Author : Rabiat Fulani Category : Tknovels
Zonan! Ya nuna min kusa da shi.
Ban zauna anan ba, sena zauna a kasa wajen kafar sa.
Fadamin meyafaru.
Ganin bani da niyar magana.
Shima se ya sakko Kasan ya zauna.
Fushi kikayi saboda na miki faɗa?
Kaina na girgiza masa.
Kiyi hakuri banasan kukan kine ɗagamin hankali yake shiyasa.
Nan na kaina na gyada masa.
Fadamin toh meyafaru.
“A hankali na bude bakina na fara bashi labarn rayuwar aurena gaba daya.
Ya Ahmad idan na tuna kalaman sa a kaina zuciya ta bugawa take da karfi fiye da tunanin ka.
Jinake tamkar zuciya ta zata fashe!
Ke har kina da bakin kiran wata mara tarbiyya?
Ai duk wani mara tarbiyya a bayan ki yake sumayya! Ba gwanda ita tana jin maganar iyayen taba, kome suka hanata tana ji.
Kefa.? Baki dauki iyayen ki a bakin komai ba! Tunda gashi kin zabi namiji akan su! I
Haka kuma kin zaɓi namiji akan aminiyar ki!!!
Kuka ne ya sarke ni nakasa ci gaba da magana.
Ya Ahmad duk abinda ya fadamin gaskiya ne dan aikata hakan.
Amman ai nayi komai ne saboda shi, saboda ina sonsa, amman ya min gori da kansa ya Ahmad.
Meye amfanin rayuwa ta a yanzu? Rayuwata bata da amfani, na...
Waye yace miki rayuwar ki bata da amfani? Kuma waye yace miki lokaci ya kure miki? Karki kuma faɗar haka.
Insha Allah zaki rayuwar farin ciki sumayya!!
Yana gama faɗar haka ya shige toilet yabarni a zaune ina kallon sa.
“ Tabbas da za’a bashi dama ace ya kashe wani a duniya babu abinda ze hana shi kashe wannan banzan mutumin.
Amman bakomai, komai lokaci.
Yanzu lokaci yayi sumayya, lokaci yayi da zaki fuskan ci gaskiya, kukan ki yazo karshe insha Allah.
Wanke fuskar sa yayi sannan ya fito, ruwa ya dakko min na sanyi ya bani, har lokacin kuma kuka nake.
Ɗauki ki sha.
Ruwan na rike amman nakasa kai shi baki na.
Ji yake tamkar ya rungume ta ya rarrashe ta, amman baze iya ba.
Tashi mutafi gida.
Mikewa kawai nayi nabi bayan sa.
Mama yace yana son magana da ita dan haka, nabasu waje na tafi na kwanta.
******** ********* *********
Baffan su dan Allah ina son magana da kai idan babu damuwa.
Gaba daya hankalin sa ya bata, ina jinki yar buzuwa ta.
Murmushi tayi kawai.
Daman akan sumayya ne, ta faɗa kaman me ɗar ɗar.
Har lokacin da murmushi a fuskar shi, yace meyasa Meta?
Daman akan halin da take ciki ne, dazun Ahmad yazo, kuma yayi magana da ita.
Ya nuna yanada kyau Sumayya ta samu canjin waje yanda zata samu sakewa da farin ciki.
Babu damuwa gobe da kaina zan kaita gidan haleemahn, hakan yayi miki?
Godiya ta fara masa.
Akan ɗiyar mu kike min godiya kuma?
Makaranta kuma nama siya mata foam na islamiyya zata fara zuwa insha Allah.
Nima ina sane da ita ai, muci gaba da yi mata addu’a insha Allah komai se wuce tamkar be faru ba.
Wani irin farin ciki ne ya lullube mama jin furucin baffa hakan yana nufin baya fushi da sumayya yanzun.
Godiya ta masa sosai ta bayyana masa yanda tayi farin ciki da maganar sa.
******** ********* **********
Da safe ina kwance baffa ya shigo da sallama.
Tashi nayi ina gaishesa.
Ki shirya zamu unguwa.
Toh baffa.
Wanka kawai nayi na dakko kaya na saka, dan yanzu ni ba kwalliya nake ba.
Muna hanya yana ta min hira kaman dai, ba wannan baffan nawa, damuke kasance cikin faɗa ko yaushe ba.
Koda mukaje gidan best be shiga ba, yace naje na mata hutu.
