Author : Zahra Muhammad Surbajo Category : Arewa Pen
ko ke sekin tausaya masa kuma itama tanasonshi,amman ganin mijin marik'iyartane yasa tak'i amincewa wlh dukansu suna cikin wani hali abin a tausaya musu,dan cewa tayi inde tarasashi to ita da aure har abada shine take neman shawara".
Ajiyar zuciya Khairat tayi sannan ta shafo kan Yasmeen tace.
"Wannan ba abin tada hankaline ba inde akwai fahimta ita da marik'iyartata tanasonta tsakani da Allah inaga bazata damuba dan hakan takasance, duba da cewa bazataso taga yarinyar batayi aureba kamar yadda tayi ikirari,inaga ta amince kawai inde marik'iyar nasonta tsakani da Allah bazata hanaba sede zataji zafi amman ba kamar akawo mata bareba wannan shine kawai".
Murmushi Yasmeen tayi bayan ta kashe recording d'in datasa tad'au muryar Khairat sanda take bata amsa sannan tace.
"Wlh bahaushe yayi gaskiya dayace aykin me shawara baya b'aci,da saura kad'an ta guntulawa kanta,wajan hana zuciyarta abinda takeso, Kai wallahi zama da Manya masu zurfin tunani,masu sowa d'an uwansu abinda suke sowa kansu da dad'i mungode Aunty da shawara kuma insha Allahu zan fad'a mata wannan shawarar,mukwana lfy".ta mik'e da gudu tabar d'akin tana dariya.
Khairat itama dariyar tayi aranta tace,
"kai Yasmeen wlh akwai hankali bata abu kai tsaye seta nemi shawara Allah de yay mata zab'i da miji nagari".
Yasmeen ko tunda ta koma d'akinsu inbanda dariya ba abinda takeyi, Iman har haushi taji dan ta d'auka ita takewa dariyar akan ba'a je da ita shan ice cream ba.
WhatsApp Yasmeen tahau tana chatting da k'awayenta cike da farinciki da annashuwa.
muje zuwa readers
Maman Yusuf.
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
📓📓📓📓📓📓📓📓📓
*CIN AMANA KO FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓📓
Zahra Muhammad mahmud
*Some People Have Nice Eyes, Some Have a Nice Smile & Some of Them Have a Nice Face But Yoy Have All of Them Inclluding a nice Heart.INNAH IBRAHIM KIME.*
*page 47-48*
Washe gari da safe dukansu sukayi breakfast,a tare Hydar se mamakin irin wani kallo da Yasmeen take watso mishi yake, kallone dake nuna tsantsar soyayya.
Yanason magana da ita Amman ba hali tunda yau weekend ne yana gida kuma tare da Khairat,dan haka fakar idon su yayi ya Kara hannunshi a kunne,Yasmeen na kallonshi alamar tabashi number wayarta.
Ho Yasmeen!!!halinki seke.
Tunda ta fahinceshi ay kawai setayi murmushi ta waiga gurin Khairat tace.
"Aunty don Allah d'an karantomin number na naga kamar kin rik'e, ni wlh ban rik'eba gashi wanine zanturamawa yadameni da tambaya yanzu haka gashi nan online,kuma kinsan number danake whatsApp bada ita nake receiving calls ba".
"Lalle Yasmeen yanzu number nakine baki rik'eba? sannunki da shiririta, niko ko daga bacci kika tasheni zan karantomiki numbar ki danna rik'e"daganan tafara karanto number Hydar yana rubutawa batare da Khairat ta ganeba tana gamawa Yasmeen tace.
"Yeeeeh thanks my sweet three in one,you are perfect that's why you deserve a perfect surprise when the time comes".
Duka Khairat takaimata tace.
"Niko na k'osa naji wannan sabon sunan nawa na ukun, dannasan dole zeyi dad'i tunda my sweet two in one ce tasaminshi".
Fuska Yasmeen ta b'ata tace.
"Kai Aunty don Allah taya zaki cemin two in one? wlh nima three in one ce a gurinki,ranar dazan sanar dake d'ayan sunan naki kema seki zab'i wanda yadace kisamin, amman gaskiya niba two in one bace a gurinki ba".
