so indai ina da shi insha Allah zan baka Ahmad.

Se da ya dau tsawon lokaci kafin yayi ƙasa da kansa.

BAPPAH SUMAYYA NAKE SON KA TAIMAKA KA BANI AURE DAN ALLAH!!!

BAPPAH NAYI MAKA ALKAWARIN RIKETA DA AMANA, DAN WLH INA SONTA SOSAI.

Jinjina kai bappa yake cike da mamaki, Saida ya nisa sannan yace “Sumayya kuma Ahmad ?

Kansa kawai ya jinjina masa.

Shikenan Ina zuwa kaji.

Fitowa yayi tsakar gida yana ƙwalawa mama kira “maman yara!

Da sauri ta fito daga kitchen tana tunanin ko lafiya ? Bappa ne ya ce ta shigo dakinsa, binsa tayi tana mamaki.



Lafiya? Ta tambaye su tana rarraba idanunta.

Lafiya zauna.

Batayi musu ba ta zauna.

“Ahmad ne ya zomin da wani zance nace bara nakira ki.

Toh meyafaru? Ta kara tambayar sa cike da zaƙuwa.

“ Duk yanda sukayi da doctor ya faɗa mata.

31 / 40