Sosai naji daɗi da yace na mata hutu, kenan Bama yau zan koma gida ba.
Assalamu alaikum.
Parlow ba kowa, kawai nasamu waje na zauna.
Dan bansan ko mijin ta yana nan ba.
Kwanciya nayi akan kujera har bansan sanda bacci ya ɗauke niba.
Sakkowar ta kenan ta ga mace a kwance akan kujera taba bacci.
Hijab din jikina ne ya nuna mata tabbas nice, sannan kuma da yanayin kwanciyata da har yanzu ban canja ba.
Fuskata take leke ina bacci, murmushi tayi kawai tasata a gaba kaman tasamu tv.
Kwanciya ta na gyara, kawai naga yanda take kallo na, lafiya Madam?
Yaushe kika zo, ?
“kinacan kina bacci mana,
Ina little ?
Bata tashi ba.
Break fast ta haɗa, sedai duk yanda taso na shiga cikin su na kasa.
Gaba ɗaya jina nake a takure.
Gida zan tafi best! Wallahi baki isa ba, ai kin riga kince hutu baffa yace kiyi min.
Shiru kawai nayi mata.
Bayan ta sallami haneep ya fita, muka zauna dakin ta.
Hira muka dora kamar yau muka hadu da juna rabin hirar best tana tsinewa Khalil, yayinda Ni kuwa kuka da takaici yafi yawa a labarin nawa.
Can best tace yanzu me zamu fara ?
Zan koma makaranta.
Shine dai abun danake tunani kawai.
Hakan ma yayi Allah ya shiga cikin al’amurran ki.
Ameen.
Hira muka cigaba da yi.
Tayaya rayuwata zata dawo daidai ????? Shine tunanin da yafi tsaya min a rai
Ayi hakuri yau da late up
Ayi hakuri yau da late up
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 27
Zamana a gidan best, zan iya cewa kaso 40 a cikin damuwa ta, ta ragu sosai.
Bata barina na zauna ni kadai, ko yaushe muna tare, dataga nayi shiru zata zauna tana tuno min duk rayuwar mu ta baya.
Haneep kansa hakuri kawai yayi yabar mu tare, gaba daya ya hakura da kwana tare da ita, tare muke kwana da ita da little.
Naji dadin zaman gidan sosai.
Lokacin da zan koma gida senaji tamkar kar natafi, a haka mukayi sallama cike da kewa da kuma begen junan mu.
A ranar dana koma gida, baffa yabani foam na cike na makaranta.
Da yamma na cewa mama ta kiramin ya Ahmad.
Tana fara ringing ya daga.
Yana ganin kiran yaji a jikin sa itace.
Hello yayana.
Uhm ykk ? Alhamdullah.
Daman, daman
Daman me? Bakomai ma. Ina faɗan hakan na kashe wayar.
Jujjuya wayar hannun sa yake, yasan haka kawai bazata kira shi ba dole seda dalili.
Office dinsa kawai ya rufe ya tawo gidan su.
Bayan sun gama gaisawa da mama yace mata yunwa yake ji.
Abinci ta kawo masa ya zauna yaci abincin sa hankali kwance.
Mamah dan Allah zan bata sako a mota.
Kai da kanwar ka.
Murmushi kawai yayi.
Zama mukayi acikin motar sa.
Meyasa kika kirani?
Babu komai.
Buzuwa!
Lumshe idona kawai nayi, na manta rabon da wani ya kira ni da wannan sunan gaba ɗaya.
Yar buzuwa magana nake fa.
Murmushi ne ya subuce min ban shirya ba, jin yanda yayi maganar.
Oya fadamin meyafaru kinji yar kanwata.
Makaranta zan fara zuwa, kuma kawai na hau kame kame.
Shikenam toh tunda bazaki iya fadamin ba, tafi gida.
Ka gaida umma da suhailat.
Zasuji.
“ Bansan meyasa nake jin kunyar sa ba, yanzu wallahi.
Mai da sabulu nake so irin wanda ya taba kawomin saboda tabon jiki na, amman narasa ta yanda zan faɗa masa.
Da daddare ina zaune naga humaira nata kwalliya.
Bandai ce mata komai ba, har ta gama.
Waya aka mata ta mike zata fita.
Ina zaki ? na tambayeta ina kallonta.
Sallama ake dani a waje!
Sosai nake kallon ta, zance fa ? Ah lallai yan matan mama ta girma ashe se aure.