Sosai Khairat taji dad'in kalaman Yasmeen,rungumeta tayi tace.
"Wlh Sis bansan irin sonda nake mikiba komai naki burgeni yakeyi wlh, Allah de yahad'aki da miji na gari daze rik'eminke amana".
"Aunty na kenan ay wlh nafi sonki,sabida kinga nide yarinyace ko?to wlh bazan tab'a yarda Inga Daddy yashigo da wata bare a matsayin kishiyar muba, dan in yamiki kishiya ni yayiwa dole mutashi mud'au mataki, shiyasa ma Nafad'i a gabansa dagamu bak'ari inde ya amince to muma mun amince".
"Wlh Sis tunda muke baki tab'a farantamin rai irinna yauba,gaskiya nayarda da soyayyarki gareni tunda har bakyason ayimin kishiya gaskiya nagode".
Hydar zan iya cewa kusan suman zaune yayi dan abinna Yasmeen yafi k'arfin tunanin shi,cikin hikima tana magana dashi amman Khairat bata ganeba,se shid'in data.keyi dashi shine yaganen,dank'ari lalle akwai bala'i a gidanshi, sede addu'ar Allah ya yayyafa mishi ruwan sanyi.
gyara murya yayi sannan yace.
"Lalle ma mutanennan wato abin y'ar son kaice?,ina laifinma kuce kun yarda na k'aro wata a wajen bayan ku, Amman seku rik'eni ku kad'ai gaskiya bakuyi adalciba".
Yasmeen turo baki gaba tayi sannan tace.
"wlh muddin bayanmu kana tunanin k'ara wata to wlh kadena danmu aka yika kamar yadda kaima dankai aka yimu, koya kikace Auntyna?"ta waiga tana kallon Khairat wacce ta d'auki zancan Yasmeen a matsayin irin wasan da akeyi tsakanin miji da k'anwar matarsa cike da farinciki tace.
"wannan zance naki gaskiyane my Sister".
"To inde hakane yazama wajibi kudage da nunamin so da k'auna kamar yadda nima nake nuna muku,ma'ana kurik'eni amana inde kukamin haka to Hydar nakune ku kad'ai dan lokaci, yayi da zan shida muku kune zab'ina dana jima ina nema yau gashi kun tabbatarmin da hakan, gaskiya innace banji dad'iba nayi k'arya, nagode sosai wlh Allah yabarmu tare yasa mucinye duk wani k'alubale dazamu fuskanta".
Da sauri Yasmeen tace,"Ameen Ameen".
Oh my God jama'a kuna ina sunmaida Khairat banza.
A gabanta suna musayar magana amman bata ganeba, Dan k'arshema da gudu taje ta rungume Hydar dan ita zatonta da ita yake wannan dad'ad'an maganganu shima rungumeta yayi ya Kalli Yasmeen yace.
"Wannan shine fatana wata rana"yana nuna mata yadda Khairat ta rungumeshi.
Kunyace ta kama Yasmeen da gudu tabar gurin ita da Iman wacce tun d'azu dariya kawai takeyi.
Khairat ranar wani tattalin Hydar takeyi da bashi kulawa jin yace daga ita ba k'ari, itako dama ba abinda ta tsana irin kishiya, Tunda ko yace baze mataba itako bataga abinda bazata iya yimasa ba don ta faranta masa.
Hydar besamu damar kiran Yasmeen ba seda yafita masallaci, bayan an idar da sallah ya tsaya a garden d'in gidan yakirata a waya,bugu biyu ta d'auka cikin muryarta me kwantar da hankali tace.
"Ran hydara na yadad'e,karkayi mamaki, sanin zaka kira shiyasa na kama suna dannasan kaid'inne".
Murmushi Hydar yayi sannan yace.
"Such amazing My heart,d'azu kin rikitani wlh, wai dagaske kin amince dani to be your husband kode wasa kikemin?".
"Bana wasa da abu me muhimmanci kamarka tunda nace na amince I mean it babu wani wasa aciki".
Nande infad'amuku, suka kwashi soyayarsu me dad'in saurare, dan basu denaba seda aka kira sallar la'asar,yakashe yatafi masallaci.
koda yadawo gida Khairat tacemishi meya zaunar dashi, amsa yabata da wa'azi akeyi a masallacin shine yazauna ji se yanzu aka gama.🤣🤣
Kai Hydar, kai tun kafin kayi mata biyun kafara shirgota.
Muje zuwa readers.
Maman Yusuf.
📓📓📓📓📓📓📓📓📓
*CIN AMANA KO FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓📓
Zahra Muhammad mahmud
*The value of life does not depend on the length of time on this Earth but rather on the amount of love given and shared to the people we care about.am really appreciate the way you care about me Safina Sulaiman(Maman sultan)*
*page 49-50*
Soyayya fa tayi k'arfi tsakanin Hydar da Yasmeen kullum cikin nunawa juna kulawa suke koda kuwa a gaban Khairat ne,sun iya takunsu babu ta yadda zata gane.
Su Yasmeen sun gama makarantar su lafiya ita da Iman, se murna sukeyi Hydar kuwa harda party ya shirya musu,anyi taron tayasu murna lfy gami da musu fatan alkha'iri.
Yau asabar kowa yana gida dayake weekend ne zaune, suke a falo suna kallon casset d'in party da sukayi,Hydar ne yay sallama yashigo daga training ya dawo,da sauri Yasmeen ta mik'e taje taryarsa,suka tsaya a bakin k'ofar,tace.
"Sannu da zuwa me gidan Aunty na dafatan kadawo lfy?".magana take tana juya ido.
"Nadawo lfy Amarya ta, yakike ya Auntynki? dafatan kina kulamin da ita? kinsa itace heart beat d'ina".
Murmushi tayi sannan tace.
"Ka tambayeta kaji kullum ina kulawa da ita sabida sanin muhimmancinta a gurinka dan itama nasan kullum da tunaninka take kwana take tashi, kaide karik'e ta amana kuma ka gaggauta bata mulki na sarauniyar zuciyarka shine zesa tak'ara yadda ita d'in itace heart beat d'in taka".
Khairat ce tak'araso gurinsu tana dariya tace.
"Ikon Allah, wlh shiryawarka da Yasmeen ba k'aramin rana tayimin ba tunda gashi a sanadin hakan kana fallasamin sirrin zuciyarka wanda da baka tab'a fad'aminba, yanzu ne nake sanin matsayina a zuciyarka"dafa Yasmeen tayi sannan taci gaba da cewa.
"Ay wlh kede Sis sede ince Allah ya rabaki da bak'in cikin duniya da lahira Allah ya d'aga darajarki a idon mijin dazaki Aura fiye da duk wata mace afad'in duniya yazamana yana hannunki se yadda kikayi dashi".
Wata shegiyar dariya suka kwashe da ita Hydar da Yasmeen atare suna kallonta itama dariyar takeyi,Yasmeen tace.
"Wai Aunty anya wannan addu'ar batayi tsauri da yawa ba kuwa? kide sassauta dan inason inkin tashi bani sunana na uku agurinki kibani me dad'i amman wannan zazzafar Addu'a haka Aunty, ay seki jamin zagi a idon duniya ace na mallakeshi yazama mijin tace".
Carab Hydar yace.
"Ay ni wlh da za'a kiran mijin kan tacema akan Antynki so zanyi,dan matsayine babba agurina faruwar hakan".
Rungumeshi Khairat tayi sabida jin dad'i,tana jikinshi take ba Yasmeen amsa.
"Addu'a ce me kyau namiki Sis bazaki san amfaninta ba se ranar dakikayi auran, bazakiso ki koma komabaya a gurin mijinki ba dan haka kedai kawai kice ameen".
"Ah to tunda kika ce hakan nasan abune me amfani danhaka ameen ameen Aunty na daddy kai baka tayani cewa ameen d'in ba"ta fad'i tana kallon idonshi.
Murmushi yayi yak'ara rungume Khairat sosai ajikinshi sannan yace.