Dariya kawai tayi ta fice.
Acikin raina nake mata addu’a, Allah ya tsare ta.
Washe gari da yamma, sega ya Ahmad a gidan mu, banma san zezo gidan ba.
Yanda nake a haka na fito ban saka komai ba.
Jakar hannun sa ya miƙomin , ga wannan na rubuta miki komai a jiki, ni zan wuce.
Sallama yayi wa mama sannan ya juya ya tafi.
Buɗe jakar nayi wani murmushi ne ya subuce min, ina fito da kayan ciki, mayuka ne da shower gel da sabulu, se wadan su magunguna.
Kotaya ya gane abin da nake so?
Banyi sati biyu ina amfani da abubuwan ba jiki na yafara dawowa daidai.
Koda baffa yayi maganar makaranta mama ce tace ya dan kara mana lokaci.
Yau ina zaune ya Ahmad yazo wajen mama, bansan ya sukayi da shiba, kawai tace natashi na shirya na bishi.
Toh kawai nace ina tunanin ina kuma zamu je.
Sosai nayi mamaki ganin unguwar da na zauna muka nufa tare da shi.
Kallon sa nake amman yayi tamkar be san ina kallon saba.
A kofar gida na, muka tsaya.
Bansan meyasa naji wata matsananciyar fargaba ta rufe niba.
Banason ki fara sabuwar rayuwa da hakkin kowa akanki, kin nemi yafiyar Kowa banda shi, dan haka shima ya kamata ki nemi yafiyar sa.
Kaina kawai na gyada masa.
Sannan ya fita a motar, knocking be jima a tsaye ba aka bude.
Nidai naga yana magana amman bansan dawa yake Maganar ba, se kuma ya nufo motar.
Sakko muje.
Kunya nake ji fa.
Ganin ba fuskan yi masa rigima kawai na fito.
Har cikin gidan muka shiga da sallama.
Wata ce ta amsa mana, sannan tace mu shiga.
Yace ku jirasa yanzu ze fito.
Ina jin sallamar sa nayi kasa da kaina, wata matsananciyar kunyarsa ce ta rufe ni.
Tamkar babu abinda ya faru yace sumayya babu magana.
Kasa kawai na sakko na haɗe hannaye na, kaina a kasa na fara magana a hankali.
Bani da bakin da zan baka hakuri akan duk abubuwan dana aikata maka, amman dan Allah kayi hakuri ka yafemin, Allah yasaka maka fiye ma da yanda ni na kuntata maka, dan Allah ba danni ba.
Ya isa haka sumayya, dan adam baya tsallake wa ƙaddarar sa, na yafe miki duniya da lahira.
Amman zan iya baki shawara ?
Kaina kawai na gyada masa.
Ki kula kodan gaba, su iyaye duk abinda suka nuna basa so, ka hakura da shi yafi maka Alkhairi.
Yanzu kalli yanda kika koma, da kinwa iyayen ki biyayya da duk haka ne faru dake ba.
Bawai ina faɗa miki haka dan baki zauna dani ba a’a ina faɗa miki dan ɗa na kowa ne.
Allah ya kiyaye gaba yasa hakan ya zamar miki darasi anan gaba.
Sosai ya Ahmad yayi masa godiya, nima namasa godiya.
Matar sa ya kara kira muka kara gaisawa sannan muka yi masa sallama muka wuce.
Ko a mota nasiha yaci gaba damin sosai kuma nasihar ta shi ta shiga jiki na.
A kofar gida ya saukeni sannan ya wuce ko gidan be shigaba.
Koda na shiga, tun kafin mana ta tambaye ni na faɗa mata duk yanda mukayi.
********* ********* *********
Lafiya kalau na fara zuwa islamiyya, bani da matsala kodan nasaka wa raina karatun zanyi ne bansani ba amman sosai nake gane karatun.
Bana kula kowa a ajin mu, abinda ya kaini shi kawai nake yi.
Duk yanda mutum yake son shiga jiki na, baya samun fuska.
Musamman da ajin mu ya kasance akwai maza, sosai na kara kame kaina.
Dan Allah yana gani na tsani duk wani namiji a rayuwa ta, dan gani nake duk halin su daya babu wani banbanci.
Sosai nake karatu na, dan hadda ma nake, koyaushe da Kur’ani a hannuna ko kuma chasbaha.
Ba wani sakewa nake a gidan muba dan haka bansan meyake faruwa ba.