"Wacce ameen zance anan nida har a Sallah ina fad'awa Allah yabaki Wanda yake sonki kema kuma kike sonshi kuzauna lfy, amman tunda Auntyn kice tayi addu'ar kuma kinsan irinsu addu'ar su na amsuwa nima nace ameen d'in".
Janshi Khairat tayi suka haura sama suka bar Yasmeen da b'acin rai dan ta tsani taga Khairat ta rungumar mata Hydar.
Tofa kuji k'arfin hali don Allah.
Soyayya kullum se abunda yayi gaba koda wasa Khairat bata gano bakin zaranba, ita ta d'auki alak'arsu a matsayin wasan miji da k'anwar matarsa,ko shan ice cream yanzu duk Sunday se sunfita shida Yasmeen, wani time d'in suje da Iman wani lokacin da Khairat, ko su tafi da meema da Arfat dayake sun iya takunsu bawanda yaganosu.
Hydar ne yamatsama Yasmeen akan shifa yanaso tabashi dama yatura gidansu neman auranta,hak'uri tadunga bashi akan yad'an k'ara hak'uri ba yanzuba.
To yaude ko shawartarta beyiba da asubar fari ya kama hanyar kaduna shida drivern sa,yafiso ayita tak'are yagaji da b'oyewar dayakeyi shi ba mak'aryaciba Amman duk yagama zama mak'aryaci a gurin Khairat sabida hakan, shiyasa shi yak'osa ayita ta k'are Tunda yasande d'ayan biyu ne ko nasara ko akasin hakan.
Tafe suke shide se addu'a yake akan Allah yabashi nasara.
Yasmeen yau tun safe takejin gabanta nafad'uwa tarasa dalili addu'a kawai tayi akan Allah yasa alkha'irine,a kitchen suka had'u da Khairat gaisheta tayi ta amsa fuskarta d'auke da walwala.
Yasmeen tace, "Aunty yau ina soulmate d'in naki naga kinsakko da wuri haka?".
Murmushi Khairat tayi sannan tace.
"Wlh yau tun asuba yatafi kaduna shida driver yace ya kwana biyu beje ya gaishesu ba shine yau yatafi gobe ze dawo yace".
Hankalin Yasmeen ne yay mugun tashi tabbas tasan zuwan Hydar kaduna ayau nanufin tayi bankwana da farinciki a rayuwarta, meyasa yatafi be sanar da ita ba?.
Khairat ce ta tab'ota ganin gaba d'aya lokaci guda ta firgice tashiga damuwa,a rud'e ta waigo tana kallon Khairat,tambayarta tayi.
"Lafiya kuwa Yasmeen?meke faruwa haka?daga cewa Hydar yatafi kaduna duk kin tada hankalinki".
K'irk'iro murmushi tayi sannan tace.
"Wlh dama naso nabishine duk lokacin dazeje shine kuma naji yatafi bansaniba shiyasa kikaga nashiga damuwa amman bakomai wlh".
"To kidena damuwa in ze koma wani lokacin sekuje tare kinji my Sis".
Kai ta d'aga mata sannan tafice a kitchen d'in takoma d'akinsu,rasa me zatayi tayi addu'a kawai tashigayi dan tasan halin Ummanta in zancannan yafito zata iya nakasata da duka ita yau yazatayi,?wata zuciyarce tashiga k'arfafa mata guiwa da cewa "ay ba ke kad'aice cikin tashin Hankalin ba Khairat ma tana ciki in har da gaske kina da burin fansa a ranki dole kicire tsaron komai a ranki dan dole sekin daure zuciyarki".
shawara da zuciyarta ta bata itace ta k'ara mata kwarin gwuiwa yazamana memakwan tashiga tashin hankali sema wata natsuwace take shigarta.
Had'a kayanta tayi guri guda tayadda bame ganewa dan tasan zamanta a gidan yakusa zuwa k'arshe data fita ba shiri gwanda ta shirya.
muje zuwa.
Maman Yusuf.
📓📓📓📓📓📓📓📓📓
*CIN AMANA KO FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓📓
Zahra Muhammad mahmud
*Never say gud bye 2 sum1 who luvs u.Never say thanx to sum1who really needs u.Never blame a person who really trusts u.Never 4get a person who think u as LIFE,Juwairiyyatu(Anty Arfat)*
*page 51-52*
Hydar ya isa Kaduna lafiya kai tsaye gidan iyayensa yanufa.
Sunyi murna sosai da ganinsa dan ba k'aramin so suke masa ba kasancewarshi shikad'ai Allah yabasu,shiyasa suke tattalinsa, kuma koba dan hakaba Hydar mutumne dayasan daraja da girma na iyayensa dole ko zuciya taso me kyautata mata.
Part d'inshi nagidan yasauka, bayan yayi wanka ya kintsa fitowa yayi yanufi b'angaren iyayennasa, gaishesu yasake yi sannan yace.
"Alhaji dama akwai wata magana data kawoni inaso kufahinceni kunsan bazan tab'a yin abinda yasab'awa addini ba,shiyasa wannan ma inaso ku d'aukeshi a matsayin k'addarata ce tazo a haka".
Natsuwa sukayi suna sauraraonsa dan sun fahimci zancannasa me muhimmancine,cigaba yayi da cewa.
"Bakomai bane dama illah inason Yasmeen k'anwar Khairat kuma inaso kashigemin gaba gurin neman auranta".
"Innalillahi wainna ilaihirrajiun, Hydar kanka d'aya kuwa?,kasan abinda kake furtawa kuwa?,so kake kazama abokin shaid'an wajan tarwatsa zumunci?ina katab'a ganin haka?to wlh tuntuni inma bacci kake ka farka,wannan zancan bame yiwuwa bane",inji Hajiya wacce ke magana cikin fushi.
"Ah Hydar naji duk bayaninka kuma nagamsu dashi tunda nasan a addinancema ba laifi bane,sede Hydar iyayen yaran bazasu aminta subaka aurannanba dan ze tab'a zumuncinsu,kuma in akayi hakan kamar da cutarwa aciki, duba da ganin Khairat itace ta rik'e yarinyar harta girma,bawai nace bazan maka jagora bane aa kod'aya shawarace zanbaka inda hali ka hak'ura da wannan maganar kaji",Alhaji ya fad'a cikin sigar rarrashi.
Afusace Hajiya ta amshi zancan.
"Au lalle ma Alhaji koda yake ay duk sunanku maza,amman taya zaka goyawa yaro baya akan abinda kasan badede bane? tonide wlh ba hannuna aciki, dan bazan goyi bayan cin amana ba".tana gama magana tabar gurin tana huci.
Hawayene suka zub'o a fuskar Hydar na rashin kwarin guiwa, Mahaifiyarsa ma bata goyi bayansaba bayajin iyayen Su Yasmeen zasu amince subashi auranta,Alhaji ne ya katse masa tunani tahanyar dafashi yace.
"Haba Aliyu Hydar zakin fama namijin mazaje,karka bani kunya mana, taya akan wannan maganar zaka tada hankalinka?katunafa yak'i kad'auko bedace tundaga farko kanuna ka gazaba, dole seka nuna juriya da jarumta kuma dama su mata haka suke, sekaga abu al-adace kawai amman sesu fifitashi fiye da addini kuma kosu gidan yaran inaga ko za'a samu matsala to daga matanne,kaide kadage da addu'a yanzu katashi kaje da kanka kafara yi musu maganar in yaso yadda kukayi dasu zuwa gobe semuje tare".
Maganganun Alhaji sune suka k'ara masa kwarin guiwa, godiya yayi masa sosai sannan ya fita yanufi gidan iyayansu Khairat.
Da isarsa k'ofar Gidan Abban Khairat yasamu ya fito daga gida zashi masallaci, da sauri yafito a motor ya nufeshi, shima Abban ganin Hydar ya nufoshine yasa ya tsaya fuskarsa d'auke da fara'a.
Hydar tsugunawa yayi har k'asa yagaisheshi,yana d'aya daga cikin halayansa dayake sawa surukannasa ke sonsa shine girmamasu dayakeyi batare da yayi la'akari da matsayinsaba,ruwan alwala Abban yasa aka kawomishi yayi alwalar suka nufi masallacin tare.