Shiri naga mama tanayi, kayan snacks da sauran abubuwa, baffan mu be fita kasuwa ba, kuma naga yan uwan sa wasu ma sunzo.
Sedai nakasa tambayar meyake faruwa.
Wajen karfe uku na yamma sega best.
Da ihu ta shigo gidan kaman mahaukaciya Allah yasa little bata hannun ta.
Amarya! Amarya!! Kina ina ?
Da mamaki na fito ina kallon ta, yau kuma haukan nata tanan ya biyo kenan ? Ko wace amarya kuma oho mata.
Mama ta rike tana rawa, har lokacin ina tsaye a gefe ina kallon su, murmushi kawai nakeyi, hannuna ta janyo amman nakasa biye mata muyi kaman yanda muka saba.
Wai mama ina Amaryar ne ? batanan.
Se lokacin nayi magana waike wacece amarya ?
Mtssss ke baki da hankali matsala ta dake kaman ya wacece amarya kuma sashi na.
Wallahi bansaniba dagaske fa.
Bakisan yau aka saka ranar auren humairah da yaya haleepha ???
Gaba daya nama kasa magana, narasa tacewa.
Wanne ya haleepha ? na tambayeta gaba ɗaya idona a waje.
Mtssss!!!
Mamah amman shine baki fadamin ba, nayi Maganar kaman zan samata kuka.
Toh kin maida kanki matar kulle ya kike so na miki, kullum kina ɗaki, magana wannan bazaki ba, ya kike ayi dake toh ?
Amman mama base ki fadamin ba.
Dallah nizo muje mu tattauna.
Hannuna taja muka shige daki muka zauna.
Wai yaushe zaki dawo rayuwar ki kaman da ne sashina ?
Babu rana best! Na fada kamar nayi kuka.
Dafani tayi “Meyasa ?
Saboda ni kaɗai nasan ya nake ji a cikin zuciya ta.
Tunaninsa kike yi ne ?
Meze saka nayi tunanin sa best ?
Kawai dai zuciya ko yaushe tana min zafi akan abubuwan dana aikata.
Ki godewa Allah sashi na, kin tuba batare da lokaci ya ƙure miki ba, sannan iyayen ki sun yafe miki, kuma kince min doctor ya kaiki gidan baba Abbas, toh kinga zuwa yanzu ya kamata ace kin manta da komai da komai.
Yanzu ya kamata ki tsaya ki fuskanci gaba, Nidai gaskiya ina son sumayya ta dawo! Ina son ganin buzuwa a tare dake sashi na, amman gaskiya bana son wannan sumayyar.
Yanzu burina, kema kiyi auren ki, ki......
Aure ????? na katse ta da sauri kamar wacce ta kirawo min mutuwa.
Nida shi ai munyi hannun riga, yayi gabas nayi yamma, na fada ina kau da kai.
Baki da hankali amman ko ? Ta tambaya tana hararata.
Yanzu nidai fadamin yaushe yaya haleepha ya fara soyayya da humaira ? duk matan duniya se wannan yar yarinyar ze aura ? Na fada ina tabe baki.
Dallah to kina bakin ciki ne ?
Ganin yanda take hararata tana kumbura fuska ne yasani dariya.
Natuba kanwar ango yayar amarya.
Yawwa me dame zamuyi da biki, wata uku kacal fa a kasa ka.
Babu abinda zanyi nidai Allah ya sanya Alkhairi kawai na fada da murmushi a fuskata.
Hmmm!!!! Kawai tace min.
Ya makarantar ? Ta fada tare da kau da maganar.
Alhamdullah karatun na mini daɗi sosai.
Hira muka ci gaba da yi, duk da rabin hiran akan bikin ne.
“Zan iya cewa Alhamdullah dan duk tabon jiki na ya fita, sedai tabon da yake a zuciya yana nan babu inda yaje, shima jiki na ya fara dawowa, dan haka babu abinda zan cewa Allah sedai godiya.
Ta ɓangare daya karatuna ya fara nisa, dan daman can da karatuna sedai shiririta kawai.
Ga shirye-shirye bikin humaira nata matsowa, shiri ake babu kama hannun yaro.
Gyaran jiki sosai ake mata a gida.
Har yau bandena mamakin wai ya haleepha ne ze aure taba.
Sosai yanzu muke shiri da baffa tamkar wani abu bata faruwa na rashin jituwa a tsakanin mu ba.
Yau haka kawai naji