Bayan an idar da sallah kai tsaye cikin gidansa yaja Hydar d'in suka gaisa da Umman Khairat, daganan sit room suka koma suka zauna aka kawo musu abinci Abban tilastawa Hydar yayi suka ci tare, duk kunyar Abban ta gama kama Hydar bayan sungamane Hydar yace yanada maganar data kawoshi,murmushi Abban yayi yace.
"To Hydar ina sauraronka".
Rasa Ta inda ze fara yayi gaba d'aya Abban yamasa kwarjini,amman bashida zab'i dole ya furta,cikin rawar murya yafara maganar.
"Abba don Allah ku fahimceni wlh k'addarace ta hau kaina bana nufin kawo tarnaki acikin familynku banida yadda zanyine don Allah kugafarceni".
Mamakine yakama Abban to me Hydar yamusu da yake neman gafarar su haka.
"Hydar ka natsu ka sanar dani abinda yake faruwa, ni mahaifinkane zanmaka duk abinda uba yake wa d'ansa, meyasa kake shayin sanar dani damuwarka?ni na maka alk'awari kowacce irice insha Allahu zanyi k'ok'arin taimakamaka, Danhaka kasanar dani ina sauraronka"Abba yayi maganar cikin yanayin k'arfafa guiwa agareshi.
"Abba Yasmeen nakeso ka auramin idan har da gaske kai ubane agurina, inaso kayimin ranar da uba yakewa d'ansa yayinda d'an yashiga tashin hankali"ya k'arasa maganar yana kuka tamkar anmasa mutuwa.
Tashin hankali ba'a samaka rana.
Abba jiyayi kansa na shawagi a sararin samaniya gaba d'aya kalma ta gudu daga bakinsa gumi se karyo masa yakeyi.
Hydar zuwa yayi yakama k'afarsa yana kuka yake fad'in.
"Abba naso hak'ura tun kan kuji maganar amman nakasa, wlh Abba inbaka auramin Yasmeen ba zan iya rasa raina, don Allah katausayamin kuma wlh bazan wulak'anta muku y'ay'aba".
Dakyar Abba yasamu abin cewa.
"Hydar ka kwantar da hankalinka bana tunanin zaka wulak'antasu,kawai zumuncinsu ake dubawa,amman ba komai gobe dama munada family meeting,zamu tattauna maganar a gurin kaje ka kwantar da hankalinka Hydar kanada uba tsayayye,idan har inada iko akan Yasmeen inkuma Allah yayi matarkace koda duka dangi basu yardaba ni zan auramaka ita,kuma inda Hali inaso taron dazamuyi gobe da azahar yazamana Khairat da Yasmeen su halarta".
"Insha Allahu zasu halarta Abba nagode Allah yasaka da alkha'iri Allah yak'ara girma",godiya Hydar yakeyi kamar zeyi sujada.
Abba k'arfafa masa guiwa yayi sosai gamida alk'awari.
Hydar gidan su Yasmeen yashiga suka gaisa da iyayanta sannan yamusu sallama ya wuce gidan iyayensa.
Maman Yusuf.[5/5, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓
*CIN AMANA KO FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓📓
Zahra Muhammad mahmud
*Earth may stop rotating, Birds may stop flying, Candles may stop melting, Fishes may stop swimming, Heart may stop breathing,But i will never stop Missing you my friend.ESHAT MUSTAPHA insha Allahu your forever start now between you and your Husband,Happy marriage life*
*page 55-56*
Hak'uri Abban Yasmeen ya durk'usa yana ba yayannasa,sauran family ma suka sa baki sannan ya hak'ura aka ci gaba.
Yasmeen se kuka takeyi sabida ta daku a zuciyarta ko fad'i take,"wlh ko kasheni za'ayi sena aureshi".
Khairat gaba d'aya komawa tayi kamar wata mahaukaciya se zare ido kawai take tana soshe soshe, abin gwanin ban tausayi, duk da bata gama yarda da abinda ake fad'inba.
Abba ne yaci gaba da magana.
"Yasmeen inaso kitashi kiyimana bayani kinason Hydar ko